Skip to content
Part 19 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Alhaji Hassan Paki dan asalin karamar hukumar Paki ne da take jahar Kaduna. Kasuwanci shine sana’ar gidansu, kuma ko da ya tashi yaga yanda wannan kasuwancin ya watsa ‘yan uwanshi gari-gari a cikin Najeriya, inda wasu kasuwancin ya zame musu sanadin ketarawa kasashe domin karfafa shi, shi daya ketara kasar Ingila a wancen lokacin karatu ne ya kaishi, in da yayi digirin shi ta farko da ta biyu kafin ya dawo ya tsunduma harkar noma, kasancewar fannin daya karanta kenan. Yayi mamakin yanda ‘yan uwanshi suka bashi goyon baya dari bisa dari, ta hanyar bashi shawarwari, da kuma hadashi da manyan mutanen da suka sani ta hanyar kasuwancin su. Hankalin shi yafi karkata wajen noma shinkafa, da kudin gadon shi da ribar daya samu ya fara siyo injinan shi na sarrafa shinkafa. Ko da sukayi masa maganar aure baiki ba, dan yana da niyyar, akwai Hajiya Hasina da Allah ya hadasu ta sanadin ‘dan uwanta da yake babban amini a wajen shi.

Ba’a wani bata lokaci ba akayi komai, duk da da yawa a cikin ‘yan uwanshi suna ganin kamar bata dace dashi ba saboda irin arzikin gidansu, duk da shima Alhaji Hassan din harka ta fara bude masa, kuma ba’a cikin talauci ya tashi ba. Kawai dai a lokacin idan ana lissafa masu kudi a garin Kaduna to fa zai wahala a lissafa goma mahaifin Hajiya Hasina baizo a na sha daya ba. Cikin shekaru biyar ya zamana in dai shinkafa ce ta gida, mai kyau da inganci, to a wajen shi duk wasu yan kasuwa suke sari a garin Kaduna, da yaga yanda komai yake tafiya cikin nasara a garin Kaduna saiya fara ketarawa Kano inda duk wani tushe na kasuwanci yake, kusan za’a ce ya shiga Kano da kafar dama, kuma sanin abinda yake so da duk wani tsare-tsare sai bai wahala ba, dadin da garin yayi masane yasa shi samun gida ya siya. Hajiya Hasina batayi mamakin ganin ya siyi gidan mai bangaren biyu ba, ko da wasa bai taba nuna mata alamar zai zauna da ita kadai ba.

Cikin shekarar kuwa ya karo aure inda ya auri Hajiya Shafa, jin kai da ki fadi irin na Hajiya Hasina yasa ta danne duk wani kishi ta bashi goyon baya akan auren, su kansu dangin Hajiya Shafa da suka kawota da niyyar yada maganganu irin na mata don su turawa Hajiya Hasina haushi sai suka kasa, ganin ‘yan uwanta da irin shigar alfarmar da sukayi, ga hidima tun daga kan abinci da abin sha da ake tayi dasu. Sai jikinsu yayi sanyi, suka koma yiwa ‘yar uwarsu fadan ta zauna da ita lafiya dan ba sa’ar kishinta bace, dan alamu sun nuna ita bada arzikin miji kawai take takama ba. A lokacin Hajiya Hasina ta haifi Babangida da Farhana. Sai dai lokacin da Hajiya Shafa take ta murna arzikin mijinsu ya karu, ya bude rassa kanana na wasu kasuwancin, zasu sake sabon gida, sai duk murnarta ta koma ciki lokacin da labari yazo mata na cewar zai kara aure. Nan fa ta tashi hankalinta

“Kinji labari Alhaji aure zai kara?”

Ta samu Hajiya Hasina da maganar

“Banma jiba, Allah ya tabbatar da alkhairi”

Mamaki ne ya kusan kasheta ganin halin ko in kula da Hajiya Hasina ta nuna

“Haka akace fa yarinyar sadakar yalla ce, me zaiyi da sadakar yalla? Yanzun haka ma ba haka ta barshi ba, kin sansu da neman asiri”

Banda

“Allah ya kyauta”

