Skip to content

Tekun Labarai 1 | Rana Ta Uku

4
(1)

<< Previous

Kashegari Sarki ya zauna a fadarsa, sai Wazirinsa mai suna Bakunu ya faɗi gabansa ya yi gaisuwa ya ce, “Sarki mai martaba mai daraja kamar ka bai kamata ya yi sakaci wajen ɗaukar mataki a kan wanda ya ci amanarka ba. Hakan zai magance irin surutun da mutane za su yi kan cewa ka ƙyale wanda ka gan shi da idanunka a kan gadonka tare da matarka.” Sarki na jin haka sai ya harzuƙa, ya sa aka zo da yaro, ya daka masa tsawa yana mai cewa, “kai wannan mai taurin kan, ka jawo mana abin kunya, ka keta haddinmu. Don haka a yau zan yi maganinka ta hanyar aikewa da kai lahira.” Yaro ya ce, “ya Sarkin zamani, ina fata ka zama mai haƙuri a dukan al’amuranka. Domin shi mai haƙuri bai taɓa yin asara ba musamman a ƙarshen al’amari. Ka ga shi haƙuri kan mayar da ƙarami zuwa babba kamar yadda ya yi sanadin fitowar Abu Sabiru daga rami ya danƙa masa sarauta.” Sarki ya ce, “wane ne haka? Me ya same shi a rami?” Yaro ya ce, “bari na faɗa maka labarinsa.”

Mai Hakuri Ya Kan Dafa Dutse….

A wani ƙauye akwai wani mutum  ana kiran sa Abu Sabiru, ya kasance mai tsananin haƙuri da kawar da kai akan wasu al’amura. Dalilin da ya sa ma ake kiransa Abu Sabiru kenan. Yana zaune tare da matarsa kyakkyawar gaske da ‘ya’yansu biyu. Yana da shanu da yawa da yake kiwo. Sai ya kasance duk dare sai Zaki ya zo garken shanunsa ya yi masa ɓarna, ya kashe na kashewa ya karya na karyawa, har dai ya raunana garken sosai. Matarsa ta ce da shi, “ka ga zakin nan ya yi mana ɓarna da yawa, ya kashe mana fiye da rabin dabbobinmu. Ka tashi ka hau dokinka, ka ɗauki makami ka yaƙe shi.”

Abu Sabiru ya ce da ita, “yi haƙuri dai. Kin ga dai wannan zakin shi ya ke aiwatar mana da zalunci. Tun da ba mu da haƙƙi a kansa, to da sannu Allah zai yi mana maganinsa.”

Babu jimawa kuwa sai Sarkin ƙasar ya zo garin nan farauta, suka yi ta yawo ba su samu dabba ko ɗaya ba. Har sun ɗebe ƙauna da samun komai, sai suka yi arba da zakin nan. Suka rufu a kansa da sara da suka da harbi har sai da suka rinjaye shi ya faɗi. Suka kashe shi sannan suka sassara namansa. Da labari ya zo wa Abu Sabiru sai ya ce da matarsa, “kin ga amfanin haƙuri ko? Da a ce na tafi yaƙar sa ni kaɗai, da ƙarshenta ya hallaka ni. Amma ga shi yanzu ya gamu da gamonsa.”

Kwanaki kaɗan sai wasu da ba a san ko su wane ne ba, suka kashe wani bafaden Sarki a ƙauyen su Abu Sabiru. Sarki ya aiko da mutanensa suka riƙa shiga gidaje suna wasoso har gidan dagaci ba su ƙyale ba. Suka wawashe ragowar dabbobin da suka rage. Matarsa ta ce, “ka ga kai ma mai sarauta ne, kuma mutanen Sarki sun san ka. Ka tafi wajensu su ba ka dukiyar da suka wawashe maka.”

