Skip to content
Part 2 of 3 in the Series Tsaka Mai Wuya by Umar bin Ally

Bansan ina sojojin nan suka kaini ba abinda nasani kawai shine an ajiyeni awani daki mai matukar duhu wanda ko tafin hannuna bana iya gani bana gane safiya ce ko dare ban kuma san kwana nawa na yi ba a cikin dakin sai dai kawai na barshi a matsayin sati daya.

Ina cikin wannan hali kawai najiyo hayaniya daga waje dai kuma naji anshigo an daukeni anfitar dani koda nayi arba da hasken rana saina kasa koda bude idanuwana bansan ina akayi dani ba nidai kawai na tshinci kaina acikin wani gida a tsakiyar daji gidane ginin katako abakin ruwa saidai wannan karon ba kulleni akayi ba kuma duk wani abun bukata nayau da kullum ina samu

Wata safiya ina zaune ina tunanin halinda nake ciki kawai sai naga tsaiwar wata mota namaida kallona izuwa ga motar cikin mamaki sainaga zainab Sadeeq ce tafito fuskarta cike da damuwa ta karaso gareni tafara da cewa bansan da wane ido zan kalleka ba bansan da wanne kalamai zanfara baka hakuri ba tabbas na cutarda rayuwarka bantaba sanin menene so ba sai akanka kai nafara so kuma bayan kai banajin zan kara son wani da namiji arayuwata tana zuwa nan a zancenta kuka yaci karfinta nan take tausayinta ya kama zuciyata na matsa kusa da ita na rike hannunta nace da ita tabbas mutum baya taba gujewa kaddararsa kuma kidaina tuhumar kanki akan abinda yafaru domin kuwa nima banga laifinki ba Allah yariga ya tsara faruwar hakan akaina bayadda zanyi nakaucewa hakan

Dakyar nasamu na lallabata tayi shiru sannan ta kara da cewa bantaba son mijina ba kuma bazan taba sonsa ba ya siye iyayena ne da kudi suka aura masa ni alokacinda nahadu dakai naso narabu dashi dan masamu rayuwa ingantacciya amma bansan taya tasamu labarinka ba haryasa aka kamaka tun daga lokacin da naji ankamaka nake neman hanyar da zanbi na kubutar dakai bansamuba saida nayi amfani da kudi saye wasu daga cikin sojojin mijina suka kubutar dakai

Kuma da alama angane duk shirinsu dan duk wanda sukayi wannan aikin ansamu gawarwakinsu saboda haka zamanka anan gurin gaskiya babu tsaro sole kabar gari nan tadauki kudade masu yawa tabani sannan tabani sabuwar waya tace akwai number ta aciki duk inda naje na nemeta

Da natashi tafiya ban tsaya ko ina ba sai wani kauye agarin katsina garin su wani tsohon abokina da yataba zuwa garinmu almajiranci harmuka saba dashi nasake suna nafara gudanarda sabuwar rayuwa a matsayin dan uwansu zainaba sadeeq tana kirana nima ina kiranta muka sake sabon sabo da juna muka zama daya

Wata rana wannan abokin nawa ya nufo inda make da gudu ya nunamin wani wani mummunan labari da wani sashin labarai suka wallafa “An kama matar ministan tsaron kasarnan wato Aliyu ahmad da laifin kashe mijinta har lahira bayan ya gano tana soyayya da wani matashi

Iya abinda na iya karantawa kenan naji numfashi na yana neman daukewa dakyar nasamu nadawo hayyacina tun daganan narasa nutsuwa ta gani nake koda yaushe za,a iya zuwa akamani ta wani bangaren kuma tunannin zainab sadeeq ahike damuna Allah sarki baiwar Allah an tozarta rayuwarta ta hanyar bata wanda bataso gashi kuma yanzu zata kare a kulle

An saka kudade masu yawa akaina za,a badasu ga duk wanda yakawoni hakan yasa nakasa sakewa da zama agarin gani nake akoda yaushe wano zai iya bada masaniya akaina azo akamani da anokin nan nawa ya fahimci halinda nake ciki sai yabani labarin wasu mutane dake ketare iyakar kasa ta baraunjyar hanya wanda har sukan iya zuwa kasashen turawa sannan yamin alkawarin zai sani a tawagarsu mutafi tare asirrince da zarar sunzo garinsu

Bayan kwana uku ayarin nan dake niyar tsalleke kasa suka iso wannan kauyen alokacin nima na daura aniyar tafiya munyi sallama da abokin nan nawa munkama hanya bamu sha wata wahala ba sosai muka shiga kasar Niger naji sunce yanzu kuma zamu dauki aniyar tafiya kasar ne Libya

Rashin sani yafi dare duhu da ace nasan azabar dake hanyar zuwa Libya dana tsaya a niger kai garama ace nadawo ankamani nasan cewa dama kulleni akayi tafiyace cikin sahara babu guzuri ga zafin rana ga yunwa da kishirya haka muka ahafe kwana hudu daganan karfina yagaza tafiya gashi ba wanda nasani atawagar bawanda yadamu dani gashi suma nasu guzirin bazai ishesu ba ballantana suhada dani koda sukaga zan zame musu nauyi kawai suka yanke shawarar subarni suci gaba da tafiya

Haka suka taxi suka barni acikin zafin sahara ba gida gaba ba gida baya ga yunwa ga kishin ruwa ga gajiya nadama kuwa ba kalarda banyi ba nayi fatan ace ma namutu da wannan wahalar ahaka naci gaba da tafiya bansan inda na nufa ba da wahala tayi wahala kawai jinayi na yanke jiki na fadi

Ban farka ba sai cikin dare ina tashi kuwa naganni akwamce agefena kuma wani mutum nagani fa babbar riga da rawani akansa ya kunna wuta yana zaune agefenta agefe kuma naga rakuminsa a kwance azuciyata nace tabbas wannan buzu ne domin kuwa dukda bantaba ganinsu ba amma nasan labarinsu

Ganin na farka yasa wannan mutumim yanufo gareni yamikomin wani kofi banyi ko tunani ba nayi saurin karbar kofin a hannunsa nakafa kaina nafara sha shayi ne amma maimakon naji zaki sainaji dandanon gishiri ga yaji amma saboda tsananin yunwa da kishin ruwa haka nashanye gaba daya

Yabude jakarsa yadauko min nama da ruwa naci nasha sannan nadawo hayyacina nayi masa godiya sannan nakwashe labarina nabashi yayi matukar tausayamin musamman ma da yaga karancin shekaruna sannan nagayamasa kudirina nazuwa kasar yaso ace ya taimakamin a tafiya ta saidai shima akwai inda yanufa kuma shima guzurinsa yana shirin kare masa

Tafiyace ta kwana biyu tsakanina da shiga Libya ya saitani a hanya sannan ya bani ruwa da abinci naci na koshi nadauki hanya nacigaba da tafiya saida nayi kwana uku nasamu shiga Libya nashigo ba wanda nasani ba wanda yasanni abinda bansani ba shine a lokacin garin yana cikin dokar tabaci sakamakon sani rikici da ya faru na harin ta’addanci abun yabani mamaki da naga bakowa awaje aikuwa ban ankara ba saijin harbi nayi akafa ta nantake nafadi kasa sumamme.

<< Tsaka Mai Wuya 1Tsaka Mai Wuya 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.