Hajiya Hasina bata sake cewa komai ba, saima taja girar sama data kasa ta tsuke, Hajiya Shafa ba zatace suna zaman arziki da Hajiya Hasina a shekarun nan ba, ba kuma zatace suna zaman tsiya ba, yanda duk tayi kokarin ganin ta shige ma Hajiya Hasina sam bata samu fuska ba, dan ta kula tana da ji da kai kamar wadda ta hada jini da gidan sarauta. Kawai dai bata taba hana yaranta shiga bangaren Hajiya Shafar ba, haka itama nata yaran suna shiga can, idan abin jaje ko murna ya faru kuma Hajiya Hasina na shiga har bangarenta tayi mata, kuma zata kirga sanda ta taba zuwa mata wani biki ko suna, jajen rashin lafiya dai ko gaisuwar mutuwa tana kokarin zuwa duk da bata jimawa. Sai dai har ranta ta dauka wannan karin Hajiya Hasina zata ajiye wannan girman kan nata su kashe su binne tunda maganace data shafe su, magana ce ta karin auren da mijinsu zaiyi, kuma ma sadakar yalla, idan ta shigo duk ta fitar dasu daga gidan fa?

Amman Hajiya Hasina ta nuna bata damu ba kwata-kwata. Ko da suka koma sabon gida, hankalin Hajiya Shafa ba karamin tashi yayi ba, ganin irin dukiyar da aka narka a gidan, da kuma ganin bangare har hudu, nufin Alhaji Hassan saiya cike su hudu zai hakura da karin aure kenan? Aikuwa ko da yazo ya fada mata batun karin auren da ta riga taji a gari, fada sukayi, wani irin fada da basu tabayin irin shi ba

“Idan ba zaki zauna ba, ga hanya nan saiki fice, amman banga dalilin da zaisa ki dagamun hankali dan zan kara aure ba, inace da matata a gida sanda na ganki na auro, mutuwa kikaga tayi? Ko nace miki ta dagamun hankali?”

Ganin da gaske aurenta na shirin yin rawa yasa ta ajiye makaman yakinta, ta rungumi hakuri yanda Hajiya Hasina tayi, sai dai ta kasa samun natsuwa sam, gani takeyi da shuwar nan ta shigo zata iyayin asiri ta rabata da gidan mijinta. Tayi mamaki, ta kara mamaki da tasa aka bincika mata yarinyar, ta kuma saka a ranta idan ba asiri ba babu yanda za’ayi Alhaji Hassan ya auro musu yarinyar da akace asalinsu ma babu wanda ya sani, gudun Hijira sukayo zuwa Kano, kuma gadi babanta yakeyi, mahaifiyarta ma aikatau takeyi kafin ta rasu wajen haihuwa, ance mahaifin nata bai kara aure ba, kuma tazo wajen shine a gidan abokin Alhaji Hassan inda yake gadi, anan ya kyalla ido ya ganta. Sai dai bayan bikin, da ta ga yarinyar da ba zata wuce shekaru ashirin da biyu a duniya ba mai suna Kausar, sai ta koma bangarenta jikinta a sanyaye.

Tunda take, tanajin labarin mutanen da ake cewa kyau kamar su sukayi kansu, da tayi tozali da Kausar sai ta ga labari kuma ya kare, a maimakon ace kyau kamar mutum yayi kansa, kawai a dinga misali da Kausar, ace kyau kamar Kausar. Kyawun da yanzun ta tabbata shine abinda yaja mijinsu babu wani asiri. Idan ma ya juya musu baya tabbas ba zata ga laifin shi ba, ta tabbata inda Kausar cikin gatanta take, ba tazo a yar gudun Hijiri ba, to ba kananun kudi Alhaji Hassan zai narkar ba kafin ya iya mallakar mace kamarta, idan ma sun bashi ita din kenan. Ita kanta Hajiya Hasina da take ganin zuwa yanzun ta kai matsayin da kishin Alhaji Hassan zai daga mata hankali, yaransu uku ga cikin na hudu nan, meye zai dameta? Hajiya Shafa ma ta zame mata jiki zuwa yanzun. Amman da Kausar ta shigo bangarenta dan ta gaishe da ita sai da zuciyarta ta buga.

Ita din kyakkyawa ce, tun kafin ma samarin da suka dinga layi a gidansu su fara jaddada mata ta sani, tana kuma ji da wannan kyawun nata, musamman da take ganin shi hade da hasken Alhaji Hassan a fuskokin yaranta. Sai dai tasan inda su biyun fitilu ne, hasken Kausar ko daya bar kusa da ita, za’a jima ba’a ga kyallin nata ba, kishin data dauka ta binne ya taso yayi mata wata irin tokara a kahon zuciya. Bata taba zaton zatayi farin ciki har hakoranta su bayyana ba sai da shekara ta zagayo Alhaji Hassan ya cike su hudu da Hajiya Umma, tayi murna, ta kara murna ganin kyawun Kausar bai isa rufe zuciyar shi da idanuwan shi daga hangen wata ba, kuma sai farin cikin nata ya karu ganin su duka ukun ma sunfi Hajiya Umma kyau, tana dai da dirarren jiki da hasken fata, amman bata da wani abu da zata nuna musu.

