"Subuhanallahi.
Cewar Goggo wacce tayi furucin tana Mai toshe hancin ta Saboda warin tutun da wasila ta saki a tsakiyar D'akin Wanda ya marabci Goggon da Yi Mata lale marhabin.
"Me nake Gani haka wasila? Kamar fa tutu nake Gani a D'akin wane irin Abu ne haka ?
Wasila da fuska tayi jage jage da hawaye kunya da wata irin muzanta da taji tayi k'asa da kanta tana fadin
"Ki yafe mini don girman ALLAH Goggo. Nayi Miki laifi nayiwa Ubangiji har gani cikin wata irin jarabawa da na tabbatar da mugun Aiki na ne ya sa nake. . .