Rana Ta Bakwai
A rana ta bakwai Sarki ya zauna. Fada ta cika ana ta kwasar gaisuwa. Sai Waziri na bakwai wanda ake kira Bihkamal ya faɗi yana mai gaisuwa sannan ya ce, “Allah ya ba ka nasara ina mamakin yadda ɗan ƙanƙanin yaron nan yake wahalar da sha’anin mulkinka. Ka sani cewa idan ka bar shi ya ci gaba da yi maka walagigi da harshensa, babu shakka talakawa za su zarge ka, ƙarshenta ma su daina yi maka biyayya, saboda ka kasa ɗaukar mataki a kan wanda ka kama ƙiri da muzu bisa cin amanarka.” Sarki ya tunzura da waɗannan kalamai ya buga tsawa ya ce, “a kawo saurayin nan ya karɓi hukunci!” Aka shigo da shi a ɗaure aka dangwarar gaban Sarki.
Sarki ya harare shi ya ce, “kaitonka maci amana! Yau la shakka baka da wani hanzari da zai sa na fasa sa wa a fille maka kai.” Yaro ya ce, “Allah ya huci zuciyar mai martaba, babu inda afuwa ke da ƙima kamar a yayin da aka aikata babban laifi. Haka nan hukunci mai zafi ya kamaci mai babban laifi muddin ba a yi masa afuwa ba. To amma ni har ga Allah, ya sani ban aikata wani mummunan laifi ba, duk da haka ina neman afuwa gare ka, ba wani abu ba ne girman ikonka ya kau da bisa ga kuskurena domin duk wanda ya kauda kai ga ɗan ƙaramin laifi, Allah zai hore masa alheri yayin da ba shi da wani mai kula da shi. Wanda kuwa ya zama mai zalunci mara afuwa babu shakka wata rana sai ya afka tafkin da na sani. Da Allah ya taimaki Sarki Bihikadu ya yi afuwa sau ɗaya a rayuwarsa ai ka ga ta yi masa amfani.” Sarki Shamsuddini ya ce, “wane ne kuma Sarki Bihikadu? Me ya jawo ya yi afuwa alhali ba ya yin ta?” Yaro ya ce, “Allah ya ba ka nasara ga yadda abin yake:
Afuwa ƙwaya Ce, Ka Shuka Ɗaya Ka Girbi Goma
Cikin ƙasashen Mongol an yi wani babban Sarki mai yawan jarumai ana kiran sa Bihikatu. Shi wannan Sarki jarumi ne amma mugu ne na ƙin ƙarawa. Tun da yake bai taɓa yin afuwa ga wanda ya saɓa masa ba. Ba a taɓa ganin dariyarsa ba sai a kan ƙeta. Don haka jama’a ke shayinsa ƙwarai da gaske. Wata rana ya fita farauta shi da mutanensa, sai wani hadiminsa ya ɗauki mashi ya jefa sama. Mashin kuwa ya dawo sai ya karci Sarki a kunnensa har ya tsarga shi biyu. Sarki ya fusata ya ce a nemo wanda ya jefa mashin nan. Aka shiga aka taho da wannan hadimin mai suna Yatari, aka gurfanar gaban Sarki. Sarki na ganin sa ya ce a tafi a kashe shi.
Yatari ya kada baki ya ce, “Allah ya ba ka nasara, wallahi ba da sanina na jefo mashin inda kake ba, iyakar sanina wajen babu kowa, ban san kana wurin ba. Ina neman afuwarka domin girman Allah. Ka ji ƙaina, sai Allah ya ji ƙanka a ranar ba ka buƙatar komai sai jinƙan.” Da wannan sai Sarki ya ji sanyi a ransa, ya yafe wa Yatari aka sallame shi.
To shi wannan hadimin, ɗan Sarki ne da ya yi wa ubansa laifi ya gudu, ya je ƙasar Sarki Bihikatu yana masa hidima. Ana nan sai ubansa ya samu labarin inda yake, ya aiko masa da takarda yana mai cewa ya yafe masa laifin da yayi masa amma bisa sharaɗin ya koma gare shi. Da saƙon ya same shi sai ya shirya ya sulale ba tare da sanin Sarki Bihikatu ba, ya koma wajen mahaifinsa. Uban ya karɓe shi da girmamawa ya ba shi muƙami, sannan ya yi masa aure gudun kada ya sake guduwa.
