Skip to content
Part 11 of 12 in the Series Tekun Labarai by Danladi Haruna

Rana Ta Goma

Wannan ranar ta kasance ana gudanar da biki na musamman a ƙasar, domin tunawa da ranar da Sarki Shamsuddin ya dawo kan kujerar mulkinsa. Mutanen birnin maza da mata, yara da manya sukan tafi fada gaba ɗaya su gaida Sarki. Su yi masa addu’a suna sake jaddada goyon bayansu gare shi.

Tun cikin dare Wazirai  suka riƙa bin manyan mutane suna shirya musu abin da za su faɗa wa Sarki game da yaro. Da gari ya waye kowa ya ci ado aka hallara ƙofar fada. Bayan gaisuwa da addu’a sai Sarki Shamsuddin ya ce, “jama’a ko kuna da wata buƙata gare ni?” Sai babbansu, wani dattijo mai yawan shekaru ya miƙe tsaye ya ce, “Allah ya taimaki Sarki, ya tsare shi daga dukan abin ƙi. Mu a wajenmu ka kasance abin yabo, saboda adalcinka da yadda kake hukunci tsakaninmu bisa gaskiya da kyautatawa, kuma ka kasance mai taimakonmu a duk lokacin da muka nemi haka. To amma game da al’amarin wannan yaro, ya Sarki muna ganin ka yi sakaci. Ka bari kullum yana cika maka kunnuwa da hauragiya da soki burutsu, alhali kai ne ka tsamo shi daga halaka, ka mutunta shi, ka gyara halinsa. Amma da yake ɗan jemage ne, ga shi nan ya koma halinsa da ya taso a cikinsa na ƙarya da cin amana. Na tabbata ba ka san abin da jama’ar gari ke faɗa game da cin amanar da ya yi maka, da kuma sakacin da ka yi a kansa, har yau ba ka yanke masa hukunci ba.” Daga nan dattijo ya zauna.

Sarki ya ja dogon numfashi ya miƙe tsaye ya ce, “ya ku jama’a, haƙiƙa ba na kokwanto ko kaɗan bisa irin ƙaunar da kuke min, kuma kuna kishi bisa duk wani abu maras daɗi da ya same ni. Na gode muku, Allah ya yi muku albarka. Kuma na tabbata bisa ƙarfin ikona, da zan sa a kashe rabin mutanen da ke wurin nan, ba zai wuyata a gare ni ba. To don me zan kasa yanke wa ɗan ƙaramin yaro hukunci? Wanda na tabbata bai wuce sa’an ɗan da na haifa ba? Na ƙyale shi ne ba domin labaran da yake bani ba sai domin na ƙara samun hujjoji masu ƙarfi a kansa yadda babu wanda zai ji wani abu a ransa bayan na zartar da hukuncin kisa a kansa.” Daga nan ya sa aka shigo da yaro gabansa. Ya faɗi ya yi gaisuwa Sarki bai amsa ba ya hau magana yana cewa, “kaiconka, duba nan ka gani, duk mutanen nan sun zo gare ni, kuma sun yarda na zartar maka da hukunci bisa abin da ka aikata. A zatonka zan yi biris da maganar su ne na sake ka ka tafi?”

Yaro ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ni dai a iyakacin yarda ta, waɗannan dattijan mutanen kirki ne, babu komai tsakanina da su sai alheri, kuma basu san komai da faruwar lamarin nan ba. Amma waɗannan waziran naka, su ke shirya komai. Na yi imanin ma su ne suka ƙulla wannan makircin a kaina, domin su nuna cewa jama’a duka sun san zancen. Kuma da sannu sharrinsu zai koma kansu. Ga ni dai a hannunka ya Sarki, kamar tsuntsun da ke cikin tarko sai yadda ka yi da ni. Ni dai na yi imani da cewa Allah shi ke da ikon komai, idan ya zartar da abu to babu makawa, komai wuya komai daɗi sai ya faru, a lokacin da ya so, a wurin da ya so, bisa yadda ya so. 

Shi ɗan adam a kullum yana aikata aibu bisa tsammaninsa na kautar da wani abu da ba ya ƙaunar sa, amma idan Allah ya ce sai abin ya tabbata, to bai isa ya hana ba. Ka ga ɗan Sarki Sulaiman duk da makircin da ya ƙulla wa ɗanuwansa da ɗan ɗanuwansa hakan bai sa ya tabbata a mulki ba lokacin da hukuncin Allah ya zo.”

Sarki ya yi tsaki ya ce, “kai wai ba za ka rabu da surutun nan ba? Faɗa min wane ne Sarki Sulaimanu? Me ya faru ga ‘ya’yansa? Yi maza ka faɗa mana kada ka ɓata mana lokaci, domin yau za mu halaka ka.” Yaro ya yi murmushi ya ce, “Allah ya ba ka nasara ga labarinsu:

Komai Da Lokacinsa Babu Abin Da Zai Yi Jinkiri Ko Ya Yi Gaggawa

A nan ƙasashen Bahar maliya an yi wani babban Sarki ana kiransa Sulaimanu, wanda ya kasance mai adalci da kyautayi da hikima wajen gudanar da mulkinsa. Yana da ‘ya’ya biyu; babban ana kiran sa Bahaluwan, ƙaramin kuma sunan Maliku Shahu. Bayan su akwai wata yarinya ‘yar ɗanuwan Sarki Sulaimanu ana kiran ta Shahkatun. Tana da matsanancin kyawu da cikar halitta da hankali da yawan ilmi. Sarki Sulaimanu yana matuƙar son ta, sannan kuma yana tausaya mata saboda maraicinta. A zuciyarsa ya yi nufin ya aurar da ita ga ɗaya daga ‘ya’yansa.

