Rana Ta Biyu
Da gari ya waye, Sarki Shamsuddin ya fito majalisa ya zauna bisa karaga ana ta fadanci. Gaba ɗaya ya manta da zancen saurayi. Sai Wazirinsa na biyu wanda ake kira Baharunu ya matsa, ya faɗi ya yi gaisuwa sannan ya ce, “Allah ya ba ka nasara ya baka lafiya da nisan kwana. Ya kamata a yanke wa yaron nan da ya ci amanarka, ya keta rigar alfarmarka hukunci daidai da mugun aikinsa.” Sarki ya sa aka fito da yaro daga kurkuku. Ya ce masa, “kaitonka! Tabbas aikinka ya jawo maka zan kashe ka mugunyar kisa, domin ya zama darasi ga na bayanka.” Saurayi ya ce, “ya Sarkin zamani Allah ya huci zuciyarka. Ina jiye maka tsoron gaggawa da hanzarin yanke hukunci ba tare da ka kai ƙarshen lamarin ba. Shi ganin ƙarshen lamari ginshiƙin sarakuna ne. Domin masu gaggawa da yawa suna kasancewa tamkar yadda ta faru ga attajiri. Amma ga wanda ya tsaya nazari har zuwa ƙarshen al’amari, to ya kan tabbata cikin farin ciki, tamkar yadda ɗan attajiri ya aikata.” Sarki ya ce, “me kuma ya faru ga attajiri? Me ɗansa ya aikata?” Saurayi ya ce, “bari na faɗa maka labarinsu.”
Saurin Fushi Na Kawo Da Na Sani
An yi wani attajiri wanda yake da dukiya mai ɗumbin yawa. Ya kasance ɗan kasuwa ne mai tafiya gari zuwa gari yana gudanar da kasuwancinsa. Ran nan ya shirya zai tafi kasuwanci, a lokacin matarsa na da tsohon ciki, ya ce mata, “da yardar Allah kafin ki haihu zan dawo.” Ya yi mata sallama ya tafi. Ya riƙa tafiya gari zuwa gari yana saye da sayarwa, har ya isa wani gari inda Sarkin garin ya gan shi mutum ne mai kamala da zurfin ilmi a kan lissafi. Dama kuwa Sarkin yana tsaka da neman wanda zai danƙawa amanar dukiyarsa. Da ya gwada amanar attajiri ya gamsu, sai ya bashi muƙamin ma’aji. Ya zaunar da shi a fadarsa yana kyautata masa.
Bayan shuɗewar shekaru suna tare, sai begen ganin gida ya kama shi. Ya tafi ga Sarki ya nemi iznin tafiya amma Sarki bai yarda ba. Ya ce, “Allah ya ba ka nasara, iyalina suna can suna zuba ido don ganin zuwana, na yi kewarsu.” Sarki ya sa shi ya rantse kan cewa idan ya je zai dawo. Ya ɗauko jaka ƙunshe da dinari dubu ya ba shi. Attajiri ya yi harama ya shiga jirginsa ya tafi garinsu. Da suka isa sai ya zauna cikin jirgin shi ɗaya ya yi barci bisa zummar idan ya farka zai ƙarasa gida wajen matarsa.
Ita kuwa matarsa bayan tafiyarsa babu jimawa ta haifi ‘yan tagwaye duk maza. Yara suka tashi kai ɗaya, har suka kai shekara bakwai – bakwai. A lokacin ne matar ta yi nufin tafiya wajen mijinta, domin ta samu labarin inda yake. To a wannan daren da ta kammala shirin tafiya, sai ta samu labarin cewa wani jirgi daga garin da mijinta yake ya zo ɗauke da kaya da mutane. Ta ce da ‘ya’yanta, “ku tafi bakin kogi ku tambayi labarin mahaifinku, ku faɗa musu sunansa wane.”
Yara suka tafi inda aka aike su, amma da suka isa sai suka kama wasanni suna ƙiriniya. Mahaifinsu yana daga ciki hayaniyarsu ta sa ya farka. Ya fito a fusace ya daka musu tsawa ya ce, “kai yara, ku yi mana shiru, kun dame ni da hayaniya!” To garin ya taso sai jakar kuɗin nan da Sarki ya ba shi ta faɗi cikin ɗaurin kaya. Ya laluba bai ga jakar ba, sai ya kama yaran nan cikin fushi ya hau dukansu da sanda yana cewa, “ku fito min da jakar kuɗina. Na tabbata ku kuka ɗauka, domin babu kowa a nan sai ku!” Yara suka rika kuka da kururuwa suna rantsuwar cewa ba su ɗauki jakarsa ba.
