Skip to content
Part 12 of 12 in the Series Tekun Labarai by Danladi Haruna

Rana Ta Goma Sha Daya

A wannan ranar Wazirai suka fito da sassafe suka sa mutanensu suka shiga birni suna kiran mutane su taru a tsakiyar gari inda za a rataye Kabir. Mutane suka cika ana ta turmutsutsu har ba masaka tsinke, kowa na son ganin wanda ya ci amanar Sarki alhali ya amince masa. Daga nan Wazirai suka wuce gidan Sarki, kowanensu ya yi ado kamar ranar Idi. Suka faɗi gabansa suka ce, “Allah ya ba ka nasara, jama’ar gari gaba ki ɗaya sun hallara domin shaida hukuncin kisa a kan wannan yaro mai tsaurin ido.” Sarki ya sa aka fito da shi aka gurfanar gabansa. Babban Waziri ya dube shi ya ce, “kai Sarkin surutu, ko kana da wani zancen da za ka sa Sarki ya fasa zartar maka da hukunci kamar yadda ka sha yi a baya? Ka sani yau ƙaryarka ta ƙare, baka da sauran zancen da za ka faɗa a ƙara maka koda sa’a ɗaya.” Yaro ya dubi Waziri ya ce, “haba tsohon makiri! Ai ni ban taɓa yanke ƙauna daga ceton ubangijina ba. Na tabbata Allah cikin ikonsa da ƙudurarsa zai kuɓutar da ni ta hanyar da babu wanda ya yi zato ko tsammani. Allah shi ke taimakon mara ƙarfi ya ƙasƙantar da masu ƙarfi komai yawansu, kamar yadda ya kuɓutar da wani tsararre daga mutuwa.” Sarki ya ce, mene ne labarinsa? Amma kada ka tsawaita, domin kuwa, idan muka ga lokaci zai ƙure za mu katse ka.” Yaro ya ce ba wani dogon labari ba ne amma burina ku fahimci darasin da ke ciki.

Taimakon Allah Ya Fi Taron Dangi

Akwai wani babban Sarki da aka yi a ƙasashen Armeniya. Wata rana ya sa aka kama wani mutum aka tsare shi a kurkuku saboda an samu jini face – face a ƙofar gidansa. Sai aka ce wani ya kashe cikin dare. Danginsa da duk jama’a masu son sa sun yi juyin duniya domin a sako shi abin ya gagara. Babu irin hanyar da ba su bi ba amma Sarki ya ƙeƙasa ƙasa ya rabu da su. Kullum cikin dare sai mutumin ya riƙa addu’a yana cewa, “Ya Allah masanin sirrin dake sammai da ƙassai, na roƙe ka alfarmar sunayenka kyawawa ka kuɓutar da ni, ba ni kowa sai kai. Haƙiƙa kai ne mai ji kuma mai gani. Na tabbata ba za ka taɓar da ni ba!” Sarki ya kan zauna a kusa da kurkukun yana jin muryar mutumin yana addu’a, ransa ya kan ɓaci idan ya jiyo shi.

Ran nan dai cikin dare da ya gaji da addu’ar mutumin sai ya sa aka fito da shi aka gurfanar da shi gabansa. Ya daka masa tsawa ya ce, “don me a kan laifin da ka aikata ka ke neman taimako? Shin kana tsammanin za ka kuɓuta daga hannuna ne?” Ya dubi dogarawa ya ce, “a tafi a rataye shi a bayan gari!” Suka cakume shi zuwa wurin rataya.

A daren kuwa ana wata irin iska mai cike da ƙura. A hanya iska na bule su, suna ƙara gaba cikin wahala, har suka isa wurin. Ashe wasu ‘yan fashi sun yi shirin shiga gari domin aiwatar da nufinsu, sai suka yi kiciɓis da dogarai. Suka yi tsammanin sun samu labari ne za su kama su. Nan fa suka afka musu da yaƙi, suka yi ta harbin su suna suka suna saran su. Nan da nan suka tarwatsa su, mutumin nan ya samu kansa cikin masu gudu bayan ya samu ya warware marin da ke ƙafafunsa.

