Basma da ta ga Haj ta fita sabgar ta ana ta Shirin Auren Labuda kanwar ta da tsohon mijin ta Abdullahi Bata dauka Al Amarin na gaske bane sai da taga an saukewa Labuda akwatunan lefe seti Biyu yayin da Haj Baraka sai SHIGA da fita take don hattama kayan hidimar ta.
Basma ta Kira Labuda ta iso d’akin ta tana Duban ta kafin tace Mata
“Wai ke Kin yarda da Abinda Haj take nufin Yi da ke Naga Baki ce komai ba bare kiyi boren ba Kya son shi ko Kuwa dama munafunci ne kina son Abdullahi har Ake Neman k’ak’aba mishi ke ? To a KUL din ki Wallahi Abdullahi Bai sake ni ba ta Ina kike zaton kina da wuri a gidan mijin da na Aura har kike Shirin yin gugar jigida Dani? To ki kama kanki don zan koma gidan miji na ne wace irin kwamacalar Ake Shirin Yi min tamkar dai ana Jira na.?
Sai Basma ta Soma Sababi tamkar Zata Rufe labuda da duka.
“Wai Yaya Basma wannan sakon in ce dai nawa ne kawai ba hajiya kike turawa shi ba ko? In dai nice sai nace Miki mijin ki ba a Gaba na yake ba don ke kin San ni irin kallon da nakewa Duniya bare har na Kalli Wani Abu da zan amfana akan sa har ido na ya Rufe. Amma idan da Haj kike nufin fadawa bak’ar magana don tace min tayi min miji da mijin ki Basma sai nace karya kike ki fadawa Uwa ta magana Wallahi. Ko wuta tace na shiga Wallahi zan shiga na San ba zan kone ba don Haka in har Haka Haj take nufi to na shirya . Kuma ke kina son komawa kika zo nan kika tare? Ki koma Mana tun yanzu in bori gaskiya ne to a hau sama a fado in yanzu kika tashi kika koma gidan Abdullahi kalas bani da matsala da ke .
Haj da take tsaye tana Jin su ta juyo tana Fadin
“Yauwa Labuda allah yayi Miki Albarka ke Kam fa ai na san kin Haihu tunda Ina ce Miki ga yadda za ayi kika ce an gama Amma ita wannan har Wani cika Baki take zata koma Gidan Abdullahi? Ki tuna Mata to in ta manta irin abubuwan da tayi a zaman makokin Abdullahi Babu Abinda Bai dawo mini ba . Kuma In don Bata ji Abdullahi yace komai akan ta ba to ya ce din zo ga Abu Nan ki dauko Mata in ta karanta wata Kil zata yarda an mayar da ita gefe.
Haj ta dauko ambulan din ta watsowa Basma a kofar D’akin tana Fadin
“Karanta wannan ki Gani tunda har anzo gab’ar da kike dab da ce mini jahila saboda nayi madadi da kanwar ki to duk jahilci na dai bana zak’ewa akan abin Duniya Kuma bana iya yin kisan Kai don na mallaki Abinda ba zai Mana nawa ba haka Kuma ban iya kunji kunji ba Kinga kuwa ai jahilci na ma Mai salla ne Bai kafurta ba tunda Bai kaini hanyar da ya Kai Ahalin bil ama Dan ba aura ba da ilimin nasu na manuba da son danne hakki ne .
Wannan magana ta daki kirjin Basma wacce Bata zaci Hakan daga Uwar tata ba
Jiki a Sanyaye ta dauki takardar wacce ta gama zana ko ta mecece wato Saki.
Ta Bude tana ganin kyakkyawan Rubutun Abdullahi layi Daya Amma Kuma Mai Bak’in ciki fiye da tiriliyan .
Hawaye ya Soma sauka idon ta ta dafe kanta tana Jin Wani irin Bak’in ciki.
“Kuka Kuma ai Baki fara shi ba tunda kika ce ke hanyar shaidanci kike bi ba ga irin ta Nan ba? Ai karya fure take Bata Ya’ya.
