Skip to content
Part 12 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Kwallin data gama sakama idanuwanta ta ajiye a gefe, ta dauki hula ta saka a kanta, sannan ta mike ta fita tsakar gidan, tana dan kankance idanuwanta saboda hasken da takeji kamar yayi mata yawa

“Sa’adatu…”

Fa’iza da take gyaran kayan miya ta fadi cike da mamaki, kamar ganin Sa’adatu a tsakar gidan shine karshen abinda yake cikin jerin tsammaninta

“Sa’adatu”

Wannan karin Abida ce tayi maganar, sai ta juya tana kallonta.

“Amma…”

Ta amsa muryarta can kasan makoshi, idan ba idanuwanta bane sukeyi mata gizo, sai taga kamar Abidar ta rame, kamar kuma akwai wani yanayi a idanuwanta da yake nuna kamar bata da lafiya

“Zo ki zauna ga kujera…”

Fa’iza tayi mata tayin data karba ta hanyar karasawa ta zauna kan kujerar, dai-dai lokacin da Abdallah ya shigo da sallamar da Sa’adatu ta riga kowa amsawa

“Sa’adatu”

Ya kirata da saurin shi yana karasawa ya tsaya, fuskarshi dauke da murmushin da ya haska har cikin idanuwanshi

“Yaa Abdallah”

Cewar Sa’adatu da sigar gaisuwa, tana dorawa da

“Bakaje makaranta ba?”

Murmushin shi ya kara fadadawa

“Yanzun na dawo, karfe sha biyu saura fa, ko baki duba agogo ba? Lakca biyu nayi…abinci zanci in wuce gareji”

Kai ta jinjina tana rasa abinda zatace masa kuma,duk tarin kalamanta a satikan nan sun bace, tare da wani abu da takejin filin daya bari a cikin kirjinta. Abdallah kuwa ya kasa daina kallonta, satika hudu kenan da juyewar komai, a cikin satikan Sa’adatu tayi na farko ne a cikin dak, akan katifa, a kwance. Bayan ruwan alwala jikinta baiga wani ruwa ba, a rana dakyar yake samu ta mike ta karbi furar da yake siyowa ta sakama cikinta, ranaku biyun farko ma tana gama sha takeyin amanta

“Saki uku ne Amma…saki uku yayi mata”

Kalaman shi suka dawo masa a ranar, bayan sun shigo gida, Sa’adatu ta samu wata kwana a cikin dakin Abida ta zauna, taja kafafuwanta ta hadesu a jikinta da yake ta bari, shikuma ya kama hannun Abida ya jata sun fito tsakar gida, dan tunda suka shiga babu mai natsuwar yin sallama, sai ganinsu tayi sun daga labule, sun sameta tana ninkin kaya, dan duk gyaran dasu Amira sukayi mata, ganin dakin takeyi a hargitse. Kuma gidan daga ita sai su Asma da Jidda, data leka ta ga bacci sukeyi daga sauraren wata dirama a gidan radio, ta kuma san gajiya ce take dawainiya dasu. Shisa ta dinga mamakin su Amira da suka tafi kasuwa, ko dan ita tana so ta juya ne washegari. Abdallah ba zai manta kallon da Abida tayi masa ba da wani yanayi a cikin idanuwan shi, saiya mika mata takardar da take hannun shi

“Ni Tahir na saki Sa’adatu saki daya, biyu, uku”

A tsakanin daya, biyu, da kuma ukun, zaka ga wani bambanci a kowacce kalma, kamar a dayan yaso tsayawa, saiya kara biyu, sai kuma ya kasa hakuri ya kara dayan. Har mamakin yanda yayi hanzarin rike Abida da jiri ya diba yayi

“Inalillahi wa ina ilaihi rajiun…”

Shine abinda take fadi tana sake maimaitawa, har ya jata ya zaunar kan kujera ta kasa furta wani abu bayan wannan. Shi kanshi jirin ne yake neman yin nasara akanshi, ba zaice ga abinda yake rike dashi a irin bugun zuciya da kuma tashin hankalin da yayi masa rumfa ba. An dauki wasu dakika, koma awa, ko awanni, ba zai iya tantancewa ba, Abida dai ta kai hannuwa ta dafe fuskarta dasu, daga yanda jikinta yake bari kuma zai tabbatar maka da kuka takeyi, saiya kauda kanshi gefe, ba zaiyi kuka ba, ba zaiyi kuka ba, yake ta fada a zuciyar shi, idan ya fara kuka kuma Sa’adatu itama ta fara, waye zai lallasheta? Shi yana tsaye, ita tana zaune, duka an rasa wanda zai shiga daki wajen Sa’adatu, kamar yanda aka rasa wanda zai sake cewa wani abu.