Saida Kausar ta shekara biyu a gidan tukunna ta samu ciki, wani ciki da tunda ta same shi batayi lafiya ba, duk rashin imaninka idan kaganta saika tausaya mata, fuskar nan tayi fayau sai dogon hancin. Cikin dare nakuda ta kamata, lokacin Alhaji Hassan yaje Kaduna, yar aikin Kausar ce ta bugawa Hajiya Hasina kofa ta fita, halin da taga Kausar din a ciki saida tayi kwalla, nan tasa aka fito da mota suka tallafo kausar din suka nufi asibiti. Haka ta kwana tana abu daya, washegari Alhaji Hassan ya dawo, har yamma Kausar bata haihu ba, ya saka hannu kenan don ayi mata aiki a ciro yaran da suka jima da sanin guda biyu ne akace ga shi can ma ta haifo daya, namiji, cikin ikon Allah ba’a rufa mintina talatin a tsakani ba ta kara haifo yarinyar da ko awa batayi ba ta koma saboda wahalar da ta sha, itama Kausar din sai fama akeyi jini yaki tsayawa.

Daga Alhaji Hassan har Hajiya Hasina hankalinsu ba’a kwance yake ba, ita dai banda ruwan shayin da aka kawo bata iya saka komai a cikinta ba, yanzun ma ruwa taje siyowa ta dawo ta samu Alhaji Hassan tsaye da jariri a hannu da kuma wani yanayi na dimuwa a fuskar shi

“Ta rasu, sunce itama ta rasu”

Ya fadawa Hajiya Hasina da ruwan robar ya subuce daga hannunta saboda kaduwar da tayi, lokaci daya kuma hawaye ya wanke mata fuska, ita dai rayuwar mace a kowanne mataki cike take da hatsari, sanda take gaban iyayenta hankalinsu ba’a kwance yake ba, saboda hatsarin lalacewar tarbiyarta, basa taba samun natsuwa sai sunga sun aurar da ita. Idan kuma tayi auren ta fara fuskantar wata rayuwa ce ta daban, lokacin da zatayi ciki ta shiga wata duniya mai mata maraba da juyo kamshin zama uwa sai ta dinga jin duk duniya babu wanda ya kaita sa’a, lokacin da nakuda zata kamata sai ta fuskanci irin hatsarin da kowacce uwa take saka kanta kafin ta amsa sunan uwa, yanzun dai ga Kausar nan, ta amsa sunan uwa a yau, ta kuma koma ga mahaliccinta batare da ta rike abinda ta haifa din bama. Kaunar nata yaran ya tsirga mata, tunanin itama zata iya barinsu ya kara mata firgicin mutuwar Kausar.

Da Alhaji Hassan ya mika mata yaron karbar shi tayi tana rungume shi cike da tausayawa. Haka suka dawo gida akayi jana’izar Kausar, mahaifinta ne kadai ya rage mata a duniya, shima kuma ana fada masa rasuwar ya yanke jiki ya fadi, har aka dawo daga kaita ma baisan wake kanshi ba. Wannan faduwar da yayi kuwa ko da ya farka bai kara lafiya ba har Allah ya dauki abin shi. Hajiya Hasina zatace duka yaranta an kama mata wajen rainonsu, masu aikinta suke tayata sosai, amman yaron Kausar da yaci suna Jabir, tunda Alhaji Hassan ya mika mata shi a asibitin nan batajin ko bacci ya rabasu, ko da Alhaji Hassan ne a bangarenta kuwa, dan gadon shi na jarirai yana gefe, da ya motsa zata tashi ta duba shi. Tayi takaicin yayen da tayi sanda aka haife shi, da ta shayar dashi ba’a dinga bashi wannan madarar ba.

