Rana Ta Biyar
Rana ta biyar, Sarki ya zauna a fada sai Wazirinsa na biyar mai suna Jahabauru ya je gabansa ya faɗi ya yi gaisuwa sannan ya ce, “haba mai martaba Sarki! Ka tuna fa, ka kasance da za a samu wani talaka yana ƙoƙarin shiga gidan wani talaka ba tare da izni ba, za a iya cire masa idanu. Amma ga shi har an samu wani ya shiga gidanka gidan sarauta, ya haye bisa gadon sarauta. Sannan an tabbatar da cewa iyalin Sarki yake son ya aikata wa ɓarna. Duk da haka kwana da kwanaki ba a yi masa hukuncin komai ba. Shin wannan yaron magajinka ne ko kuwa? Ya kamata ka magance mana kunyar da muke sha ka kashe shi kowa ya huta. Mu ba mu zo maka da wannan shawara ba sai domin wanzuwar wannan daular taka, kada maƙiya su samu abin faɗa a gare mu. Mu masoyanka ne masu ba ka shawara ta gari kamar yadda ka yarda da mu. Bai kamata yaron nan ya sake ƙara sa’a ɗaya a duniya ba.” Sarki ya tunzura da shawarar Waziri Jahabauru, ya yi tsawa ga dogarai ya ce, “a kawo lalataccen yaron nan!” Suka kawo shi ɗaɗɗaure cikin sarƙa. Sarki ya harare shi ya ce, “mutumin banza! Yau kam babu makawa ka girbin irin abin da ka shuka. Babu komai a gare mu idan mun kashe ka!” Yaro ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ni kam kuɓutacce ne daga zargin da kuke min, don haka nake fatan rayuwa nan gaba, domin duk wanda yake kuɓutacce daga laifi ba zai ji tsoron hukunci ko ɗauri ba. Haka nan duk wanda ya aikata laifi ko ba daɗe ko ba jima sai sakamakon laifinsa ya same shi kamar yadda miyagun ayyukan Sarki Dabdinu da Wazirinsa suka juyo kansu. Shi kuwa Galadima Hassan da ya yi abin kirki, sakamakon da ya same shi na alheri ne.” Sarki ya ce, “kamar yaya ta faru gare su?” Yaro ya ce, “Allah ya ba ka nasara ga labarinsu.”
Abin Da Ka Shuka….
A ƙasar Tabaristan an yi wani Sarki da ake kira Dabdinu, yana da Wazirai guda biyu, na farko ana kiransa Zurkanu na biyu kuma sunansa Kardanu. Waziri Zurkanu yana da wata ‘ya ana kiranta Arwa, kyakkyawa ce wadda babu kamar ta a wannan lokacin. Ta kasance mace mai yawan ibada da kula da sha’anonin addini. Saboda ɗumbin ilminta har zuwa wurinta ake yi domin fatawa da neman sani. Labarinta ya cika lungu da saƙon ƙasar, duk inda ka shiga zancenta ake yi. Ana haka har Sarki ya ji labarinta sai ya ji yana son ta da aure. Ya kirawo Waziri Zurkanu ya ce da shi, “ina neman auren ‘yarka a wajenka.” Waziri ya ce, “Allah ya taimake ka, ni da ɗiyata da iyalina duka bayinka ne sai yadda ka yi da mu, amma ina neman alfarma zan shaida wa yarinyar, domin na yi mata alƙawarin ba zan aurar da ita ba sai da yardar ta.” Sarki ya ce, “to ka hanzarta ina jiranka da sadakina.”
Waziri ya tafi wajen Arwa ya shaida mata buƙatar Sarki gare ta, sai ta ce, “ni ba zan auri Sarki ba, domin ya wuce ni muƙami. Ba zan auri kowa ba sai wanda muke daidai da shi ko ƙasa da ni, domin hakan zai sa ya zamana tare da ni ba tare da ya kula kowa ba. Amma idan na auri Sarki, to zan zama tamkar baiwa a gidansa.” Mahaifin ya koma wajen Sarki ya faɗa masa abin da ta faɗa. Maimakon ya haƙura sai begenta ya ƙaru a zuciyarsa. Ya ce da shi, “idan ba ka aurar min da ita cikin daɗin rai ba, to zan ƙwace ta da ƙarfi ko kana so ko baka so.” Waziri ya koma wurin ‘yarsa cikin damuwa ya shaida mata abin da Sarki ya yi iƙrari. Duk da haka ba ta yarda ba ta ƙeƙasa ƙasa cewa ba za ta aure shi ba. Waziri ya ji tsoron kada Sarki ya aiko a yi masa wasoso sai ya tattara iyalinsa ya yi nufin gudu daga ƙasar.