Mutane suka taru a wurin, sai suke cewa da shi, “bincike su da kyau, yaran garin nan ɓarayi ne komai ƙanƙantarsu.” Ya yi rantsuwa cewa idan ba su fito masa da jakarsa ba zai tsunduma su a kogin nan. Yara tun suna kuka har ya gagara. Da dai ya tabbatar ba za su fito masa da jaka ba, sai ya ɗaɗɗaure musu hannaye, mutane suka taya shi ya jefa su cikin kogi, ruwa ya yi awon gaba da su. Sannan ya koma cikin jirgi ya kwanta abinsa, kamar bai aikata komai ba.
Da uwar ta ga yara sun jima ba su dawo ba sai ta biyo sawu. Ta ga taron jama’a a wurin ta shiga tambayar su, “jama’a ina cigiyar wasu yara su biyu masu kama kaza da kaza, suna sanye da kaya iri kaza.” Can sai wani ya faɗa mata ai sun yi sata mai kayan ya jefa su cikin ruwa sun tafi. Tana jin haka sai ta hau kururuwa tana cewa, “shi ke nan sun raba ni da yarana, ga shi ubansu bai taɓa ganin su ba. Sun dasa min baƙin ciki!” Wani ya tambaye ta sunan mijinta ta ce, “shi ne attajiri wane ɗan wane.” Attajirin nan yana cikin jirginsa yana ciccika, sai ya ji murya mace kama da ta matarsa, bai mai da hankali ba saboda asarar da ya yi. Amma da ya ji ta ambaci sunansa sai ya leƙa ya gan ta. Nan take ya shaida ta, ya fita zuwa gare ta, ita ma ta shaida shi. Cikin kuka ya ce mata, “ni na jefa su cikin ruwan nan ya tafi da su. Ni kam na kashe kaina da kaina! Wannan shi ne sakamakon saurin fushi. Wannan shi ne sakamakon saurin yanke hukunci ba tare da tunani ba!” Suka tafi gida suna kuka da baƙin cikin faruwar wannan lamari. Daga nan suka yi aniya suna cewa, “ba za mu zauna ba sai mun nemo yaranmu da yardar Allah.” Suka bazama garuruwan gefen kogi suna neman labari, amma babu wanda ya ce ya gansu.
Su kuwa yaran nan a yayin da igiyar ruwa ke hankaɗa su, sai igiyar da aka ɗaure musu hannaye ta warware. Iska ta kaɗa kowane sashi dabam a bakin gaɓa. Na farkon da ya isa gaɓar, sai yaran Sarkin garin suka tsince shi suka ɗauke shi suka kai wa Sarkinsu. Da Sarki ya ga yaron kyakkyawa, sai ya ji yana son sa, ya karɓe shi daga hannunsu ya shiga da shi gidansa.
To Sarkin nan ya kasance ya taɓa haihuwar wani yaro namiji wanda aka yi shagali mai yawa, aka raɗa masa suna Saburunu. Yayin da yaro ya isa zama sai zazzaɓin hudowar haƙori ya kama shi, ya yi ta rashin lafiya har ya mutu. Sarki ya yi tsananin baƙin ciki da mutuwar sa amma bai faɗa wa mutanensa abin da ya faru ba shekara da shekaru. Don haka da ganin wannan yaron sai ya shirya ya fita da shi fada ya ce musu Saburunu ne ya girma, dama ya ɓoye shi ne sai ya kai shekaru bakwai tukuna. Mutane suka gan shi suka yarda da Sarki suka so shi. Sarki ya ja Saburunu a jiki sosai, ya nuna masa sha’anin sarauta gami da taskokinsa. Ya koya masa ilmi, da yaƙi, da sukuwar doki, da jifa da mashi. Ana nan bayan wasu shekaru Sarki ya rasu. Babu wata jayayya aka naɗa Saburunu a matsayin magajin sa.
