Dari-darin da Jabir ya kula tanayi dashi ya hanashi rike mata hannu, duk da tsoron da yake gani cikin idanuwanta, har likitan na zolayarta saboda ta kalli Jabir tace
“Amman dai ba za’ayi mun allura ba ko?”
Ko dama akace Sa’adatu ta tashi, ta sake kallon shi saiya dauke kai yana hade fuska, ai dari-dari takeyi dashi tun safiyar ranar, sai yanzun ne zata kalle shi da idanuwanta dake masa ihun neman taimako? Taje ita kadai, tafiyar kuwa sukayi tana jan kafarta kamar ba zata bi bayan likitan ba. Gashi abinda take gudu din shine ya faru, dan cikin gwaje-gwajen da akeyi mata saida aka dibi jini, macece maiyi mata gwaje-gwajen. Gata da fara’a duk da kabila ce, haka ta dinga janta da kananun hira cikin harshen turanci, ita kuma tana amsa mata, a hankali sai gashi ta saki. Haka kuma matar ta dingayi mata tambayoyi tana rubutu a wani abu da yake hannunta, harda lokacin al’adarta, da kuma kwanakin da takeyi.
Zuciyar Sa’adatu sai bugawa takeyi, shikenan ko? An fara, lissafin lokacinta tare da Jabir ya fara tafiya. Yanzun kwai za’a dasa mata, koya ma ake dashen kwan oho, yanzun take ganin wautarta da bataje google ta duba ba, idan kuma akace sai anyi mata karamar tiyata fa? Bugun zuciyarta taji ya karu har makoshinta na bushewa. Fargaba ta lullubeta kamar bargo. Nan matar ta fice ta barta zaune a bakin gadon da yake cikin dakin, ta tabbata duk wanda zai shigo idan ya nutsu, ba zaiji komai ba sai karar AC da take fita a hankali sai kuma sautin bugun zuciyarta da ya danne duk wani motsi idan akwai shi. Ta dade sosai, har taji kamar lokacin da tayi a zaune ya ninku kafin matar nan ta dawo tana ce mata ta fito, ai kafin ma ta rufe bakinta Sa’adatu ta sauko ta saka takalminta ta kuma bita a baya.
“Muje”
Kawai Jabir yace mata, yana juyawa ya fara tafiya, binshi tayi a baya har suka fice daga cikin asibitin, tayi mamakin ganin ya bude wata mota ya shiga, ya matsa can ciki, saita shiga itama. Shiru na ratsa motar, tambayoyine fal cikinta, so take taji yaushe za’a dasa mata kwan, amman batasan ta ina zata fara ba. Sai tayi shiru, ta bari kawai in suka karasa saita duba wayarta taga yanda abubuwan suke, da suka karasa ma baice mata komai ba kamar yanda batace masa komai ba, sai binshi da takeyi a baya. Suna shiga daki ta zauna a falon, Jabir ya shige can ciki, ta warware mayafin da ta nade kanta dashi, tabar hula, filon kujera ta dauka ta matsa can gefe tayi kwanciyar ta a kasa kan kafet bayan ta dauki wayarta. Kanta tsaye ta shiga browser ta fara bincika abinda take nema, ta jima kafin ta soma ganin bayanan daya kamata saboda rashin sanin asalin abinda zata bincika din kai tsaye.
Tana karatun tanajin natsuwa na saukar mata saboda dai duka abubuwan data gani ba masu daga hankali bane ba, bugun zuciyarta taji yana dai-daita, saima bacci da taji ya fara fisgarta, ta kuma kara gyara kwanciya, ita ta karya kafin su fita, Jabir ne baici komai ba. Tana baccin kuma ya wuce ta ya fita yana nufar sashin da zai samu ya sakama cikin shi wani abu, ya kuma shaki iskar da bata gauraye tare da Sa’adatu. Likita ya bashi shawarar anfi samun dacewa idan lokacin ovulation ne, kuma wadannan ranakun a lissafin da sukayi daga bayanin da suka tattara daga wajen Sa’adatu sun wuce, sai dai zasu iya dorata akan maganin na sati biyu, saboda ko an dasa kwanma akwai kaso mafi rinjaye da za’a iya samun rashin nasara.
“Banda wannan lokacin, ayi kawai, in baiyi ba zamu dawo a kara a karo na biyu.”