Ya ce mata, “ban faɗa miki cewa haƙuri ne maganin komai ba? Tabbas Sarki ya aikata min ba daidai ba kuma zai ga ba daidai ba, amma haƙuri yana da riba idan aka bi a sannu.” Ashe wani maƙwabcinsa ya ji maganar nan da ya yi, dama kuwa yana jin haushin sa saboda sarautar da aka ba shi. Ya garzaya wajen Sarki, ya kwashe zance ƙarya da gaskiya ya faɗa masa. Sarki ya fusata, ya sa dakaru suka zo suka wawashe ragowar dukiyar da ta rage musu. Ya kori Abu Sabiru da iyalinsa daga ƙasarsa. Suka tafi basu san wurin zuwa ba cikin daji.

Matarsa ta ce, “ka ga duk wannan ya faru ne saboda sakacinka.” Ya ce, “na faɗa miki haƙuri na da ranarsa. Ya fi rashin haƙuri riba.” Suka yi ta tafiya cikin daji inda suka gamu da ‘yan fashi suka ƙwace musu ragowar abin da ya rage musu. Sannan suka tafi da ‘ya’yansu.” Matar ta fashe da kuka ta ce, “haba mijina! Dubi fa abin da suka yi mana. Ka bi su ka basu haƙuri, ƙila su ji tausayin mu su maido mana da ‘ya’yanmu.” Ya ce, “sake yin haƙuri dai har lokacin da Allah zai yaye mana. Domin duk wanda ya aikata mugunta kansa za ta ƙare. Mai haƙuri kuwa da sannu zai dafa dutse ya dahu.” Ta shiga kuka mai tsanani tana aibata shi saboda halin ko – in – kula da ya nuna. Shi kuma ya riƙa rarrashin ta yana cewa, “kin ga idan na bi su to ɗayan biyu; ko dai su tilasta ni ma na bi su, ko kuwa su ɗauki takobi su doki wuyana su kashe ni. Amma da sannu za mu ga sakamako mai kyau, domin Allah ba ya son zalunci.”

Suka tafi har suka isa wani gari wanda kogi ya ratsa ta gefensa. Ya ce da matar, “zauna nan, bari na shiga cikin gari na samo mana masauki.” Ya tafi ke nan sai ga wani mahayin doki ya zo domin shayar da dokinsa. Da ya gan ta sai ya ji yana son ta. Ya ce da ita, “zo ki hau dokina mu tafi na aure ki.” Ta ce, “ka jiƙai na domin girman Allah. Ka sani ina da miji da aurena.” Ya zare takobi ya nuna ta da shi ya ce, “ko dai ki yarda ki biyo ni ko na sare miki wuya yanzun nan.” Da ta ga babu mafita gare ta sai ta rubuta a ƙasa cewa, “ya mijina, ka yi ta zaman haƙuri har sai lokacin da haƙurin ya zama ba shi da amfani. Na farko dukiyarka ta tafi, sannan ‘ya’yanka, yanzu kuma matarka da kake son ta take son ka. Na tabbata wannan haƙurin naka ba zai taɓa haifar maka da ɗa mai ido ba.” Ta bi mahayin dokin suka tafi tana kuka.

Da Abu Sabiru ya zo bai ganta ba amma ya ga abin da ta rubuta. Sai ya zauna a wajen ya yi ta rusa kuka har ya gaji ya daina. Bayan hankalinsa ya dawo ya ce da kansa. “Tabbas haƙuri na da ranarsa, har yau ban fidd a ran samun sakamako mafi alheri daga asarorin da na yi ba.” Ya tashi ya shiga cikin garin yana ta yawo, har ya zo wani wuri da mutane ke yiwa Sarkin garin gini bisa tilas ba tare da biya ba. Masu kula da aikin na ganin sa suka kama shi suka shigar da shi aikin. Ya kasance a wannan aikin tsawon wata guda, kullum ana ba shi gayar gurasa da ruwa.

Wata rana wani mutum ya hau tsani sai ya zame ya fado ƙasa, ƙafarsa ta karye. Ya riƙe wajen yana kuka. Abu Sabiru ya tsuguna gabansa yana ce masa, “da ma ka yi haƙuri domin kukanka ba zai amfane ka da komai ba sai wata wahalar. Haƙuri shi ya fi alheri kan komai.” Mutumin ya harari Abu Sabiru ya ce, “haka ake haƙuri kullum ina cutuwa har da lafiyar jikina?”