Ana nan har su duka suka isa aure, Sarki ya kira Shahakatun ya zaunar da ita gare shi ya ce, “na yi nufin aurar da ke, amma ba zan matsa miki ba, ina so ki zaɓi mijin da kike so a ba ki.” Ta ce, “kai ka zama tamkar mahaifi gare ni. Na tabbata ma ƙaunar da kake min ba kowane mahaifi ne zai yi wa ɗiyarsa haka ba. Tun tasowata ba ka buƙatar abin da zai ƙona min rai, ko na samu matsala. Don haka na ba ka wuƙa da nama sai abin da ka zartar.”

Sarki ya ce, “Allah ya yi miki albarka Shahakatu. Na baki Maliku Shahu idan kin yarda.” Yarinya ta rusuna ga Sarki ta ce, “Allah ya saka maka alheri ya babana.” Da ma tana son sa amma ta ɓoye a ranta. Da haka aka yi shirin biki aka ɗaura auren yaran suka tare a gidansu. Ango ya shiga wurin amarya suka yi amarci.

Ashe shi kuma Bahaluwan ya jima yana son Shahakatu, amma bai bayyana ba, musamman yadda uban bai damu da shi ba saboda munanan halayensa na mugunta da rashin kula da mutane. Don haka ya fi mayar da hankalinsa ga Maliku Shahu.  Wannan aure ya ƙona ransa, ya zamana ya kasa zaune ya kasa tsaye. Zuciyarsa ta cika da baƙin ciki da ɓacin rai, musamman yadda ya haƙiƙance cewa uban ya nuna magajinsa kenan tun kafin ya ƙaura, ga shi an ƙwace masa matar da yake so. Duk da haka ya ɓoye abin a ransa bai nuna wa kowa ba.

Ana nan har Shahakatu ta samu ciki, ta haifi ɗa namiji kyakkyawa kamar farin wata. Nan fa ƙiyayya ta sake huruwa a ran Bahaluwan, ya yi ƙudurin kawo ƙarshen wannan ɓacin ran. Cikin dare ya ɗauki sharɓeɓiyar wuƙa ya shiga inda ake rainon jaririn ya tsaya kansa, kuyanga mai kula da shi tana sharar barci. Har ya juya zai fita sai wata zuciya ta ingiza shi, shaiɗan ya tunzura shi, ransa ya fisga ya yi sama. Ya kama wuyan yaro ya soka wuƙa. Allah da ikonsa bai samu yanke maƙogwaron ba sai dai ya yi wa wurin mummunan rauni.

Kai tsaye ya wuce ɗakin kwanan Maliku Shahu da matarsa Shahakatu, ya tarar suna barci. Ya sa wuƙar nan ma ya cire kan ɗanuwansa, ita ma Shahakatu ya yi nufin kashe ta, sai ya tuna za ta iya zama matarsa nan gaba. Ya fice ya doshi makwancin mahaifinsu, to amma yawan masu tsaron wajen ya sa ya fasa aniyarsa. Daga nan fa sai tsoro ya kama shi, ya gudu wani waje domin kada uban ya sa a kamo shi. Da gari ya waye, kuyanga mai rainon jariri ta tashi ta ga jini a jikinta, ta duba ta ga yaro na numfashi sama – sama. Nan fa ta yi kururuwa mai tsanani wadda ta zo daidai da lokacin da Shahakatu ita ma ta tashi ta ga mijinta babu kai ga jini nan ko ina face – face ta yi kururuwa mai tsanani.

Sarki ya samu labari ya rasa inda zai sa kansa domin baƙin ciki. Aka shaida masa cewa jaririn da sauran numfashinsa tun da raunin bai illata maƙogwaronsa ba ya dai yi huda mai zurfi a wurin. Nan da nan ya aikawa mai maganinsa ya zo, ya ɗinke wurin, aka shiga ba shi magani. Mahaifinsa kuwa aka tafi aka binne shi. Duk wannan abin da ake yi, Bahaluwan na ɓoye, bai yarda ya fito ba, mahaifinsa ya aika neman sa ciki da wajen birni amma babu shi babu labarinsa. Uban ya haƙiƙance cewa shi ne ya aikata wannan aika – aika. Ranar suna aka raɗa wa jariri sunan mahaifinsa watau Maliku Shahu. Sarki Sulaimanu da kansa yake kula da jaririn da mai shayar da shi.  Allah ya ƙaddara rauninsa ya kame ya riƙa samun sauƙi cikin hanzari.

Bahluwan kuwa ya arce daga birnin cikin dare, domin tsoron hukuncin da mahaifinsa zai yanke masa. Ya zamana yana yawo tsakanin sarakuna yana kai sukan mahaifinsa, yana neman taimakonsu a kansa. Duk wajen Sarkin da ya je masa da irin wannan buƙatar sai ya yi masa nasiha ya sallame shi. Sarki Sulaimanu kuwa ya ci gaba da rainon jikansa yana masa addu’a a kullum yana fatan ya girma ya warke masa ciwon da ɗansa ya haddasa masa. Yayin da ya kai shekara biyar sai ya hau doki ya zagaya da shi gari, mutane suka fito suna yi wa yaro addu’a suna masa fatan alheri ya zama Sarki.

Duk abin nan da ake yi labari na zuwa kunnen Bahaluwan daga wasu matsegunta, baƙin cikinsa da hassada suka ƙara bunƙasa gare shi. Ya shirya babban yaƙi da mahaifinsa. Ya tafi ƙasar Sin ya shiga fada wajen Sarki ya shirya labarin ƙarya gaba da baya ya shaida wa Sarkin  cewa mahaifinsa ne ya kore shi ya ɗaukaka wani yaro mara uba, mara asali domin ya zama magajinsa. Sarkin Sin ya aika wa da Sarki Sulaimanu takarda yana neman bahasi game da iƙrarin Bahaluwan.

