Skip to content
Part 23 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Lokacin data amince da Tahir, saita manta ya rayuwarta take kafin shi, babu wani abu da take hangowa a lokacin sai ita dashi, daga farko har karshe
Da aka daura musu aure kuwa, zuciyarta sai tayi wata irin natsuwa, tana jin tabbatuwar har abada a tsakaninsu
Ashe kaddara ta rantse akansu ne kawai, za’a daura musu aure, zata amsa sunan matar shi na kwana daya da yini, kafin da hannun shi ya rabata da kanshi kamar bashi ya roketa ta kasance dashi ba
Ya dandana mata wata rayuwa da tana numfashi amman a lokaci daya abubuwa da yawa sun mutu a tare da ita, wasu abubuwa da zuwa yanzun ta gama aminta ba zasu taba tashi ba, ya kuma tafi da wani kaso mai girma daga zuciyarta

Sanda taji ta gama jinyar rashin Tahir kuma, duk wani abu da soyayyar shi tasa ta jingine a gefe, wasu burukanta da son shi ya sanyaya mata, sai suka dawo. Shisa ma da Alhaji Danladi yazo ta amince dashi saboda tana ganin auren soyayya ta gama shi akan Tahir, shima kaddara sai tayi mata kwalele dashi, ta nuna mata samuwar duk wani buri nata a tare dashi, saida ta mika hannu dan ta rike shi, kawai kaddara ta janye shi tana barinta tsaye ita kadai, cike da bakin ciki da kuncin zuciyar saka ran da tayi. Da taga Jabir kuma babu wani abu data hango, asalima mamakin yanda al’amarin shi yayi mata kane-kane takeyi, sai kaddara ta bata mamaki ta hanyar cakuda hanyarta data Jabir da ko a mafarki akace mata mutum mai matsayin shi zai taka inda take takawa zata bude ido ta kwashe da dariyar jaye-jaye irin na mafarki.

Da ta saka hannu a takardar nan ma ta dawo gida sai ta dinga jinta wata sama-sama, da kwanaki suka dinga zuwa suna wucewa kuma batare da taji daga Aisha ko Jabir ba, sai shirun nasu ya fara karya mata zuciya, ko shima wannan din wani abune da kaddara zatayi mata kwalele dashi? Ko dai da aka saka mata Sa’adatu, haruffa uku na farkon a iya sunanta zasu tsaya? Rayuwarta ba zata taba haduwa dasu ba? Da daddare haka ta dinga kallon lambar Aisha tanajin kamar ta kirata, har wasu hawaye masu zafi taji sun silalo mata bayan ta kwanta, ashe zata wayi garine da sakon da ta rasa farin ciki ya sakata ko akasin hakan? Ta dai san zuciyarta ta dinga dokawa, ta kuma bude baki yafi sai goma tana rasa ta inda zata fara yiwa Fa’iza magana.

Dakyar ta iya tattaro karfin hali tace

“Matar Yayaa, akwai fa wanda mukayi magana dashi, ban fada miki bane nabari inji magana mai karfi daga wajen shi tukunna”

Da fara’a sosai a fuskar Fa’iza take kallon Sa’adatu, saboda yanda idan akazo sallama da ita take cewa bata nan yana damun Fa’izar, so take taga ta samu farin ciki itama, ta sha wahala tun akan Tahir, kuma tana yi mata addu’a sosai ta samu nagartaccen miji, tayi aurenta itama, in yaso inma karatun ne da taketa kiran zata cigaba saita cigaba a gidan mijinta

“Alhamdulillah, Alhamdulillah, wannan ai labarine mai dadi Sa’adatu, dan ina ne?”

Murmushi Sa’adatu tayi

“Dan nan Kano ne”

Amsar ta kwace mata, tana kuma saka tunani, saboda duk da Jabir na hausa, baiyi kama da dan Kano ba, baima yi kama da cikakken bahaushe ba, to idan ba dan Kano bane dan ina ne?