Ya yi gudu har ya gaji ya faɗi ƙasa yana haki kamar ransa zai fita. Wani zaki ya saɗaɗo zai banke shi, sai ya lura da shi ya zabura da gudu, ashe gabansa wani babban rami ne bai sani ba sai ya faɗa. Ya yi ƙoƙari ya riƙe saiwoyin bishiya da suka firfito a ramin, don haka bai ji rauni bai mai yawa ba. Yana nan kwance a ramin har gari ya waye. Ya lura ƙasa  sai ya ga tarin ƙasusuwan mutane da yawa ciki. A gefe ɗaya kuma ya ga jakar dinarai saboda jimawa har sun farfashe. A nan ya ƙaddara cewa fatake ne suka taɓa faɗa wa ramin suka mutu babu wanda ya sani. Ya tattara dinarin da zai iya ɗauka, ya ɗura a jaka sannan ya kama saiwoyin bishiya yana dabara har ya samu ya fita. Yana fita ya sake ido huɗu da zakin nan kamar jira yake ya fito. Zaki ya ce ‘da wa aka haɗa mu ba da kai ba?’ Mutumin ya yi ta gudu iya ƙarfinsa, har sa’a biyu zakin bai daina bin sa ba. Har ya kusa yanke ƙauna ya ba da kai sai ga gari a gabansu. Ganin haka zakin ya juya da baya zuwa inda ya fito. Mutumin ya zube a nan kamar matacce ya zauna a wannan hali har zuwa asubahin wayewar gari sannan ya motsa. Ya samu wuri ya binne jakarsa sannan ya shiga gari. Mutane suka ba shi gudunmawar tufafi da abinci sannan ya dawo ya kwashi dukiyarsa ya tafi wani garin ya kafa kasuwanci.”

Yaro Kabir ya dubi Sarki ya ce, “to ka ji yadda Allah ya kawo wa wannan mutumin taimako, har ya ƙara masa da dukiya.” Sarki ya yi murmushin da bai kai zuci ba ya ce, “kai yaro, har yaushe za ka yi ta ɓata mana lokaci da zantukanka?  Yanzu kam lokacinka ya yi babu sauran surutu kuma.” Ya ce a tafi da shi a rataye. Ya sa aka kai masa kujerarsa ya zauna domin tabbatar da cewa an zartar da hukuncin gare shi. Matar Sarki ma ta fito ta zauna kamar yadda Wazirai  suka shawarce ta.

Aka zarga masa igiya a wuya, sanƙira ya tashi gaban jama’a ya ce, “wannan yaron mai suna Kabiru, Sarki ne ya fanshe shi daga wasu mutane da suka kamo shi daga tawagar ‘yan fashi. Ya jawo shi jikinsa, ya naɗa shi wakilin dukiyarsa, ya amince da shi amma daga ƙarshe ya ci amanar Sarki ta hanyar ɓarnar dukiya yana neman mata da su. Kai da ya ƙasaita ma sai da ya nemi ya afkawa uwargidan mai martaba Sarki.” Mutane suka yi gurnani gaba ɗaya, wasu na zagin sa wasu kuma na masa addu’ar shiriya, yayin da wasu ba su yarda da waɗannan kalamai ba. Sarki ya dubi yaro ya ce, “ko ba haka ba ne?” Yaro ya ce, “Allah ya ba ka nasara shari’a ake min ko hukunci kawai ake shirin zartar min?” Sarki ya fusata da wannan maganar ya harari hauni mai kisa ya ce, “a janye dirka!” Hauni ya yunƙura zai janye dirka bisa umarni Sarki ke nan sai ga wani mutum ya keto jama’a ya ture shi gefe guda. Gaba ɗaya kallo ya koma wajensa.

Ya rusuna gaban Sarki yayin da ya ke masa wani tsattsauran kallo ya ce da shi, “wane ne kai?”

“Allah ya ba ka nasara duk laifin da yaron nan ya yi har ya cancanci kisan kai to na ɗauke masa, na karɓa a zartar min da hukunci a maimakonsa.” Sarki ya sake maimaita tambayarsa, “wane ne kai daga ina ka zo?”

Mutumin ya ce, “kafin na faɗa maka ko ni wane ne ina so na shaida maka cewa, wannan yaron a hannuna ya girma tun yana jariri. Na san shi ƙwarai da gaske,  wallahi ba zai aikata ɗayan abin da ake zarginsa ba. Ni ne shugaban ɓarayin Tumbas. Na tsinci wannan yaron yana jariri a ƙarƙashin dutse, rana ta zo kansa yana kuka. A gefensa na ga jaka cike da dinari dubu. Kuma na ga an yi masa shimfiɗa da dardumar zinariya. Na ɗauke shi na raine shi bisa zummar ya zama mai gadona amma ya ƙi bin irin hanyata, maimakon haka ma sai wa’azi yake mini kan na bar wannan sana’a tawa.

