Skip to content
Part 2 of 12 in the Series Tekun Labarai by Danladi Haruna

Rana Ta Daya

Washegari tun da sassafe Wazirai  suka ji abin da ya faru sai suka yi ta murna, suka taru domin shirya yadda za su sa a kashe yaron. Bayan sun gama ƙulle – ƙullensu, babban Wazirin Sarki ya zo wajensa ya faɗi ya yi gaisuwa sannan ya zauna kamar bai san abin da ya faru ba. An jima kaɗan Sarki ya gyara murya ya ce, “Waziri ashe yaron nan da nake yaba hankalinsa maci amana ne?” Waziri ya ji an taɓo inda ke masa ƙaiƙayi ya gyara zama ya ce, “Allah ya taimake ka me ya faru?” Sarki ya kwashe dukan zance ya shaida wa Waziri. Ya ƙara da cewa, “na sa a tsare su duka a kurkuku har sai na yi bincike tukuna.”

Waziri ya ce, “ai da ma tsintacciyar mage har abada ba ta zama mage. Tun da yaron nan ɗan ɓarayi ne, to kuwa har abada ɓarawo zai kasance. Ba zai yi wani abu wai shi riƙon amana ba. Ita kuwa sarauniya ba ma zargin ta da wani aibu, tun da tsawon zamanku shekara da shekaru ba ta taɓa aikata haka ba. Ta yiwu yaron ne dai ke son ƙulla mata wani sharri.” Daga nan ya sake gurfana gaban Sarki ya ce, “ina neman izninka ya mai martaba, zan shiga wurin sarauniya a inda take tsare domin na bincike ta. Na san za ta faɗa min gaskiya.” Sarki ya yi masa izni. Ya tashi  ya shiga wajenta.

Da ya je sai ya ce mata, “wacce irin sha’awa ce ta rude ki ga wannan ƙanƙanin yaron marar asali haihuwar ɓarayi, girman sata? Wannan abin kunya ta yaya za ki kalli idon mutane da shi?”

Sarauniya ta ce, “ni ban san wannan abu da kuke magana a kansa ba. Kuma ka sani cewa da  zan yi irin wannan fasadin ba zan aikata da yaro ba, wanda da a ce ɗan da na haifa yana nan a raye, bai wuce sa’ansa ba.” Waziri ya gyaɗa kai ya ce, “da ma ba ma zargin ki da wani abu, amma ga dabarar da zan shirya miki domin ki wanke kanki a gaban Sarki kuma ki fita kunyar mutanen alkarya.” Ta ce, “wace dabara ce?” Ya ce, “idan Sarki ya tambaye ki ki ce masa, ‘ni ban taɓa ganin wannan yaron ba sai ran nan na fito shan iska ya hange ni tare da kuyangina. Da na dawo gida sai ya aiko min da saƙo cewa yana so zai zo wajena cikin dare mu keɓe. Ya ce zai ba ni jakar lu’ulu’u ɗari wadda kuɗi ba zai iya sayenta da sauƙi ba. Da na ji haka sai na yi dariya saboda wautarsa da ƙarancin hankalinsa, na ƙi ba shi amsa ballantana haɗin kai. Ana nan sai ya aiko min da saƙon zagi yana cewa, tun da na ƙi ba shi haɗin kai to kuwa zai ƙulla min sharri, ya ce zai je ya shawo giya ya zo ɗakin barcinmu ya kwanta. Idan Sarki ya ga haka zai sa a kashe shi, ni kuma ya jefa ni cikin ƙunci da kunya da wahala.”

Sarauniya ta amince da wannan shawara kamar yadda Waziri ya tsara mata. Daga nan Waziri ya koma wurin Sarki ya ce masa, “da ma na shaida maka yaron nan algungumi ne, shi ya shirya komai.” Ya kwashe duk zancen nan da ya tsarawa sarauniya ya faɗa masa a matsayin abin da ta faɗa.