“Ba ka san cewa haƙuri kan fito da mutum daga ƙarƙashin ƙasa ya mayar da shi saraki ba?” Duk wannan maganar da suke yi Sarki ya zo ganin aiki yana jin su. Ya sa aka kamo Abu Sabiru aka gurfanar gabansa ya ce masa, “watau kai mai wayo isasshe, shi ne ka ke bada wata gurguwar hikima ko? To bari mu jefa ka cikin ramin mu ga yadda za ka fito ka zama basarake.” Sarkin yana da wani kurkukun ƙarƙashin ƙasa, ya sa aka jefa shi ciki ana ba shi gurasa biyu da ruwa a kullum.

A duk safiya sai Sarkin ya zo saman kurkukun ya tsaya yana cewa, “kai mai ƙaramar ƙwaƙwalwa, ban gan ka har yanzu ka fito ka zama basarake ba.” Shi kuwa yana ciki bai yi magana ba. To shi Sarkin nan yana da wani ɗan uwa da suke uba ɗaya, tun jimawa ya kama shi ya jefa shi wannan ramin ya kulle shi. Ya jima da mutuwa a ciki, amma mutane ba su sani ba, suna tsammanin har yanzu yana nan da ransa, sannan ba su san ana tsare da Abu Sabiru ba.

Mutane suka nuna gajiya da zaluncin Sarki, suka riƙa tuna irin kirkin mahaifinsu, suka riƙa fatan ɗanuwansa da ke tsare shi ma ya zamana mai kirki kamar yadda aka sha yabonsa. Suka tattara mayaƙa na ciki da na waje suka auka wa Sarkin suka kashe shi. Sannan suka buɗe kurkukun suka fito da Abu Sabiru wanda suka yi tsammanin shi ne ɗan uwan Sarkin nan. Suka ce da shi, “mun kashe ɗan uwanka saboda zaluncinsa, yanzu kai ne Sarkinmu.” Abu Sabiru ya yi shiru bai ce komai ba, domin ya san cewa sakamakon haƙurinsa ne ya soma bayyana. Ya sanya tufafin sarauta, sannan ya zauna bisa karaga, duk mutane suka yi masa mubayi’a. Ya riƙa hukunci tsakaninsu yana naɗawa da tuɓewa, yana bayarwa da hanawa.

Ana nan sai Sarkin garin nan da ya wawashe masa dukiya ya kore shi, wasu mayaƙa suka kai masa hari suka kashe masa dakaru, suka nemi hallaka shi amma ya samu ya gudu. Ya taho garin da Abu Sabiru ke sarauta bai gane cewa dagacin ƙauyen da ya taɓa yi wa wasoso ba ne.  Abu Sabiru kuwa ya shaida shi, da ya ji abin da ke tafe da shi na daga neman taimako sai ya ce a ransa. ‘Amfanin haƙuri ya zo, yanzu Allah ya ba ni iko a kanka.’ Ya sa fadawansa suka  ƙwace duk abin da ke tare da Sarkin na daga dukiya shi da jama’arsa ya sa aka ƙwace tufafinsu aka ba su tsummokara sannan ya kore su. Mutane suka riƙa mamaki suna cewa wannan wane irin Sarki ne mai mugunta haka? Ta yaya mutumin da ya zo neman taimakonka za ka tsiraita shi ka kore shi? Mu dai ba mu taɓa ganin haka ba domin ba al’adar sarakuna ba ce.’ Abu Sabiru bai ce komai ba, ya ci gaba da mulkinsa yadda aka saba.

Ana nan sai wata rana mutanen ƙauye suka kawo kukan ‘yan fashi sun matsa musu, Sarki Abu Sabiru ya shirya mayaƙa suka tafi suka yaƙe su, suka kamo su gaba ɗaya. To su ‘yan fashin nan su ne waɗanda suka tare su a daji tare da iyalinsa suka ƙwace musu dukiya da ‘ya’yansu. Ya gane babbansu tun lokacin da aka gurfanar shi gaban sa.

