Hannunta rawa yakeyi, dakyar ta iya tattaro natsuwa ta saka hannu a jikin takardar da ko karantawa batayi ba, kafin ta fito daga gida saida ta fadawa kanta saita karance duk wata takarda da Aisha zata bata kafin ta saka hannu. Ta gama nata tsarin kamar yanda taga alamun sun jima da gama nasu, to me tayi ma a kwanaki takwas din nan idan ba tsare-tsaren ba? Aikine akwai masu kamawa sosai, sai kuma goyon yaron da takeji kusa da zuciyarta, ko ba don sunan Habibu da aka mayar masa ba suna kiran shi da Abba, jinin Abdallah ne. Dole ma taso shi, shima yanzun ya shiga cikin lissafin mutanen da take so ta zama sanadin canzawar rayuwar su, in dai yayi kuka, ba dai na rashin wani abu bane ba. Sosai taji natsuwa ta shigeta, har wani nishadi na daban take ji lokacin da ta shiga adaidaita sahu, musamman da iska ta dinga kadata, hijabi ne ta saka dogo kan riga da skirt din da yake jikinta sai yar karamar jaka da ta saka wayarta, earpiece da kuma kudi a ciki.
Banda man lebe, fuskarta fayau take. Cike da karsashi ta gaisa da maigadin tana shiga cikin gidan, ta kwankwasa, taji Aisha tace mata ta shiga, da sallama ta shiga, zuciyarta ta buga, ta sake bugawa kafin taji tayi kasa tana neman inda tayi ta rasa, ko kadan bata tsammaci harda shi ba, ta dauka Aisha ce ita kadai, rigace a jikin shi ruwan madara mai dogon hannu, kamar ta sanyi, tana da fadi sosai, dan bata kama shi ba, sai wani bakin wando, Aisha na zaune a gefen shi, sunyi kyau ba kadan ba, sai kamshi falon yake na turaren wuta da kuma nasu daya gauraye ya bada wani tsadadden kamshin da gidan yan gayu masu kudi irinsu ne kawai zakaji irin kamshin. Kafarta har rawa takeyi lokacin data karasa cikin dakin tana gaishe dasu bayan ta zauna a kasa kan kafet maimakon kujerar da Aisha ta nuna mata.
Gabaki daya ta daburce, ga wani dumi na daban da taji jikinta ya dauka, kamshin dakin a gauraye yake, amman sai takejin kamar hancinta na zuko mata wani kamshi da zuciyarta ke ce mata na turaren Jabir ne, sai ta sake rikicewa
“Banajin akwai wata sauran magana da bamu rigada munyi ba Sa’adatu, ga takardar da zaki saka hannu nan”
Kara matsawa tayi wajen teburin, data saka hannu ta janyo takardar da biron gabanta, kawai saita daga kanta, ta kuwa sauke idanuwanta cikin na Jabir da ya kafeta da nashi, da sauri ta sauke nata tana kallon takardar da rubutun jiki ya hade mata, a lokaci daya kuma ko’ina na jikinta na rawa. A gefe daya kuma kirjin Jabir ne yaji ya buga, daga jikin wannan yarinyar da alamu suka nuna da wahala idan ta wuce shekara sha takwas dan shi ko yar shi zai fito? Zata iya? Anya tama gama fahimtar abinda suke so daga wajenta kuwa? Wani sashi na zuciyar shi yace ko bata gama fahimta ba in dai ta saka hannu shikenan, in dai zasu samu biyan bukatarsu shikenan, amman ya kasa dauke idanuwan shi daga kanta, hannunta da take rike da biro yake kallo, ta sha jan lalle da ya turu sosai, yatsun dogaye, sai lokacin ya dauke idanuwan shi daga kanta yana mayarwa kan Aisha, nata hannun yake kallo, yatsunta, ko a cikin mata nawa, aka rufe masa ido aka ce ya rike hannayensu, to tabbas yana rike nata zai ganota, duk wata tsaga da take jin hannunta ya gama haddacewa, amman yau saiya tsinci kanshi da kallo yana so ya auna tsayin su dana Sa’adatu.