Jidda ce ta fara fitowa ta same su

“Me ya faru?”

Ta tambaya tana karasowa ta dafa Abida, data kalli Abdallah saiya kauda kanshi gefe, Jidda tun tana yarinya ko wani ta ga yana kuka itama saita dauka, shisa bata jira amsarsu ba ta fara hawaye tana zama a kasa kusa da Abida ta dora kanta a jikinta. Asma kuwa sarkin tsoro, tana fitowa ta gansu a wannan yanayin saitayi sauri ta koma daki, ta samu waje ta takure zuciyarta nata bugawa

“Shisa fa ni bana son zuwa kasuwa da Hafsatu, saboda wutar ciki, ko ciniki ba zata bari kayi da kyau ba”

Cewar Amira, bayan sallamar Nabila, hannuwanta rike da manyan ledojin da zaka iya ganin sunyi mata nauyi bana wasa ba, ga kuma goyo, da alama duk kayan nauyin ne suka jibga mata, sanin cewa ba zata tabayin mita ba, ko da suna gidan, idan aikensu akayi, duk wani abu da kowa bayason ya rike, Nabila suke mikawa, har Hafsatu da Sa’adatun da suke kannenta, ko magana Abida tayi zatace

“Bakomai Amma, zan dauka”

“Ba dai kingama siyen abinda zaki siya ba?”

Maryam tace don ta gaji dajin mitar Amira, Fa’iza da take bayansu tayi dariya, don ita fadan Amira da Hafsatun dariya yake bata, saida ta tambayi Nabila, don tana son tabbatarwa ba Hafsatu ke bin Amira ba, ko cikin hidimar bikin, suna wanke-wanke saida suka raba hali, Amira ta kwala mata kofi, ita kuma ta fara fadar yanda take da aure da yara yanzun, dole Amira ta fara bata girman da takejin ya hau kanta

“Amma? Lafiya? Me ya faru?”

Muryar Nabila ta kutsa cikin kawunansu tana sakasu maida hankulansu kan Abida, kafin kusan a tare suka karasa kusa da ita sunayi mata rumfa, Nabila ma harta fara hawaye, takardar da take kan cinyarta ta dauka ta mika musu, Maryam ce ta karba tana karantawa, sai take ganin kamar ta kasa fahimtar sakon dake ciki, ga idanuwansu tanaji yana yawo akanta cike da son tayi musu bayani, ganin bata da niyya yasa Amira fisge takardar ta karanta

“Inalillahi wa ina ilaihi rajiun…na shiga uku, Tahir ya saketa? Ya saketa fa nake gani, saki uku? Tahir ya saki Sa’adatu saki uku!”

Ta karasa maganar tana kallonsu da wani irin rudani a tare da ita, sai dai kafin suyi wani yunkuri, Sa’adatu ta juyo karadin Amira ta fito daga dakin Abida tana kare musu kallo. Kusan zatace kamar bacci ne ya soma fisgarta, saboda gajiyar da takeji a ruhinta, kamar wadda aka kwadawa mari haka kalaman Amira suka tasheta, kai tsaye kuma ta ratsa su Nabila ta karasa inda Amira takeyi ta fisge takardar daga hannunta tana dubawa

“Ya sakeni Yaa Amira…saki uku…Yaa Tahir ya raba igiyoyin da aka kulla a tsakaninmu jiya…”

Saita juya wajen Abida

“Amma da bamu wahalar daku ba ashe, kinga har komai ya kare, ya aureni harya sakeni”

Sai tayi wani murmushi mai sauti

“Ya sakeni…”