Haka aka Soma bikin labuda da Abdullahi Basma Kuma tana cike da Bak’in ciki har Ciwon zuciya Yana Shirin sarkar ta har Allah ya sa taga Ranar da aka Daura Auren aka Kuma wuce Kai Amarya Amma Bata iya fita ba tana gida tana kuka. Kukan Bak’in ciki da nadama yau da mijin da take so kamar ta kashe Kanta ya fice ta ya koma mallakin Farida da Labuda. Shine fa Wanda taso sauya halitta don ta burge shi take ta Shaye Shayen magungunan Mata duk don ta mallake shi Amma Ashe Al Amarin KAMAR A MAFARKI zai Zame mata . Sai ga Basma tana Shirin zarewa.
Farida kam a matukar Rikice take duk yadda ta dauki kaikayin kishi a Ranta Ashe ya wuce yadda ta fasalta shi
Aka kawo labuda har sashin ta aka damka Mata Amanar ta inda Haj baraka ta bayar da sako a bawa Farida na Cewa ace tayi Hak’uri da Abinda akayi Mata na bawa Abdullahi Auren labuda don Kar taji Wani Abu a Ranta.
“Kucewa Haj ita din Uwar mu ce duka na sani na kuma Kara Sani iyayen mu ne su ko Babu Auren Basma da labuda Dole ne mu neme su mu girmama su Allah ta ala ya bamu zama lafiya a tsakanin mu ya fidda Mana dukkan Wani Abu da ba Alheri ba a tsakanin mu .
Haka akayi walima aka kare Shima Mai gayyar sai da ya Kira labuda tazo har sashin Farida yayi musu nasiha ya Kuma fadawa Farida yadda Al Amarin Auren shi da labuda ya samo Asali dama Allah ya zana Hakan sai Basma ta tafi labuda zata zo don haka zaman lafiya yake so tare da su Kuma kar wacce ta dauko zancen wata ta kawo mishi . Yace da labuda itace bakuwa ya San Halin matar sa a matsayin ta na k’arama Dole tayiwa Farida biyayya itama Faridar ya zama Dole tayiwa labuda Adalci ta sanar da ita Abinda Bata sani ba a game da shi da Kuma harkar gidan sa.
“In Sha Allah ai na San labuda ko Babu komai mahaifin su da mahaifiyar su iyayen mu ne Kuma Dole mu girmama dukkan Wanda ya fito daga gareka kowaye shi don haka ni a Yar Uwa Nake kallon labuda Allah ya tabbatar Mana da zama lafiya da Aminci Kuma labuda duk Abinda kika Gani Wanda Baki fahimce shi ba kiyi min Magana ko kika ga na shiga hakkin ki kiyi min Magana don Allah kin San Dan Adam ajizi ne.
“In Sha Allah Nagode Sosai Allah ya bani ikon Yi muku biyayya Kuma Nima da anga na karkace don Allah a gyara min don Ina son Mai nuna min kuskure na ko Yaya yake kuwa.
Farida da ta Dawo da su Nabeela da Najwa wurin ta tana Kuma tarbiyantar da su akan Rayuwar Ya’ya Mata da Kuma nuni irin na yarinta . Yayin da labuda kuwa tana bin Farida sau da kafa komai Zatayi zata je sashin ta ta sanar Mata don ita labuda Dayan sashin aka Sanya ta don Abdullahi yace ba zata Zauna a tsohon wuri ba inda Basma ta zauna sai aka Saka ta Dayan sashin .
