Skip to content
Part 16 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Sa’adatu ta rasa waye ya rarraba sunayen mutane kwatankwacin arzikin da yake tunanin suna dashi. Talakawa, masu rufin asiri, masu kudi, sai kuma attajirai. Ya kamata ace akwai wani wasu sunayen kamar guda biyar a saman attajirai, watakila a cikin wadannan sunayen inta duba zata iya samowa mammalakin gidan da ta kasa yarda tana zaune a cikin shi a halin yanzun. Ashe hasashenta bai kai hasashe ba? A littafi idan akace attajirai, ko idan ana labarin yaran manya irin su Dangote da Bua, ko aka hasko wani sashe na rayuwarsu a kafafen sada zumuntar da takeyi, ta tsaya kallon sutturar da take jikinsu tana misalta kalar rayuwar da suke ciki, duk wannan zai rushe wata rana. Idan ya rushe din harma yasa mata tunanin anya a garin Kano take? Ko sune dai attajiran aka ware musu wani waje na musamman da ake kira da cikin Kano din, amman kuma a wajensu ba Kano bace ba.

Tunda suka karya kwanar unguwar da taji an kira da Sharada, suka nufi wani yanki, sai ta fara jinjinawa karfin halin mai adaidaita sahun da suke ciki, ta dinga tsammanin wasu ma’aikata da suke gadin unguwar zasu iya bullowa a kowanne lokaci su tare su don jin dalilin da zaisa su aikata zunubin shigo musu da adaidaita sahu cikin unguwa irin wannan. Sai da suka wuce wata makekiyar kofa, kamar unguwar ce a kebe a gefe, saboda tunda suka shiga cikin kofar nan taga bambancin da yake tsakanin gidajen da wanda suka baro a baya. Kawar Maman su Haulatu da ta kira kanta da Lami, da tazo gidansu Haulatu aka kira mata Sa’adatun suka gaisa sai ta dora da

“Alhamdulillah, gaskiya kinyi sa’a sosai, saiki shirya gobe idan Allah ya kaimu inzo muje gidan suganki… Za dai ki iya ko?”

Ta kuwa daga kanta, dan bata tabajin wani abu daya shiga ranta irin maganar aikin nan ba. Kasa bacci tayi dan doki, sai ta tsinci kanta dayin sallah tana addu’ar Allah yasa gidan masu kudine sosai. Inda ko bata samu alkhairi da yawa ba, dan gidan zai ganta yaji duk duniya babu wadda yake so sai ita, a kada a raya, mahaifiyar shi taki, sai Baban ya dawo daga kasar waje yace ai abinda Son yake so shi za’ayi. Yanda dai taga yana faruwa a litattafai, tazo bayan auren ya sota kamar ranshi, ita bama sai mahaifiyar tashi ta saduda ba, taje can ta karata, in dai tana cikin daula meye zai dameta? Ko Tahir da zamansu yayi tsayi ba shikenan ba, da yanzun suna nan cikin kwanciyar hankali, Asaben da zata zame musu matsala kasa ta rufe mata idanuwa.

Har mamakin yanda taki barin ranta takeyi, sanda taji mutuwar Asaben, tana cikin nata jimamin, sai daga baya in ta zauna, data fado mata a rai sai taji wani irin yanayi marar misaltuwa, tana tuna rayuwar su tare da abubuwa da yawa. Ko babu Tahir kuma, ko babu Abdallah, wannan rayuwar da sukayi da Asabe, rayuwar da rashin jin dadi yafi dadi yawa, zata cigaba dayi mata addu’ar samun Rahma duk idan ta fado mata a rai. Duk da taso tayi tunanin akwai abinda su Nabila suke boye mata lokacin rasuwar Asaben, amman daga baya kuma ta watsar, tunda meye kuma zai rage da za’ace a boye mata? Idan akwai dinma batajin zai dameta tunda komai ya kare. Yanzun duka hankalinta ta tattara shi wajen gina rayuwarta.