Sarki na jin haka ya cika da fushi, ya tunzura, ya kawo har wuya. Ya sa aka fito da yaro daga kurkuku. Ya sa hauni ya wasa takobi, sannan aka ɗaure hannun yaro ta baya. Sarki ya dubi hauni ya ce a fille kansa. Hauni ya miƙe tsaye ya zagaya yaro sannan ya dubi Sarki ya ce, “da izninka zan fille masa kai bisa zunubin da ya aikata maka.” Sarki ya gyaɗa kai ya ce, “na amince.” Hauni ya maimaita faɗin haka, Sarki ya amince. Ya sake maimaita faɗa ta uku, a lokacin sai yaro ya yi ajiyar zuciya har kowa ya ji a wurin. Sarki ya dube shi ya ce, “kaitonka ma ci amana! Na fanshe ka da dukiyata, na ba ka ‘yancinka, na amince da kai, na baka amanar dukiyata, amma ka keta alfarmata, ka shiga cikin iyalina domin ka aikata ɓarna ka fallashe ni. To ka sani duk abin da ya same ka sakamakon haka ba ka da kaito!” Sarki na wannan maganar ne cikin fushi. Yaro ya ce, “Allah ya ɗaukake ka, ba ina juyayin abin da ya same ni ba ne, amma ba ni da zaɓi sai wanda na tsinci kaina a ciki tun da sa’a ta kuɓuce min to kuwa ba zan yi mamakin haka ba. Burina dai na yi ƙarƙon dabino saɓanin ƙarƙon kifi tamkar yadda ta faru ga bafatake a lokacin da sa’a ta kuɓuce masa.” Sarki ya ce, “wane bafatake? Yaya aka yi sa’a ta kuɓuce masa?” Yaro ya ce Allah ya ba ka nasara a bari ka ji yadda abin yake.

Idan Farauta Ta Ki Ka….

Ka sani ya kai Sarkin zamani, an yi wani bafatake mai nasibi a harkar saye da sayarwa, duk abin da ya kama sai ya yi daraja. Akwai lokacin da dirhami ɗaya ke jawo masa ribar dirhami hamsin. A kwana a tashi sai kasuwancin ya juya masa baya, duk abin da ya saya sai ya yi asara. Ya nemi dalilin haka ya rasa. Saboda haka ya yanke shawarar ya koma garinsu ya zauna ya riƙa saye yana sayarwa a can. Ya raba dukiyarsa kashi biyu ya sayi alkama a lokacin bazara ya ce, “idan ɗari ya zo zan sayar da ita da riba mai yawa.” Ya adana ta bisa wannan aniyar. To amma yayin da hunturun ya kama, sai farashin alkama ya faɗi ƙasa zuwa rabin kuɗin da ya saye ta. Bafatake ya yi baƙin ciki mai yawa a kan haka. Ya fasa sayar da alkamar, ya bar ta har zuwa wata shekara, bisa zummar kafin nan ta sake daraja. Amma sai ta sake zubewa ƙasa fiye da bara.

Wani abokinsa ya ce masa, “ba ka da rabo a wannan alkamar, ka fitar da ita kurum ka sayar a farashin da ya samu.” Amma ya ƙeƙasa ƙasa da wannan shawara ya ce, “na jima ban samu ribar komai ba sai wahala nake yi. Zan ajiye wannan alkamar nan da shekara goma da yardar Allah sai na samu alheri da ita.” Ya jibge alkama cikin ɗaki ya rufe, sannan ya sa laka ya toshe ƙofar. Allah da ikonsa shekarar ta zo da mamakon ruwan sama har ya sa ɗakin ya riƙa yoyo ya ɓata alkamar nan ta yi baƙiƙirin har ta soma wari. Tilas ya sa aka farke ɗakin ya biya aka kwashe ruɓaɓɓiyar alkamar, aka zubar a bayan gari gudun kada warinta ya dami mutane.

Abokinsa ya dawo gare shi ya ce masa, “na faɗa maka ba ka da rabo a kasuwanci yanzu. Ka zo mu je wajen wani malami ya ba ka taimako.” Bayan sun jima suna jayayya, daga bisani ya amince suka tafi wajen malami mai duba. Bafatake ya shaida masa matsalarsa gaba ɗaya, sannan ya nemi a ba shi laƙanin samun nasara. Malami ya duba ƙasa, ya lissafa ya ce da bafatake, “ka haƙura da saye da sayarwa a halin yanzu domin baka da nasibi a ciki.”

Bafatake ya tashi cikin fushi ba tare da amincewa da shawarar da aka ba shi ba. Ya buɗe ragowar kuɗinsa, watau rabin abin da ya mallaka shekaru uku da suka gabata, ya gina jirgi babba ya zuba masa duk abin da ake buƙata na tafiya. Ya bar jirgin cikin ruwa sannan ya tafi wurin ‘yan kasuwa ya tambaye su abin da kasuwarsa ke garawa. Suka faɗa masa wani gari mai nisa wanda idan ya sayo abu daga can zai samu riba ninki goma. Da haka ya yi aniya, ya tafi cikin sabon jirginsa. Tafiyar kwana da kwanaki a tsakiyar teku iska ta kifar da jirgin ya tarwatse. Allah ya sa bafataken nan ya kama wani allon jirgin ya maƙale, iska ta riƙa tura shi har zuwa gaɓa. Ya gode wa Allah da ya ƙaddara kuɓutarsa.