“Kina da account?”
Aisha ta tambayeta bayan ta saka hannu ta ajiye biron, kai ta daga mata, Tahir ya sakata budewa lokacin, har atm tana dashi, sau biyu dai ta taba amfani dashi, kuma kamar ma in bata manta ba akwai ragowar yan kudi a ciki duk da basu da yawa
“Yawwa to ki turomun ta text, ko ya ake ciki zamuyi magana”
Kai Sa’adatu ta sake jinjinawa, tana samu ta mike, dan haka kawai jikinta gabaki daya babu karfi take jin shi, ko sallamar da tayi musu a sanyaye ta fito.
“Ki tsaya Jay zai kaiki saiya ga gidanku”
Maganar Aisha ta daketa kamar an watsa mata ruwan kankara, sai taji yanzun ba jikinta bane kawai yayi sanyi, har kasusuwanta ma a sanyaye suke, gwiwoyinta kuwa kamar an buge mata su da icce haka takejin su. Ta gabanta shi da Aisha suka wuce, dakyar ta iya bin bayansu har wajen motar, da Aisha bata bude mata gabanba, to tabbas da ta diririce ta rasa inda ya kamata ta shiga
“Ba zaki zo muje tare ba ko?”
Jabir ya fadi yana kallon Aisha, duk da ta gefen Sa’adatu take, kuma ta nan ya juyo yana maganar, ko da wasa idanuwan shi basu bi ko takan hijabin jikinta ba, akan Aisha suke tsaye, Aisha da tayi siririyar dariya
“Dan Allaah kaje ka dawo, zanyi editing paper din nan ne, ga kuma recording din nan da nace maka yayi iska da yawa, banajin sosai saina gyara shi”
Ta gefen idonta Sa’adatu taga har lokacin Aisha yake kallo, da wani yanayi a fuskar shi da yasa Sa’adatu tabbar da inda ita yake yiwa kallon da tuni ta narke tabi kasa, amman dariyar dai Aisha ta sakeyi
“Bye bye…a dawo lafiya”
Ta fadi tana juyawa, hakan yasa shi gyara zama yana kunna motar
“Zaki gane hanyoyin tun daga nan?”
Kai ta girgiza, tana nemo yawu dakyar kafin ta iya ce masa
“A’a…”
Dan ta dan juya ne ta kalle shi taga yana kallonta da alamun tambaya, wayar shi ya zaro daga aljihu yana dan daddanawa, batare daya raba kanshi da kallon wayar ba yace mata
“Ya sunan unguwar?”
Dakyar ta iya ce masa
“Bachirawa”
Kai ya jinjina, yana kara dan danna wayar kafin ya makalata a jikin wani abu a gaban motar, tukunna yaja suna fita daga gidan da maigadi ya bude musu. Tana kallon hannun shi yanda yake murza sitiyarin a gayance, sai dai lokaci zuwa lokaci taji wayar shi tayi magana tana ce musu su karya kwanar haggu ko dama, hankalinta gabaki daya ya tafi kan kallon yanda yake tuki cike da kwarewa, kamar bata taba ganin wani yana sarrafa mota haka ba, ko dan motoci nawa ma ta taba shiga idan lissafi za’a tsaya yi? Muryar shi sai tazo mata a bazata
“Mun shigo Bachirawa…ina zamuyi?”