Uban ya rubuta amsa, ya shaida masa gaskiyar abin da ya faru, ya ce, “wannan yaron da ya kawo ƙarata wurinka ɗana ne, ni na haife shi amma ya bijire min. Ya zama mashiririci mai girman kai da rashin jin maganarmu kuma yana musgunawa talakawa. Haka kawai ya shirya ya kashe ƙaninsa da ɗansa.” Ya ɓoye masa cewa yaron na nan bai mutu ba. Sarkin Sin ya yi mamakin wannan abu, ya aiko da amsa cewa, “babu shakka yaron nan ya tabbata fanɗararre, idan ka yi min izni zan sa a fille masa kai a aiko maka da kan ka gani.” Sarki Sulaimanu ya aika da amsa ya ce, “ni kam babu ruwana da shi, domin hanyar da ya ɗauko ba mai ɓullewa ba ce, amma ka ƙyale shi zunubinsa zai kama shi da kansa, idan ba yau, akwai gobe.”

Dalilin wannan zumunci ya ƙullu tsakanin Sarkin Baitil Amini Sulaimanu da Sarkin Sin Imrana Shahu. Suka riƙa musayar takardu da kyautuka tsakaninsu. Sarkin Sin ya samu labarin bazawara Shakatun, ya ji irin kyawunta da kwarjininta, sai ya aika yana neman aurenta. Sarki Sulaimanu ya shiga wurinta ya shaida mata buƙatar da Sarkin Sin ya aiko. Da ta ji haka sai ta fashe da kuka ta ce, “ya Abbana yanzu wa zai yarda ya aure ni na tare da ɗan ɗan baffana?” Ya ce, “ki sani yanzu girma ya soma zuwa min, kwanakina suna kan ƙarewa ina kusa da halartar kabari. Don haka burina shi ne ɗanki ya gaje ni, a maimaikon mahaifinsa da ya mutu. Shi ya sa na ɓoye al’amarinsa zan riƙa kula da shi da kaina. Hatta Sarkin Sin na faɗa masa cewa wan mahaifinsa ya kashe su tare da mahaifinsa.” Da ta ji haka sai ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Sarki ya shirya ta aka ɗaura aure, ya aika wa Sarkin Sin ita. Ta kasance kullum cikin tunanin ɗanta take yi, amma babu damar ta furta zancensa ga Sarkin Sin kada ya ɗauki kawunta a matsayin maƙaryaci. Bahaluwan kuwa da ya ji labarin auren Sarkin Sin da Shahakatun, sai baƙin cikinsa ya ninku fiye da ƙima, ya rasa abin da ke masa daɗi a duniya.

Yayin da Maliku Shahu ƙarami ya kai shekara goma a duniya, sai jama’a daga ko’ina suka riƙa ɓarkowa ga Sarki Sulaimanu suna caffa ga Maliku Shahu a matsayin magajin kakansa.  Ana nan bayan ya kai shekaru sha ɗaya a duniya sai Sarki Sulaimanu ya kwanta ciwo. Bayan wasu ‘yan kwanaki ya ce ga garinku nan.

Daga cikin manyan fada sai wasu suka taru suka tattauna tsakaninsu, suka tsaya bisa ra’ayin yaro ƙarami wanda bai balaga ba, ba za a ba shi mulki ba. Don haka suka tafi a ɓoye suka zo da Bahaluwan suka ɗora shi bisa mulki, amma bisa sharaɗin ba zai kashe Maliku Shahu ƙarami ba. Ya amince da wannan sharaɗi amma sai ya sa aka kama yaron aka jefa kurkuku. Ba a ƙara taso da zancen sa ba sai da aka shafe shekaru bakwai, lokacin ya kai shekaru sha takwas a duniya. Mahaifiyarsa ta ji labarin abin da ya samu ɗanta amma babu halin magana, tilas ta yi shiru ba ta faɗa wa kowa ba ta miƙa al’amarinta wurin Allah mai kowa mai komai domin ya kawo mata mafita. 

Sarki Bahaluwan na zaune a fadarsa ana ta zancen duniya, har zance ya faɗo kan mulkin mahaifinsa da irin burinsa a duniya. Bahaluwan ya ce, “a son ran ubana fa, wai na riga shi zuwa lahira. Na tabbata da zai dawo duniya ya gan ni a gadon nan sai ya sake mutuwa domin baƙin ciki.” Gaba ɗaya fada aka fashe da dariya. A cikinsu akwai wani dattijo da ya zauna da Sarki Sulaimanu, ya san ɗabi’arsa da mutuncinsa, da ya ji abin da ake magana a kai, sai ya kada baki ya ce, “babu shakka haka ne burin mahaifinka, amma ga shi Allah bai nufa ba, ko da zai dawo duniya haka zai haƙura ya rungumi ikon Allah. Amma mamakina gare ka ya Sarki, yadda ka tsare yaron can a kurkuku ka manta da shi yau shekara bakwai. Yaron nan bai taɓa jin daɗin rayuwa ba. Tun zuwansa duniya yake shan wahala har yanzu da ya balaga. Ni ban ga hikimar tsare shi ba, matuƙar dai ba burinka ka halaka shi don kada ya hau gadon kakansa ba.” Duk fada aka yi tsit saboda tsoron Sarki da irin matakin da zai ɗauka a kan dattijo. Amma sai aka ji Sarki ya yi gwauron numfashi ya ce, “haka zancenka yake dattijo, bari na fito da shi na ba shi muƙami a masarautar nan.” Mutane suka hau murna, suna sa wa Sarki albarka bisa wannan kyautayi nasa. To amma shi Sarki yana da wata manufa a ransa.