To amma Sarki ya samu labari ya aika da runduna mai yawa suka tare shi a hanya. Sarki ya hau da kansa ya same shi ya sa takobi ya sari wuyansa ya kashe shi nan take. Sannan ya kama Arwa bisa tilas ya aure kuma ya sadu da ita a wannan daren. Ya kashe ƙishirwan da ke addabarsa. Arwa ta miƙa lamuranta ga Allah ta zage dantse wajen bauta gare shi kamar yadda take yi a gidansu. Ta cire duk wata damuwa a ranta ta tsaya tsayin daka domin kyautatawa mijinta Sarki Dabdinu duk da kasancewar ba auren so ta yi ba.
Suna nan a haka wata rana Sarki ya yi nufin yin rangadi cikin ƙasashensa, sai ya kirawo Wazirinsa na biyu watau Kardanu ya danƙa masa gari a hannunsa, sannan ya wasicce shi da ya riƙa kula da matarsa har ya je ya dawo. Ya ƙara da ce masa, “ka kula da ita da kyau da aniya, domin ka sani ba ni wani abu da nake tamkar wannan matar tawa.” Waziri Kardanu ya ce, “na aminta kuma zan yi bakin ƙoƙarina wajen kula da lafiyarta har Allah ya dawo da kai lafiya gare mu.” Sarki ya ci gaba da shirin tafiya har lokacin da aka tsara ya yi, ya tafi da rundunarsa duka. Waziri ya riƙa aika wa matar Sarki da kayan abinci da sauran abubuwan buƙata, amma a cikin ransa sai ya ji yana buƙatar yin tozali da matar nan da Sarki ke jaddada masa cewar ya kula da ita da kyau. Ya ce a ransa, “da a ce ba mai kyau ba ce Sarki ba zai damu da ita haka ba.” Ya shirya yadda zai yi ya ganta, cikin dare ya shiga gidan Sarki babu wanda ya gan shi ya leƙa ɗakin barcinta, ya ƙare mata kallo. A nan ya shaida irin kyawunta da cikar halittarta, ya ji sha’awarta ta kama shi. Ya ji ba makawa sai ya shirya yadda zai sadu da ita ya tara da ita. Da gari ya waye ya aika mata da kyauta mai yawa kuma ya rubuta mata saƙo cewa, “ya gimbiya, ki ji tausayin bawanki, ki sadar da shi daga ni’imar da Allah ya horewa jikinki.” Da ta ga saƙon sai ta mayar masa amsa tana cewa, “ka ji tsoron Allah ka guji niyyar aikata fasadi. Ka ji tsoron Sarki, ka guji shiga gonarsa da ta keɓanta da shi. Ka sani duka mata ɗaya suke, ka nemi biyan buƙatarka wajen matarka ta halali.” Maimakon wannan saƙon ya karya masa zuciya ya fasa aniyarsa sai ma ya sake zage dantse, ita kuma ta riƙa yi masa nasiha ba tare da ba shi fuska ba. Da dai ya ga ba zai samu biyan buƙatarsa ba, ga shi kuma ya riga ya tona asirin zuciyarsa gare ta, sai tsoro ya kama shi. Ya ga cewar idan Sarki ya dawo ya samu labari to kuwa la shakka kashinsa ya bushe. Nan fa ya shiga tsara dabarun da zai fitar da kansa salum alum.
