Rana Ta Shida
Yayin da rana ta shida ta zo, fada ta cika, Wazirai duk suka hallara. Tun cikin dare suka zauna suka tattauna tsakaninsu kan yadda za su samu nasarar shawo kan Sarki Shamsuddin ya kashe yaron nan kowa ya huta. Don haka sai uku daga cikinsu suka gurfana gaba ɗayansu a gaban Sarki suka ce, “mu dai mun san ka ɗauke mu aiki, musamman domin mu ba ka shawara ta gari, kuma a kan haka muke. Muna mamakin yadda kake kawar da kai daga wanda ya ratsa tumbinka, ya keta mutuncinka, ya nemi shiga inda babu mai ikon shigarsa sai kai. Ba don komai ba sai kurum don yana cika maka kunne da surutai marasa kan gado. Mun tabbata idan ka bar shi ba ka ɗauki mataki a kansa ba, to kuwa talakawa za su raina ka. Wataƙila ma a samu wani da zai sake irin wannan aika – aika a cikinsu.” Da Sarki ya ji haka, sai ya kumbura, ya kawo iya wuya, ya daka tsawa ga dogarai ya ce, “ku kawo ja’irin nan na yanke masa hukunci!” Aka shigo da shi aka dangwarar gabansa. Sarki ya nuna shi da yatsa ya ce, “tun yaushe na tabbatar maka da cewa idan ka zo gabana ba ka da wani mataimaki daga takobi ya sha jininka?” Saurayi ya ce, “ni ban jingina komai a sha’anina ba sai ga Allah maɗaukakin Sarki. Da shi na dogara, kuma shi ne zai fitar da ni daga dukan ƙangi. Domin duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa. Ba na neman taimako daga kowane mahaluki sai Ubangiji maɗaukakin Sarki. Haka nan duk wanda ya miƙa lamarinsa ga Allah to kuwa zai isar masa kamar yadda ya isar wa Sarki Baktazaman.” Sarki Shamsuddini ya ce, “Wane ne Baktazaman? Mene ne labarinsa?” Saurayi ya ce, “bari ka ji labarinsa.”
Dogaro Ga Allah Jari
Akwai wani babban Sarki, ana kiransa Baktazaman. Ya kasance babu abin da ya tsare sai yawan cin abinci da shaye – shaye da nishaɗi. Ana nan wata rana abokan gabarsa suka kawo hari cikin ƙauyukan da ke ƙarƙarshin mulkinsa. Ɗaya daga manyan fadarsa ya ce masa, “ya Sarki, ka sani waɗannan mayaƙan fa kai suke nema su raba da mulkinka. Ya kamata ka san yadda za ka ɓullo musu.” Sarki ya ce, “Ai ni na fi ƙarfin su saboda ina da mayaƙa da makamai da dukiya.” Hakimi ya ce, “ka dogara ga Allah shi zai fisshe ka sharrinsu.” A fusace Sarki ya ce, “don me zan dogara da wani, alhali ina da ƙarfi da dukiya da makamai da askarawa?” Hakimi ya yi shiru, jin maganar ta fi ƙarfinsa.
Babu jimawa kuwa mayaƙa suka shigo cikin birnin, suka kashe mutane, suka ƙona gidaje sannan suka ɓarnatar da dukiya wadda babu wanda ya san adadinta sai Allah. Sarki Baktazaman ya tsira da ransa da ƙyar ya isa wani birni inda abokinsa ke mulki. Ya faɗa masa halin da ya shiga, sannan ya nemi agajinsa domin ya yaƙi abokan gabarsa ya koma kan sarautarsa. Ya samu gagarumin taimako na daga mayaƙa da makamai, da dawaki, da dukiya mai yawa. Ya juyo yana mai alfahari da tinƙaho yana cewa, “tilas na karya waɗannan mutanen, na koma sarautata.” Hakimin nan ya ce masa, “ba ka ce in Allah ya yarda ba.” Ya ce, “ba wannan ne a gabana ba.” Suna isa garin, bugawar farko aka lanƙwame shi. Aka yi masa ta’annati fiye da a baya.
