Rana Ta Daya
Washegari tun da sassafe Wazirai suka ji abin da ya faru sai suka yi ta murna, suka taru domin shirya yadda za su sa a kashe yaron. Bayan sun gama ƙulle – ƙullensu, babban Wazirin Sarki ya zo wajensa ya faɗi ya yi gaisuwa sannan ya zauna kamar bai san abin da ya faru ba. An jima kaɗan Sarki ya gyara murya ya ce, "Waziri ashe yaron nan da nake yaba hankalinsa maci amana ne?" Waziri ya ji an taɓo inda ke masa ƙaiƙayi ya gyara zama ya ce, "Allah ya. . .
Kano state