Al Amarin Najwa da Nabeela kam ya Soma lalacewa don tun da suka fara Zuwa wurin Basma da ke gida sai ta Soma Yi musu Sak’a da mugun zare inda Kuma suka Soma Gallabar farida suka Nuna Labuda itace tasu don haka Suka jide kayan su saga sashin Farida suka koma wurin Labuda wacce ta ce ba zasu Zauna Mata ba su koma wurin Farida don ita Kam ba zata dauki wannan mugun Halin nasu ba Amma da yake akwai fahimta tsakanin Labuda da Farida sai Farida ta bawa labuda hak’uri tace ta bar su ko Ina suna da right din zama Abinda zasuyi su tsaya bil hakki akan Yaran don suna bukatar tsawatar wa musamman Najwa da idon ta ke Neman Budewa.
Abdullahi ma a tsaye yake don ya Sha Alwashin ba zai taba nunawa Duniya Cewar su Najwa ba jinin sa bane don haka yake tsaye yake Kuma cewa labuda da Farida su tsaya mishi akan Su Domin ALLAH duk Halin da suka ga zasu shiga su sanar Dashi.
Mamman da aka sallame shi daga Asibitin sai ya zarce gidan su Basma wacce ta dauke mishi wayar da kudaden sa suke ciki
Yayi sallama a kofar gidan akayi mishi magana da ita ta fito ba don ta San shine ba sai kawai tayi Arba da mamman da katon bandejin shi manne a goshi.
“Me ya kawo ka Nan ?.
Basma ta fada tana auna mishi Wani shegen kallo.
“Waya ta da kika dauko na biyo na karba .
“Wayar ka? Dama Kai kana da waya ne? To na Rik’e wayar ka akan kudade na da suke hannun ka ko layin ba zan iya baka ba saboda in ka kula da irin kudaden da nake fiddawa zaka nemi tayar min da Hankali don haka motata da take gareji taci kuturus kaje na bar Maka ita ka Siyar ka siyi waya Amma wannan wayar taka Wallahi ta zama haramiyar ka kar na Kuma Ganin kafar ka a Nan in kuwa ba haka ba zakaji jiki Wallahi.
Mamman yayi murmushi yana fad’in
“To shikenan Nagode Amma ki tsaya mu fahimci juna don wannan kudin da suke cikin wayar Nan nayi nufin mayarwa masu su Kuma kema in kin fidda kudin motar ki a ciki kinyi garaje don Dole zan fahimtar Dake motar ki na siyar da ita Kuma in baki kudin ta Amma sauran kudin da suke ciki ko kinci su Wallahi Zakiyi Aman su don Yanzu haka na Sanar da Duk mutanen da na zambato cewa zan dawo musu da kudin su gara ki bani wayar Nan tun Al Amarin Bai zamar Miki damuwa ba.
“Uwar Uwar damuwar mamman Kai in fa baka bar Nan ba zan Tara Yara su Raka min Kai Wallahi.
Ya wuce Bai Kuma ce mata komai ba inda tabi shi da Kallon SHEGEN gora Mai zubar da nonon sautu wai ita zaiyiwa barazana.
Ai kuwa sai ta Soma kwashe kud’in da suke cikin account din mamman don ya Fadi pin din sa tun a office din C I D ta kuma Rik’e don haka sai ta juye kudaden a nata account din.
Bai Rufa awa Biyu da tafiya ba sai ga motar Yan sanda sun taho tare da mamman ya Kuma nuna Basma wacce aka fito da ita jiki Yana kyarma.
Koda suka Isa ya karanta Abinda kenan ga Kuma mutanen da ya karbi kudin su inda yace wayar shi tana Hannun Basma wacce zai mayar da kudin kuma ta Hana.
Amma ana dubawa aka ga Babu komai cikin account din ya Kuma ce suna wurin Basma wacce da ita ne Suka hada Bak’ar kasuwar su sai gashi kuwa an soma matsar Basma ana karbar tata wayar ana mayarwa mutane kudin su har sai da mamman yayi zambar tashi aka Saka mishi kud’in motar Basma wacce duk yadda taso karyata shi ba a saurare ta tana Ji tana Gani mamman ya salhe sauran kudun ta ita Kuma aka barta da kangon account empty.