Ta maimaita a hankali tana mayar da numfashi, sai taji babu abinda take so irin ta kwanta, da tayi hanyar dakinsu, matsa mata sukayi, suka kuma bita da kallo harta shige daki, dan komai ya daina isa kunnuwanta a wannan lokacin, shisa bataji koke-koken dasu Amira sukeyi ba, asalima rufe idanuwanta tayi tana barin duhun da take taji yana tunkarar rayuwarta yayi nasara akanta. Kukan da sukeyi dinne kuma yasa Abdallah komawa dakin shi, ganin zasu karya abinda yayi saura a zuciyarshi. Daya kwanta wani irin kuncine yaji yana naushin kirjinshi, ko rantsuwa yayi ba zaiyi kaffara ba, Asabe na da hannu dumu-dumu a wannan abin daya faru. Ya dauka ta hakura, tunda ta kaddara tafi karfinta, bashi za’a daurawa auren ba, amman tunda ya farka da asubar jiya gabanshi yake faduwa, jininshi yake kan farce har saida suka fito daga masallacin da aka daura auren Tahir da Sa’adatu.

Yanajin duk wata matsala da zata tunkaro shi zai iya daukarta, tunda har aka daura auren nan, tunda Sa’adatu ta samu cikon farin cikinta. Ashe Asabe tana can gefe rike da almakashi, jira kawai take su sauke numfashi ta wargaza musu komai. Ya sha ganin yara sun zamewa iyayensu jarabta, bai taba dai ganin iyaye sun zamewa yaransu jarabta ba sai yanzun, sai akansu da Asabe

“Sannu da zuwa”

Muryar Fa’iza ta kutsa cikin tunanin shi, tana saka shi kallonta

“Nagode…”

Ya iya furtawa cikin wani yanayi daya saka Fa’iza jin inama tana da damar ko da rike hannuwan shi ne, ta dumtsa cikin nata, ta dumtsa, idan ya saka idanuwan shi cikin nata ta fada masa ta fahimta, ta fada masa babu komai, addu’arta iri dayace da tashi, Allah ya yafewa Asabe laifukan da suke tsakaninta da Shi, Allah kuma ya kusanto ranar da Sa’adatu da Tahir zasu ce sun yafe mata abinda tayi musu. Tace masa ya daina boye mata, ya taimaka ya yaye wannan mayafin kunyar da muzantar da ya saka a tsakaninsu tun ranar sadakar bakwai din Asabe har zuwa yau. Tun ranar da Uwani ta shigo gidan a birkice, mayafinta shine ta daura a saman kanta, dankwalin kuma tayi mayafi dashi, takalminta wari da wari ne, idan a hanya kuka hadu, sak mahaukaciya sabon kamu, su kuma a lokacin ne suka fito dan tafiya gida, da yake a gidan Alhaji Salihu ake zaman makokin.

“Kunji wai Asabe ta mutu?”

Shine abinda ta fara fada tana kai hannu ta riko Abida hadi da girgizata

“Baiwar Allah na tabaki da alheri, kinga yau na daga waya na kirata inji ya aka kwana da zancen Tahir, koya saki Sa’adatun, naga bata nemeni ba, shine akace mun ta mutu…mutuwa dai wannan da akeyi”

Kallon juna sukayi

“Duka yaushe mukaje wajen Malam Naketare muka karbo taimakon nan, shi Tahir dinma ne ya kaimu gidan fa, ni na barbada ruwan nan a bakin kofa, suka saukeni, ita ta tafi da wanda zata bashi yasha gida…ashe mutuwa na bibiyarta bata sani ba…ko dai tare take binmu ne ta dauketa saura ni? Jama’a ban kai ga tuba ba, Allah zai yafe mun kuwa? Su Tahir din fa? Asaben fa?”

