Hannunta da yake rike cikin na Jabir take kallo, a lokaci daya kuma tana wasa da kafarta cikin rashin sanin abinyi. Duk da wajen tar yake da hasken fitilu bai hana garin yin luf alamar yammaci ba. Zuciyarta wasai ta tashi da safiyar lahadin, saboda Asabar dinta tazo da abubuwan da ta kwana tana nishadinsu, Jabir ya aiko da direba kamar yanda yayi mata alkawari, ya kaita gida. Tunda safe ta shirya daman, ta samu ledoji ta dibi naman kaji, kifi, harda na gwangwanaye. Dayar ledar kuma duk wani lemo da take dashi sai da ta diddiba ta zuba, harda kwai rabin crate ta dibar musu. Dankali ta soya da safiyar, tana da sauran sauce din kifi, ta dibarwa maigadi, data dawo, dokin zuwa gidan sai taji ya cika mata ciki. Haka ta dinga kallon agogo kafin direban ya karaso.
Haka ta shiga gidan da sallamarta, ta kuma ji dadi ganin Fa’iza tazo ta rungumeta tana murna sai kace sun shekara basu ga juna ba. Sai murmushin jin dadi takeyi, data shimfida mata tabarma harda darduma ta dora akai, sai tasa tana ta kallonta kawai, in ba aure mai daraja ba, yau itace ake shimfidawa darduma akan wannan wankakkiyar tabarmar da Abdallah kawai ake shimfidawa ita? Hira suka shigayi bayan taje ta dauko yaron Fa’iza da tayi kewa sosai, sai taga kamar ya kara wayau a yan kwanakin da tayi bata tare dasu. Nan fa Fa’iza ta dinga ina zata saka Sa’adatun
“Kinga alale zanyi harna gama gyara waken, ko akwai abinda kike marmari?”
Kai Sa’adatu ta girgiza
“Ai matar Yayaa kawai kiyi mana alalar nan, ga kifi nazo dashi sai a saka mana a ciki, ko ayi mana yar sauce din manja mu hada.”
Dariya Fa’iza tayi
“Yanda amarsu tace haka za’ayi.”
Tana cigaba da aikinta, sai dai sosai tsoro ya bayyana a fuskarta da tazo ta dauki ledojin tana ganin kayan da suke ciki.
“Sa’adatu…”
Ta fadi cike da wani yanayi
“Ya dai sani ko? Kin fada masa kafin ki dibo mana wadannan kayayyakin, kinsan babu kyau.”
Baki Sa’adatu ta tura gaba, itafa duk a cikin ganimar yarjejeniya ce, sai ace dan zata dibo saita fada masa? Bashi yace idan ya kare ta fada masa ba.
“Aikuwa komawa zakiyi dasu, dan ba dani za’ayi rashin hankalin nan ba, kinsan Yayanki ma idan ya dawo ya gani fada zaiyi mun.”
Cewar Fa’iza tana mayar da wasu cikin kayan data fito dasu, ita kuma Sa’adatu ta janyo jakarta tana ciro wayarta daga ciki, ta lalubo lambar Jabir, sai dai idan ta kira me zatace masa? Bawai kunya takeji ba, ita talaucinsu bai taba sa taji kunya ba, kawai tana son dai taga bata kare rayuwarta cikin shi bane kawai, balle kuma Jabir din ai yasan su din ba masu hali bane, tunda duk cikin neman rufin asiri ne taje aikatau gidansu har kaddara ta hada hanyarsu. Kawai ta inda zata fara masa maganar ne bata sani ba, sai ta bude wajen tura sako ta fara rubutu
“Har nazo gida. Na dibar musu nama haka da lemukan daka kawomun da su kifi, shine Anty Fa’iza take tamun fada saina dawo dashi saboda ban fada maka ba.”
Ta karasa rubuta sakon tana tura masa, kafin ta daga idanuwanta tana sakawa cikin na Fa’iza.
“Na fada masa yanzun, kuma fa naga dai kayana ne, tunda da sunana yake aikowa, yanzun sai ya zama laifi dan na dibo muku? Bafa shinkafa bace ba.”
Kai Fa’iza take girgizawa.