Da aka fito da Maliku Shahu ƙarami sai ya tufatar da shi ya ba shi kayan sarauta, ya naɗa shi shugaban wata runduna ya ce su tafi su yaƙi ‘yan tawayen da ke kawo farmaki daga arewacin ƙasar suna ɓuya cikin duwatsu. Su waɗannan ‘yan tawaye tun zamanin Sarki Sulaimanu yake fama da su, mafasa ne, kuma mayaƙa masu tsananin taurin kai, duk wanda ya je yaƙar su ba ya samun nasara. Don haka ma Sarki Sulaimanu ya yi nufin sakar musu yankunansu kowa ya huta. Ko da yake hakan bai tabbata ba, amma kusan babu wata alamar mulkinsa a sassansu, domin komai nasu dabam ne hatta kuɗi ma nasu dabam suke amfani da shi. To shi Bahaluwan sai yake amfani da wannan damar yake aika duk wanda yake so ya ga bayansa zuwa yaƙar su, domin ya tabbata ba zai iya rinjayar su ba.

Maliku Shahu ya shirya ‘yan mayaƙan da aka ba shi ya tafi. Dukansu ba su san shirin da ke ƙarƙashin ƙasa ba. Tafiyar kwana huɗu suka yi a daji ba su da sanannen ciki, sai  suka ji ana harbinsu da kibau. Kafin su ankara mayaƙa marasa adadi suka rufe su. Suka auka kansu da yaƙi da kisa, suka karkashe da yawansu. Suka kama wasunsu ciki kuwa har da Maliku Shahu. Suka jefa su cikin wani kurkukun rami suka riƙa gana musu azaba har wata goma sha biyu. To bisa al’adar mutanen garin idan aka shiga sabuwar shekara sukan fito da tsararrun yaƙi su hau da su wata doguwar hasumiya, su jefa su ƙasa, faɗo su ragargaje, ba za a ɗauki gawar a binne ba sai bayan mako guda, wasu kafin nan ma namun daji sun ci rabonsu.

Da lokacin ya yi, sai aka fito da tsararru ciki har Maliku Shahu ƙarami aka hau da su bisa doguwar hasumiya, aka riƙa jefa su ƙasa ɗaya bayan ɗaya. Da Allah ya ƙaddara da sauran shan ruwan Maliku Shahu,  sai ya faɗo kan mutanen da suka riga suka mutu. Nan take kuwa ya suma. Bayan kwana biyu yana yashe a wannan wuri ƙarfinsa ya dawo, ya rarrafa kafin masu kwashe gawa su zo su ƙarasa shi ya nufi daji a ƙasa yana cin ganyaye da tsirrai. Kwana da kwanaki yana tafiya sannan ya isa wani ɗan ƙauye. Suka tausaya masa, suka ba shi abinci da sutura ya huta. Bayan kwana biyu ya buƙaci su yi masa kwatance zuwa birnin ka kansa inda kawunsa ke mulki.

Yana kusa da shiga garin ya haɗu da wasu mahaya dawaki, bayan ya sha fama da yi musu bayani suka gane shi. Suka nuna masa ƙauna ƙwarai da gaske sannan suka tausaya wa halin da yake ciki. Suka ce da shi, “ya shugabanmu, muna roƙon ka kada ka shiga birnin nan, domin muddin baffanka ya yi ido huɗu da kai to kuwa babu makawa sai ya kashe ka. Ka tuna cewa ya aika da kai yaƙin nan ne domin ka mutu a can.” Ya ce, “to yanzu mene ne abin yi?” Suka ce, “ka tafi birnin Sin wajen mahaifiyarka, ko da dai Sarki mijinta bai san da kai ba, amma za ka iya zama a matsayin talaka, ka zauna har zuwa lokacin da Allah zai yaye maka al’amarinka.” Suka fito da kuɗaɗe suka harhaɗa gwargwadon ƙarfinsu sannan suka ɗauke shi a wani doki suka wuce da shi nesa sosai da garinsu. Bayan sun tabbatar ya haure iyakar ƙasar sai suka nuna masa hanya suna masu fatan alheri gare shi suka juyo.

Game da mahaifiyarsa kuwa, labarinsa ya daina zuwar mata, domin mai kawo mata labarin ya hannun wata tsohuwa sun rasu. Ya kasance ba ta san halin da yake ciki ba. Ta kasa nutsuwa ta ci abinci, haka nan barci ya ƙauracewa idanunta. Ga shi bata da ikon shaida wa mijinta halin da take ciki, ta haƙiƙance ba zai gaskata ta ba. To akwai wani bawa baba da ta zo da shi daga gidansu, ya kasance tare da ita tun tana ‘yar ƙarama. Wata rana da abin ya ishe ta sai ta kirawo shi suka keɓe ta shaida masa damuwar ta. Ta ce, “ina roƙon ka shirya wata dabarar da zan samu labarin ɗana walau yana raye ne ko ya mutu.” Ya ce, “ke dai kin san yanzu idan aka shaida wa mijinki labarin ɗanki ba zai gaskata ki ba, domin tun tuni an ɓoye masa zancen, kin ga kuwa ba zai yiwu ba sai da saninsa.” Ta ce, “zancenka gaskiya ne, amma ni nufina shi ne ka tafi zuwa birnin Baitil Amini ka samo labarin inda yake, sai ka zo da shi birnin nan. Alabarshi ko wurin kiwon dabbobi a bar shi, ya kasance ba na ganin sa ba ya gani na amma ina jin motsinsa a kusa da ni.” Ya ce,  “ni fa ban san yadda zan ɓullo wa al’amarin nan ba, ina za a samu kuɗin duka wannan ɗawainiyar?” Ta ce, “ga mukullin taskar dukiyata duka, ka ɗebi duk abin da zai ishe ka ka tafi ka nemo min labarin ɗana.” Ta fashe da kuka. Tausayin ta ya kama shi, ya ce, “ki kwantar da hankalinki uwargijiyata, ko ba ki ba ni komai ba tilas na bi umarninki, balle ma wannan sha’ani ya shafe mu duka.” Ya yi mata alƙawarin sai inda ƙarfinsa ya ƙare wajen neman Maliku Shahu ƙarami.