To ranar da na gaji da halinsa sai na yi nufin na nuna masa yadda muke gudanar da aikin namu bisa zaton hakan zai sa ya karkato ya bi ra’ayinmu. To Allah da ikonsa a wannan fitar ne kuma jama’ata suka gamu da gamonsu, aka kashe wasu aka kama wasu. Ni da wasu ƙalilan ne muka tsere. A cikin gawarwakin mutanenmu muka duba kaf babu shi, hakan ya sa muka tabbatar da cewa yana cikin waɗanda aka kama. Tun daga wannan ranar na sha alwashin sai na nemo inda yake a nan faɗin duniya. Na zagaya garuruwa da dama ban ji labarinsa ba, sai yanzun nan da na shigo garin nan na gan shi za a kashe shi. Ga kuma jakar da na samu ɗauke da dinarai da kuma dardumar zinariyar da aka yi masa shimfiɗa da ita.” Sarki ya karɓi kayan ya duba, nan take kamanninsa suka sauya, ya dubi yaro Kabir a ɗaure yana jiran  rataya. Bakinsa na rawa ya ce, “a kwance shi!” Hauni sai ya yi tsammanin cewa ya yi a kashe shi, ya nufi wurin da nufin ture dirkar, Sarki na ganin aika – aikar da zai y,i sai ya daka tsalle ya kai masa sara da takobi har ya datse masa yatsun hannunsa. Ya sa takobi ya sare igiyar da ke wuyan Kabir.

Ya rungume yaro yana kuka, sarauniya ma ta zaburo ta rungume shi tana kuka. Nan da nan wuri ya ɗauki sabon salo wasu na mamaki wasu na dariya wasu kuma tsaki. Wazirai kuma suka yi cirko – cirko suna zazzare idanu kamar ɓera a cikin buta.

Sarki na kuka yana cewa, “da na yi gaggawar ɗaukar mataki da na tabbata cikin nadama. Ashe gaskiyar ka da kake cewa kada ayi gaggawa, kada ayi fushi. Allah na gode maka da ka nuna min ɗana a rayuwata ta duniya.” Ya cire kambin da ke kansa ya ɗora bisa yaro sannan ya yi umarnin a tafi fada. Fada ta cika maƙil da ‘yan gari kowa na son jin yadda wannan al’amari yake. Sarki ya fito tare da ɗansa da matarsa uwar Kabir sun caɓa ado kamar ba su ba. Kowa ya miƙe domin ban girma gare su, sannan suka zauna a kujerin da aka tanadar musu kowa ma ya zauna, waɗanda ba su da wurin zama suka share ƙasa suka zazzauna.

Sarki ya miƙe tsaye ya ce, “jama’a ina gaishe ku da kyau tare da godiya bisa ƙwarin gwiwa da soyayyar da kuke nuna mana a kullum. Kamar yadda kuka sani, a ‘yan shekarun baya na samu akasi da Wazirina wanda ya kore ni ya gaje sarautata. Daga baya muka samu ƙarfi, muka dawo muka kore shi, muka zauna a kan wannan kujerar har ya zuwa yanzun nan.  To kamar yadda kuma da yawanku kuka sani shi ne, a gudun da muka yi wancan lokacin, matata na da tsohon ciki har ta haihu a tsakar daji, da muka ga wahala da haɗarin da ke gabanmu ba zai bari mu kula da jaririn ba, sai a muka bar shi a wannan wurin. Duk da mun koma daga baya muna neman wannan ɗa namu, Allah bai ƙaddara za mu sake saninsa ba sai a yau dalilin wannan mutumin.” Ya nuna madugun ɓarayi, ya miƙe, jama’a na masa sowa. Sarki ya ci gaba, “a taƙaice dai wannan shi ne yaron da kuka sani da suna Kabir ma’ajina, wanda Allah ya sa ba mu zartar da ɗanyen hukunci a kansa ba.”