Ya tsira da ƙyar bayan an tarwatsa dukan jama’ar tasa. Ya hau jirgin haya ya ƙetare iyakar ƙasashensu zuwa wasu ƙasashen. Ya sauka a wani babban gari wanda gidan sarautarsa ke tsakiya. Ya tambayi sunan garin da Sarkinsa aka shaida masa cewa sunan garin Khadistan, Sarkin kuma sunansa Khadidanu. Ya shiga ciki yana mai ɓoye kansa har ya isa ƙofar fada, ya nemi ganin Sarki aka yi masa iso. Ya shiga ya tarar da Sarki zaune kan wata katafariyar kujera da dogarai hagu da dama a tsaye zare da takubba. Ya shaida wa Sarki labarinsa kaf. Sarki ya karɓe shi da girmamawa sannan ya zaunar da shi a nan wurinsa. Duk da haka kullum tunanin Bakhtazaman shi ne yadda zai koma mulkinsa.
Ana nan wata rana abokan gaba suka kawo hari ƙasar Khadistan, Sarki Khadidanu ya naɗa Bakhtazaman ya zama Sarki yaƙi. Ya aika shi tare da runduna mai yawa. Bayan tafiyarsu Sarki Khadidanu ya shiga gagarumin shirin yaƙi. Ya hau da kansa ya haɗu da su aka shiga gwabzawa da abokan gaba. Suka fafata yaƙi mai tsanani, amma a ƙarshe Sarki Khadidanu ya yi nasara gagaruma a kan abokan gabarsa. Ya juyo da jama’arsa ana ta farin ciki.
Da Bakhtazaman ya ga haka sai ya ce da Sarki, “Allah ya ba ka nasara, ban taɓa ganin abin mamaki irin wannan ba. Na ga ka fita yaƙi da kanka babu tsoron komai, kuma ka samu nasara mai yawa, duk da cewa sun fi jama’arka yawa.” Sarki ya ce, “kai kana kiran kanka jarumi mai yawan dukiya mai makamai da askarawa, amma ka manta cewa nasara ba ta dogara a kan yawan waɗannan abubuwa ba?” Bakhtazaman ya ce, “ni da abin da na dogara ke nan.” Sarki Khadidanu ya ce, “to wallahi duk wanda bai miƙa lamurransa ga Allah ba ya wahala. Babu wani ƙarfi ko rinjaye daga ɗan adam face da nufin Allah tsarkakakken Sarki, mabuwayi, mai iko a kan kowa da komai.” Ya dubi Bakhtazaman ya ƙara da cewa, “shi ya sa ka kasa samun nasara a kan maƙiyanka duk da ba su kaika yawa da ƙarfin makamai ba. Ina mai yi maka nasihar ka koma ga Allah. Ka miƙa al’muranka gare shi. Ni ɗin nan da kake gani na taɓa yin alfahari kamar kai, lokacin ina da mayaƙa dubu takwas masu tsananin jarumtaka sai wasu mayaƙa su ɗari takwas suka kawo min hari. Na aika askarawana cikin tsananin alfahari da ɗagawa, amma da yake ‘yan jaruman nan sun miƙa lamuransu ga Allah sai da suka yi min kaca – kaca ni da rundunata suka tarwatsa mu. Na gudu da ƙyar, na hau kan duwatsu domin neman tsira. A nan na gamu da wani bawan Allah wanda ya yi watsi da lamuran duniya, yana ta bautar Allah. Da na bayyana masa masifar da ta same ni, sai ya ce da ni, ‘ko ka san dalilin da ya sa ka kasa samun nasara?’ Na ce, ‘ban sani ba.’ Ya ce, ‘kana taƙama da yawan jama’arka ka manta cewa Allah maɗaukakin Sarki ne kaɗai mai ba da nasara, shi ne abin nufi da buƙata.’ Da na ji haka sai hankalina ya dawo jikina, na ɗaga hannu ina tuba ga Allah ina neman agajinsa da taimakonsa gare ni. Mai bautar nan ya yi min addu’a sannan ya ce min na koma na tattara ragowar jama’ata, na auka wa abokan gaba. Ya ja min kunnen duk abin da zan yi na dogara ga Allah, kaɗai. Na koma na tattara mutanena, cikin dare muka auka wa abokan gaba suna ta sharar barci, muka ɗaiɗaita su muka karkashe, mafi yawansu. Na shiga birnina na koma bisa ga mulkina. Daga wannan lokaci zuwa yau ba a sake samun rinjaye akaina ba.”