Suka tsara yadda zai sayi kayan haja daga nan ya kai can ƙasar su daga nan ya shiga neman labarin abin da ya kai shi. Ya tafi har cikin birnin Baitil Amini cikin shigar fatake ya riƙa bibiyar labarin wanda ya zo nema. A nan ya samu labarin cewa ai tuni ya fito daga kurkuku an tura shi yaƙi wajen ‘yan tawaye sun kashe shi tare da dukan rundunarsa. Da ya ji haka sai ya yi ta kuka saboda tausayin halin da uwarsa za ta shiga idan ta ji wannan labari. Ya yi shirin komawa gida da baƙin labari. A hanya ya gamu da wani mahayin doki wanda yake ɗaya daga waɗanda suka taimaki Maliku Shahu ƙarami suka hayar da shi iyakar ƙasar zuwa birnin Sin. Suka shaida juna suka shiga tattaunawar bayan saduwa. Mahayin doki ya ce da bawa, “zan faɗa maka wani sirri amma sai ka rantse min za ka kiyaye shi.” Ya ce, “na yi maka rantsuwa tsakani da Allah ba zan tona ka ba.”

“Ka sani yanzun nan muka dawo daga rakiyar ɗan uwargijiyarka.”

“Me?” Ya zabura domin jin cikakken bayani. Mahayi ya kwashe labari kaf ya shaida masa. Ya ƙara da cewa, “mu ne muka ce ya tafi birnin Sin kusa da mahaifiyarsa domin idan baffansa ya ji labarin yana raye a birnin nan, la shakka kashe zai yi.” Bawa ya ce, “to ni ma kuwa zuwan nan da na yi labarinsa na zo nema domin uwarsa na can ta kasa zaune ta kasa tsaye, bata ci bata sha saboda rashin sanin halin da yake ciki.” Ya ce da mahayin, “na baka amana, ka raka ni inda kuka rabu da shi.” Mahayi ya ce, “zo mu je.” Suka rankaya har zuwa inda suka rabu da shi, sannan ya tsaya ya ce, “a nan muka rabu da shi, shi kuma ya yi nan. Zancen da nake maka matuƙar tafiyar zai yi sosai yanzu haka yana cikin ƙasa mallakin Sarkin Sin.” A nan suka yi sallama, bawa ya miƙa hanya yana tambaya duk garin da ya je ko an ga saurayi mai kama kaza da kaza kamar yadda mahayi ya siffanta masa shi. Yana cikin tafiya sai ya wuce wani mutum kwance ƙarƙashin bishiya yana barci. Har ya yi nisa sai ya tsaya tunani, ya juyo da baya ya ƙare masa kallo. Daga bisani dai ya tashe shi daga barci ya ce, “daga ina kake kuma ina ka nufa?” Ya ce, “ni baƙo ne zan wuce nake hutawa a nan.”

“Wane ne mahaifinka, kai ɗan wacce ƙasa ce?” Yaro ya fashe da kuka ya ce, “ubana ya mutu tun ina da kwana ɗaya a duniya. Na kasance wanda daula ta kuɓuce wa saboda zaluncin baffana.” Ya ci gaba da tambayar sa yana ba shi amsa, har dai bawan ya haƙiƙance shi ne wanda ya fito nema. Nan ya durƙusa yana sumbatar sa yana kuka. Ya shaida masa halin da mahaifiyarsa ke ciki game da rashinsa da buƙatar ganinsa da take. Suka rankaya suka tafi birnin Sin. Sun kusa shiga garin ke nan ‘yan fashi suka tare su suka ƙwace musu kaya sannan suka yi musu dukan tsiya suka jefa su wani rami suka kama gabansu. Bawa ya duba ya ga irin halin da suke ciki sai ya fashe da kuka. Maliku Shahu ƙarami ya ce masa, “haba don wannan bai dace ka yi kuka ba.” Bawa ya ce, “wallahi ba kuka nake saboda halin da muke ciki ba, amma saboda halin da mahaifiyarka za ta shiga idan ta ji shiru babu ni babu kai. Kuma ina kuka saboda mummunan halin da kake ciki haka tun tasowarka babu wani jin daɗi da ka yi sai wahala.” Yaro ya ce, “komai da lokacinsa. Idan Allah ya tsara abu babu makawa ya tabbata, a daidai lokacin da ya so, babu daɗi babu ragi.” Suka zauna a wannan yanayi har suka kwana. Da gari ya waye yunwa ta gallabe su, suka shiga hauma – hauma suna neman abin da za su ci amma babu komai. Yunwa ta matsa musu ƙwarai har suka miƙa kai ga mutuwa, suka kasa motsawa sai huci da nishi da gurnani.