Sai da Lami ta kai hannu ta tabata bayan sun sauko daga adaidaita sahun, ta sallame shi, dan gate din gidan da suke tsaye kawai ya dauke mata hankali. Da suka shiga ciki sai taji kamar tabaro wata duniyar ce zuwa wata da ko mafarkinta bai taba haska mata ita ba, wata irin haraba ce da za’a iyayin shagalin biki a cikinta, daga can gefe tana hangen wata harabar da akayiwa rumfa, motoci ne a ciki, ta dai hangi guda takwas data kirga, da suka karayin gaba kuma taga wasu motocin da ba’a ajiye a karkashin rumfar ba, su daban-daban suke ajiye a harabar gidan. Daga waje dai da suka karasa taga bene hawa biyu, sun kuma taka wata matattakala guda uku kafin kofar da suka jima a tsaye Lami na danna wata yar kararrawa, tukunna akazo aka bude musu, anan bakin kofar suka cire takalmansu.

Kafet ne malale tun daga bakin kofa har karshen ganin Sa’adatu, dan inda duk ta waiga kafet din take gani, tama kasa sakin jikinta ta taka kafet din sosai. Duk yanda ta tsaya tayi wanka, ta fesa turaruka, ga hijabinta ta sha guga, gani takeyi akwai wani sawu na rashin cancanta da kasancewa a wajen da zata iya bari a kan kafet din. A kasa suka zauna, sai da Sa’adatu tasa hannu ta dan taba kujerar dake gefenta saboda tayi mata kyau sosai. Sai kalle-kalle takeyi, idan tace zata tsaya misalta kyawun falon ma bata san ta inda zata fara ba, ta dai san kayatuwar da yayi ya hana mata ganin dadewar da sukayi a zaune kafin wata mata ta sauko, doguwar rigace a jikinta ruwan madara, sai hula da tadan tura baya, zai wahala ka iya kintatat shekarunta, saboda jikinta da yake a murje, ba haske ta cika ba, kwarjini tayiwa Sa’adatu sosai.

Hajiya Hasina, Uwargida a gidan Alhaji Hassan, macen da takeji da iko da isa, take kuma da tsananin son a girmamata, in dai zakayi mata wannan to zakaji dadin zama da ita, abin hannunta bai rufe mata ido ba, gashi bata da wulakanci

“Lami, har an samo yarinyar ne?”

Ta dora akan amsa gaisuwar Lami din tana zama

“Ina kwana…”

Sa’adatu ta fadi muryarta na fitowa can kasa saboda kwarjini da cika mata idanuwa da Hajiya Hasina tayi.

“Wallahi kuwa Hajiya, shine nace bari inzo da ita kigani ko tayi miki…”

Sake gyara zama Sa’adatu tayi tana tattaro duk natsuwa ta yafa a fuskarta, idan Hajiya Hasina tace batayi mata ba ai kuwa da ta gama da ita. Irin wannan gidan ace kana da damar shigowa duk sanda kaso ma kawai alfarma ce, balle kuma ace kana magana da ‘yan gidan, baka da shamaki da kitchen.

“Ai daga ganin yarinyar akwai nutsuwa. Kawai dai bana son karambani ne, aikin da zata dingayi sharar cikin gidan ne da dakuna, mopping, wankin bayi da ‘yan goge-goge sai kuma wanke-wanke…kin fada mata dubu talatin ne albashinta ko?”

Ta fada mata, ta kuma ce mata zata dinga bata dubu biyar ne a ciki, Sa’adatu duk ta amince.

“Ni da zata fara yau ma da zanfi son hakan”

Da sauri Sa’adatu ta amsa da

“Babu matsala zan iya farawa”

Dan so takeyi taga sauran dakunan, taga kalar gadajen da suke ciki ko zasuyi dai-dai da abinda tunaninta ya hasko mata. Ai kam nan Lami ta barta

“Hibba!”