Arwa kuwa tun da ta samu ya daina yi mata aike sai ta fita harkarsa ta maida hankali ga ibadarta. Yayin da Sarki ya dawo, tun kafin ya shiga gida Waziri Kardanu ya tare shi yana kuka yana zuba ƙasa a kansa. Sarki ya dube shi cikin damuwa ya ce, “lafiya? Me ya faru ne Waziri?” Waziri ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ina tsoron yi maka zancen da zai kawo salwantar raina.” Sarki ya ce, “na baka amana, ba zan kashe ba komai munin maganar.” Da ya ji haka sai ya sake langaɓe kai kamar yana jimami ya ce, “Allah ya taimake ka, ka ba ni amana ƙasa na riƙe, ka bani amanar iyalinka na riƙe. Sai dai iyalin ba ta riƙe kanta ba.” Nan take fuskar Sarki ta sauya, ya ce, “faɗa min abin da aikata.” Ya ce, “ashe duk ibadar nan da take yi munafurci ce, domin tana ha’intarka a ɓoye. Bayan tafiyar ka da kwanaki kaɗan wani mutum ya zo ya ce min, “ka je ka ganewa idanunka abin da matar Sarki ke aikatawa.” Na tashi na shig cikin gidan, na ganta kwance tare da Abuhairi, wani bawan ubanta. Dukansu zigidir haihuwar uwayensu. Da na ga haka na sa aka kama Abuhairi aka kashe shi.” Ya numfasa sannan ya ce, “wannan ne abin da na gani yake ɗaga min hankali game da amanar ta da ka danƙa min.” Sarki na jin haka zuciyarsa ta ɓaci idanunsa ya juye saboda tsananin fushi. Ya daka wa bayinsa tsawa yana mai cewa, “ku tafi ku kamo ta ku kashe ta!” To amma sai galadima ya zube ƙasa gaban Sarki yana hurwa gami da ahi ya ce, “Allah ya ɗaukake ka, kashe ta ba zai kawo maka maslaha ba domin ba za ka rabu ɗacin zuciya ba. Abin da ya kyautu shi ne, Sarki ya sa a tafi da ita can ƙungurmin daji inda babu gida gaba babu gida baya, babu itace babu ruwa a bar ta a nan, idan tana da gaskiya Allah zai kuɓutar da ita, in kuwa bata da gaskiya sai yunwa da ƙishirwa su halaka ta. Ka ga ba za a ce kai ka kashe ta ba tun da ta kasance kana tsananin ƙaunar ta.” Sarki ya gyaɗa kai ya ce, “na’am, wannan shawara ta yi.” Ya ce da babban baransa a tafi a aiwatar tamkar yadda Galadima ya ba da shawara. Aka sa wani bawa ya ɗibiya ta bisa raƙumi ya ja ta zuwa faƙo inda babu ruwa ko alama sannan babu tsiro ko ƙanƙani ya ajiye ta daga ita sai suturun jikinta. Da ta samu kanta a wannan waje sai share ƙasa ta yi taimama sannan ta duƙa sallah domin samun sauƙi daga abin da ya same ta.
A daidai wannan lokacin kuwa akwai wani hadimin Sarki Kisira da ya shigo wajen a firgice yana neman raƙumi. Ya kasance ya je wani gari ya karɓo harajin garin dukiya mai yawa ya labtowa raƙuma. To babban wanda ya kasance ɗauke da dukiya fiye da ta sauran sai ya ɓata, Sarkin Kisira ya yi masa barazanar muddin bai tafi ya nemo shi ba to zai ɗanɗana kuɗarsa. A hanyar sa ta dawowa bayan ya samo raƙumin ya biyo ta wurin da Arwa ke sallah.
Ya tsaya yana mamakin ganin ɗan adam kuma mace mai ƙarfin halin yin ibada a wannan faƙon. Da ta idar sai ya yi mata sallama ta amsa masa. Ya ce da ita, “me ya kawo ki wurin nan ya shugabar kyawawa?” Ta ce, “Ƙaddarar Allah bisa hukuncinsa akaina.” Ya ce, “da za ki yarda sai ki biyo ni mu zuwa gidana ki samu yin ibadar ki a nutse.” Ta ce, “bani da muradin haka, amma idan taimako kake son yi mini, to ka kai ni inda dausayi ya ke yadda zan samu sauƙin alwalla.” Bai mata musu ba ya shige gaba har inda wata ƙorama ke gudana, daga nan ya yi mata sallama ya tafi.
Da ya isa Sarkin Kisira ya tambaye shi game da raƙumi da kuma dukiyar da ke tare da shi ya ce ya samo su duka. Sannan ya kwashe labarin matar da ya gani a daji ya faɗa wa Sarki. Ya ƙara da cewa, “tun da nake ban taɓa ganin mace mai kyau mai zati mai nutsuwa yayin sallar ta kamar wannan ba. Ni ba don ma kada a ce shara ta nake yi sai na ce aljana ce.” Zuciyar Sarki ta yi tsuntsu zuwa begen wannan matar, ya sa runduna aka tashi gaba ɗaya aka dumfari wannan faƙo inda Arwa take.