Sai ta saki Abida, ta nufi taron mazan dake cikin rumfa tana tsugunnawa da nufin yi musu gaisuwa, surutan nan dai ta cigaba dayi. Kuma saboda hankalin kowa yayi kanta, Fa’iza kadai ta kula da Abdallah da yasa danyatsa ya dauke kwallar da ta taru a gefen idanuwan shi, ita kuma kadai taga yanata kokarin hadiye wani abu da alamu suka nuna yayi masa tsaye a wuya. Kafin kuma hankalin su Abida ya dawo kanshi harya fice daga gidan gabaki daya. Ko alamar shi basu gani ba a hanya, tun ranar ya rage hada idanuwa da ita, dan kusancin da take murnar ta fara samu dashine yake nema ya rushe. Batajin kuma zata iya barin hakan ya faru

“Amma ina kunu na da ban sha ba? A bani mu sha ni da Sa’adatu…”

Ya karasa maganar yana shiga cikin gidan sosai inda Abida take zaune tana lissafin kudin cinikin safiyar ranar

“Hajiya Amma, na dawo a sa’a kenan, sai a bani nawa kason in an gama lissafi”

Dariya Abida tayi mai sauti tana daga kai ta kalle shi, tausayinshi ya lullubeta, tun ranar sadakar bakwai, bayan surutan Uwani, har wajen karfe goma na dare bai shigo gidan ba, ta dinga kiran wayarshi a kashe, hankalinta sai yaki kwanciya. Da kanta ta saka hijabi ta leka waje, sai ta ganshi tsaye a kofar gida

“Abdallah? Me kakeyi anan cikin duhu?”

Bata iya ganin shi sosai, tunda babu hasken lantarki, kasancewar ranar an dauke musu wuta tun da yamma. Jin yayi shiru ya sata mantawa da babu takalmi a kafafuwanta ta fita ta kamo hannunshi tana janshi, sai yaja turjiya a soron gidan

“Ka ci abinci?”

Ta tambaya, yanayin yanda yaja numfashi yasa ta gane kuka yakeyi

“Abdallah…”

Ta kira muryarta na rawa

“Ya zan kalli Sa’adatu? Amman ya zan kalleku? Inajin kunya, sosai, saboda so nake in tsugunna akan gwiwoyina in roki ku yafe mata saboda kokwanton da nake dashi akan kwanciyar kabarinta, amman ina ganin idan nace ku yafe mata banyi muku adalci ba…”

Yayi karasa muryarshi na karyewa, data sake riko hannunshi saiya rankwafa yana kwantar da kanshi a jikin kafadarta ta dama, tana jin dumin saukar hawayen shi, itama kukan takeyi

“Ni na jima da yafe mata Abdallah, to me zakayiwa mamaci banda wannan? Shikenan fa, muma lokaci muke jira, kuma zamu so wanda muka batawa su tausaya mana su yafe mana…wallahi na yafewa Asabe duk wani abu da ta tabayi mun, Allah ne shaida ban taba riketa ba, saboda ku, kuma Sa’adatun ma ka bata lokaci, babu abinda ba zata iyayi saboda kai ba…dan Allah karka sa abin nan a ranka…”

Duk da haka kwana biyu baya iya hada idanuwa da ita

“Abdallah ko Margayiya fa ta jima da yafe mun kai, ko ka manta kai nawane tuntuni? Da kuma bai kamata yanajin nauyin mahaifiyar shi ba”

Kasa kawai ya sakeyi da kanshi, saboda hawayen da yaji sunayi masa barazana, da gaskene Asabe haihuwar shi kawai tayi, amman zaice a hannun Abida ya tashi, komai nashi itace, kafin Asabe ta numfasa da fadanta taji damuwar shi Abida taji. Yana kaunar Asabe, kaunar da bai taba tsayawa ya auna girmanta ba sai da yaga gawarta a gabanshi, lokacin ya dinga tunanin lokuttan da gudun fadanta yasa yayi mata nisa, ya dinga hasaso duk wata dama, karama da babba da ya samu na ya zauna suyi hira, ya watsar. Saboda yana ganin yana da lokacin da zai iyayin hakan a gaba, saboda shi din dan adam ne da lissafin mutuwar makusanci yake bacewa. Daya sani kuwa yayita babu adadi, idan ya farka cikin dare, yayi alwala da nufin yin nafila kamar yanda ya saba, da kyar yake iya hada raka’a biyu, saboda a sujjadar farko kuka yake kwace masa, kukan maraicin da ya zagaye shi, kukan duk wani abu da zai zama a rayuwa iyayenshi duka biyun basa nan balle su gani

“Gareji nake son wucewa”

Kallon shi ta sakeyi

“Ba zaka bari kaci abincin rana ba? Wake da shinkafa nakeyi fa…”

Dan sosa kai yayi cikin tunani

“Anya kuwa Amma?”