Wata rana Sarki Bihikatu ya shirya jirgi tare da jama’arsa, suka shiga ruwa domin farautar kifi suka nausa. A tsakiyar teku sai guguwa mai ƙarfi ta taso, ta buga jirgin nasu da wani ƙaton dutse. Jirgin ya farfashe, jama’a duka suka hallaka, wasu kuma suka warwatse cikin ruwa. Sarki Bihikatu ya kama wani allon jirgi, da ƙyar ya tura shi zuwa wata gaɓar teku. Ya kwanta a nan cikin wahala bai san inda kansa yake ba, duk kayan jikinsa sun yayyage ana ganin tsiraicinsa. Wannan gaɓar tekun da ya tsinci kansa kuwa, nan ne garin da uban Yatari ke mulki. Da gari ya waye mutane suka fito, sai suka ga wani mutum a kwance an kashe shi, gefe ɗaya kuma ga wani matsiraici nan kamar mahaukaci a kusa da gawar. Sai suka ce, “wannan mahaukacin ne ya kashe mutumin nan.” Suka kama shi suka kai wajen Sarki. Wahalar da ya sha a teku ta sa ko magana ma ba ya iya furtawa. Sarki ya yi umarnin a kai shi kurkuku a ɗaure, kafin a duba al’amarinsa.
A cikin kurkukun Bihikatu ya yi ta nadamar abubuwan da ya aikata wa mutane na zalunci da rashin afuwa. Yana cikin wannan halin sai wata tsuntsuwa ta sauka bisa katangar gidan da yake. Da yake shi mutum ne mai son farauta sai abin ya motsa masa. Ya ɗauki wani dutse mai kaifi ya jefe ta da shi. Tsuntsuwar ta tashi, dutsen kuma ya wuce kai tsaye wani ɗan Sarki ƙanin Yatari na wasan doki, dutsen ya same shi a goshi ya faɗo daga dokin jini na ta zuba.
Fadawa suka garzaya neman wanda ya yi wannan jifa, aka gano shi, aka cukumo wuyansa zuwa ga ɗan Sarki, ya ba da umarnin a kashe shi. Nan da nan aka zarga masa igiya aka ƙunƙunce hannayensa, za a rufe masa ido ke nan sai ɗan Sarki ya ga kunnensa a yanke, sai ya ce, “dama can kai mai laifi ne, ga kunnenka nan a yanke shaidar ka taɓa aikata laifi a baya aka yi maka haka.” Bihikatu ya ce, “ba haka ba ne wallahi, dalilin yankewar kunnena shi ne abu kaza.” Ya ba shi labarin sarautarsa da yadda aka yi kunnensa ya tsage. Yayansa Yatari na ciki yana jinsu. Da ya ji Bihikatu na ba da labarinsa sai ya fito ya ce, “ko kai ne Bihikatu?” Ya amsa, “ƙwarai kuwa ni ne.”
“Ka shaida ni?”
“A’a ban shaida ka ba.”
“Ni ne wanda ka yi wa afuwa yayin da na yi jifa da mashi ya yanke maka kunne.” Ya yi umarnin a kwance shi, ya tafi da shi wurin mahaifinsa, ya nuna shi yana mai cewa mahaifinsa, “shi ne Sarkin da ya yafe min alhali bai taɓa yi wa kowa afuwa ba.” Sarki ya marabce shi, ya zaunar da shi, sannan ya shirya masa liyafa.
Bayan ya huta Sarki da ‘ya’yansa suka shirya masa dukiya mai yawa tare da bayi da hadimai suka aika da shi zuwa garinsa ya ci gaba da mulkinsa.”
Yaro ya dubi Sarki ya ce, “to Allah ya ba ka nasara ka ji yadda afuwa take tsiruwa ta girma har ta hayayyafa ta zama bishiya. Da a ce Sarki Bihikatu ya kashe Yatari, babu shakka shi ma da ya rasa ransa. Ita afuwa komai ƙanƙantar ta ba ta taɓa tafiya haka a banza.” Da Sarki Shamsuddini ya ji haka, sai ransa ya yi sanyi ya ce, “a mayar shi kurkuku kafin gobe mu gani.”