Skip to content
Part 28 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Aisha yake kallo, ta fito wanka tana ta kai kawon data saba da shafe-shafen da baya gajiya da mamakinta akai, da daddare inka yi wanka ba shikenan ba? Sai dan turare da zaka fesa mai saukin kamshi. Tunda ai a ganin Jabir kayi wankan ne dan ka fitar da duk wani maiko da gajiya da zata takura maka, amman a lokacin ne Aisha take nemo wasu mayukan da zata laftawa jikinta, wai na dare ne, masu gyara fata da wanne bayanai ne da ba saurare yakeyi ba, randa ma take neman rigima dashi saita matso a hannu ta tinkaro shi saita shafa masa. Shisa ya koyi yin shiru da bakin shi ya bita da ido kawai, yana kallo ta gama ta rage musu wutar dakin zuwa mai saukin haske, ta hau kan gadon, kafin ta kwanta shiya mike yana gyara zaman shi, sai itama ta fasa kwanciyar tunda taga alamar magana zaiyi ko yake sonyi da ita.

“Tasha…”

Ya kirata, akwai mutane da muryoyinsu suke canzawa a yanayi daban-daban, amman Jabir duk inda akace Magriba tayi, Aisha bata san ko ita kadai bace ba, sai taji muryar shi ta canza mata, tana fitowa a sanyaye, kamar da gajiya, kamar kuma wanda bacci ya cinye karfin shi, duk da bai cika sonyin magana ba a irin wadannan lokuttan, haka takan jashi da hira kawai don yanda muryar shi takeyi mata dadi idan ta sautin yayi kasa haka.

“Me yasa tun satin auren nan nake jina ni kadai bayan ina tare dake?”

Ya karasa maganar yana sauke idanuwanshi cikin nata, tana jin kaifinsu duk da hasken da bai wadaci dakin ba, ta bude baki duk da bata gama sanin me zata fada ba ya hutar da ita ta hanyar cigaba da magana

“Me yasa zaki barni ni kadai? Haka muka tsara? Da na kyalekine inga zuwa lokacin da uzurinki zai kare, sai dai kinsan shiru ba abu bane dana saba dashi, ba kuma nason barin abu a raina ya dameni”

Kasa tayi da kanta, tanajin hawaye nayi mata barazana, gaskiya ya fada, tare suka tsara komai har suka cimma matsaya. Kafin lokacin kuma ta kwana, ta tashi da fargaba iri-iri, kuka ya zame mata abokin hira duk dare kafin bacci ya dauketa, tayi tunanin abinda take so kuma alamu suka nuna akwai yiwuwar ba zata taba sami ba. Data gama wannan jinyar, ta karbi wannan kaddarar da har yanzun bata saba da nauyinta ba. Sai tunanin Jabir ya auro wata ba kuma dan wani abu ba, sai kawai dan ta gaza ta wata fuska yayi mata sallama. Lokacin daya dinga tafiya sai yaki ya tafi da fargabarta, musamman lokacin da yayi wata tafiya zuwa New York, a karo na farko a lokacin da ta laluba jakar daya dawo da ita da takardun duk da ta gani, badon ta kammala masa ba, sai don ta bincika ko zata ga takardun asibiti a ciki. Haka wani abu ya dinga tsikarinta yana tabbatar mata da Jabir din ya nemarwa kanshi magani, ya kuma dace ya barta da matsalarta da bata da karshe.

Sai dai shi da bakinshi baice mata komai ba, itama kuma yanda duk taso tambayarshi saita dinga neman ta inda zata fara tana rasawa. Tayi kuka dai kashi-kashi, harta dinga mamakin yawan hawayen data mallaka da har zuwa lokacin basu kare ba, da kuma sukayi maganar surrogacy din nan, da yace mata zasuyi amfani da tsarin dashen kwan haihuwar shine da ake kira da (Artificial insemination) a turance, amman dai zasu nemi kwararren likita a fannin dan suji shawarar da zai basu, haka ta dinga kallon shi. Sai da daddare da ta kasa bacci, tanata juye-juye a jikinshi ya riketa yana tambayarta

“Menene? Kinsan banason ana barin abu a rai ko? Gashi nan kinki bacci, kin hanani yi nima”

Numfashi ta sauke

“Na dauka…ina nufin matsalarka, kai akwai maganinta, na dauka duk fitar nan da kakeyi, a daya daga ciki ka samu ka sake ganin likita kayi abinda ya kamata”

Saida ya dan gyara kwanciyar shi tukunna yace mata

“Nayi tuntuni, I’m okay yanzun”

Har ranta, tayi masa murna

“Naji kace za’ayi amfani da dashen kwaine, na dauka tunda ka samu lafiya…”

Ta kasa karasa maganar, ta fara kokarin hadiye wani abu daya tokare mata makoshi, murmushi mai dan sauti ya kwace ma Jabir, yana sa ta mintsinin shi, ya kama hannun nata yana dan matsawa

“Idan na rama sai kice naci zalinki ko?”