Jingina yayi da bango suna dan taba hira, kafin yace zai leka waje ya dawo. Dadewar da yayi a wajen ne yasa Abida tunanin koya wuce, dan lokacin daya shigo gidan biyu tayi, tun daga sallamar shi da kuma yanayin sanyin jikinshi yasa ta gane ba lafiya ba

“Alhaji Nura ne ya rasu, ina fita ana fadamun, sai naje muka zauna aka kawo gawar daga asibiti, yanzun ma daga wajen jana’izar muke”

Salati Abida ta saka, idanuwanta na cika da kwalla, babu abinda ya fara zuwa mata sai kirkin Alhaji Nuran, da karamcin shi da zaka jima baka samu ba a tare da mutanen yanzun, musamman idan akace wanda ya hada wannan zumuncin baya raye. Daman ana cikin hidimar bikin Sa’adatu taje dubashi, yanata fama da hawan jini, ta kuma ji yana asibiti, dan akwai yaran shi da suke aji daya da Jidda a makarantar Islamiyya, kawai dai abubuwan da suke kantane da yawa, shisa ta manta. Gashi yanzun jikinta duk ya mutu. Ko abincin da ta zubawa Abdallah ma kadan yaci, yake ce mata ya fasa zuwa gareji, zaije su zauna a karbi gaisuwa dasu. Da Furaira ta dawo kuma, bayan isha’i suka shiga gidan tare, sukayi ma matan shi gaisuwa. Yanayin tashin hankalin da suke ciki, duk saiya famawa su Abida nasu rashin, haka suka hadu suka sha kuka kafin su koma gida.

Ko kadan, daga Abida har Abdallah babu wanda ya kawo tunanin rasuwar Alhaji Nura zata tabasu fiye da jimamin da suka taya iyalinshi, balle kuma Furaira da ba zaman gidan ta cikayi ba, tana can wajen cinikin gwanjonta. Kwanaki arba’in bayan rasuwar Alhaji Nura, babban danshi ya doka musu sallama, Abdallah ma baya nan, sai Abida ce ta fita, da rawar kafa ta dawo, wata irin zufa na biyo kafofin jikinta

“Daman maganar rabon gado ce ta taso, dan a saukewa shi Margayi nauyi…”

Tun kafin ma ya karasa taji wani abu ya daki kirjinta, ta san karshen zancen ba zai wuce su tashi ba, ai kuwa notice dinne suka basu na wata uku. Data kwanta sai taji ciwon kai yana kwankwasa mata kofa saboda tunanin daya hade mata waje daya. Ta ina zasu fara? Yanda gidaje suke wahalar samu ga talakan da kudin hannunshi ba wasu masu yawa bane, idan kuma sun samu sana’arta fa? Tun daga yanda ta amsawa Abdallah sallama yasan babu lafiya, kuma irin tashin hankalin da takeji, shine take gani akan fuskar shi, cike da karfin hali yace

“Bakomai, Allah zai kawo mana mafita, gobe idan Allah ya kaimu zan fara saka cigiya, dan a duba mana ko za’a samu nan kusa…”

Ta jinjina kai

“Zan yiwa Furaira magana, ko zamu sake kamawa tare in tana so, ko kuma in zata kama daban ne dai, ta san halin da ake ciki”

Mikewa Abdallah yasoyi, sai kafafuwanshi sukaqi bashi hadin kai bayan maganar Abida. Baisan yaushe zuciyarshi ta fara kallon Fa’iza a matsayin wani bangare na rayuwarshi ba, harya manta cewa ko yaushe zasu iya barinsu kamar yanda suka same su

Wani abu ne yake neman danne damuwar da yake ciki
Wani abu mai kama da tsoron Fa’iza tayi masa nisa…

<< Tsakaninmu 11Tsakaninmu 13 >>

1 thought on “Tsakaninmu 12”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×