Allah ya ba ka nasara da yake ba a ƙaddara mutuwarsu a wannan lokacin ba, sai ga Sarkin Sin ya iso tare da mutanensa sun dawo daga farauta. A hanyarsu ta dawowa suka biyo ta wajen ramin nan, sai suka bi wata dabba har ta gangara zuwa wannan ramin. Wani daga cikinsu ya bi ta a kan dokinsa ya kama ta ya kashe ta. Ya durƙusa yana gyara naman ke nan sai ya ji murya ƙasa – ƙasa ana nishi irin na wahala a cikin ramin nan. Ya hau dokinsa ya tsaya har ‘yan uwansa suka ƙaraso, ya faɗa musu abin da yake ji, suka saurara suka ji haka ne. Sarki ya sa a shiga a fito da su. Aka fito da su gaba ɗaya sun fita hayyacinsu saboda yunwa da rashin wadatacciyar iska ga ƙishirwa. Aka ba su ruwa suka farfaɗo. Sarki ya dubi bawan nan sosai ya gane shi sai ya ce, “yaya haka ta faru gare ka?” Bawa ya ce, “Allah ya ba ka nasara na tafi aiken uwargijiyata kamar yadda ka sani, na dawo nan kuma sai ‘yan fashi suka tare mu suka yi mana tatik sannan suka jefa mu ramin nan bayan sun dake mu.” Sarki ya tausaya musu, sannan ya dubi yaron nan ya ce, “wannan kuma fa?” Bawa ya ce, “ɗan wata kuyangarmu ce da muka hadu a birnin Baitil Amini, ta ba ni shi domin ya shiga hidimar Sarki. Na amince ya biyo ni saboda na lura da haziƙancinsa da wayonsa.” Sarki ya sa aka ɗibiya su a bisa doki aka tafi da su gida. Ya sa aka ba su magani da abinci da tufafi suka wartsake sannan ya shiga tambayar bawa yaya labarin Sarki Bahaluwan. Bawa ya ce, “Allah ya ba ka nasara yana nan mulkinsa babu adalci balle tausayi. Babu mai son sa babba da ƙarami, sai addu’a ake Allah ya kawo ƙarshensa.”

Bawa ya shiga wurin Shahakatu ya bata labarin komai tun daga azabar da Bahaluwan ya gana wa ɗanta a kurkuku da yadda ya tura shi halaka, da yadda ya same shi zuwa fashin da aka yi musu duka. Koda yake kafin ya zo mata da zancen Sarki ya shigo mata da labarin cewa ya tsinto bawanta bayan ‘yan fashi sun kusa halaka shi. Yayin da ta ji cewa suna tare da ɗanta sai ta ji kamar ta tsaga ihu, amma ta tuna babu dama, sai ta haƙura, idanunta suka cicciko da hawaye. Shi kuma Sarki sai ya yi tsammanin tana kuka ne saboda asarar dukiya da ta yi. Ya hau ta da faɗa yana cewa, “don kin rasa dukiya wani abu ne? Ake rasa rai ma a haƙura balle abin za ki iya samun ninkinta nan gaba?” Ta ce, “ka san mata rauninsu na da yawa.” Da haka zancen ya wuce.

Sarki ya naɗa Maliku Shahu ƙarami a matsayin mai kula da shuke – shuken gidan Sarki. An amince masa ya shiga har farfajiyar sashin mata, ya duba shuka ya bata ruwa, ya barbaɗa mata taki. Uwarsa sai ta kasance duk sa’ad da ya shigo sai ta tsiri wani aiki a wannan sashen domin ta kalle shi, shi ma yana kallon ta amma babu damar yiwa juna magana. Haka dai kullum zuciyarta na ƙara tafasa a kansa har dai ya kai lokacin da ta ji ba za ta iya jurewa ba, ya zo ban ruwa da sassafe, ta kama shi ta rungume shi, sannan ta shafa kansa tana kuka. Hakan yasa shi ma ya fashe da kuka.

Suna cikin wannan hali sai babban bawan Sarki ya shigo sashen, ya ga matar Sarki a wani irin yanayi da bai taɓa ganin ta ba. Ga kuma yaro a gabanta ta rungume shi. Nan da nan a fice kafin su gan shi jikinsa na rawa yana tantamar gaskiyar abin da idanunsa suka gani. Sarki ya gan shi a wani irin yanayi na ruɗewa da rikicewa, ya tambaye shi bahasi, bawa ya yi shiru bai ce komai ba. Sarki ya sake tambayar sa har dai ya matsa masa kan ya faɗi abin da ke damunsa. Bawa ya rusuna ya ce, “Allah ya ja zamanin Sarki, haƙiƙa ina tsoron raina game da dalilin firgicina.” Sarki ya ce, “na ba ka amana, babu abin da zai same ka daga furucinka.” Ya ce, “na shiga sashen amarya sai na gan ta rungume da yaron nan da bawanta ya zo da shi suna kuka. Don haka na yi hanzari na fita kafin su gan ni.”

Da Sarki ya ji haka, sai gaba ɗaya duniyar ta yi masa baƙi ƙirin, annurin fuskarsa ya ɓace, idanunsa suka kaɗa suka koma jawur kamar dunƙulen rana yayin faɗuwarta. Ya zabura ya tafi wurin Shahakatu, ya tarar ta kwance tana kuka. Sai ya yi tsammanin kukan jin daɗi ne bisa gamsuwa da yaron da ta yi. Ya sake fusata, ya daka mata tsawa ya ce, “annamimiya maha’inciya, macuciya! Ashe haɗin baki kika yi da tsinannen bawan nan naki, kuka shigo min da saurayi gidana domin ku ci amanita? To Allah ya toni asirinku daga ke har shi. Kuma wallahi kin ci darajar baffanki da ya aura mini ke da sai na tsinke miki wuya. Amma yanzu na bar ki da fitowar rana da faɗuwarta.” Ya tofa mata yawu ya fice. Ta sake ɓarkewa da wani kukan, tana da hujjar da za ta faɗa masa, amma ta san ba zai yarda da ita ba. Hasali ma hakan zai iya ƙara buɗe wata rigimar mai yawa. Haka ta haƙura ta miƙa al’amarinta ga Allah.