Yayi maganar yana zame hannunshi yanda ya sarke yatsunsu waje daya, kafin a tausashe yace

“Nasani Tasha, gara muji da abu daya ko? Muji da kaddarar ki da bamu hango ba, bana so in kara miki da hasasoni tare da wata bayan yaro ko yarinyata da zata dauka. Na tambayi halaccin ta daukarmun kwan batare da aure ba, aka fara kafa mun hujjoji da Ayoyi da Hadisin da bani da zabi daya wuce komai ya faru karkashin inuwar aure…”

Hawaye taji sun silalo mata, kafin zuciyarta ta cika fam da kaunar shi har tanajin babu sauran waje, bai karasa ba, kuma bata bukata, ko bai furta ba, amman a ranar maganganun shi sun mata nuni da abubuwa da yawa, tarin kaunar da yakeyi mata, matsayinta a wajen shi da yanda ya girmama al’amarinta ya kuma nuna mata lalurarta ba tata bace ita kadai, tasu ce su biyun. Haka ta sake shigewa jikinshi, hawayenta na sauka a kirjin shi, ya zagaya hannun shi yana shafa bayanta cikin lallashi

“Ina sonki, ko ban fada kullum ba, ko shakku zai darsu a ranki a zamantakewarmu Tasha, karki taba shakka akan son da nakeyi miki”

Kai take daga masa, tana tuno wata ranar litinin da ta zama mafarin alakarsu, wata litinin mai cike da abubuwa da yawa, a wajenta bakunta, doki, da taradaddi kala-kala da kowacce daliba take tsintar kanta a ciki a sabuwar makaranta, kuma ajin farko na Sakandiri, kusan su duka yan aji dayan ma idan ka kallesu zakaga sunata rarraba ido, kusan gabaki dayansuba diririce suke a layin assembly din, a cikin wannan rashin sabon ne da kuma kalle-kallen da Aisha takeyi idanuwanta suka sauka akan Jabir. Shima saboda yana layin da take tunanin inta kirga dai-dai to na ‘yan aji hudune, yana daga can baya, ya jingina kanshi da bayan yaron da yake gabanshi kamar wanda yake bacci, tureshin da yaron yayine yasaka shi dagowa taga fuskar shi, bata kuma san me yasa tun a lokacin taji kamar ta sanshi, kamar duka fadin makarantar shi kadaine wani abu da ba bako ba a wajenta.

Watakila sa’artace tayi nasara a wannan lokacin, ko kuma kaddarar da zata hadasu zama karkashin inuwa dayace ta fara aikinta a ranar, sai ya kalli inda take, suna hada ido, kuma sai taga yayi mata murmushi, murmushin da tayi hanzarin mayar masa dashi saboda taji a jikinta zai zame mata wata garkuwa da batasan ya zata fassara matsayinta ba

“Ina sonka sosai”

Sumbatar kanta yayi batare da yace komai ba. Tun ranar kuma ta saki jikinta suka tsara komai, har zuwa ranar da suka samo Sa’adatu. Sai dai tun satin bikin jikinta yayi sanyi, kirjinta kuma yayi mata nauyi, musamman yanda ‘yan uwanshi suka dinga zirga-zirga a gidan, kiran waya, jaddada mata cewar karin auren da Jabir zaiyi baya nufin wani abu a wajensu, har kullum zasu kasance tare da ita, karta daga hankalinta, da sauran maganganu na kwantar da hankali, sai taji kamar tace musu auren yarjejeniya ne, amman idan ma auren yarjejeniya ne, aurene dai. Kuma koyane Sa’adatu fa zata amsa sunan matar Jabir ne. Da yanda auren yake kusantowa da yanda nauyin kirjinta yake karuwa. Lokacin da Hajiya Safiyya, mahaifiyarta tazo har gidan, wani abu da Aisha zata kirga sau nawa ya taba faruwa saboda kawaici irin na matar, ta kuma soma yi mata nasiha, sai hawaye suka balle mata

“Kiyi addu’a sosai kinajina? Da kinji kishi na neman rufe miki ido ki tashi ki roki Allaah Ya sassauta miki, sannan karki yanke buri, fadar likita baya nufin Allaah ba zai iyayin ikon shi ba…”