“Alhamdulillah, kai naji dadin wannan labarin sosai wallahi”

Cewar Fa’iza

“Daman ke ai so kike kiga nayi aure, na kunshe a cikin gida yanda kike a kunshe”

Dariya Fa’iza tayi

“Ke ba zaki gane ba yarinyar nan, aure ai Rahma ce, kuma rayuwar mace da aure shine cikar mutuncinta, duk macen da zaki gani burinta ta samu nagartaccen miji ta nutsu waje daya”

Jinjina kai Sa’adatu tayi, wani lokacin sai Fa’iza tayi irin maganganun take tuna akwai tazarar shekaru a tsakaninsu, kuma Fa’izar ma dai mai zurfin tunani ce sosai

“Yana so ya turo manya ne ayi magana, ki fadawa Yaa Abdallah dan Allaah ni kunya nakeji”

Nan Fa’iza ta sakata a gaba da tsokana, wai zata kira harsu Nabila ta fada musu wani ya cafke zuciyar Sa’adatun, banda murmushi ita dai ba abinda take iyayi, saboda da gaske kunyar ta tsinci kanta a ciki, har abin ya dinga bata mamaki. Aikuwan kiransu Fa’iza tayi, kafin dare kowa yaji labari, daya bayan daya suka dinga kiranta, kowa kuma banda farin ciki da fatan alkhairi babu abinda yakeyi, sai tsokanarta sukeyi, har Amira na fadin

“Wato yarinyar nan kinji labari na shiga adashi hannu biyu shisa kika jajibo aure ko? Dan ki tungultani, ni da nacewa Babansu Muhsina tari nake zai cikamun in tafi Umarah”

Dariya Sa’adatu tayi sosai, wata kaunar ‘yan uwanta na sake shigarta. Sai dai data koma daki ta kwanta bayan Magriba, zumudin da farin cikinsu ya fado mata, sai wani abu na daban ya tsirga mata, auren nan ba kamar kowanne aure ne ba, fatansu ba zai taba kaiwa mizani ba, watakila haka zasu kalleta, duk yanda suke son ganinta zauna a gidan aure bata da wannan rabon, sai dai zata canza musu rayuwa, zasu samu rufin asirin da take fatan ya zama katanga tsakaninsu da talauci, ai tanajin hakanma nasara ce

“…za’ayi komai ne a karkashin aure, auren yarjejeniya, idan kika haihu saiya sakeki”

Wasu cikin maganganun Aisha suka dawo mata, sai dai Tahir ma da ta aura dan soyayya ai sakinta yayi, babu kuma wani abu da zata nuna na ribar data samu ta auren shi banda wahalar jinyar zuciyarta da ta sha, koba komai wannan auren akwai riba a ciki. Sosai ta dinga karfafawa kanta gwiwa, tana kuma nakalto duk wata riba da zata samu ta auren Jabir din. Ko Abdallah daya kirata, ya tsareta da idanuwan nan nashi masu matukar kwarjini sai zuciyarta ta raunana, taga kamar in tayi wani dan kuskure kalilan zai gane rashin gaskiyarta

“Waye shi Sa’adatu? Tun yaushe kuke tare?”

Shiru tayi tana tauna karyar da zatayi

“Ba’a jima ba sosai, sunan shi Jabir”

Shiru yayi, tasan nazarin maganganunta yakeyi, a lokaci daya kuma duk da bata dago ba, tanajin idanuwanshi akanta suke

“Bana son gaggawa, ina so inga kin natsu waje daya, amman bana son gaggawa…ni ban sanshi ba, sai yace a saka musu ranar da manya zasu zo neman aure? Zamuyi bincike dole daga bangarenmu”

Zuciyar Sa’adatu ta buga, cikin rawar murya tace

“Gaisuwa zasuyi dan asan dashi, sai ayi binciken kafin a amsa musu”

Tunda tanaji a jikinta babu wani abu na aibu da za’a binciko. Numfashi  Abdallah ya sauke mai nauyi

“Zanje in samu Anty Talatu, tunda ba magana bace ta waya, in sun tsayar da lokaci sai kiyi masa magana. Allaah Ya tabbatar mana da alkhairi”