Data kalla kuwa sun shiga din, abin saiya bata mamaki, ai akwai nisa sosai a tsakani, mintina nawa ne suke kaita a adaidaita sahu? Ga kuma cunkoso, ko yau hanyar fayau take? Wajen zuwa ai da dan cunkoso duk da rana batayi ba sosai, ga tsayuwar danja kuma. A hankali ta dinga yi nuna masa hanyoyin da zai shiga, to shi Aisha da tace yazo, ina zai gane wannan kwanonin? Ai sai dai in bakin hanya zai tsaya azo a tafi dashi. Tunda yake a garin Kano bayajin ya taba zuwa wannan yankin, ga cunkoso. Har kofar gida ya kaita
“Nagode”
Ta fadi, kai kawai ya jinjina baice komai ba, yana ganinta ta fita, ta rufe masa murfin motar, ta taka tana shigewa wani gida da yake mamakin kankantar shi, tunda aiga iya fadin gidan nan ta waje, tunda ga wasu gidaje nan daga gefe da gefen gidan nasu. Daya juya motar kuwa, sai da ya fita daga layin saida yayi tambaya ina zaibi ya fita titi aka nuna masa. Haka kawai tunanin yanda cikin gidan nasu Sa’adatu yake in har yana da wannan kankantar daga waje ya cika masa zuciya.
*
Batayi mamakin maganar karin auren Jabir ba, tunda duk sallar da zatayi saita roki Allaah daya karkata hankalin shi akan kara aure ko zata ga jinin shi, haka azumin daya wuce, duk wasu lokutta da sukazo a matsayin lokuttan da ba’a juyar da addu’a idan anyi, to Jabir ne farko sannan sauran abubuwa su biyo baya, yau daya ce mata zai kara aure, murmushi kawai tayi tana jera hamdala a zuciyarta. Tasan lokacine kawai daman, Allaah ba zai juyar da addu’ar da tayi cike da yakini ba. Ta kudurce gobe zata saka ayi abinci sadaka a rabawa mabukata. Sai dai Hajiya Hasina ta girgiza da yace ai tasan yarinyar da zai aura din
“Nasanta?”
Ta tambaya cike da rudani, a yaran yan uwanta ta fara lissafawa, dan kawayenta duka yaransu mata sunyi aure, sai mazane suka rage, wadanda basuyi auren ba kuma suna kasashen ketare karatu, batajin sunzo gidan har Jabir ya gansu. Tana wannan lissafin ne ya katseta da fadin
“Kinsanta Hajja, Sa’adatu, yarinyar da takeyi miki aiki da”
Harga Allaah kanta Hajiya Hasina taji yayi murfi, Sa’adatu? Mai mata aiki? Mai mata aiki yace, kallon shi takeyi, watakila rudanin da yake kan fuskarta ya gani shisa yayi mata karin bayani, fuskar yarinyar ta fara fado mata kafin komai.
“Ba wadda nake turawa gidanka tana taya matarka aiki ba?”
Kai ya jinjina mata
“Jabir kana da hankali kuwa?”
Ta tambaya, da take ta addu’a ya kara aure batana nufin ya wulakanta matar shi haka ba, ita tana so taga yaran shine kawai, da matar shi lafiyayya ce, ai a cikin yaranta Jabir na daya daga cikin wadanda ba zatayiwa fatan hada mata biyu ba, saboda rashin son hayaniyar shi, saboda batason duk wani abu da zai daga masa hankali, amman mai aiki? Mai aikinma wadda har gidanshi ta turata ta taya matar shi aiki, karshen wulakancin da namiji zai yiwa matarshi kenan ai, ba zai duba wadda ta dace tayi kishi da ita ba, ko dan ya rage mata radadin karin auren da zaiyi. Sai ya jajibo mata ‘yar aiki? Me ma ya samu Jabir din?
“Kanka daya? Yar aiki? Yaushe kaganta? Kukayi magana har kuka kulla soyayya kace zaka aureta?”