Hajiya Hasina ta kira, daga wani dan lungu yarinyar da aka kira da Hibba ta fito

“Ga sabuwar mai aiki nan, ki nuna mata inda komai yake…fita zanyi, ki kula da komai kina jina?”

Kai Hibba ta daga a hankali kafin ta kalli Sa’adatu da take kallonta, zai wahala idan Jidda bata girmeta ba, ko dan hutu na taimakon yan gayu sosai wajen boye shekarunsu

“Ina kwana…”

Hibba ta gaisheta tana bata mamaki ba kadan ba, kafin ta samu ta amsa ta dora da

“Kizo muje in nuna miki inda ake ajiye komai…”

Mikewa tayi tana bin bayan Hibba, a nutse kuma take kara kallon tsaruwar gidan. Wani dan dakine da aka ajiye tsintsiyoyin shara da su mopper, kamar an tanadi wajen ne don ajiye irin wadannan abubuwan, banda kai babu abinda Sa’adatu take iya dagawa lokacin da Hibba ta cigaba da zagayawa da ita dakunan tana kuma yi mata bayanin yanda “Hajja” tafi son ayi mata komai. Hijabinta Sa’adatu ta cire a dakin da Hibba ta kaita tana fada mata idan ta gama aiki tana son hutawa nan zata shiga, ko idan uzuri ya kamata bayin cikin dakin zatayi amfani dashi. Bata ga daudar da gidan yayi ba, earpiece dinta ta saka a jikin waya ta kunna waka, ta soke wayar a gefen siket dinta ta fara aikin. Duk da a cikin nishadi takeyi bai hanata gajiya ba.

Ba wai dan basa aiki a gida ba, kowa yana kamawa, kuma rabawa akeyi, ita sai taso takeyin nata, tana iya yiwa su Jidda dadin baki su hada suyi da nata kason. Babu ma abinda yafi gajiyar da ita irin mopping din, sai gata tana maida numfashi kamar wadda tayi gudu, abu kamar wasa sai ta samu waje ta zauna, kugunta da wani kashi a gadon bayanta take ji suna amsawa, wakar da ta saka daman tuni ta kasheta, ta zaro wayar daga kugunta tana samun waje ta ajiye. Dakyar ta samu ta karasa, wani wajen ma da taga babu kurar da yayi saita goge sama-sama. Ita da ta hango ta karasa aikin ta koma dakin ta kunna talabijin din da ta gani a ciki, sannan tabi lafiyar gadon, sai gashi kwanciya kawai tayi tana tunanin wannan na daya daga cikin dalilin da yasa su Abdallah suka dinga mata dariya, gashi tun yau tana jin kamar idan ta tafi gobe ba zata dawo ba. Tana nan kwance bacci ya soma fisgarta taji an kwankwasa kofar kafin a turo a hankali.

Hibba ce hannunta rike da filet, ta karasa cikin dakin tana mika mata

“Bansan ko kin karya ba, kici wannan kafin a gama abincin rana…”

Tashi zaune tayi ta karba

“Nagode…”

Ta furta idanuwanta akan abinda yake cikin plate din, dankalin turawa ne da akayiwa wata irin suya da bata taba gani ba, sai plantain, itama gata dai plantain ce, amman nade take a jikin kwai da ya sha yankakkun kayan miya. Harda nama mai hade da wata miya-miya a gefe, ta kuma saka mata cokali mai yatsu a ciki. Har Hibba ta fita kallon filet din Sa’adatu takeyi. Abinci mai dadi na daya daga cikin manyan dalilan da yasa take son kudi, take son tayi rayuwar jin dadi. Yanzun ace kullum ne zata dinga samun irin wannan anya akwai wani abu da zai bata mata rai kuwa? Idan ma ran nata ya baci saita fasa kwai ta soya taci taji dadi, ta dafa kaza tayi farfesu ko ta soya ta barbade da yaji ga lemo mai sanyi a gefenta. Ta caki nama yanka daya da cokali ta kai bakinta, kawai Tahir ya fado mata, wani yanayi ya kawo mata mamaya yana sa ta kasa jin dandanon naman da take taunawa.