Bayan ya huta a gaɓar ruwan, ya miƙe yana tafiya duk tufafinsa sun zama tsummokara har ya hangi wani ƙauye gaba gare shi. Ya isa ƙauyen ya samu wani dattijo ya gaishe shi sannan ya habarta masa abin da ya same shi. Dattijon nan ya tausaya masa matuƙa, ya shiga gida ya kawo masa tufafi da abinci da ruwa. Bayan ya nutsu suka sake gaisawa, ya yi masa jaje sannan ya ce masa, “ka zauna a nan wurina kana kula da gonata zan riƙa baka dirhami biyar kullum.” Da haka ya fara aikin gona. Dama hatsi ya nuna yana jiran girbi. Ya girbe ya ɗadɗaure su dami – dami.

Mai gonar nan bai taɓa leƙowa inda yake ba ko ya aiko wani ya duba shi. Sai ya ce a ransa, ‘tsohon nan da ƙyar zai bani haƙƙina yadda ya kamata. Abin da ya fi, bari na ɗebi gwargwadon hatsin da ya kama sallamata. Idan na ga ya yi min shiru na je na sayar, idan kuma ya ba ni, shi ke nan sai na dawo masa da abinsa.’ Ya ɗebi hatsi gwargwadon yadda yake sallamarsa ne ya ɓoye. Sannan ya tafi wajen mai gonar ya shaida masa ya kammala komai. Tsoho ya duba ya ga komai ya yi daidai. Sai ya ɗauko jakar kuɗi ya ba shi ya ce, “ga sallamarka, tun da ka soma aiki zuwa yau. Da za ka yarda ma sai ka zauna kana min aiki har shekara goma ko fiye. Ka ga a sa’annan ka samu jarinka da ya salwanta.”

Bafatake ya tafi yana mai nadamar hatsin da ya ɗaukar wa mutumin, ya tafi inda ya ɓoye su da nufin ya dawo masa da kayansa, sai ya tarar wurin babu komai. Ya koma yana mai baƙin ciki da nadama. Tsohon nan ya tambaye shi me ya faru. Ya kada baki ya ce masa, “wallahi zato nake ba za ka biya ni ladan aikina ba, sai na ɗebi hatsi gwargwadon biyana na ɓoye bisa zummar idan ka biya ni na dawo maka da abinka. Ga shi yanzu na koma wajen da na ɓoye ban ga komai ba.” Tsoho ya harzuƙa ya ce da shi, amma ka tabbata mara amana mara tunani, ka tuna na yi maka haka ne don kawai ka samu jari arzikinka ya dawo, amma ga shi gaggawarka ta hana maka sa’arka ta yi aiki. Tunda haka ne ka tafi ba na buƙatar aikinka.” Ya ƙwace jakar kuɗin da ya ba shi.

Ya tafi yana mai nadama da bac’in zuciya. Ya nufi gaɓar teku ya zauna ya haɗa kai da gwiwa bai san abin yi ba. Yana nan zaune sai wasu kwarawa suka zo bisa sha’aninsu suka gan shi ya yi tagumi. Ɗaya daga cikinsu ya shaida shi lokacin da yake da dukiya, suka tambaye shi abin da ya same shi, ya kwashe zancensa kaf ya faɗa musu. Suka tausaya masa sosai. Sai babbansu ya ce, “zauna nan, za mu shiga cikin ruwan mu yi lalube, duk abin da muka samo za mu raba biyu ka ɗauki rabi.”

Suka tsunduma cikin ruwa suka jima a ƙasa sannan suka ɗago suka tattara abin da suka samo. Gaba ɗaya an samu kwanson lu’ulu’u ashirin, kowane akwai dunƙule biyu. Shugaban kwarawan ya ce da shi, “lallai tauraruwar sa’arka ta sake bayyana. Dubi abin nan da muka samu ba mu taɓa samun kamar su ba. Babu shakka wannan ya ishe mu jari mu duka.” Aka raba biyu, suka ɗauki goma suka ba shi goma. Suka ba shi shawarar ya sai da biyu ya yi jari, ya ɓoye takwas saboda gaba.

Bafatake ya ɗinke dunƙule takwas cikin rigarsa, biyun kuma ya cusa a bakinsa. Ashe duk abin da yake yi wani ɓarawo na kallonsa. Ya kira ‘yan uwansa suka yi ta bin sa a baya har ya je inda babu jama’a suka kewaye shi suka ƙwace rigar suka gudu. Ya rage saura dunƙule biyun da ya ɓoye a bakinsa. Ya tafi da su kasuwa ya danƙa wa dillali da nufin a sayar ya samu abin jari.