Sarki kuwa, yana fita sai ya sa aka kama bawan nan nata tare da Maliku Shahu ƙarami aka jefa su kurkuku bayan an zane su tsaf da bulala. Ya ce, “haka zan yi ta azabtar da ku har sai kun mutu!” Daga ranar ya daina shiga wurin Shahakatu ya yanke mu’amalar komai da ita. 

Sarki ya kasance yana da wata uwar goyo wadda ta raine shi tun yana wata ɗaya a duniya, har ya girma ta yaye shi. Ya zamana a wurinta yake ‘yan wasanninsa. Ta kasance mace mai wayo da sanin dabarar zaman duniya. Ta fahimci lallai Sarki na da wata damuwa da ke damun sa, haka nan matarsa amarya, ta lura komai ya sauya a zamantakewar gidan. Ta shirya ta samu Shahakatu a ɗakinta tana kwance tana tunani ta ce, “ya uwargijiyata, ban cika son damun ki a lokacin da kike son keɓewa ke kaɗai ba, amma lamarin ne ya tsawaita dole na cusa kaina a ciki.” Shahakatu ta tashi zaune ta ce, “uwata me kika gani a tare da ni?” Ta ce, “haba ‘yar nan, ai babu wanda zai gan ki a watan jiya ya sake kallon ki yau bai fahimci kina cikin mawuyacin hali ba. Na lura kina cikin wata damuwa da kike buƙatar agaji. Ki faɗa min ko mene ne zan samar miki da mafita iyakacin iyawata da yardar Allah.” Shahakatu ta yi ajiyar zuciya ta ce, “wannan abu kam yayewarsa sai ikon Allah, amma bari na faɗa miki ko aƙalla idan ba za ki iya kawo min mafita ba, na san za ki iya yarda da ni.” Ta kwashe labarinta da na ɗanta kaf ta shaida mata. Ta ƙara da cewa, “Sarki bai san ɗana ba ne, domin tuni an faɗa masa cewa yaron ya mutu, domin kada ya fasa aure na cewar zan kawo masa agola gida. To yanzu ga yaron har ya girma ban san yadda zan yi ba.” Ta fashe da kuka. Tsohuwa ta shiga rarrashin ta ta ce, “wannan abu ne mai sauƙi, domin ku ba ku gane halin Sarkin nan ba, mutum ne mai sauƙin kai da fahimtar rayuwa. Na tabbata ba zai ƙaryata ki ba a kan haka.” Ta miƙe ta ce, “ki jira ni zuwa gobe zan zo miki da mafita da yardar Allah.”

Daga nan ta wuce ta samu Sarki shi kaɗai a turakarsa ta zauna sannan ta ce, “ya shugabana, ka sani tun kana yaro nake tare da kai, nake ƙaunar abin da kake ƙauna kuma nake ƙin abin da kake ƙi. Na lura a ‘yan kwanakin na ba ka fara’a, ba ka sakin jiki kamar yadda kowa ya san ka. Haka nan iyalinka babu walwala da nishaɗi kamar baya. Shin ba za ka sanar da ni ba, ta yiwu na samar maka da mafita?” Sarki ya yi ajiyar zuciya sannan ya yi gwauron numfashi ya ce, “ban so na bayyana wannan abu ga kowa ba, amma kasancewarki amintacciya gare ni, mai taimako na tun bani da wayo har zuwa yanzu da nauye – nauye ke kaina, zan faɗa miki. Domin ina da yaƙinin ko ba za ki iya kawo min mafita ba, to ba za ki yayata zancen ga kowa ba.” Ya kwashe labarin gaba ɗaya ya faɗa mata, sannan ya ƙara da cewa, “wallahi amanar da ke tsakanina da baffanta ne kurum ya sa na ƙyale ta.” Da ta ji haka sai ta ce, “ka yi min izni zan zo maka da mafita zuwa gobe, wataƙila ba abin da kake tsammani ba ne ya auku.” Sarki ya ce “je ki aikata abin da kike ganin shi ne mafita.”

Tsohuwa ta tafi ta sa aka kamo mata balbela ta yanka, ta cire zuciyarta ta cuɗa cikin wani garin magani kamar gaske. Ta ɗauka ta kai wa Sarki ta ce, “na san kai mutum ne mai son gaskiya, mai mu’amala da gaskiya, kuma duk inda gaskiya take za ka rungume ta da hannu bibiyu. Wannan abin da na haɗa maka, ka shiga ɗakin Shahakatu yau idan tana barci ka ɗora mata a tsakanin nonuwanta, sannan ka kirayi sunanta, za ta ji kamar a mafarki kana magana da ita. Sai ka tambaye ta duk abin da kake buƙata. Za ta faɗa maka gaskiyar magana tiryan – tiryan. Muddin kuma wannan yaron masoyinta ne to za ta faɗa maka babu kuskure. Kai kuma daga nan sai ka yanke hukuncin da kake so a kansu duka.” Sarki ya gode wa uwar goyonsa kuma ya ƙuduri aniyar aikata hakan.

Daga nan tsohuwa ta zarce wurin Shahakatu ta ce, “yau Sarki zai shigo wurinki, ki yi bakam kamar kina barci, kada ki motsa, zai sa miki wani abu a ƙirji kada ki ji komai. To duk tambayar da ya yi miki ki faɗa masa gaskiya babu noƙe – noƙe. Zai yi tsammanin barci kike yi.” Ta gode mata sosai bisa wannan dabara. Ta jira har dare lokacin barci ya yi. Ta yi shiri ta kwanta. Babu jimawa Sarki ya aiko aka duba masa cewar ta yi barci, sannan ya shiga shi kaɗai ya rufe ƙofa. Ya ɗauko zuciyar balbelar nan ya ɗora mata a ƙirji sannan ya ce, “Shahakatun, Shahakatun, Shahakatun, yanzu wannan ne sakamakon da za ki yi min?” Ta ce, “wane laifi na yi maka ya shugabana?” Ya ce, “wane laifi ne ya fi wannan da kika aikata min? A ce kina tsarkakkiya, ‘yar tsarkakke matar tsarkakke amma ki riƙa neman shigo da dauɗa da ƙazanta gare mu? Ki ɓata kanki mu ma ki ɓata mu? Yanzu me kika ƙaru da shi a jikin yaron nan da ba ki ƙaru da shi a jikina ba?” Ta ce, “haba maigidana, ka sani wallahi ni ban damu da jima’i ba. Kuma ko cikin yaranka da hadimanka da ke wannan fadar akwai waɗanda suka ninka wannan yaron kyau da zati da diri amma ban taɓa sha’awar ko ɗaya ba, ballantana wannan da yake ɗana cikina da na haife shi.”