Bak’in cikin ta ta yadda komai ya Zame mata Toka ga mamman ya yaudare ta wanna shi ya bawa Basma Damar cewa Najwa take samo Mata kudi a gidan su ko ma ajin Abdullahi. Ai kuwa Najwa ta Soma lalubar kudi tana kaiwa Uwar ta Abinda yaso haddasa husuma tsakanin Labuda da Abdullahi don zai ajiye kudi Najwa ta kwasa ba tare da labuda ta sani ba sai yaxo yaga Babu.
Sameer Kam ya dangana da Farida ya Gane ba zata tab’a dawowa gareshi ba sai ya Rik’e matar shi wacce yayi bala in Saka ido akan shigar ta da futar ta har ya Gane sakaci ne ya sa take Wani Abun Amma a yanzu ko tafiyar kwana uku Zaiyi zai Saka ta a mota su tafi tare itama Kuma da ta Samu kulawar da take so sai ta manta da babin Rayuwar da ta dauka don ta Gane Babu komai a ciki sai kunyata da muzanta tunda har Uwar ta da haj Sukaji Abinda tayi tin daga Ranar ta daura aniyar kame kanta Banda zunubi ma ga tozarta Kuma wai basa son Ya’yan su suyi abinda sukayi Anya kuwa ba a so Kai da yawa ba?.
Da ya tashi yin wata dabara ma sai ya gyara gidan su inda ya siyi Wani floti ya hade ya Kuma fidda part din da ya dawo da Aisha kusa da Haj sai Hakan ya saukar mishi da nutsuwa Aisha tana gida kusa da Haj don har yanzu zuciyar Bata Hak’ura da zargi ba tunda akan Hakan aka hadu Dole Aminci yayi Wahala.
A lokacin da mamman ya koma Nijar mahaifiyar shi taso Ganin ya zo Mata da yaran da yace nasa ne Amma ta ganshi Hannu Biyu ya kuma shirya Mata wata karyar ya linke ta ta Kuma yarda baiwar Allah wacce tayi ta mishi matashiyar yayi Aure kafin ta komawa Ubangiji sai kawai yaga ya koma wurin Basma in ta yarda suyi Maja tunda shi Kam tayi mishi a Mata Kuma a yanzu dai Bashi da wacce ta Kai ta bare ta fita.
Lokacin da ya iso da maganar sai ya samu Haj baraka wacce a take ta sallama mishi tace ya turo magabata ta bashi Auren Basma wacce ma Bata San wainar da Ake Toyawa ba sai dai taga mamman Yana faman zarya Gidan su
Sai fa Ranar da aka Daura Auren ne Haj take mata Bayanin Auren Su da aka Daura da Mamman.
“Ni ? Haj Aure? Da mamman ? Sai Kuma ta Saka kuka tana Fadin
“Haba Haj da girma na da komai ayi min Auren Dole? Nijar fa yake Haj sai kawai a kwashe ni Akai Nijar?.
“Kin manta inda yake ne lokacin da kika Rik’a kashe fila dashi a gidan Wani? Ai ni na San burge ki yake ne shiyasa har kukayi Abinda kikayi kuma kin manta ne na tuna Miki? Ke da shi sunan ku irin Daya ne ko a cikin Al Kur ani ance iren iren ku Dana sai ku don haka ba Nijar ba ko agadez yake Babu inda Aure baya Kai mace Kuma ni ai taimakon ki Nayi Wanda yayi abin nan da Auren sa ma Ina ga Kuma Babu Auren? Ai gara kawai ku Rufawa juna Asiri ke da shi .
Haka Haj ta fice daga D’akin ta barta da share HAWAYE wai mamman ne aka aura Mata irin Auren keta Darajar Nan Babu Neman yarda Babu shawara.
Da dare kuwa sai ga mamman ya iso Gidan Haj ta tarbe shi Suka gaisa Yana tambayar Basma tana Nan?
Haj ta Nuna mishi d’akin tace tana ciki shiga.