Attajirin nan da matarsa kuwa suka yi ta yawo garuruwa suna cigiya gami da shiga kasuwanni wajen cinikin bayi amma babu labari. Yayin da suka sauka a wani tsibiri, attajirin ya shiga kasuwa, sai ya ga wani mutum riƙe da wani yaro yana nufin sayar da shi. Ya ce, ‘bari na sayi wannan yaron, ƙila ya zame mana madadin yaranmu da muka rasa.’ Ya yi ciniki yaro ya biya ya tafi da shi gida. Matarsa na ganin yaro ta yi kururuwa ta ce, “wallahi wannan ɗana ne!” Yaro ma ya shaida uwarsa. Suka yi ta murna suna gode wa Allah da ya ƙaddara dawowarsa gare su. Suka tambaye shi game da ɗanuwansa ya faɗa musu abin da ya faru.
Haka suka haƙura suka zauna da wannan yaron nasu shekara da shekaru. Yayin da ya girma sai mahaifinsa ya ɗora shi a kan harkar saye da sayarwa yana tafiya garuruwa yana komowa. Wata rana ya shiga ƙasar nan da ɗan uwansa ke mulki, aka shaida wa Sarki cewa wani matashin bafatake ya kawo kayan ado irin na sarakai. Ya aika aka kirawo shi zuwa fada. Yayin da suka ga juna ba su gane kansu ba, amma jini ya yi bege ga jini. Sarki ya ji yana ƙaunar bafatake. Ya ce da shi, “ina so ka zauna nan tare da ni, ka zama kana kula da wasu sha’anoni nawa. Za ka samu biya fiye da kasuwancinka.” Ya amince da tayin Sarki. Suka kasance kullum suna tare, barci ne kaɗai ke raba su. Sarki ya amince masa ya sakar masa al’amuransa. Shi kuwa ya miƙe ƙafa kullum sai ƙara azama yake wajen hidima ga Sarki. Da ya ga ba zai iya barin garin ba sai ya aika iyayensa suka dawo nan garin kusa da shi.
Ana nan ran nan Sarki ya fita bayan gari shi kaɗai domin ya sha iska ya ɗan yi tattaki. Ya dawo gida a gajiye sai ya kwanta barci mai nauyi. Ɗan uwansa da ya ga haka sai ya ce a ransa, “babu shakka Sarki na buƙatar tsaro na musamman a wannan dare. Zan je na kula da shi da kaina albarkacin karamcinsa gare ni.” Ya tafi ƙofar ɗakin Sarki ya zare takobi, ya tsaya yana gadi. Wani baran Sarki da ya gan shi sai ya zo ya tambaye shi abin da yake yi a nan cikin dare, ya faɗa masa aniyarsa. Daga wannan bai sake ce masa komai ba ya tafi. To su barorin nan duk suna jin haushin saurayin, saboda ya ƙwace musu fada, ya hana su kataɓus gaban Sarki, suna neman hanyar da za su ga bayansa.
Da gari ya waye sai ya shaida wa abokan aikinsa, sai suka ce, “wannan ce damar da za mu yi amfani da ita domin ganin bayansa.” Suka tashi gaba ɗaya suka ɗunguma gaban Sarki suka zube suka yi gaisuwa sannan suka ce, “ya Sarkin zamani, mun zo maka da zancen gaskiya gami da nasiha.”
“Ku faɗi abin da ke tafe da ku.” Sarki ya ce da su bayan ya saurare su. Suka ce, “yaron nan da ka jawo a jiki ka fifita shi fiye da mutanenka da bayinka da hadimanka har da sarakunanka kaf ya fi su daraja a wurinka, to maƙiyinka ne, domin kuwa so yake ya samu hanyar da zai bi ya kashe ka.” Kamannin Sarki suka sauya, ya ji ransa ya ɓaci nan take. Ya ce da su, “wace hujja gare ku ta faɗin haka?” Suka ce, “jiya da ya lura ka gaji sai ya ɗauki takobi ya zo kanka ya tsaya zai kashe ka. Da muka gan shi sai ya sulale ya gudu.” Sarki ya yi shiru yana tunani cikin fushi. Da suka ga zance ya soma shigarsa sai suka ce, “idan kana son ka tabbatar da iƙrarinmu, to yau ka nuna kamar ka gaji, ka kwanta kamar jiya za ka gan shi.” Sarki ya amince da wannan shawara.