“Aiko kwayar Maggi ce Sa’adatu, ko dai kin manta karatun ne? Ko kuma mirsisi kikaso kiyi ki manta da Mala’ikan gefen haggu…”
Wannan karin Sa’adatu ce tayi dariya
“Ai shikenan, yanzun sai a diba ayi mana miyar kifin…”
Ledar Fa’iza taja tana fadin
“Babu ma wani bata lokaci kuwa.”
Sa’adatu ta bude baki zatayi magana taji kara, alamar sako ya shigo wayarta, da sauri ta dauka, tana tsintar kanta cikin taradaddi, ta bude wayar da bugun zuciya tana shiga sakon
“Duk wani abu da yake cikin gidan nan, ba saikin fadamun ba, ki dibarwa wanda kike so. Da kin fadamun dai, sai a karo ki tafi dashi.”
Wani sanyi taji ya ratsa zuciyarta, har batasan murmushi ya kwace mata ba, murmushi sosai daya bayyana hakoranta.
“Bari inyi aikina kiyi soyayyarki.”
Cewar Fa’iza tana mikewa, murmushin dai Sa’adatu ta sakeyi
“Nagode. Allaah Ya saka da alkhairi Ya kara budi.”
Ta kuma saka a zuciyarta sanda duk zata dawo to zata fada masa, dan ya siyo mata abinda yayi niyya ta kawo musu. Direban bai koma daukarta ba sai da akayi sallar Magriba, taji dadin hakan tunda Fa’iza ta kira Abdallah, saiya dawo gidan suka gaisa, shima yaji dadin ganin tana cikin walwala, da zata tafi dubu biyar ta bashi cikin kudin da take dashi, dakyar ya karba. A mota kuwa sai murmushi takeyi ita kadai, ashe haka hidimtawa dan uwan da kake so yake da dadi? Ta kudurta a ranta ba zata tabajin kunyar yiwa Jabir tuni ba duk sanda zatazo gida. Kuma zata dinga adana kudaden da yake bata tana taimakawa Abdallah. Haka ta kwanta zuciyarta fari tas, da safiyar lahadi kuwa, kayanta ta dauka, Abaya ne duka, har wadda zata saka a jikinta, saboda yanda takejin dadinsu, sai kuma inners data dauka suma kala biyu, riga da wando na bacci, sai turare da man shafawa.
Cikin saitin akwatunan lefenta, akwai wani da yazo da wata yar jaka, a cikin jakar ta hada duka wani abu da take tunanin zata bukata. Sai yar jakar hannu baka data saka cajar wayarta, kudaden da take da yakinin babu abinda zatayi dasu, sai kuma katin zaben da ta dauko daga gida. Ta tafasa taliya da rana, amman ta kasa cin abin kirki, wani yanayi ne takeji da ta kasa misalta shi, sai tunani takeyi, da Aisha zasu tafi? Daga ita sai Jabir? Idan da Aisha za’a tafi ya zatayi? Tunda aka daura auren basu saka juna a ido ba, idan kuma daga ita sai Jabir ne fa? Hakan na nufin zasu kwana waje daya, a karin farko, a wani bakon waje, hakan ma na nufin abubuwan da in zata lissafa batajin tana da lambobin da zasu kididdige su. Tana kwance cikin saka da warwarwar da takeyi aka kira la’asar, sai wani abu a gefen cikinta ya kulle, da tazo alwala gani tayi kamar hannuwanta na rawa a hankali.
Ta jima a zaune tana Istigfar bayan ta idar, saboda tasan sallar nan cike take da tarin kurakurai, tunda ba cikin wadatacciyar natsuwa tayita ba. Da taji motar Jabir, sai taji kamar wani abu yana mata yawo a kasan ciki, ga zuciyarta da take bugawa da sauri da sauri. Tanajin shi ya kwankwasa yana kara mata bugun da zuciyarta yakeyi, data tashi taje ta bude masa har sarkewa kafafuwanta sukeyi. Cikin rawar murya ta gaishe dashi, yana amsawa da
“Kin shirya?”
A takaice, da wani yanayi a muryar shi daya sata daga kai ta kalli fuskarshi, ba zatace ta sanshi ba, amman wani abu cikin idanuwan shi na fada mata ranshi a bace yake, sosai. Saita daga kai tana dorawa da.
“Eh…mayafi na kawai zan dauko.”
