Rana Ta Uku
Kashegari Sarki ya zauna a fadarsa, sai Wazirinsa mai suna Bakunu ya faɗi gabansa ya yi gaisuwa ya ce, "Sarki mai martaba mai daraja kamar ka bai kamata ya yi sakaci wajen ɗaukar mataki a kan wanda ya ci amanarka ba. Hakan zai magance irin surutun da mutane za su yi kan cewa ka ƙyale wanda ka gan shi da idanunka a kan gadonka tare da matarka." Sarki na jin haka sai ya harzuƙa, ya sa aka zo da yaro, ya daka masa tsawa yana mai cewa, "kai wannan mai taurin kan, ka. . .
Naji dadin labarinna