Bata amsa ba, tayi masa saida safe ta fice daga dakin. Alarm ya saka a wayar shi dan karma yazo bai farka lokacin da yake so ba, haka yayi salatul-istikhara yana nemawar Sa’adatu zabin alkhairi a wajen Ubangiji. Yanzun ji yakeyi kamar daga Abida har Habibu suna kallonshi, suna kuma ganin ko zai sauke amanar kula da Sa’adatu da yakejin ta rataya a wuyan shi. Da kanshi ya samu Anty Talatu ya fada mata washegari, zuwa yamma kuwa ta kirashi tace suna laraba, to ranar juma’a suzo, za’a sanar da duk wanda ya kamata ayi gaisuwar tare dashi. Kuma Amira ma da kanta ta kirashi sukayi magana sosai, akwai kudin kayan dakin Sa’adatu da aka siyar lokacin, ba duka Abida ta taba ba, ta bata ta juya ma Sa’adatun sai a dinga boye ribar, ita kuma sanin nagarta da kuma yarda da amana irin ta mijinta sai ta bashi kudin.

Kuma account daban ya bude, duk wata riba da aka samu saiya saka a ciki, kuma Alhamdulillah kudin sunyi albarkar da yanzun hankalinsu ba zai tashi maganar kayan dakinta ba, dai-dai na talakawa dai kam ba za’a ji kunya ba. Shi kanshi saiya ji ya samu natsuwa bayan sunyi maganar. Sai dai wanna natsuwar ta murmushe ne ta zama garin da yabi iska lokacin da Anty Talatu ta kirashi muryarta har rawa takeyi tana sanar dashi waye Jabir, tana fada masa dan gidan Alhaji Hassan Paki ne, lokaci daya makoshin shi ya bushe, jikinshi ya fara rawa. Har yau a gidan Radio in dai kai ma’abocin saurare ne to zakaji wani labari daya danganci daya daga cikin yaran na Alhaji Hassan Paki, kamar ma akwai guda daya a cikinsu daya taba tsayawa takarar dan majalissa, sai dai baisan ko yaci ko baici ba.

Kuma ana yawan yi musu talla, bayan kamfanin sarrafa shinkara, suna da rassa na kasuwanci da dama a cikin jahar Kano, kama daga kan kayan yara dana manya, irinsu atamfa, shaddoji da lesuka. In ba mantawa yayi har wajen saida kayan katako suna dashi. Ina hadin kifi da kaska? Yaushe wutsiyar rakumi zata tabo kasa? A ina Jabir din yaga Sa’adatun? Ko a fim dai da zakaga mai kudi ya nemo yar talakawa ya aura ba mai kudi kamar Jabir ba, ba kuma yar talakawa kamar Sa’adatu ba. Shi da yake cewa da kanshi zai tafi har unguwar su Jabir yayi bincike akanshi, idan yaje don yin wata tambaya ai ba zai rasa wadanda zasu kamashi a hadashi da jami’an tsaro a tuhume shi dalilin da mutum kamar shi zaije yana tambayoyi akan mutum kamar Jabir, kilanma ace wani makiyin Jabir dinne ya tura shi dan ya cutar dashi, idan yan sandane ma suna iya lankaya masa wani laifin da za’ayi masa daurin buhun goro, fitar shi sai ikon Allaah.

Da zazzabi a jikin shi sanda ya dawo gida, ko takan Fa’iza da takeyi masa sannu baibi ba ya fara kwalawa Sa’adatu kira, a dan rikice ta fito

“Jabir din dan gidan Alhaji Hassan Paki ne daman?”

Ya tambaya, kai kawai ta tsinci kanta da daga masa dan ita batasan sunan Baban shi ba, ta daiji Paki tabbas, shima kawayen Hibba ne da sukazo gidan lokacin tana can taji sunata kiranta da Paki din, ta dauka ma irin sunayen nan ne da kawaye suke lakabawa juna, ko kuma hakan ake cewa Hibbar

“Shine wanda yake siyasa?”

Ya sake tambaya, dan idan shine to zaice bin Malaman tsubbu da bokaye da akace ‘yan siyasa sunayi dan nasara da farin jini ne, a cikinsu wani yaba Jabir din sa’a, yace ya nemo matashiyar budurwa da bata cika shekara ashirin ba, shine ya kyallo Sa’adatu, tunda idan ma jininta ya bayar sai dai su jira aje lahira, yasan basu da karfin yin shari’a dashi anan duniya dai, ko daga maganar ma ba zasu farayi ba, kafin ya makasu a kotu da laifin bata suna, duk a tattarasu a watsa kurkuku, sai Sa’adatu ta girgiza masa kai, batajin Jabir dan siyasa ne, dan siyasa ba zai samu lokacin da taga kamar Jabir na dashi ba

“Ina kika hadu dashi? Me yasa mutum irin shi zai nemi aurenki Sa’adatu?”