Batare da ta jira amsar shi ba kuma ta juya tana komawa dakinta, saboda yanayin da yake kan fuskar shi ya tsoratata, ba kuma taso ta bashi dalili komin kankantar shi da zai sauke ko da kadan ne daga bacin ran da take gani tare dashi. Mayafin abayar ta dauka, tayi rolling dinshi kan hular dake kanta, tana saka dan abin makalewa yanda ya zauna mata das dashi. Ta saka takalminta, ta dauki karamar jaka, sai kuma jakar da kayanta suke ciki ta fita. Sai dai Jabir ne tsaye, ya dora wata yar jaka-jaka da batama kula ya shigo da ita ba kan kujera, ya kuma bude jakar, yanajin karasowarta ya kalleta da cewa
“Bani jakarki, akwai space anan…”
Duk da ta mika masa jakar, sai taji ta takura fiye da yanda take a takure, idan akwai waje a tashi jakar, yana nufin su hade kayansu waje daya? To inners din data dauka kuma fa? Haka zai fito dasu ya gani kafin ya saka a tashi jakar? Wanne irin terere ne wannan da bata shirya masa ba, wata irin kunya marar misaltuwa taji ta lullubeta, musamman da Jabir ya fito da komai da yake cikin jakar, kuma abinda take kunyar suka zamana a sama, sai dai hankalin shi kwance ya sake dauka yayi musu wajen zama a cikin jakar shi, kamar hakan ba sabon abu bane a wajen shi, kamar kuma yayi hakan yafi a kirga.
“Yayi mana.”
Wani sashi na zuciyarta ya fada mata.
“Yana da mata ko kin manta?”
Numfashi taja ta sauke a hankali, bata manta ba, ina ma Aisha din take? Ko tana mota? Amman idan tana mota zai fara hade kayanta da nashi waje daya kuwa? Ko su kadai zasu tafi?
“Na dauki turare, ya ishemu.”
Muryar Jabir ta katse mata zancen zucin da takeyi, tana kuma maida hankalinta kan turaren daya ajiye akan kujera, yana karasa saka kayanta, ya zage jakar tashi ya dauka.
“Muje?”
Kai ta jinjina masa, jikinta kamar an zare mata duk wani karfi da take tare dashi. Kafafunta ma nauyinsu takeji ba kadan ba lokacin da tabi bayanshi. Sai dai a maimakon ya shiga gaba, gidan baya ya bude ya shiga, barin murfin a bude da yayi yasa ta karasa bayan ta zauna itama, tana kuma jan murfin ta rufe. To tunda direban ya ajiyesu filin jirgin sai taji duk ta diririce. Jabir ya mika hannu ya karbi karamar jakarta batare da yace mata komai ba, ya hada da dayar ya rike a hannu daya, bata gama fahimtar abinda ya faru ba yasa dayan hannun shi ya kama nata, yayi mata riko da ko wani yayi niyyar ratsawa ta tsakanin hannuwan nasu sai yayi da gaske hakan zai faru. A maimakon tayi kalle-kalle sai idanuwanta sukayi tsaye kan kafafuwan Jabir, tana kokarin mayar da nata duk inda ya cire nashi.
Ya kamata ace ta morewa idanuwanta, ta rike duk wani abu da yake faruwa a cikin filin jirgin kasancewar shi karonta na farko, amman ko tsayawa sukayi tana bayan Jabir, hannunta cikin nashi, idanuwanta akan bayanshi, hancinta na shakar mata kamshin shi da yau takejin kamar harda na turarukan wuta irin wanda takeji lokacin tana aiki a gidansu. Kwata-kwata bata maida hankali kan komai ba, haka inda za’a tsareta ace tunanin me takeyi, ba zata iya fadin abu guda daya ba, watakila dai zata iya bada labari, sunje wani sashi, inda ya danyi mata magana kan voter’s card dinta, ya mika mata jakar data nuna masa yana ciki, ta bude ta dauko, ya nuna wani abu a wayar shi da batasan meye ba, aka kuma dauki abin, sannan ya nuna nashi I.D card din, itama ya dan jata gaba ta nuna nata, takardun da aka mike musu shiya hada ya dauka duka. Ya jata suka wuce wani waje inda ya ajiye jakunkunan, suka wuce, inda bata san ya akayi ba, ta dai sake ganin karamar jakarta a hannun shi.