Suka aika wani daga cikinsu zuwa wajen saurayin nan ya ce da shi, “mun ji Sarki na yabon gadin sa da ka yi jiya, amma ya ce ya so ka matsa kusa da kansa kana kula da shi, don ba ya son matsa maka ne. To yau ma ya fita kilisa, ta yiwu ya dawo a gajiye, ka aikata masa kamar yadda ka yi jiya, kuma kada ka manta ka matsa kusa da kansa tun da ya fi son haka.”
Saurayi ya ji kamar zancen haka yake da gaske. Ya shirya har zuwa lokacin barci, ya ɗauki takobinsa a zare ya tafi. Ya kuwa ga Sarki ya yi bakan kamar yana barci. Ya zo daidai kansa ya tsaya da nufin yi masa tsaro. Sarki na ganin haka sai ya harzuƙa. Ya tashi a fusace ya cafke shi yana mai cewa, “irin sakayyar da za ka yi min ke nan?” Hadiman nan na maƙe suna sauraro. Suna jin maganar Sarki sai suka yi kazazat suka fito suka kama saurayi suka ɗaure masa hannaye. Suka ce da Sarki, “ba mu izni mu kashe shi.” Sarki ya ce, “A’a, ba zan yi hanzarin yanke hukunci ba, domin dana sani na tattare da duk wanda ke hanzarin yanke hukunci ba tare da bincike ba.” Ya sa aka kai shi kurkuku.
Washegari Sarki ya mance da maganar saurayi ya ci gaba da sha’anin sarauta. Da suka ga bai yi maganarsa ba sai suka zo gaban Sarki suka yi gaisuwa suka ce, “yaron nan da ya so ya hallaka ka, ya kawo ƙarshen mulkinka, ka gaggauta nuna masa cewa kai ba tsararsa ba ne.” Yana jin haka ya yi tsawa ya ce a kawo shi nan cikin fada. Aka kawo shi a ɗaure, aka ɗaure masa ido. Hauni ya miƙe da takobi zai fille masa kai sai Sarki ya yi tsawa ya ce, “dakata tukuna har na yi tunani bayan na bincika sha’aninsa!” Aka mayar da shi kurkuku.
Labari ya je wa iyayensa suka yi ta kuka. Mahaifinsa ya rubuta wa Sarki takarda ya tafi da kansa ya bashi. Sarki ya buɗe takarda ya ga bayan gaisuwa ta ƙunshi bayani cewa, “ka ji tausayina kada ka aiwatar da hukunci a kan ɗana cikin fushi. Domin ni ma na kasance na aikata haka a baya, inda na tsunduma su cikin ruwa shi da ɗanuwansa. Har yau ban daina nadama ba. Idan kuma ga ba za ka haƙura ba, to ka riƙe ni a madadinsa.”
Bayan Sarki ya gama karanta takarda, ya dubi dattijon nan da kyau wanda ke ta rusa kuka yana shafe hanci. Ya ce masa, “dattijo ba ni cikakken labarinka.”
Ya kwashe labarinsa kaf ya faɗa masa har da yadda ya jefa ‘ya’yansa cikin ruwa bisa rashin sani sakamakon ruɗin zuciya. Da Sarki ya ji haka sai ya fashe da kuka cikin murya mai ƙarfi ya sauko daga karagar sarauta ya rungume mahaifinsa yana mai cewa, “babu shakka kai ne mahaifina, wannan kuma ɗan uwana ne.” Ya ba wa jama’ar wajen labarinsa gaba ɗaya aka yi ta murna. Ya ce da mahaifinsa, “da ba ka yi gaggawar yanke hukunci bisa zato ba, da ba ka kasance cikin nadama da baƙin ciki tsawon shekaru ba.” Ya aika aka zo da mahaifiyarsa, wadda nan take ta gane shi suka zauna cikin farin ciki da jin daɗin rayuwa.”
Daga nan saurayi ya dubi Sarki Shamsuddin ya ce, “Allah ya ba ka nasara idan ka zama mai sauƙin fushi bisa gaggawar yanke hukunci, da sannu za ka ci ribar hakan a ƙarshen al’amari.” Sarki ya ce, “ku mayar da shi kurkuku sai gobe domin ya yi mana nasiha mai amfani a wannan ranar.”
Yaushe zamu samu cigaban labarinnan?
ALLAH YAKARA BASIRA
YAYI KWAI SOSAI