Sai dai Fa’iza ce ta tare shi da fadin

“Me kake cewa haka? Shi aure ai nufin Allaah ne”

Kai ya girgiza mata

“Ba tsakanin irin shi da irinta ba Fa’iza, mai kudi da matsayi irin nashi ba zai auri irin Sa’adatu batare da wata manufa ba…haka kawai ba zai tsallake masu kudi ‘yan uwan shi yayo kanta ba…”

Ya karasa yana girgiza kai, wani tashin hankali yakeji yana kawo masa mamaya, ita kanta Sa’adatu tasan ba karya yayi ba, amman ko sama da kasa zasu hade, a bakinta dai, ko bata saka hannu a takardar da take matsayin barazana a wajenta ba, bata da karfin zuciyar kallon idon Abdallah tace masa ita taji ta gani, ta kuma amince da manufar Jabir akan aurenta

“Dan gidan da nayi aikine fa, acan muka hadu dashi sai…”

Kallon da Abdallah yayi matane yasa tayin shiru, saima ta juya ta koma dakinta. Kasa hakuri yayi a daren ya tafi gidan Anty Talatu, hankalin shi saiya kara tashi da yaga dakinta shakare da lemuka katan katan, ruwa, biskit, alawoyi da kuma cingam, harda kudi naira dubu dari duka a matsayin kayan tambayar aure, kamar za’a bude shago, ko goro irin wanda ake nadewa a takardar nan saida idonshi ya hango guda biyar, kuma gaya masa takeyi duka wanda suka karbi gaisuwar auren saida sukayi musu ihsani na daban

“Wato Sa’adatu na da kashin arziki, ka duba Alhaji Danladi badan wannan matar tashi data kwashe kayanta daga gaban Ma’aiki ba, da gaskiyar Hajiya Allaah Ya jikan rai da take cewa akwai wani haske na daban a tare da yarinyar nan shisa takejinta har ranta”

Da mamaki yake kallon Anty Talatu

“Kuma sunce su a shirye suke, basa son abin ya wuce wata biyu, ba komai suke so ba, wani kayan daki ko wasu abubuwa, yarinya kawai dansu ya gani, kuma ita kadai suke so akai musu”

Tabbas dole zasuce ita kadai suka gani suna so, saboda suna da wata boyayyar manufa

“A kirasu a basu hakuri a mayar musu da kayansu Anty, su din ba sa’annin hada aure da irinmu bane ba”

Abdallah ya fadi muryar shi na rawa cike da tsoro, ai sai Anty Talatu ta haushi da sababi tana tafa hannuwa, harda cewa

“Ko da za’ayi wa Sa’adatu hassada ai banyi zaton zaka kasance daga cikin mutanen ba…”

Hayaniyar da takeyi ce ta janyo hankalin mijinta daya shigo, harda kwallarta sanda take fada masa, shi yaja Abdallah bangaren shi ya zaunar

“Abdallah wadannan ba mutanen da zasu dauko kafarsu suzo neman aure a hanasu bane ba, wallahi kwarjininsu kadai zaisa a amince, ba kananun mutane bane ba…”

Kai Abdallah ya jinjina

“Nasani Kawu, amman tsakanin mutane irinsu da mutane irinmu sai dai ji a radio, sai kuma tsananin rabo idan sun fitar da zakka ko suna rabon kayan abinci, magana akeyi ta aure, kana tunanin manufarsu me kyau ce? Zasu tsallake attajirai da sarakuna haka kawai suzo neman auren Sa’adatu?”