Ashe a wannan daren kuma an shiga rumfar wani attajiri mai sayar da jauhari an sace masa dunƙulen lu’ulu’u goma waɗanda suke daidai da girman na bafataken nan. Dillali na tsakar tallan lu’ulu’un bafataken nan sai ga attajiri ya zo, ya ga kamar nasa ne da aka sace. Ya tambayi dillali mai waɗannan abubuwa, ya nuna masa mai su. Attajiri ya dube shi yana cikin tsummokara duk ya ƙuge ya lalace. Sai ya haƙiƙance cewa shi ne ya yi masa sata.

 Yana zuwa wurinsa sai ya ce masa, “ina ragowar takwas ɗin?” Bafatake na tsammanin wannan mutumin ya san batun adadin dunƙulen lu’ulu’un da aka ba shi. Sai ya ce, “ɓarayi sun tare ni sun ƙwace.” Attajiri na jin haka ya sake sakankancewa ga ɓarawon kayansa. Ya riƙe shi da kyau yana yi masa kururuwa, mutane suka taru a kansu. Aka tafi da bafatake wurin Magajin Gari. Magaji ya sa aka zane bafatake, sannan aka jefa shi gidan sarƙa aka manta da shi har shekara guda.

Wata rana sai shugaban kwarawan nan ya aikata laifi, aka shigar da shi kurkuku inda bafataken nan yake. Yana ganin sa ya shaida shi, ya tambaye shi abin da ya same shi. Ya kwashe labarinsa kaf ya faɗa masa. Bakwaren nan ya yi mamaki da rashin sa’arsa. Ya kuma yi masa fatan nasara. Washegari da Sarki ya sa a fitar da bakware sai ya shaida wa Sarki labarin wannan bafatake, kuma ya ba da tabbacin cewa shi ne da kansa ya ba shi waɗannan lu’u’lu’un.

Sarki ya ji tausayin sa ƙwarai da gaske. Ya sa aka sake shi, sannan ya ba shi masauki a cikin fadarsa ya kuma rubuta masa albashi duk wata. Duniya ta sake dawowa bafataken nan sabuwa, ya gode wa Allah yana mai cewa, “taurarin sa’ata sun dawo, dama bayan wuya sai daɗi.” To amma da yake farauta tuni ta juya masa, sai ya ga wata ƙofa da aka toshe a jikin bangon ɗakin. Ya sa hannu ya cire duwatsu da aka liƙe ta, sai ya ga ashe taga ce aka toshe ta.

Ɗakin ya kasance a kan bene yake, sai ya ci gaba da cire duwatsu har tagar ta buɗe gaba ɗaya. Sai ya leƙa domin ya ga abin da ke waje. Kwamfa, ashe cikin gidan Sarki tagar take inda matansa da iyalinsa suke. Nan da nan cikin tsoro ya dawo da kansa ya shiga hanzarin mayar da duwatsun yadda suke. Da yake tuni sa’a ta bar shi, ashe lokacin da ya leƙo wani bawa ya gan shi, ya garzaya ya shaida wa Sarki. Sarki ya taso da hanzari zuwa ɗakin ya ga bafataken na ƙoƙarin mayar da  duwatsun da ya cire. Ya harzuƙa matuƙa ya ce da shi, “kai maci amana, na jiƙanka na jawo ka jikina, amma iyalina kake son afka wa ko?” Bafatake ya shiga rantse – rantse, amma Sarki bai saurare shi ba. Ya sa aka kama shi aka ɗaure. Ya ba da umarnin a ƙwa’kwule masa ido ɗaya. Cikin hanzari suka aiwatar da umarnin.

Bafatake ya ɗauki ƙwayar idanun nan a tafin hannunsa yana kuka yana cewa, “ya ke rashin sa’a, kin cinye min dukiyata yanzu kuma gaɓɓaina kike muradi? Na tabbata ma nan gaba ba za ki bar ni da raina ba.” Ya kasance cikin baƙin ciki da ɓacin zuciya.

Saurayi da ya kawo nan, sai ya dubi Sarki ya ce, “kamar ni kenan ya Sarkin zamani. A baya da sa’a tana garawa da ni, komai na aikata daidai ne, amma yanzu da sa’ar ta gushe daga gare ni, ga shi nan na zama abin tsana abin wahalarwa.” Da Sarki ya ji wannan labarin sai fushinsa ya ragu ɗan kaɗan. Ya ce da fadawa, “a mayar da shi kurkuku saboda yanzu yamma ta yi, gobe za mu duba al’amarinsa.” Suka mayar da shi kurkuku ya kwana.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tekun Labarai 1Tekun Labarai 3 >>

1 thought on “Tekun Labarai 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×