Numfashi taja a hankali tana fitarwa, tayi hakan wajen sau biyar kafin ta samu ta dawo dai-dai. Ta rasa dalilin da zaisa sai tana cikin nishadi sai kawai ya fado mata yana dagula komai. Sai dai ta kasa cinye ko da rabin abinda yake cikin filet din, da yawa Hibba ta zuba mata, kuma gashi bata tare da yunwa, dan saida taci abinci kafin su fito daga gida, ajiyewa tayi da niyyar ta samu leda in zata tafi saita juye abinta. Anan tayi sallar azahar, harma da la’asar, abincin da aka bata da rana sai da yayi matukar bata mamaki, abinda bata sani ba shine har masu gadi irin abincin da aka basu kenan, kwata-kwata basa bambanta abinda zasuci da kuma wanda ma’aikatansu zasu ci. Idan shinkafa ce to kowa shinkafar zaici harda nama kuwa akai, wasu ranakun ma Hajiya Hasina zatace kowa a daukar masa lemo mai sanyi a hada masa dashi.

Tayi wanke-wanke mai yawa dai, da tayiwa Hibba magana ko zata samu leda, kallonta tayi da wani yanayi a fuskarta

“Leda?”

Kai Sa’adatu ta jinjina mata

“Zan juye sauran abincina ne da ban cinye ba…”

A cikin kitchen din ta duba ta dauko mata wata roba mai murfi, me kyau sosai

“Ki dinga zubawa anan…bari in dubo miki yar jakar da zaki saka a ciki”

Robar ta cika taf da abincin nan, har saida ta danna da murfin kafin ta iya rufewa, wata yar jakace da hoton jaririya mai kyau, kamar ta suna ce da aka raba, godiya Sa’adatu tayiwa Hibba da ta mika mata dubu daya

“Hajja tace a baki ki hau mota.”

Sosai take mamakin wanne irin mutane ne su masu kirki da haka, ashe masu kudin ba duka bane suke da wulakanci kamar yanda take gani a litattafai, akwai masu kudin da suka san darajar mutane. Sallama sukayi da Hibba bayan ta karayi mata godiya, tukunna ta fice daga gidan, a hankali take tafiya, tana jin wata irin gajiya na saukar mata. A harabar gidan taga wani matashi ya fito daga mota cikin shigar shadda tana ta daukar ido kamar hular kanshi, daga inda take tana jin kamshin da yakeyi

“Ina wuni”

Ta tsinci kanta da furtawa, ya kalleta da mamaki kafin ya danyi gajeran murmushi yana amsawa da

“Lafiya kalau. Nagode…”

Ya wuceta zuwa hanyar da zata sadashi da cikin gidan, itama tafiya ta cigaba dayi tana nufar gate din gidan, aka bude mata karamar kofa ta fice. Sai dai data tuna tafiyar da zataci kafin ta karasa titin da zata iya samun abin hawa sai taji idanuwanta sun cika da hawaye saboda gajiyar da take ji, tunanin anya zata iya wannan aikin ya sake dawo mata, lokacin da taci tafiya ta wajen mintina ashirin saboda yanda take jan kafa kamar bataso sai ta tabbatar da bakinta dole ya hakura da kayan dadi, jikinta ba zai juri wannan wahalar ba. Ji tayi an danna hon din mota da karfin gaske, taja siririn tsaki tana juya idanuwanta, tunda ta san ba akan hanya take ba, asalima mota nawa ta wuceta, babu wanda ya danna mata hon, tafiya ta cigaba dayi aka sake danna hon din, sai ta juya taga wanne isashe ne ba zai barta taji da abinda yake damunta ba. Data juya sai taga mota ruwan toka, kirar Hilux, irin motar da saurayin nan ya fito daga ciki dazun.

Daya zage gilashin kuwa sai taga shine

“Ina zakije?”