Ya kuma jata wajen wasu kujeru inda mutane da dan yawa suke zazzaune, kowa da abinda yakeyi, masu yara nata fama dasu, masu danna waya nayi, wadanda suke zaune kawai suma haka. Waje ya samu daga can gefe inda yake da saukin mutane ya fara janta ta zauna, sannan ya saki hannunta yana zama a kujerar gefenta. Kamar shirunsu ne yasa taga sun dade sosai a zaune, tunaninta dai yayi nisa sosai, tunda saiji tayi Jabir na riko hannunta yana fadin.
“Taso.”
Ta kuwa tashi ta bishi, sai dai zuciyarta ta buga ta sake bugawa data ga sun nufi jirgi gadan-gadan, duk girman shi da take gani a fina-finai da hotuna, da yanda take hasasowa ya wuce haka, ganin shi tayi wani shirim, tsoro taji ya shigeta, kafafuwanta har rawa sukeyi lokacin da suka fara taka matattakalar da zata hadasu da cikin jirgin, musamman da Jabir ya saki hannunta yana sakata a gabanshi, ta juyo yakai sau hudu kamar tana son tabbatar da yana nan a bayanta, bai barta ita kadai ba, da suka shiga cikin jirgin ma, hannu ya dansa a bayanta ganin yanda ta diririce, har sukaje karasa inda yake nema, ita ya fara sakawa a gefe, kusa da kofa, sai shi ya zauna a kusa da ita, ya kuma dan gyara ya daura mata wani belt da bataga daga inda ta janyo shi ba. Ta tabbata zuwa yanzun yana ganin yanda jikinta yake rawa, da gaske ne kuma ya gani din. Saiya kara gyara zaman shi sosai, ya riko hannunta yana wasa da yatsun da ya rasa meye a tare dasu da yake yawan jan hankalin shi.
Ko yanda suka zauna a cikin nashine kamar an auna? Ko kuma yanda inya rikesu kalar fatarta sai ta hadu da tashi da tafi duhu ta bada wata kala ta daban ne? Ko kuma kawai kyaune da yatsun nata har haka, ya kasa ganewa, ya gane a tsorace take, sosai
“Kinsan cikin abubuwan da na tsana harda makaranta? Bana son karatu ko kadan.”
Ya fadi yana saka ta kallonshi, kai ya jinjina mata.
“Ni na rigada nasan kasuwanci nake so inyi, to tunda na iya rubutu da karatu me yasa za’a ce kullum sai naje makaranta…da ina secondary kullum sai na sa yan gidanmu sunyi latti, saboda zan boye a bayi, ko a dakin wani ayita nema na, in suka gaji suka tafi kuma, na fito Hajja tace sai an kain.i”
Dariya tayi.
“Nikuwa ina son makaranta.”
Ta tsinci kanta da fadi, saboda tana son karatu, har yau tana da burin yin karatu
“Makarantar? To bakina kamar zai taba bango lokacin dana gama secondary akace sai naci gaba.”
Dariyar da tayi me sauti ce.
“Ni kuwa ina so in cigaba da karatu.”
Kwantar da kanshi yayi jikin kujerar yana kuma juyar dashi yanda zai kalleta sosai.
“Zaki iya ai tunda kina so.”
Yayi maganar kamar zabin duka nata ne.
“Hmmm”
Tace, ya jinjina kanshi.
“Eh mana, wacce makaranta kike so? Kin gama secondary ne?”
Itace ta daga masa kai.
“Harma an shekara harda wani abu dana gama.”
Da mamaki a fuskarshi yake kallonta
“Kina zaman me to? Ba kina so ba.”
Ta inda zatayi masa bayani ya fahimta take nema.
“Dana gama nayi aure da nufin sai inci gaba daga nan, sai auren bai yiwuwa ba, to kuma hidimar da yawa shisa ban samu na cigaba ba.”
Sosai yake juya kalamanta, yanajin ta sake dumtse hannunshi sosai da jirgin yazo tashi. Babu wanda zai tsaya mata tayi karatun ne? Ko kudin ne babu?
“Babu wanda zai biya miki ne?”
Ya tambaya a hankali, yanajin kamar bai kamata ya tambayeta ba.
“Yaa Abdallah ne kawai, kuma hidimar da take kanshi da yawa sosai.”