Dan daga kafadu likitan yayi, Jabir yasan zaice bashida matsala ranshi tunda dai bashi zai kashe kudaden ba idan ba’a samu nasara ba. Sun rigada sunzo kuma sai su karbi magani su koma? Duk abinda suka saka shi yayi? Ai a gwada, idan baiyi ba sun dawo a dorata akan maganin kafin a sake gwadawa. Sun kuma yi washegari zasu koma ayi, shisa ma zaman cin abincin da yayi yake tunanin idan ya koma ya sai musu tikitin komawa na yammacin goben kamar irin yanda sukazo, in yaso suna gama komai da komai goben sai su wuce. A nutse ya gama karyawa ya mike ya koma dakin, baccin Sa’adatu takeyi, dan yanzun ma ta sauka daga kan filon kujerar tayi matashi da hannunta, wayar kuma tana can gefe ta ajiyeta, hularma ta cire, dan tana cikin mutanen dake sakin jikinsu sosai idan baccinsu yayi nisa, kawai sai yaji dariya ta kwace masa, ya girgiza kai kawai ya wuce daki.
Yama za’ayi ace ta saki jiki haka tana bacci a kasa kan kafet? Saida ya fara siyen tikitin tukunna ya rage kayan jikinshi ya kwanta, bai dauki lokaci ba shima baccin ya dauke shi. Sa’adatu ta rigashi tashi, jikinta yayi mata wani irin nauyi, ta jima da bude ido kafin ta mike zaune tanayin mika, ta dauki hularta ta saka, tayi mamakin ganin biyu da rabi, dakin ta nufa tana kwankwasawa a hankali, jin shiru yasa ta turawa da sallama a bakinta. Bacci taga Jabir nayi hankali kwance, kamar mai tafiya kan kaya haka ta lallaba ta shiga bayi, ta kama ruwa tayi alwala, jikinta takeji duk ya bushe mata, shaf ta manta da ya kamata ta dauko man shafawa, danma ba lokacin sanyi bane ba, ko brush haka ta dinga godewa Allaah tana karawa data ga sabo a bandakin, da dole haka zatace ma Jabir bata dauko brush ba, kilanma yace mata kazama, ko yayi zargin rashin sabone yasa ta manta da dauko abu mai muhimmanci irin wannan. Data fito ma haka ta lallaba ta fice tana jan kofar a hankali, ba zatayi gigin tashin shi irin na safe ba, da sauri ma ta girgiza kanta tana son batar da tunanin da yake neman dawo mata, duk da haka saida jikinta ya dauki dumi.
Sallah tayi, ta dauki wayarta tana kiran Fa’iza da ta dinga tsokanarta wai taje Abuja ta samu miji ta manta da ita, dariya ta dingayi kunyar duniya ta lullubeta
“Karkiyi wasa da damarki Sa’adatu, mijinkine, kiyi duk wani kokari wajen jan hankalin shi, kin sha zumar dana baki ko?”
Cikin rawar murya ta amsa da
“Eh na sha, In Shaa Allaah matar Yaya.”
Duk wata magana da Fa’iza takeyi tana jinta, data san ba irin auren da suke tunani bane data daina wahalar da kanta, ga kunya saboda maganganu ne takeyi mata masu nauyi ganin kamar abune daya kamata ta sani yanzun da take da miji. Haka sukayi sallama ta sauke wayar hadi da numfashi mai nauyi, kan kujera mai zaman mutum biyu ta koma, sai dai taja kafafuwanta ta nadesu, littafinta ta bude tana cigaba da karatu, yunwa ta fara damunta, kuma bata ga alamar abincin da suka rage da dare, dama wanda ta rage da safe ba. Duk an kwashe an goge ko ina, har wani kamshi taji dakin nayi sanda suka dawo. Da safen daman ba wani sosai taci ba saboda batajin yunwa, kamar tacewa Jabir abar shi sai sun dawo, sai kuma ta rabu dashi. Sai lokaci take dubawa, shisa akan idonta hudu tayi, tana da alwala saita tashi tayi la’asar ta koma kan kujera. Wannan karin kwanciya tayi saboda cikinta da taji hanjin sun tattare sun koma waje daya. Duk jikinta yayi mata wani laushi, karatun ma ya daina mata armashi shisa ta fita tana yan danne-danne. Karshe ta fada manhajar Twitter da har yanzun ba wani gane kanta takeyi ba.
Duk idan dai taga wanda yayi wani rubutu daya burgeta sai tayi like, wani lokacin ta bude profile tayi following. Ita ba wani abu ma takeyin posting ba, takanyi comment dai a wasu wajajen. Daga baya kuma saita ajiye wayar duka tana tunanin ko taje ta tashi Jabir. Shikuma daya farka saiya shiga bayi, ya watsa ruwa mai zafi ko jikinshi zai warware sosai yayi alwala ya fito, saida yayi sallar azahar ya mike daga wajen ya dauki wayar shi, ya ware idanuwa yana duba lokaci ganin biyar ce yake gani na yamma.
“Biyar fa.”
Ya furta a fili yana sake dubawa cike da mamaki, wanne irin bacci yayi haka? La’asar ya koma yayi, ya sake kaya yana fita falon, hango Sa’adatu a kwance yasa shi tunanin ko itama baccin takeyi, sai dai ai da a kasa take, ko farkawa tayi ta sake komawa to? Da sauri ya karasa cikin falon, tana jin motsin shi kuwa ta mike zaune.
