Ban farka ba sai kashe gari ina farkawa kuwa sai ganina nayi awani daki mai ban tsoro gawasu mutane akwance ko motsi basa yi gasunan da suffar ban tsoro fuskarsu cike da gemu. Ashe wadanda aka kamane da laifin kai harin ta'addanci tsautsayi ya ritsa nashigo garin alokacin da ake farautarsu aka kamani aka hadani dasu.
Bansan kwana nawa nayi ba amma har tsahon kwanakin ko ruwa basu bamu ba ballantana abinci sai nau'ikan azaba kala-kala, nasafe daban na dare daban. Ana jiran ranar da za'a kaimu a yanke mana hukunci nayi iya bakin kokarina akan. . .