Rana Ta Hudu
Yayin da gari ya waye a rana ta huɗu, Waziri na huɗu mai suna Zuhushadu ya zo gaban Sarki ya faɗi ya yi gaisuwa, sannan ya ce, “ya Sarkina kada ka bari ɗan ƙanƙanin yaro ya hilace ka, domin ƙarya yake sharara maka a kullum. Muddin dai yana nan da ransa ba ka kashe shi ba, to za mu kasance abin dariya, mutane kuma za su yi ta zunɗenmu kan mun kasa taɓuka komai ga wanda ya ci amanarmu. Sannan shi kuma zai samu wani girma na musamman a wurinsu. Ka ga kuwa idan haka ta faru, mutuncinmu ya zube kenan.” Sarki ya yi kururuwa yana mai cewa, “wallahi ka faɗi gaskiya Waziri Zuhushadu!” Ya sa aka fito da yaro cikin sarƙa, aka gurfanar gaban Sarki. Sarki ya dube shi a fusace ya ce, “yau na gaji da ƙarairayinka. Ka shafe kwanaki kana yi min surutu. To yau alkadarinka ya karye, babu makawa na aika da kai lahira a yau!” Yaro ya ce, “ya Sarkin zamani, ni ban ƙi ka kashe ni ba a duk sa’adda ka ga dama. Amma ina tsoron kada ka dawo daga baya kana da na sani, domin kuwa duk wanda ya yi gajen haƙuri, babu shakka a ƙarshe a kan bar shi da cizon yatsa. Kamar yadda ta faru ga Bihizadu, ai ka ga gaggawa da gajen haƙuri ba su haifar masa da ɗa mai ido ba.” Sarki ya ce, “wane ne kuma Bihizadu? Me ya same shi?” Yaro ya ce, “bari ka ji nasa labarin.”
Gajen Hakuri Ba Shi Da Ribar Komai
A ƙasashen ƙetare an yi wani ɗan Sarki ana kiran sa Bihizadu. Ya kasance kyakkyawa ne, kuma yana da kirki domin kuwa yana zama tare da talakawa da fatake da attajirai. Mutane suna son sa, sai dai yana da saurin ƙagauta a al’amuran rayuwarsa. Wata rana wasu fatake na zaune a ƙofar fada, ya zo ya wuce ta gabansu suka gaisa, ya shiga ciki ya zauna kusa da mutanen ta ciki yana jin abin da suke faɗa. Sai ya ji suna tattaunawa a kan kyawunsa da cikar halittarsa. Wani ya ce, “kai ai duk duniya babu saurayin da ya kai Bihizadu kyau.” Sai wani ya ce, “A’a, akwai sarauniya Nuratu, ‘yar Sarki Hamzatu ɗan Shaharilu, ta ninka shi kyau nesa ba kusa ba.” Sai wani ya ce, “Lallai kam Allah ya ba wa gimbiya Nuratu kyau. Ina ma za ta sadu da Bihizadu su yi aure, da sun haifar da kyawawan da duniya ta jima ba ta ga irinsu ba.”
Bihizadu na zaune yana jin su, sai zuciyarsa ta harbu da son wannan yarinya. Ya sa aka kirawo mutumin da ya kawo zancen ta ya ce da shi, “kada ka ji tsoron komai, ina so ka faɗa min labarin wannan yarinya. A ina take, ‘yar wane ne, yaya zan yi na sadu da ita?” Tajiri ya ce masa, “sunanta Nuratu ‘yar Sarki Hamzatu mai mulkin Hairala’a.” Ɗan Sarki ya kwana yana begen yarinya kamar zai zautu. Da mahaifinsa ya ji labari, sai ya sa aka kirawo shi ya shiga rarrashinsa yana cewa, “wannan yarinyar ita da ubanta duk muna da iko akansu. Ka bari a bi a sannu za mu aika a nema maka auren ta.” Amma saboda ƙagara, Bihizadu ya ce, “ni kam ba zan iya haƙuri ba zan tafi neman ta da kaina.” Da mahaifinsa ya ji haka sai ya tashi ‘yan aike da takarda zuwa ga Sarki Hamzatu, ya bayyana masa muradinsa.
Sarki Hamzatu ya dawo da amsa cewa ya ba da ‘yarsa ga Bihizatu bisa sadaki da dukiyar aure gaba ɗaya dinari dubu ɗari. Sarki mahaifin Bihizatu ya duba taskarsa, ya ga adadin dinarin da ke ajiye bai kai yawan sadakin ba. Ya ce da ɗansa, “tun da an riga an baka, ka sake haƙuri har zuwa mu sake samun wasu adadin nan da lokaci kaɗan.” Bihizatu ya ce, “ni kam ba ni da sauran haƙuri sai na mallake ta.” Ya tafi ya ɗauki takobi da garkuwa da mashi ya hau dokinsa ya zabura zuwa birnin Hailara’a yana gudu yana keta daji. Saboda gaggawa bai bi hanya shararriya ba.