Suka iske ta tana ta sallah, suka jira ta idar sannan Sarki ya gabatar da kansa gare ta, ya ce, “ni ne Sarkin sarakai Sarkin Kisira, na zo domin neman amincewar ki zo wajena ki zauna.” Ta ce, “Allah ya ja da ran Sarki ba zan zo wajenka ba sai ka yi min alƙawari wani abu.”
“Wanne abu ne?” Sarki ya tambaya.
“Ka sa a kamo Sarki Dabdinu na ƙasar Tabaristan da Wazirinsa Kardanu da Galadimansa Hassan.”
“Saboda me?”
Ta kwashe labarinta kaf ta faɗa masa. Sarki ya sake nutsewa cikin son ta, ya fito fili ya nuna mata buƙatarsa gare ta na aure. Ta ce da shi, “na yarda da nufinka bisa sharaɗin nan na da na faɗa maka.” Daga nan Sarki ya yi umarnin a tafi zuwa gida. Isar sa gida ke da wuya ya sa askarawa suka zabura zuwa Tabaristan suka shaƙo wuyan Sarki Dabdinu da Waziri Kardanu, shi kuwa Galadima Hassan aka ɗora shi kan doki aka yi masa ado zuwa gaban Sarki Kisira.
Sarki Dabdinu ya gan shi gaban Sarkin Kisira sai tsoro ya kama shi ya kama rawar jiki. Aka tsayar da su gaban Arwa wadda ke cikin ɗaki da labule tsakaninsu. Ita tana kallonsu su kuwa ba sa ganinta. Ta ce, “miƙe tsaye kai Waziri Kardanu.” Ya miƙe jikinsa na rawa. Ta ce, “ka sani nan wurin shari’a ne, wurin tabbatar da gaskiya daga gaskiyar furuci bisa gaskiya aiki. Idan ka faɗi ƙarya za ta zame maka wahala da nadama a inda bata da amfani. Ina so ka faɗi dukan abin da ya faru tsakanina da kai a lokacin da Sarkinka ba ya gari. Ka faɗi yadda ka shirya min makirci ga Sarki da yadda nufinka bai tabbata ba.” Da ya ji haka sai ya haƙiƙance cewa Arwa ce musamman daga abubuwan da ta faɗa kuma ya shaida muryar ta. Cikin rawar jiki ya shiga bayyana dukan abubuwan da suka faru, tun lokacin da ya shiga wurin barcinta ya ga surar jikinta har yadda ya yi ta neman haɗin kanta da yadda bayan ya yanke ƙaunar haɗin kai daga gare ta ya ji tsoron ransa ya shirya mata makirci yayin da Sarki ya zo. Ya ƙara da cewa, “ban aikata haka ba face domin neman kuɓuta daga takobin Sarki idan ta faɗa masa cewa na yi yunƙurin afka mata.” Sarki Dabdinu na jin haka sai ya miƙe tsaye yana kuka da hawaye ya cakumi wuyan Wazirinsa yana cewa, “amma ka cuce ni, ka cuce ni, ka gama da ni, ka sa na rabu da matar da nake tsananin so a duniya. Allah wadaranka!”
Sarkin Kisira ya daka musu tsawa ya ce, “yau ranar adalci ce da mayar da abubuwa mazauninsu bisa doron shari’a. Don haka kai Sarki Dabdinu na yanke maka hukunci kisa sakamakon kashe Wazirinka mahaifin Arwa da ka yi da hannunka ba tare da ya yi laifin komai ba. Kai kuma Waziri Kardanu na yanke maka hukuncin za a kaika tsakiyar hamada inda babu ruwa babu ciyawa babu abinci. Idan kana da gaskiya za ka kuɓuta ka dawo sarautar ka. Kai kuma Galadima Hassan na naɗa ka Sarkin Tabaristan, kuma ka zamo ɗaya daga manyan abokan shawara ta.”
Daga nan saurayi ya dubi Sarki Shamsuddin ya ce, “Kenan ya Sarki duk wanda ya aikata abin alheri da sannu zai ga sakamako, kuma duk wanda ya aikata sharri sakamakonsa zai same shi ko ba daɗe ko ba jima. Ni dai ina tabbatar maka da cewa ban aikata laifin nan da kake zargina da shi ba, kuma na haƙiƙance da sannu Allah zai fitar da ni ya bayyana masu ƙulla kowane irin makirci ne.” Da Sarki ya ji haka sai zuciyarsa ta yi sanyi ya ce, “a mayar da shi zuwa gobe mu duba al’amarinsa.
Ma sha Allah muna jira
Masha Allah Allah ya ƙara basira