Ya tambaya, wani yanayi da taji a zuciyarta sai da hawaye ya fara mata barazana

“Bachirawa…”

Dakuna fuska yayi

“Bachirawa”

Ya maimaita kamar yanayin shi nason nuna mata ko da ya tabajin sunan baisan inda unguwar take ba

“Ki dai shigo in rage miki hanya saiki karasa.”

Ai da saurinta ta karasa wajen motar tana zagayawa ta dayan bangaren, sai dai wata budurwa ta gani a gaban zaune tana danna wayarta, fuskarta akwai facemask daya hanawa Sa’adatu ganinta sosai, ko motsi kuma batayi ba balle alamar zata dago da kai, cikin sanyin jiki Sa’adatu ta matsa tana kai hannu jikin murfin motar ta bude bayan, yana zaune, ya kwantar da jikin shi sosai a cikin motar, a hankali ya juyo yana bude idanuwanshi da suke cike da bacci akanta, sai taji kamar wata guguwa ta taso tare da idanuwan nashi daya bude akanta, karfin iskar na shirin mayar da ita baya, kamar kuma iskar ta hado da kasar da taji cikin idanuwanta tana hana mata samun abu daya da zata iya dorarwa na kamannin shi. Zuciyarta sai dokawa takeyi, haka kawai jikinta ya fara rawa a hankali, dakyar ta iya shiga cikin motar tana zama a dadare, ta rufo murfin. Tazarar da take tsakanin inda take zaune dashi wasu mutum biyu ma zasu iya zama, amman a takure take jinta.

Bugun da zuciyarta takeyi nasa bakinta kafewa, a hankali take son kallon shi ta kasan idanuwanta, amman bata ganin komai sai bakin wandon da yake jikin shi, rigar shi ruwan toka mai dogon hannu. Babu mai magana a cikin motar, shirun ma sai ya kara mata bugun zuciya, har suka fita titi jikinta rawa takeji yanayi

“Ga ATM babu kowa…”

Cewar saurayin da yake tukin

“Jay…ba zaka cire kudi ba?”

Ya sake fadi yana dan sauka gefen titi batare daya kashe motar ba

“JB…”

Ya kira yana dan juyowa, motsi JB din yayi a hankali yana jan karamin tsakin da yake nuna an takura masa

“A’a sai in wuce idan ka fasa, kawai dai ba zan sake tsayawa bane ba…”

Sake motsawa yayi, yana laluba aljihun wandon shi

“Ka ciromun dubu ashirin zan maka transfer…”

Muryar shi ta daki kunnuwanta, a hankali yayi maganar, amman muryarshi a bude take da wani abu da ya wuce baccin da yakeyi. Macen da take gaba ce tayi dariya

“Ban fito da ATM card dina bane Hamma…dan Allah ka ciromun

Budurwar ce ta sakeyin dariya

“Hamma Deeni yana magana fa”

Harara Deeni ya watsa mata yana taka motar ya hau titi

“Ba zaka ciromun ba?”

JB ya fadi yana matsawa ya zura kanshi gefen kujerar da Deenin yake

“Matsa kafin in saukeka anan”

Komawa JB yayi yana gyara zaman shi, Sa’adatu na gefe kamar ruwa ya cita, ko numfashi kadan-kadan takeyin shi, sai dai ko inda take JB bai kalla ba, har kuma Deeni ya sha wani round yana sake tsayawa yace mata

“Bari in saukeki nan, saiki samu adaidaita…”

Saida ta bude bakinta sau wajen hudu kafin ta iyayi masa godiya can kasan makoshi tana bude murfin motar ta sauka, wajen rufewa ne JB ya dan juyo da kanshi yana saka idanuwanshi a cikin nata, da sauri kuma ta rufe murfin motar, tana sake rike yar jakar da take hannunta

Ta gan shi
Ta san bata san shi ba
Amman tana jin wani sashi na zuciyarta ya gane shi
Bata san bakomai bane take ji sai kama da ya yi mata da kaddararta.

<< Tsakaninmu 15Tsakaninmu 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×