Yayin Bakhtazaman ya ji haka sai zuciyarsa ta zamo tamkar atafa saboda laushi. Ya ji kamar wanda ya farka daga barci. Ya yi kururuwa yana mai ambaton Allah maɗaukakin Sarki. Ya tashi ya tafi kan duwatsu yana kuka, ya zauna a nan yana bauta wa Allah har wata guda cikakke. Wata rana yana barci sai ya ga a cikin mafarki ana ce masa, “ka tashi ka tafi ƙasarka, da sannu Allah zai ɗora ka a kan maƙiyinka. Ka sani Allah ya amshi roƙonka gare shi.” Ya farka daga barcin sai ya shiga shiri, ya tafi zuwa garinsa.
Yana tafiya sai ya tarar da gungun wasu mutane a kusa da garin, suka ce da shi, “da fatan dai ba garin nan za ka shiga ba, Sarkin garin yana neman tsohon Sarkin garin ruwa a jallo, idan ya tambaye ka ka ce ba kai ba ne sai ya sa a yi ta gana maka azaba da nufin sai ka faɗi inda za a same shi.” Bakhtazaman ya tuna a ransa cewar yanzu fa shi Allah ne gatansa, ba ya jin tsoron kowa. Ya dubi jama’ar ya ce da su, “zan faɗa muku gaskiya, ni ne Bakhtazaman, kuma ni yake nema, amma Allah ba zai ba shi iko a kaina ba.” Ya nuna musu wata alama da za ta sa su yarda na daga hatimansa. Da suka ji haka sai suka sauko daga dawakansu, suka durƙusa gabansa suka gaishe shi. Sannan suka ce, “don me ka yi kasada da rayuwarka haka?” Ya ce, “ni ban ɗauki raina a bakin komai ba, domin dogara ga Allah mabuwayi mai iko.” Suka ce, “lallai wannan kaɗai ya ishe ka nasara. Ka sani mu ne manyan mutanensa, amma mun gaji da zaluncin da yake yi. Don haka za mu ɗauke ka tare da mu zuwa cikin birnin mu shirya yadda za ka ƙwace mulkinka.” Ya ce da su, “ku aikata abin da Allah ya hore muku.”
Suka tafi da shi a ɓoye zuwa cikin gari suka ajiye shi a wani gida. Sannan suka nemo tsofaffin manyan fadawansa da suka rage suka haɗa su. Kowa ya cika da farin ciki. Bayan an natsa suka shirya yaƙi a kan Sarki, Bakhtazaman ya kashe shi ya koma kan sarautarsa. Ya ci gaba da mulkin mutane cikin adalci da kyautatawa.” Daga nan saurayi ya dubi Sarki Shamsuddini ya ce, “kamar haka ne ya Sarki, duk wanda ya miƙa lamuransa ga Allah da tsarkakkiyar zuciya, babu shakka zai isar masa. Ni kuwa ba ni da kowa face Allah, da shi na dogara kuma shi ne zai fitar da ni daga wannan al’amari da ban san hawa ba, ban san sauka ba.” Sarki ya ce, “ku maida shi kurkuku zuwa gobe mu duba sha’aninsa.” Aka mayar da shi.