Skip to content
Part 3 of 3 in the Series Tsaka Mai Wuya by Umar bin Ally

Ban farka ba sai kashe gari ina farkawa kuwa sai ganina nayi awani daki mai ban tsoro gawasu mutane akwance ko motsi basa yi gasunan da suffar ban tsoro fuskarsu cike da gemu. Ashe wadanda aka kamane da laifin kai harin ta’addanci tsautsayi ya ritsa nashigo garin alokacin da ake farautarsu aka kamani aka hadani dasu.

Bansan kwana nawa nayi ba amma har tsahon kwanakin ko ruwa basu bamu ba ballantana abinci sai nau’ikan azaba kala-kala, nasafe daban na dare daban. Ana jiran ranar da za’a kaimu a yanke mana hukunci nayi iya bakin kokarina akan nafada musu ni ba dan ta’adda bane amma sunki yarda dani.

Kasancewar ko katin shaida banida shi ballantana fasfo gashi bazan iya bada labarin waye ni ba saboda akasata ma Nigeria bansan irin hukuncinda yake jirana ba akalla zamukai 30 acikin inda ake tsare damu amma saboda yunwa da azabtarwa fiyeda rabinmu sun mutu saboda azaba nikaina saida na amsa cewa ni dan ta’adda ne kozan samu sassaucin azabar da sukemin kan cewa nafadi gaskiya.

Duk da cewa gaskiyar nake fada musu amma kullum ninkamin hukuncina akeyi wai nafadi cewa ni dan ta,adda ne shine gaskiya agurinsu aranarda na amsa laifinda ban aikataba kuwa gari yana wayewa akazo aka daukemu aka kaimu babbar kotun kasar ta li]bya baymtareda bata lokaci ba kuwa aka yanke mana huncin kisa ta hanyar rataya aka tsaida lokacin kashemu sannan akakai ajiyarmu gidan yari.

Nashiga cikin tashin hankali da nadama iri iri nagujewa hukunci akasata gashi mazo wata kasar zan mutu amatsayin dan ta,adda yadda ko Jana,iza bazan samuba ballantana yan uwana suga gawata ina cikin wannan haline har ranar yanke mana hukunci tayi sai a ranar akabani damar yin wanka nafito akaban farar jallabiyya nasaka aka fito dani izuwa ga motar da za,a debemu ina zuwa naga dukkaninmu da irin wannan shigar tawa wato dai kowa da jallabiyya.

Alokacinda aka jeramu nasamu damar irgamu naga mu nawane mu goma sha biyu ne kaf cikinsu kuma nine mafi karancin shekaru haka aka debemu aka wuce damu da rakiyar sojoji mota biyu gabanmu da bayanmu.

Munyi tafiyar kamar sawanni hudu bansan a ina mukeba sai mukaji motar ta tsaya hankalina yayi matukar tashi araina nace to munzo ahikenan kwanana yakare kawai sai muka fara jin karar harbi nayi matukar tsorata nazata kashemu aka fara yi na rufe idona inata zuba addu,a ina jiran azo kaina kawai sai ji nayi anbude kofar motar da muke ciki.

Ina dago kai sainaga wasu mutane da kayan sojoji sun nade kansu da hirami suna mana magana da wani yare wanda nidai bansan me suke cewa ba amma ganin sauran mutanen da aka daukomu tare suntashi sunbisu nima kawai sai nabi bayansu da sauri muka shiga cikin motarsu muka nausa cikin daji

Tafiya mukeyi tamkar zamubar duniya cikin matsanancin gudu muna ratsa daji har muka iso gurin wani katon dutse aka saukemu agurin sannan motar ta kara nausawa cikin daji muna tsaye kawai saiga wani mutum yazagayo ta bayan dutsen wani farin balarabe mai karamin jiki fuskarsa cike da gemu dogo har kirjinsa kansa da rawani yanufo inda muke yana murmushi..

Yana zuwa inda muke yayi mana sallama yafara yi mana magana cikin harshen larabci nidai ba abinda nakeji kawai na tsura musu ido ina kallonsu daga bisani yayi mana iso yawuce gaba mukabi bayansa yanufi bayan wannan dutsen nikuwa araina ina ta tunanin tayaya zamu iya hawa wannan dutse mai girman gaske.

Muna tafiya sai muka iso daf da wani karamin dutse da yake ajikin wannan babban dutsen batareda bata lokaciba kuwa naga suntaru sun turashi abun mamaki suna ture dutsen saiga wata kofa ba tare da fargabar komai ba naga sun kunna Kai ciki nima kuwa nabi bayansu cikin sauri.

Abin mamaki baya karewa muna shiga ta kodar nan sainaga ashe duk hitman dutsen man cikinsa ararake sai kawai na tsinci kaina tamkar awata duniyar ta daban bazaka taba cewa wannan kogon dutse bane gurine unguwa guda da jerin dakuna iri daya ga abubuwan more rayuwa Kala-kala nidai kawai kamewa nayi ina kallon ikon Allah.

Da wani dattijo ya fuskanci halinda nake ciki saiya matso kusa dani yayimin larabci nayi shiru yayimin wani yaren na daban shima dai yaga nayi shiru sai ya tambayeni da turanci yace kanajin turanci nayi masa nuni dacewa eh sannan yacigaba da magana yacedani yaya sunanka ba tareda bata lokaci ba kuwa na fada masa sannan yakara da cewa na fuskanci kamar a tsorace kake ka kwantar da hankalinka babu wanda ya isa ya gano nan wajen.

Yakara da cemin wannan gurin akalla yakai shekara samada dubu biyar tun azamanin wani sarki yasa aljanu suka rarake dutse suka gina masa fadarsa bayan shudewar sarkin bawanda yagano inda wannan gurin yake sai azamanin malaminmu yafadamin sunan wani mutumi da bazan iya tunawa ba yace dani munsamu dukiya maitarin yawa awannan gurin dasu muka sayi makamai muke aiwatarda aikin Allah.

Nace araina ashe ba abanza ba ace yan ta,Adda suna daji ankasa gano inda suke ashe irin wadannan guraren suke samu su buya tabbas ina neman mafaka amma ba irin wannan ba bazan iya zama anan gurinba kuma banga hanyar barin gurin ba na kudirce araina zancigaba da zama amatsayin dan uwansu har zuwa lokacinda zansamu dama nagudu.

Saida nayi kusan wata biyu acikin wannan gurin ina karbar horo kasancewar ni mutum ne me saurin koyar abubuwa saida nafi duk wanda muke karbar horo tare dasu kwarewa haka aka yayemu nafito a matsayim kwamandan su aranar ne kuwa akasa ranar da zamukai wani babban hari akasar ta libya aranar da zamu gudanarda wannan harin ne nasamu damar da nadade ina jira domin kuwa nabarda masaniya akan wannan harin sannan nagudu gaba daya aka kamasu akokarin su na kai harin.

Tun bayan nagudu ne kuma hankalina yakasa kwanciya domin kuwa na tabbatar da cewa wadannan yan ta,addan sai sun nemoni duk inda nashiga sun kamoni kosun kasheni.

Akokarina na samowa kaina mafita abinda yafara fadomin arai shine nasmu labarin ana tsallakawa Europe daga Libya nakuwa yanke shawarar ba abinda yadace da nayi sai na ketara zuwa Italy duk da irin labarin da nasmu na hatsarin dake hanya da yadda zamuyi kwana uku acikin ruwa sannan kuma gani mutum ne me matukar tsoron ruwa amma zuciyata ta kekeshe bana ganin wahalar nidai kawai burina shine natafi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsaka Mai Wuya 2

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.