A cikin tsakiyar dajin wani gari ya tarar da hadiman Sarki waɗanda suke farautar ‘yan fashi da suka addabe su. Nan da nan suka rufar masa da yaƙi, suka nuna masa cewa Sarkin yawa ya fi Sarkin ƙarfi. Suka ɗaure shi zuwa wurin Sarkinsu. Da Sarki ya gan shi cikin tufafin alfarma da irin kyawunsa, sai ya yi tantamar ko ba ɗan fashi ba ne. Ya ce da shi, “saurayi faɗa mana labarinka. Da ganinka ba ka yi kama da ɗan fashi ba.” Bihizadu ya ji kunyar ya ambaci dalilin fitowarsa. Maimakon haka sai ya ce, “ni ɓarawo ne kuma ɗan fashi.” Sarki ya ce, “ba za mu yi gaggawar ɗaukar mataki kan wannan saurayi ba, a ajiye shi kafin mu kammala bincike a kansa.” Aka tafi da shi kurkuku aka tsare.
Sarki Sabranu kuwa da ya duba bai ga ɗansa ba, sai ya aika da takardu zuwa ga sarakunan yankin duka, yana wassafa musu kamannin ɗansa domin idan an gan shi a dawo da shi. Cikin waɗanda ya aika wa har da Sarkin nan da ke tsare da shi. Da ya kammala karanta takardar sai ya yi hamdala, ya sa aka fito da saurayin ya nuna masa takardar ya ce, “yanzu da mun yi hanzarin yanke maka hukunci, da yanzu mun faɗa tarkon nadama. Kai me yasa baka faɗa mana gaskiya ba da muka tambaye ka?” Ya ce, “kunya nake ji.” Sarki ya yi dariya ya ce, “kunyarka da gaggawarka sun kusa kai ka su baro.” Daga nan ya sa aka shirya masa dukiya mai yawa wadda za ta biya cikon dukiyar aure ya haɗa masa da wasu kyautuka masu yawa. Bihizadu ya ce, “ya Sarki, ina so ka rubuta min takarda zuwa wurin Sarki Hamzatu na je na ga matata, alabarshi idan na kammala na koma wurin mahaifina.” Sarki ya bushe da dariya ya ce, “wannan gaggawar taka Allah ya sa ta haifar maka ɗa mai ido.” Ya rubuta masa takarda zuwa ga Sarki Hamzatu. Yayin da ya isa garin sai ya ga Sarki da kansa ya yi hawa domin taren sa. Aka sauke shi a wani katafaren gida kusa da babban gidan da iyalin Sarki suke. Nan take Sarki Hamzatu ya aika aka kirawo Sarki Sabranu mahaifin Bihizadu domin a yi bikin gaba ɗaya a idanunsa. Amarya kuma aka shiga shirya ta.
To ashe a cikin gidan akwai wani da ake zargin yana shiga ciki ba tare da izni ba. Shi kuma Bihizadu yana masaukinsa amma ya kasa nutsuwa saboda ƙagauta na son ganin gimbiyarsa. Daga inda yake yana iya jiyo hayaniyar mata har da ita. Ya samu wata kafa yana leƙawa domin ya ganta. Mahaifiyar amarya ta lura da wani da yake leƙe, sai ta yi tsammanin wanda ake zargin yana shigowa ne. Ta karɓi baƙin ƙarfe daga wajen wani bawa ta sa a wuta ya yi jawur sannan ta soka shi a daidai inda ta ga motsin. Ƙarfe kuwa ya samu Bihizadu a ido ya shige ciki. Nan take ya faɗi a wajen magashiyyan, rai kwakwai mutu kwakwai! Taron murna kuma ya zama taron kuka da baƙin ciki”
Saurayi ya ce da Sarki Shamsuddin, “Allah ya ba ka nasara ka ji yadda wannan ɗan Sarki gaggawa da gajen haƙuri ya jawo masa taɓewa da da na sani a lokacin da ba ta da amfani. Kuma ita ma matar da ta yi hanzarin yanke hukunci, ta jawo wa kanta musiba a lokacin da babu damar gyarawa. Duk wannan ya auku sakamakon gaggawa da saurin tunzura. Da wannan nake roƙon kada ka kashe ni har sai ka zurfafa bincike tukuna. Ni dai na kasance a hannunka, kuma ba ni da ikon na guje maka, ko da na yi nufin haka.” Da Sarki ya ji jawabin saurayin, sai ya ce a mayar da shi zuwa gobe tukuna.