Da wani yanayi Kawu yace

“Subhanallahi, haba Abdallah, da hankalinka? Zato fa zunubi ne ko da ya kasance gaskiya kuwa, me yasa zaka munana musu zato har haka? Shi yaron ma yana da wata matar, kara aure zaiyi, kuma Ubangiji daya halicci mai kudi da talaka, Ubangiji da ayyukanmu kawai Yake amfani dashi ba matsayinmu ba shine ya kadarta haduwar su harma aure yake shirin kulluwa. Dan Allaah ka kwantar da hankalinka, ka kuma bi abin da fatan alkhairi da addu’a, In shaa Allaah alkhairi ne”

Haka ya tashi ya tafi gida jikinshi a matukar sanyaye. Yanda duk Fa’iza taso ta kwantar masa da hankali, haka ta hakura ta rungume danta tayi bacci ta kyale shi. Saboda tsabar rudani kuwa ranar har hawayen maraicin Abida saida yayi. Saboda baisan abinda ya kamata yayi ba shi kadai bashida karfin hana auren nan duk yanda yaki shi, babu kuma wanda zai duba uzurin shi, kowa kudi da matsayin Jabir din zai duba. Ko a cikin yan ‘uwan shi kuwa washegari daya kirasu, Amira ce kawai jikinta yayi sanyi kamar nashi, da ita kuma suka dinga tattaunawa da jinjina dalilin da zaisa Jabir ya tsallake kowa yace Sa’adatu zai aura. Har Nabila kuwa haka tace masa Sa’adatun tace shi da kanshi yayi mata magana, shi yace yana sonta, dan asan bama shiririta bace ta kawo shi maganar aure ce shisa ya turo manyan shi.

Yaran masu kudi nawa ne irin shi da sai dai su yaudari yarinya su gudu kuma babu yanda za’ayi dasu, amman su ya kamata su godewa Allaah tunda itama Sa’adatun tana son shi, kuma magana ce yazo da ita ta aure ba shiririta ba. Sannan Nabila gani takeyi Sa’adatu na da kyan da zata ja hankalin namiji duk kuwa da kudin shi, a dire take, sannan ko magana take ta amsa sunanta na mace, Sa’adatu zata daga ido ta kalleka amman saika dauka yanga takeyi da idanuwan nata, duk wani motsi na Sa’adatu da tambarin mace takeyi yinshi, hakan kuma halittarta ce, tunda su ai gasu nan, wasu abubuwan kokari sukeyi wajen yinshi, idan taje zata kwantanta juya idanuwa yanda Sa’adatu takeyi da nata, musamman idan an bata mata rai, to kila idan ta tsorata mijinta ya fice daga gidan sai washegari zata ganshi.

Kome Sa’adatu zata saka a jikinta sai kaga ya zauna ya karbeta sosai, man lebe wannan idan ta shafa sai kaga kamar tayi kwalliya, balle kuma ta zauna tayi ado sosai, dama can ita din tazo a gida da tsatson talakawa ne, amman Sa’adatu matar manya ce, ko Abida lokacin yanayin halittar Sa’adatun yasa tafi kaffa-kaffa da takatsan-tsan da ita fiye da su dukansu. A ganin Nabila dan Jabir yaga Sa’adatu ya kyasa bata ga laifin shi ba, kyau yabi tunda tana dashi. Sai Abdallah da Amira duka suka yanke shawarar zasu tsananta addu’a Allaah Ya tabbatar da alkhairi. Duka sati hudu da tambayar auren suka sake dawowa aka tsayar da lokacin biki, sati takwas, wato wata biyu kenan. Tunda ance ba sai anyi kayan daki ba, sai Amira ta kira Nabila tace a samo mai gyaran jiki da ta iya sosai a gyara Sa’adatun tunda cikin masu hali zata shiga karsu rainata, kuma tun daga Sokoto ta aika kudi masu kauri ta siya mata kayansu na gyara tace a dora a motar Kano, tasa Fa’iza ta tsaya kan Sa’adatu taga tana shan komai yanda ya kamata.

Turarukan jiki, na wanka, da kuma na tsugunno duka haka Amira ta dinga fitar da kudi ana siyen masu tsada da inganci. Gyara kanwar tasu sukeyi yanda zatayi daraja a idon mijin da suka ta’allaka fatansu ya kasance shine mijin da mutuwa ce zata rabasu

Sai dai hausa sukace kaddara ta riga fata…!

<< Tsakaninmu 22Tsakaninmu 24 >>

1 thought on “Tsakaninmu 23”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×