To ko labarin da kawarta Hajiya Ummati ta bata ta dawo gida ta dinga al’ajabi da gaske yana faruwa? Yan aiki masu kyalla ido in sunga mai gida na da maiko suyi masa asiri su aure shi. Amman Sa’adatu fa, ko dai ta manta fuskar yarinyar ne, wadda mahaifiyarta ta rasu, daga ita har danginta basuyi mata kama da mutane masu halin banza ba, amman tabbas idan Jabir kanshi daya, yana kuma cikin hayyacin shi ba zai kalleta yayi mata wannan maganar ba. Shima da mamaki yake kallonta, ganin yanda hankalinta ya tashi a madadin murnar daya zata zatayi, jin kuma yau fadanta akan shi ya juyo, wani abu da bai taba faruwa ba a tsakaninsu, kome zaiyi kuwa, Hajiya Hasina bata taba daga masa murya ba, ko da yaushe nasiha ce a tsakaninsu, zata zaunar dashi tayi masa magana kamar yafi sauran hankali da shekaru, duk da ko Babangida, har yanzun da iyalinshi da komai bai wuce fadan Hajiya Hasina yabi ta kanshi ba.
Kallonta kawai yakeyi, mamakin da yake ciki ya hanashi fahimtar dalilin da yasa takeyi masa fada, ko maganar shi ta daga mata hankali
“Ita Aishar tasan abinda zakayi mata?”
Sai lokacin ne ya daga mata kai
“Saida ma muka gama magana tukunna nazo nake fada miki”
Shiru tayi tana kallon shi kawai
“Gaskiya ka nemo wata ba wannan ba”
Wani abu yaji ya hautsina masa, a ina? Tasan yanda akayi suka samo wannan din kuwa? Kai yake girgiza mata
“Ni wannan din tayi mun Hajja, dan Allaah, Tasha fa bata da matsala…”
Yake fadi wannan karin nashi hankalin na tashi, saboda yaune karo na farko da Hajiya Hasina tace masa ba zaiyi abu ba kai tsaye haka. Bayason ya fada mata dalilin da zaisa ya kara aure saboda ya santa, ya auri mace dan ta haifa mishi da ya saketa wani abune da ba zata taba amincewa dashi ba ko da kuwa shine. Shisa ya zabi komai ta tsaya a tsakanin su uku, saboda a tsarin da ya gama, tsarin da Aisha ta tayashi suka gyara, sun tabbatar da babu wata matsala a ciki, babu wani abu da zaiyi musu cikas, musamman bayan da Sa’adatu ta saka hannu a yarjejeniyar da sukayi. Ko da kuwa ya hango matsala, to babu yanda za’ayi ya hasaso daga bangaren Hajiya Hasina zata bullo
“Dan Allaah karki ce a’a, karkice ba ita ba”
Da gaske Jabir ba’a hayyacin shi yake ba
“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”
Ta furta a sanyaye tana kallon shi, to aiko lokacin auren Aisha, da sukaje gaishe da mahaifinta yaga alamar bai samu karbuwa a wajen shi ba, bata ga tashin hankali a fuskar shi haka ba
“Ina da makusa Hajja? Ina da wani abu da za’a kalla a nemi hanani aure? Nasani ni ba kamar sauran maza bane ba, bana fita wajen aiki kullum, amman kasuwancina baya bukatar inyi haka, ina da kudin da zan rike mata hudu, amman me yasa Daddynta ya dinga kallona kamar ban kai ya aura mun ‘yar shi ba? Haka fa yace mu tafi zai duba yaga idan akwai yiwuwar in tura manyana”
Abinda yace mata kenan, kuma bacin ranshi a lokacin ya ninka tashin hankalin shi, yanzun kuwa zallar tashin hankali take gani muraran a tare dashi, musamman da ya sake rokonta, sai taji gabaki daya jikinta yayi mata sanyi
“Kaje zamuyi waya”
Ta iya furtawa
“Kin amince kenan? Inyi mata magana su saka ranar da za’a je? Kinji Hajja?”