Kai kawai take dagawa tana share hawayenta

“Nasan ke bame yawan kawaye bace, kuma kina da hankalin da ba sai nace karki bari wani ya zigaki ba, auren nan kisa a ranki ko baki da wata lalura, abune da Allaah Ya halatta masa. Ba gida daya zaku zauna ba, karki zama mai bin diddigi, ki kyautata masa zaton zaiyi muku adalci, abinda baki gani ba, ba zai dameki ba koya zakiyi hasashen shi”

Maganganu Hajiya Safiyya ta dingayi mata masu cike da hikima irinta nagartacciyar mahaifiyar da take son ganin yarta batayi wasa da lahirarta da kuma mutuncinta a idon miji ba saboda zafin kishi. Sai kuma maganganun suka sa tana jin kamar auren din-din-din Jabir yayi, auren da zai dore, musamman kuma da kowa in zai bude baki sai yace

“Allaah Yasa ta zame muku alkhairi, Ya kuma bashi ikon kamanta adalci a tsakaninku”

Aikuwa daren daurin auren da zazzabi ta kwana, danma Jabir din bai gajiya ba sam wajen jaddada mata muhimmancinta a wajen shi, da kuma tuna mata auren na wani lokaci ne, aurene da a idon duniya yake aure, amman a wajensu hade yake da wata yarjejeniya, karta manta hakan, kar kuma ta manta yana sonta, ko da wata zatayi masa kyau, ita din daice a zuciyar shi. Ta fara lallashin kanta taga hotunan nan na wajen walimar da akayi, sai suka kasa bace mata, tun ranar har yau din nan, tana zaune sai su gilma mata, kyawun Sa’adatu yayi mata tsaye. Sai taji zuciyarta ta buga, kirjinta yana mata zafi. Sai kuma ta tuna bayan wannan kyawun, Sa’adatu na da lafiyar da bata da ita, tana kuma da damar da ba zata taba samu ba, yarjejeniya ko akasin hakan, zatace ta auri Jabir, za’a ce ta haihu dashi, za’a ce tana rike da dan ko yar Sa’adatu ne.

Sosai abubuwan da basuyi tunanin su ba, sune suke dawo mata yanzun. Bafa zata goge cewar Sa’adatu ce ta haifi yaron nan ba. Ko da jininshi za’a zuke a musanya masa sabo da nata jinin, balle dangin Jabir da suka san daraja da hakkin dan adam, tana da yakinin zasuce ayi ma Sa’adatun adalci, kar a yanke alakarta da abinda zata haifa. Abu daya ta sani, babu mai tirsasa Jabir saiya dawo da ita idan ya kafe cewar ya gama zama da ita, amman kafiya nawa zai nuna? Musamman idan da Hajiya Hasina a tsakiya? Wadannan abubuwan sune suka hadu suka cunkushe mata zuciya suna rage mata walwala da karsashi har a wajen aiki. Akwai Madina Salis da suke shiri da ita, kuma yanda hotunan walimar ya watsu a Instagram, kusan duk wani da yake tare da ita yasan mijinta ya kara aure, Madina ta jata gefe kwana biyu da suka wuce tayi mata magana

“Bana son wannan sanyin da nake gani tare dake Aisha. Kishi halal ne, kuma duka an halicce mu dashi, kin manta shekarata biyu da miji ya dankaromun kishiya? Dangin shi kuma duk suka juyamun baya, babu tabarar da bangani ba tunda gida daya muke zaune, dana kauda kai yanzun ba gashi itama ta zama jiki ba, dangin da suka hadu suna cusgunamun tare itama ba dadinsu takeji ba…dan Allaah ki kwantar da hankalinki, bafa waje daya kuke ba, ki cire tunaninta da komai daga ranki, sai kigama kina mantawa da ita”

To da gaske so take kona dan lokaci ne ta manta da Sa’adatu, saboda har kasan zuciyarta bata son ganinta, balle ta hasasota dauke da cikin Jabir, idan kuma tana tsaye tare dashi kan komai hakan ba zai taba faruwa ba

“Kirjina yayi mun nauyi, sosai, na dauka komai zai tafi yanda muka tsara, ban dauka zan dinga jin wannan kishin da yake barazana da numfashina ba, ban dauka zata dinga tunamun ni din ina da wani nakasu ba sam…”

Ta fadi muryarta na karyewa, hawaye na zubo mata

“Na kasa Jay, na kasa danne zuciyata, dan Allaah kayimun uzuri, kayi hakuri har in karbi wannan al’amarin shima, ka cigaba da komai kan tsarinmu, amman kayi mun hakuri tukunna, idan na samu saukin abinda nakeji komai zai dai-daita”