Wata irin kauna da tausayin shine ya samu waje yayi mata zaune a zuciya, kamar batayi kishin mahaifiyar shi ba. Su duka sun dauka Alhaji Hassan zai kara aure bayan rasuwar Kausar, sai ya basu mamaki, suka cigaba da tafiyar da rayuwarsu a haka. Fadar irin cigaba da kuma arzikin da Alhaji Hassan yayi kafin rasuwar shima bata bakine. Lokacin daya rasu Hajiya Hasina na da yara bakwai tare dashi. Babangida, Farhana, Ibrahim, Anwar, Mannir, Badiya da kuma Hibba. Sai dai ita yaranta takwas, haka take fadi, a cikin lissafin yaranta harda Jabir, da ta fada masa ba ita ta haife shi bane dan ya dinga yiwa mahaifiyar shi addu’a, kuma ga kamannin shi ma da suka bambanta, sannan bataso yaji a bakin wani, gara tayi masa bayanin yanda duk da bai fito daga jikinta ba tana kaunar shi kamar yanda take kaunar yaranta, duka yaran suna kiranta da Hajja.

Sai Hajiya Shafa da suke kira da Mama, tana da yara biyar, Mus’ab, Jamal, Deeni, Abbas sai Surayya. Hajiya Umma kuma Anty suke ce mata, ita tana da yara hudu, dan gwarne ta dingayi ma, har saida sukai mamakin lokacin da haihuwa ta tsaya mata daga yara hudu kawai. Zaid, Suraj, Aliya sai Auta Zaitun. Ba’a wani bata lokaci ba wajen raba musu tarin dukiyar da Alhaji Hassan ya bari, kowanne yaro kuma ya mallaki tsabar kudade da kaddarori, hakama matan shi, gidan da Hajiya Hasina take ciki yanzun yazo ne a gadon nata yaran, sai suka koma can. Sai dai shakuwar da take tsakanin yaran yasa ko iyayensu suka kasa hanasu bin Hajiya Hasina, itama kuma bata da zuciyar da zata shiga tsakaninsu da ‘yan uwansu kawai dan mahaifinsu ya rasu. Kowa yana da daki a gidanta in dai kana son zama, in suka bushi iska zasu tafi wajen iyayensu, basa daukar lokaci kuma suke sake dawowa.

Gidan Hajiya Hasina ya zama wata dabdala ta dangi saboda kirkinta da kuma yanda abin hannunta bai rufe mata ido ba. Macece mai kyauta da son kyautatawa duk wanda zai rabeta, hatta masu aiki a karkashinta ma yabon halayenta sukeyi, saboda tasan darajar mutane sosai. Kamar yanda in dai zata lissafa yaranta Jabir yake zuwa a farko, haka shima a wajen shi, itace komai nashi, yanda take matukar kaunar shi da jin tausayin shi, haka ta koyawa ‘yan uwan shi kaunar shi da tausaya mishi, yanda ya taso cikin wani gata da bai taba neman wani abu ya rasa ba, ya kuma tashi da tsammanin duk wanda ya rabe shi to har abada shine zai kasance cikin sadaukarwa a gare shi, wannan ne tunanin da Hajja ta dora shi akai.

“Kai saika hakura tunda shi Jabir yake so”

Maganar Hajja kenan idan an bawa kowa abu ya kyalle ido akan na ‘dan uwan shi yace shi yake so, idan ma ya saka rigimar duk biyun zai hada to fa haka za’a bar masa dole

“Ku kula da Jabir, kuji tausayin shi, bashi da kowa a duniya saiku, kuna ganina da dangina ga dangin Abbanku, bayan dangin Abbanku, Jabir bashi da dangi irin na bangare na, a duniya bashi da wani da zai kira nashi sama daku…”

Wannan hudubar ta zauna musu daram, ta kuma saka in dai akan Jabir ne to su din masu sadaukarwa ne da duka zuciyoyinsu, ba kuma yaran Hajiya Hasina kadai sukeyiwa Jabir irin wannan makahon son ba, har sauran ‘yan uwan shi da duke uba daya. Ko a makaranta hukunci ba kasafai yake bi takan Jabir ba, dan Hajiya Hasina ta taka kafafuwanta har makaranta taji dalili bakomai bane ba. A dalibai yan uwan shi kuwa waye ya isa ya taba Jabir Hassan Paki? Idan ‘yan uwanshi suka sakaka a gaba sai makarantar duka ta fita daga ranka. Daga shi har ‘yan uwan shi gani sukeyi babu wani abu da Jabir zai nema ya kasa samu a fadin duniya dai in har suna raye, ko da wasa basu taba tunanin akwai ranar da zata zo su kasa kare Jabir daga wani abu ba, ranar da zata zo tarin dukiyar su ba zai musu amfanin komai ba, a karo na farko da suka koma gefe suna kallon Jabir yana kokawa da kaddarar da basu isa su taya shi daukar nauyinta ba.

<< Tsakaninmu 18Tsakaninmu 20 >>

4 thoughts on “Tsakaninmu 19”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×