Ya ce, “me kike nufi da wannan magana? A iyakacin sanina da ke ɗanki guda ɗaya da kika haifa ya mutu sakamakon yankan da baffansa yayi masa a maƙogwaro. Kuma ƙari da wallahi ma baffanki ya aiko min da takarda game da mutuwar tsohon mijinki da ɗanki.” Ta ce, “haka ne, amma ka sani ɗana bai mutu ba, ya samu rauni mai yawa a wurin yankan da aka yi masa.  Masu magani suka ɗinke wurin suka warkar da shi. Amma baffana ya ɓoye maka al’amarin yaron ne domin kada ka ƙyamaci zama da ni tare da agola.” Sarki ya yi ajiyar zuciya ya ce, “yanzu wacce shaida gare ki da zan tabbatar da yaron nan ɗanki ne na cikinki?” Ta ce, “Sarki ya duba wuyansa zai ga tabon yankan da aka yi masa yana jariri har yau bai ɓace ba, sannan ya aika birnin Baitil Amini ya binciko waɗanda suka san haƙiƙanin zancen, ciki har da masu maganin suna nan ba su mutu ba. Kuma ka sani cewa Sarki Bahaluwan yana nan da nufin kashe shi.” Ta faɗa masa dukan wahalhalun da Maliku Shahu ƙarami ya faɗa. Sarki ya fashe da kuka saboda tausayin yaron da irin gararin da uwarsa ta shiga domin sa. Ya yi nadamar faɗar da ya yi wa Sarki Sulaimanu marigayi cewa ba ya ƙaunar agola. Ya tashi daga wurinta, a daren ya sa aka fito da yaron tare da bawan nan. Ya dubi wuyan yaron ya ga tabban yanka, bai san lokacin da ya rungume shi yana gode wa Allah da zuciya ba ta sa ya kashe shi ba.

Daga nan ya zaunar da shi a gefensa ya ba shi tufafin ado da sauran kayan alfarma. Ya shirya runduna mai yawan gaske wadda ya jagoranta da kansa ya tunkari birnin Baitil Amini. Babu wani dogon lokaci ya kame garin domin rundunar Sarki Bahaluwan ba su jima ba suna gwabzawa suka karaya, shi kuma ya tsere amma aka kamo shi. Garin kokawar kama shi wani ya yi masa rauni, kafin a zo da shi gaban Sarkin Sin rai ya yi halinsa. Nan take aka tabbatar wa da Maliku Shahu sarautar garin ya zauna bisa kujerar ka kansa. Ya jawo bawan nan na mahaifiyarsa kusa da shi, ya ɗaga darajarsa. Ba ya shawara a kan komai sai ya tuntuɓe shi. Wata rana yake ce masa, “ka ga ikon Allah ko? Ka tuna abin da na taɓa ce maka yayin da ‘yan fashi suka jefa mu rami?” Bawa ya ce, “na tuna.” Babu shakka komai na Allah na da iyaka, babu abin da zai zo kafin lokacinsa, kuma babu abin da ya isa ya zarce lokacinsa komai gaggawarmu ko akasin haka.”

“To ka gani, Allah ya ba ka nasara.” In ji yaro Kabiru mai ba da labari, “yaron nan Maliku Shahu Ƙarami, bai zama ya samu cimma burinsa lokacin da yake gaggawa ba sai da lokacinsa ya yi. Haka nan baffansa duk zaluncinsa bai ƙetare iyakar da Allah ya shata masa ba. Ko ni ma ba zan wuce iyakacin iyakar da Allah ya shata min ba, kai ma duk abin da za ka zartar a kaina walau na kisa ko alheri, tilas mu jirayi lokacinsa. Kuma komai gaggawar waɗannan waziran naka ba za su iya cutar da ni ba sai abin da Allah ya tsara.” Ya sunkuyar da kansa ƙasa. Sarki ya ce, “ku mayar da shi kurkuku. Gobe ce ranarsa ta ƙarshe a duniya.” Bayan an tafi da shi ya waiwaya ga Wazirai  ya ce, “yaron nan ya nuna ƙwarewarsa wajen iya tsara zance da magana. Don haka na ƙyale shi sai ya gama dukan labaransa, ilminsa ya ƙare kaf sannan zan zartar da hukuncin da kuke so kansa. To kuma bisa shawarar dattijan nan a gobe zan rataye shi a kasuwa kowa yana gani.” Wazirai suka cika da farin ciki suka yi godiya ga Sarki.

Daga nan Sarki ya ba da umarnin a kafa dirkar rataya, sannan mai shela ya zagaya lungu da saƙo na birnin yana sanarwa yana cewa, “kowa ya fito ya ga ƙarshen maci amana!” Wazirai suka cika da farin ciki, suka kasa zaune suka kasa tsaye, suka yi ta shiga da fice suna tattara jama’a waɗanda za su hallara domin tabbatar da cewa Sarki ya kashe yaron a washegari.

<< Tekun Labarai 10Tekun Labarai 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×