Sarauniya ta miƙe tsaye ta ce, “ya jama’armu, ku sani tun da na soma ido huɗu da yaron nan nake jin cewa jinina ne, don haka ban taɓa masa wani kallo ba face a matsayin ɗan da na haifa. Duk abin da na faɗa a kansa a baya wallahi Wazirai  ne ga su a zaune suka shirya min yadda zan faɗa.” Ta faɗa wa jama’a komai da komai, aka hau zagin Wazirai. Babban dattijo  ya miƙe gaban jama’a ya ce, “yau ranar bayyana gaskiya ce babu tsoron ƙarya. Haƙiƙa jawabin nan da na yi wa mai martaba Sarki a fada ba wani ne ya shirya ba sai Wazirai , domin ba mu san zancen ba, suka faɗa mana sannan suka tsara mana abin da za mu faɗa a fada.” Jama’a suka tsananta zagin Wazirai  har wasu ma sun soma jifarsu. Sarki ya sa dogarawa suka tsawatar.

Bayan an natsa Sarki ya miƙe ya ce, “jama’a kun ga dai halin da Waziraina suka nuna bisa wata dasisa da suka shirya a ransu. Ni dai ban san dalilin da ya sa suka tsargi Kabir ba, amma bari mu ji ta bakinsa ko shi ya gano dalili.”

Yarima Kabir ya miƙe tsaye ya gayar da jama’a sannan ya ce, “haƙiƙa tun lokacin da aka kawo ni garin nan Sarki ya fanshe ni a wurin waɗanda suka kama ni. Bayan haka, ya jawo ni jikinsa ya naɗa ni a matsayin ma’ajinsa, ni kuma na yi alƙawarin yi masa aiki tsakani da Allah babu algus. To sai na lura ashe su waziran nan wata ƙofa ce ta almundahana ta rufe gare su. Daga nan suka yi neman hanyar da za su ga bayana domin su ji daɗin ci gaba da ha’intar Sarki. Wannan shi ne dalilin, kada ka daɗa kada ka rage.” Mutane suka sake ruɗewa da hargowa suna la’antar Wazirai  waɗanda tuni dogarai sun yi cuku – cuku da su. Sarki ya ce da ɗansa, “babu shakka tun sa’adda ka zama wakilin dukiyata na ga canji mai yawa kuma na haƙiƙance a baya an sha yi min sama da faɗi. To yanzu al’amarin waziran nan duka yana hannunka, duk abin da ka zartar a kansu ya tabbata.” Mutane suka sake hayaniya, wasu na cewa “a kashe su!” Wasu na cewa, “a ƙone su!” Wasu kuma na ci gaba da la’antar su. Kabir ya ce, “ya mahaifina, shi alheri har abada baya zamowa sharri. Tunda yarda ce da aminci ta sa ka naɗa su waziranka masu baka shawara, sai kuma ta tabbata sun gaza wannan aikin. To ina bada shawarar a kwaɓe su daga wannan muƙamin, sannan a kore su daga garin nan kowa ya zaɓi ƙofar da zai fita da kansa.” Nan fa jama’a suka ruɗe suna yabawa Kabir bisa basirarsa da iya maganarsa. Nan take Sarki ya sa aka warwarewa waziransa su goma duka rawani. Ya kuma ba da iznin kowanensu ya ɗebi abin da yake so na daga mallakinsa ya zaɓi ƙofar da yake son fita daga garin. Aka naɗa dogaran da za su raka kowanne. Garin ya kasance yana da ƙofofi goma, sai kowanensu ya zaɓi ƙofa ɗaya dogarai suka yi masa rakiya har bakin iyaka.

Sarki ya gode wa tsohon shugaban ɓarayi wanda ya bayyana tubansa a gaban jama’a. Ya yi masa kyauta mai yawa, sannan ya yi umarnin duk wani mai son sa ya yi masa kyauta. Jama’a suka yi ta jefa masa kyauta tun yana tsinta yana tarawa har abin ya fi ƙarfin haka. Tufafin alfarma da kayan abinci da kuɗi sai da suka danne shi ya kasa tashi. Sarki yasa aka kwashe duk abin da ya samu aka kai masa wani gida. Ya naɗa shi shugaban masu tsaron garin da kewaye. Daga nan fa aka goce da biki ana ta nishaɗi har kwana talatin cif. Sarki Shamsuddini ya gode wa Allah maɗaukakin Sarki da ya haɗa shi da ɗansa a lokacin da bai yi tsammani ba. Suka zauna suna mulkin jama’a cikin jin daɗin rayuwa da annashuwa. Tsarki ya tabbata ga maƙagin halitta mai azurtawa mai talautawa wanda ba ya mutuwa har abada.

<< Tekun Labarai 11

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×