Ya wuce Yana Sanye da wani yadi Mai salki irin na yanken Nan Mai walwali wai shi Ango.
Basma ta Mike tana mishi kallon wulakanci tana Fadin
“Neman me kake mini? Wai Kaine da karbar Aure na mamman ? Wace tsiyar kake zaton ka mallaka da har zan iya zaman Aure da ke ? Nijar fa kake kaima tsiya da fatara ne Suka Koro ka ka shigo Nigeria shine har da Wani munafunci ka kewaye ka Karbi Aure na? To Wallahi yadda ka karbi Auren nan haka balaki zai Saka ka dawo dashi inda ka karbe shi .
“Bana jin Komai in anyi Hakan in dai nayi nasarar amsa sunan mijin ki . Kuma ko ban mallaki komai ba ai na mallaki kud’in ki na mota shine nazo na dauke ki mu tafi muci su tare Basma don ni har gobe Babu Mata a ido na sai ke farar mace tana dauka ta musamman ma doguwa Mai irin tsarin ki .
Kuka ya kwacewa Basma ta Soma rera shi da ta tuna irin yaudarar da yayi Mata.
Ya Rungumo ta Yana Rad’a Mata wata magana a kunnen ta .
Cikin satin mamman ya shirya musu tafiya suka Kuma wuce jamhuriyar Nijar a tasawa mamman yake don haka Basma ta tare duk da tazo da niyar Rashin kirki Amma kuma mamman ya sauya ta sauyin da batayi zato ba inda Kuma ta karyata Kanta fa Kallon da takeyiwa Nijar na Basu da komai sai gata da sana oi a nijar Wanda Suke kawo Mata kudi na Mamaki Kuma Uwar mamman tana Rik’e da ita cike da karimci da mutuntawa. Kan kace me ? Basma ta Gane Nijar fa tana iya fin Nigeria a gare ta .
A Shekarar Daya da Auren su da mamman ne ta Haifi Ya’yan ta Biyu tagwaye mace da Namiji Wanda Suka biyo mamman sak mahaifiyar shi Kam har da kukan Dadi yayin da mamman Kuma ya ke sana ar Madara da magi da man jarka Kuma ya tsaya akan gaskiyar sa don ya Gane duk Wanda ya bar Allah to wanin Allah zai tafi Nema . Don haka cikin Aminci Basma take Zaune da shi Yana bakin iyawar sa itama Kuma tana Rik’e da Yan Uwan shi cike da mutuntawa tana Kuma sana ar ta tana samu tana Kuma tura Kaya zuwa Nigeria musamman da lawisa ta tsaya suna kasuwancin tare.
Al Amarin su Najwa kuwa sai du a I don Abdullahi ne da kanshi ya kama Najwa tana daukar kudin shi Bai Dake ta ba sai dai yayi Mata nasiha wacce ta Sa ta kuka tana fada mishi mamar su ce ta Saka ta . To haka dai yake ta kokarin tarbiya yayin da gidan nashi yake cike da Albarkar Ya’ya. Labuda Mai Ya’ya biyar sai Kuma Farida Mai Tara Kuma duk yana kokarin tarbiya tare da kokarin sama musu Abinda suke bukata. Salman da Sulaiman an zama samari yayin da Saddam Kuma Ake can jami a . Hanan kuwa ana wurin Haj don Sameer yaso daukar ta wai ya Saka ido akan ta kar tayi Abun da sukayi Amma Haj tace ba zata bashi ita ba in ya dauke ta ai Bata da Mai Mata shara da girki Dole kuwa ya Hak’ura Amma fa har yayi Mata Miji da Dan gidan Ogan shi wato Irfan Wanda ya Ganta a lokacin da tazo pertercout ya Kuma ce Yana son ta har Uban yayi mishi magana shi Kuma yace ya bashi don haka ana jiran Irfan ya dawo daga cous din da ya tafi na pilot matukin jirgin sama a Dora Maganar Aure.