Kai ya jinjina, bai fahimta ba duka, tunda baisan sau nawa zai tuna mata auren nan na wani lokaci bane ba. Uzuri kam shi maiyi mata ne a ko da yaushe, soyayyar da yake mata mai girma ce, hannunta ya kamo ya dumtsa

“Ina sonki”

Shine abinda ya fadi kawai, batare daya sake cewa komai ba, tasan angama wannan maganar, zai kuma kiyaye sosai wajen ganin zancen bai sake tashi ba, daya daga cikin halayyarshi da take so take kuma godewa. Kusan daren ya shafe yana kokarin goge mata duk wani bacin rai da shakku cikin yanayi mai tsayawa a rai. Da safe kuwa sai suka tashi tana cikin walwalar daya kwana biyu bai gani ba akan fuskarta, tare ma suka shiga kitchen, yayi tsaye saida tayi masa pancake, ta hada ma kanta Coffee dinta na ka’ida, shikuma yace green tea yake so, ta hada masa, suka karya suna hira. Ta riga shi fita, shi saida ya biya gidansu, tukunna ya wuce wajen Sa’adatu saboda da tunanin yanda ta kwana da jiki yayi bacci, dashi ya tashi. Duk da yayi mata text ya tambaya, kuma tace masa da sauki.

Saida ya tsaya ya sai mata su ice cream, da katan din lemukan kwalaye kala-kala, Aisha na sonsu, watakila itama ta sosu, kuma baisan koma tana da abin sha a gidan ba ko babu. Saida ya kwankwasa gidan tazo ta bude masa, ta saka riga da wando da suka nuna alamun na baccine, amman kuma dogone wandon mai filawoyi a jiki, rigar green mai duhu, sai wata farar hula a saman kanta, fuskarta tayi masa wani haske daya kasa fassarawa

“Ina kwana”

Ta fadi tana matsawa gefe dan ya shiga, shigar yayi kuwa yana dan girgiza kanshi kamar yana so itama ta fado daga inda ta manne mishi ita da shigar nan da tayi, ledar hannun shi ya mika mata, yana juyawa batare daya amsa gaisuwar ta ba, saida ya gama shigowa da duka lemukan daya siyo da ruwa. Tana tsaye tana ta kallon shi, tukunna yace mata

“Ki samu waje ki zauna, ke da ba dadi kikeji ba kinata tsayuwa”

Karasawa tayi ta zauna kan kujera, tunda ta dan bude ledar daya bata taga robobin ice cream, ta kuma je ta saka a fridge ta dawo ta tsaya harya gama shigowa da komai shima

“Ya jikinki?”

Cikin sanyin murya ta amsa da

“Naji sauki sosai”

Kai ya jinjina

“Allaah Ya kara lafiya, ki dai shanye magungunan duka, babu kyau a fara shan magani ba’a karasa ba. Akwai wani abu da kike bukata a gidan?”

Kai ta girgiza masa, ya dan gyara zaman shi ya sa hannu a aljihu ya zaro kudi, dubu ashirin ne, ya mika mata

“Ki dai rike wannan a hannunki, ko zaki bukaci wani abin, ki turamun account number dinki, zan kara saka miki”

Ta mika hannu, ta karba, tana ta mamakin shi kuma, yanda yake maganar kara mata wasu kudin bayan wannan daya bata da batama san me zata siya dasu ba tunda akwai komai na bukata a gidan. Daman haka masu kudi suke rayuwarsu? Su dinga fitar dasu suna kashewa kamar basa tunanin su kare? Dubunnai fa, ba daruruwa ba.

“Nagode…”

Cewar Sa’adatu cikin rashin sanin abinda ya kamata ta fada, mikewa yayi shima

“Idan na dawo gobe ko jibi sai muyi magana, lokacin kin kara warwarewa”

Kai ta daga masa, kalamai karanci sukeyi mata in dai yana tsaye a gabanta, ta dai tsinci kanta da mikewa ta bi bayanshi ya fita ta mayar da kofar ta rufe tana tunanin maganar da zasuyi, da zata iya ma data bude bakinta tace masa suyi maganar taji sauki, tunda bata tashi tana jin ciwon komai ba, sai jikinta da har yanzun bai dawo dai-dai ba. Daki ta koma kawai ta kwanta, tana rasa tunanin da zata kama tayi, saboda yawan da takejin sunyi mata.

<< Tsakaninmu 27Tsakaninmu 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×