Ya tambaye su, “ina wasu yara da kuka kama a daji kwanakin baya?” Suka ce, “Allah ya ɗaukake ka suna nan a wajenmu. Za mu kawo maka su a matsayin gaisuwa daga gare mu, sannan za mu ba ka dukiyarmu mu tuba daga wannan sana’a.” Abu Sabiru bai saurari jawabinsu ba, ya amshi ‘ya’yansa sannan ya sa aka ƙwace dukiyar ‘yan fashi, ya yi umarni aka kashe su duka.

Mutane fa suka shiga ɗimuwa suna cewa, “wannan har ya fi ɗan uwansa zalunci. Ta yaya masu laifi sun amsa laifinsu, sun ba shi bayi biyu a matsayin gaisuwarsu ta neman sulhu, kuma sun yi masa alƙawarin tuba su daina sata, amma saboda zalunci ya kashe su? Wannan ba halin dattako ba ne.” Abu Sabiru bai ce komai ba daga guna-gunin da jama’a ke yi. 

Ana nan sai ga mahayin dokin nan da ya ƙwace masa mata ya yi gaisuwa ya ce, “ya Sarki ina ƙarar matata wadda na aura amma har yau ba ta ba ni haɗin kai ba. Ta ƙi amincewa da ni mu yi mu’amalar aure irin na miji da mata.” Sarki ya sa a kirawo matar domin a ji ta bakinta. Tana zuwa ya shaida ta cewa matarsa ce, ya gane cewa wannan mutumin ne ya ƙwace masa ita. Da ganin haka bai nemi wani ƙarin bahasi ba ya sa a fille kan mutumin. Nan fa dakaru suka shiga guna-guni mai yawa suka yi masa kallon azzalumi na ƙin ƙarawa.

Da Sarki ya ga haka sai ya tara su duka ya tsaya gabansu ya ce, “Na gode wa Allah da ya kawo ni wanan lokaci. To amma ina so ku gane cewa ba ni ne ɗan uwan Sarki ba, domin shi ya mutu a cikin kurkukun. Ni kuwa na kasance fursuna wanda wancan Sarkin ya tsare ni. Kullum ya kan zo ƙofar kurkukun yana min izgilanci sai ga shi Allah ya saka min da matsayi mai girma saboda haƙurina. Game da hukuncin da na yanke a kan mutanen nan su uku kuwa, na farko Sarkin da na yiwa wasoso, a da na taɓa zama dagaci a wani ƙauyen da yake mulki.” Ya faɗa musu dukan labarinsa da na ‘ya’yansa da matarsa da dukiyarsa.

Da mutane suka ji haka sai suka durƙusa gaba ɗaya gabansa suna tuba bisa mummunar fahimtar da suka yi masa. Suka nuna masa ƙauna mai yawa gami da yabawa da haƙurinsa wanda ya yi ta yi a tsawon lokaci yana cutuwa da shan wahala. Sai ga shi Allah ya fitar da shi daga rami ya ba shi babban muƙami a dai dai lokacin da ya cire wancan Sarkin daga muƙamin ya jefa shi rami. Sarki Abu Sabiru ya shiga wurin matarsa ya ce da ita, “kin ga sakamakon haƙuri ko? Babu shakka haƙuri tamkar ɗan itace yake, a farkonsa ɗaci ko bauri ko tsami, a ƙarshensa zaƙi tamkar zuma.”

Saurayi ya dubi Sarki Shamsuddini ya ce, “kamar haka ne ya Sarki na ke kira a gare ka da ka sake yin haƙuri a cikin wannan al’amari har Allah ya kawo mana mafita baki ɗaya. Domin haƙuri wata kyakkyawar siffa ce a wajen sarakuna nagari.” Yayin da Sarki ya ji jawabin yaro sai fushinsa ya sauka. Ya yi umarnin a mayar da shi kurkuku. Daga nan fada ta tashi.

Next >>

How many stars will you give this story?

Click to rate it!

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.