Tuni Abdullahi ma ya bayar da su Najwa da Nabeela ga Ibrahim dan Gidan Garba Abubakar da Kuma Ahmad jikan Haj kulu suna karatu kawai ake jira a Sha biki .
ISHAQ kam sai Abinda yayi gaba cikin Albarkar Arzikin sa yayin da maimuna take da Ya’ya biyar ya Kuma Kara Aure na wata yarinya daga can Ahalin mahaifin sa da aka bashi ita ya Kuma karba suna Zaune lafiya.
Sagir ya zama Eng Albarka Kam ta sauka kan Sagir yayin da Ake Shirin Auren shi duk da karancin Shekarun sa Amma Babu wani kwararren eng kamar sa don haka ya tamfatsa gida na Gani na fada inda ya nemi Yar gidan Anty murja sumayya ana dab da Biki yayin da Yusra da Zainab ma an zama Yan Mata Amma ishaq yace sai sunyi karatu ko zai yi musu Aure Amma Inna suwaiba tace wauta zaiyi in yace haka gara dai yayi musu Auren in yaso ayi karatun a D’akin Aure yace to haka za ayi tunda suna da Masu so.
Wasila Kam tana Can itama da Ya’yan da ta Haifa wa badamasi har biyar yayin da yayiwa yan matan Biyu Aure yanzu saura yan mazan shiyasa ma matsala tayi sauki matuka Gaya Kuma tana zaune lafiya ita da mijin ta. Sai dai Abinda ke tab’a zuciyar ta shine ta tuna Al Amarin da ya faru baya takan yi kuka taji Lallai Dukkan kura kuren da bayin mukeyi sau tari kuskuren kuruciya ne yayin da Wani kuma Rashin Mai fada Maka illar Abinda zaije ya Dawo ne wani Kuma son ZUCIYA ne yake kawo shi. Idan ta tuna ta kanyi kuka ta Kuma Roki Allah ya tsare Ya’yan musulmi Aikin da za ayi nadama tare kuskuren kuruciya Domin kuwa ko da TANA K’ASA TANA DABO to zata gama DABON ta fito fili kowa yaga abunda yake jima a k’asa Yana DABO.
To Alhamdulillah Masha Allah kaseeeran kaseeeran madalla da Ubangiji ya kawo mu karshen wannan Labari Mai taken TANA K’ASA TANA DABO gashi dai min zo inda ta gama DABON ta bayyana. Lallai anyi abubuwa Allah ta ala ka tsare mu aikata Abunda zamuyi nadama ka Kuma shiryi zukatan Al Ummar musulmi tun daga ni Mai Rubutun zuwa ku masu karatu Allah Aminci Aminci Godiya ga ALLAH madaukakin SARKI da ya yarje min farawa lafiya muka Kuma kare lafiya Allah ka Sa mu kare Rayuwar lafiya tare da Riskar Amincin ANNABI MUHD S A W anan nake bankwana da Yan Uwa da Abokan Arziki da ma iyayen daki na Wanda har na mutu ba zan manta su ba don ko na Daina Rubutun akwai Aminci Wanda zai Kaimu har Gidan ALJANNAH madaukakiya tare da dukkan muminai maza da Mata Ina fatan Aminci ga Dukkan Wanda Suka karanta LABARIN TANA K’ASA TANA DABO suka Kuma fahimci Abinda nake son nunawa. Ina Kuma Rokon afuwa ga Wanda yaga Wani kuskure ko ba daidai ba ya Sanar Dani ya Kuma Gane Al Kur ani ne kawai bashi da gyara Amma kirkkira irin wannan Dole a Gano ajizanci na Dan Adam Wanda Bai cika cif ba anan nake sallam da kowa da kowa sai nace mu Hadu a fira ta gaba in Allah ya Amince. GIDAN IKO nake cewa kadarallahu ni ka ana subhanakallahumma wa bi hamduka Nash hadu an la ilaha illallahu wa hadahu lah Shari kalahu…