Numfashi ya sauke, da gaske mutane da yawa na cikin yanayin rayuwa, kawai yanayin ne bai taba karasowa kusa dashi ba, ko masu musu aiki a karkashin shi, yana iya kokarin shi wajen ganin ya kyautata musu, saboda yana ganin suna da bukatar duk wani kudi da zai shiga hannuwansu, amman bai taba hasaso haka rayuwar masu karamin karfi take da wahala ba, ace hidima tayi maka yawa har baka da halin cigaba da karatu? A Najeriya fa ba wata kasar ba, ai kudin duk da baisan ko nawa bane yana da yakinin ba wasu masu yawa bane ba.
“Ina kike so?”
Kafada ta dan daga
“Ko ina na samu fa, da ni sai University, amman naga Yaa Abdallah ya sha wahala sosai wajen nema, kuma akwai tsada, tunda karshe dai FCE ya tafi.”
Yatsunta yake murzawa kamar sune abokan tayashi nazarin da yakeyi, kafin ya sauke numfashi yana saka idanuwan shi cikin nata.
“Yunwa nakeji.”
Yanda yayi maganar kamar daga sama ya bata dariya
“Ke kinci abinci? Ni tunda safe f.a”
Kai ta jinjina masa, yanda suna sauka zai nemi abinda zaici ya fada mata.
“Kamar me?”
Ta tambaya
“Bansani ba nima, ke me zakici?”
Ita ko tanajin yunwa ma anya a wannan lokacin da take jinta kamar a wata duniya ta daban zata iya kulla wani tunani?
“Komai na samu.”
Dan shiru yayi, kafin ya jinjina kai yana gyara zaman shi hadi da lumshe idanuwan shi, alamun da suka nuna mata hirar tazo karshe kenan, itama saita juya kanta tana jinjina kudirar Ubangiji, ganin kamar tayi wani irin kusa da sama, kamar inda zata bude gilashin window din, ta mika hannunta tsaf zata iya dangwalo gizan-gizan da kamar ratsasu jirgin yakeyi. A haka suka sauka, sai taga kamar basu wani dade ba, anyi awa kuwa? Daman haka Abujar take babu nisa? Ko dai don a jirgi ne shisa sukayi sauri? Jabir ne yaje ya daukar musu jakarsu, wannan karin tana rike da karamar tata, shikuma ya fiddo wayar shi suna tafiya yana dannawa, har suka fito inda yake so kafin suka tsaya. Ya ajiye jakar a kasa, ya kuma riko hannunta, lokaci zuwa lokaci yake daga wayarshi ya kalla, kamar mai jiran wani abu, kafin wata mota baka wuluk tazo ta tsaya a gabansu.
Shiga sukayi, sanyin motar ya ratsa Sa’adatu, sunyi tafiya ta kusan mintina talatin cikin shiru, kafin taji motar ta tsaya, ko da suka fito saida taja numfashi ganin kyawun wajen, daman akwai hotel me kyau haka? Sai kalle-kalle takeyi har Jabir ya kamata suka shiga ciki, duk yanda take ji da turancinta, da Jabir ya bude bakinshi saita kasa kunne sosai, tanajin kamar ta warware mayafin dake nade akanta ko zata fi jinshi da kyau, ita kanta ma’aikaciyar wani turanci takeyi daya burge Sa’adatu, kafin aka bashi mukulli, yayi godiya yana daukar jakar da wani cikin uniform yazo yana kokarin karba bayan ya gaishe su cikin girmamawa, sai dai Jabir yace masa karya damu, suka wuce. Ita dai tsaftar wajen take ta kallo da kayatuwar shi, sai taga kamarma takawar da suke sun shigo musu da kura, sukazo bakin wani daki da Jabir yasa mukullin ya bude yana turawa, itama tabi bayanshi, sai taga kamar madaidaicin falo, tunda harda kujeru a ciki, sai wani kamshi me sanyi yakeyi.
Amman taga an rubutu hotel daga waje, daman haka dakunan hotel din suke? Karasawa tayi ta samu kujera ta zauna tana karewa dakin kallo, Jabir kuma taga ya wuce da jakar tasu ya bude wata kofa ya shiga, tayi shiru tana kallon kofar
Anan zasu kwana?
Su kadai?
Ita dashi?
Thanks