Numfashi taja tana saukewa
“Zan kiraka Jabir”
Kai ya jinjina yana mikewa
“Tasha bata da matsala fa, ta riga ta yarda”
Wannan karin ita ta daga masa kai, saboda so take ya tafi ko zatayi tunani me kyau. Ganin ta kasa kulla komai ita kadai yasa ta kira Farhana tace tazo tana son ganinta. Bata kuwa bata lokaci ba sai gata a gidan, dan daga wajen aiki ma ta bada uzurin wani abu ya taso mata ta taho jin muryar Hajiya Hasinar kamar akwai matsala. Komai ta kwashe ta fada mata, duk da itama tayi mamakin lamarin, saita zabi ta kalle shi da zuciya mai kyau
“Kinsan zuciya Hajja, kuma kinsan Jabir bama komai yake burge shi ba, dukanmu shekara nawa muka kwashe muna fatan ganin yazo da magana irin wannan? Ni Allaah bana tunanin da wata matsala tunda ita matar tashi ma yace bata daga hankalinta ba…”
Kallonta Hajiya Hasina takeyi
“Kinga zataji ko bakomai, idan ita Sa’adatun tazo ta haihu dashi, iya abinda zata nuna mata kenan, ba tada wani abu da zatayi mata dagawa dashi tunda har aiki tayi mata…kibar komai a hannuna zan kira JB din, sai inji yar inace in sa ayi bincike sosai, in dai bata da wani hali marar kyau ina ganin a barshi ya aureta kawai Hajja”
Duk da hankalinta ya dan kwanta, lamarin ya kasa zauna mata. Zuciyarta taki natsuwa sam, haka dai tabi Farhana da to. Sati biyu kuma aka dauka kafin Farhana ta dawo tana fada mata iya binciken da akayi mata, yarinyar ta fito daga gidan nagartattun mutane, iyayenta sun samu shaida me kyau, kowa ya bude baki alkhairinsu yake fadi, da kuma irin tarbiyar da suka samu, haka dan uwanta da take hannun shi, duka unguwar sunyi masa shaidar arziki, ita dai ance ta taba aure, kuma ana zargin mahaifiyar mijince ta rabasu, dan auren ma bai dade ba, ita dai a ganin Farhana da duka sauran yaran gidan manyan daya kamata a tattauna maganar dasu basu ga aibun auren Sa’adatu ba tunda Jabir naso.
Jamaal ne ma ya dan jinjina batun auren da ta tabayi duk da ance bata dade ba
“Idan kaddara ta fito da daya daga cikin ‘yan uwanmu, hakan kuma ya zama wani dalili da za’a gujewa sake aurensu ya abin zaiyi maka Hamma?”
Zaid ya tambaye shi, yana saka jikinshi yin sanyi, shi daman bawai kin abin yakeyi ba, tunda Jabir yace ita yake so kuma ai shikenan. Anan suka yanke hukuncin suyi ma Jabir din magana ace a saka ranar da za’aje masa gaisuwar aure. Kuma zasuje su kara kwantarwa Aisha da hankali, tasan cewa dan Jabir zai kara aure baya nufin wani abu, su din har abada duk wani abu da Jabir yake so abin darajtawa ne a wajensu. Duk da haka akwai wani abu a kasan zuciyar Hajiya Hasina da yaki kwanciya har lokacin, sai tayi addu’a tana fatan koma meye ya juye zuwa alkhairi. Farhana ta kira Jabir tayi masa albishir din cewa komai yayi dai-dai, zai iya yiwa Sa’adatu magana a tsayar musu fa ranar da za’aje masa neman auren.
Yana sauke wayar ya rungume Aisha da take tsaye a gefen shi, su duka jininsu akan farce yake da boren da Hajiya Hasina tayi, itama saita tsinci kanta da rike shi gam, nata hankalin na kwanciya tare da nashi, bata taba hango karin auren Jabir zai sakata farin ciki haka ba, ko dan karin auren yazo da wani lamari ne na daban?
“Zan fadawa su Mummy ma idan naje gidan, kaga ba lokaci za’a dauka ba”
Kai ya jinjina mata yana kara riketa a jikinshi hadi da lumshe idanuwan shi
Yaro ko yarinyar shi yaso hasasowa
Sai yaga fuskar Sa’adatu
Yaga idanuwanta masu haske tana kallon shi
Ba shiri ya bude nashi idanuwan zuciyar shi na wani irin bugawa