“Kanata bacci.”
Ta furta da wata murya, ya numfasa ta rigashi da fadin
“Yunwa nakeji, tun dazun nakejin yunwa baka tashi ba.”
Ta karasa maganar tana hade gira cikin wani yanayi da yasa shi yin murmushi, ita kuma sam bata ga wani abin nishadi ba.
“Ba saiki tasheni ba? Me yasa baki tasheni ba.”
Baki kawai ta tura gaba tana sake kumbura fuska, dariya Jabir yayi, anya takai shekarun data fada kuwa? Yarinyace sosai.
“Tashi mu fita kawai.”
Kai ta girgiza.
“A kawo mana irin jiya dan Allaah, ba sai munje wani waje da nisa ba, ulcer zata kamani kafin mu karasa.”
Dariyar dai ya sakeyi mai sauti wannan karin.
“Ai cikin hotel din nan ne, kawai wani bangare ne, zaifi muje can muci din ne, sai anfi kawowa da wuri.”
Jin hakan yasa ta mikewa, karamin hijabin ta dauka ta saka, sai wayarta a hannu dan bata ma da karfin daukar jaka, fitar sukayi bayan Jabir ya kulle kofar. Ba wata tafiya mai nisa sukayi ba, sun dai hau bene kafin suka isa wani kayataccen waje, Jabir kuma yayi magana da wani matashi cikin uniform da yayi musu jagora zuwa wani sashi na daban, inda su kadaine a wajen sai tebir da kujeru guda biyu, ko da aka kawo musu Menu ma dan su zabi abinda sukeso, kusan abu kala shida Sa’adatu ta zaba, ji takeyi ma sunyi mata kadan, kawai dan kar Jabir yace tayi zarine. Ba’a wani bata lokaci ba aka fara jera musu abubuwan da suka zaba kan teburin. Jabir nata kallon Sa’adatu yana so yaga inda zata kai abubuwan da ta zaba.
Ko kallon shi batayi ba ta fara da farfesun kayan cikin da ya dinga mata yawo tun tana kwance, tanayi tana hadawa da doya da plantain, shikuwa taliya ce sai kaza da kuma kifi. A nutse ya soma ci shima. Sa’adatu kam tun kafin ma tayi rabi taji cikinta ya cika, sauran abubuwan ma bata ko iya tabasu ba.
“Sai kin cinye ai tas.”
Cewar Jabir ganin ta ajiye cokula ta jingina bayanta da kujera.
“Kace su juyemun to in koma daki dashi, wallahi na dauka zan cinyene, bakaji yunwar da naji ba.”
Kallonta yayi.
“Anan zaki cinye shi, babu abinda zamu dauka.”
Rau-rau tayi da ido ganin yaki yin dariyar ko nuna alamar da zata nuna wasa yakeyi. Ganin ta fara tura baki yasa shi yin murmushi, kafin ta fara mishi hawaye tunda yaga kuka baya mata wahala. Wayar shi yaji kamar sako ya shigo, yasa hannu ya ciro daga aljihu yana dubawa, sai ya ajiye kan teburin ganin ba wani abu bane mai muhimmanci. Ya cigaba da cin abincin shi, kawai Sa’adatu ta tsinci kanta da mika hannu ta dauki wayar tana dubawa, tayi mata kyau, sai dai bata ga sunan ba saboda akwai pouch a jiki, tayi mata kyau, tuntuni take son tabawa ta kare mata kallo, ta shafa jikin da yatsa tana hasashen kudin wayar.
“Tayi miki kyaune?”
Jabir ya tambaya yana nazarinta, kai ta jinjina.
“Sosai, kuma gashi babu nauyi.”
Murmushi yayi
“Kina son irinta ne?”
Idanuwanta ta saka cikin nashi.
“Ni? Taf, wannan ai babba ce sosai, nasan da tsada.”
Kai ya girgiza mata.
“Ba wani tsada, ki fasa asusunki kawai muje ki siyo irinta.”
Dariya tayi
“Kasan asusu daman?”
Wani kallo yayi mata yana jinjina kai, tabbas da kusa dashi take sai yaja kunnenta, me ta mayar dashi?
“Kince wani abu Sa’adatu.”
Dariya takeyi sosai.
“Yi hakuri, Allaah bakayi kama da zaka san asusu bane.”
Mutumin da bai taba dandana wake da shinkafa da mai da yaji ba, idan yace asusu ai dole ayi mamakin inda yaji kalmar.
“Ai kin kyauta.”
Lemon shi da yake cikin kofi kawai ya karasa shanyewa, ya barta a wajen yaje ya biya ya dawo yace mata ta tashi su tafi. Dakin suka koma, duka suna zama a falo, sai taji koshin da tayi gajiya ta saukar mata, Jabir ya kunna musu tv din dake dakin ya dauki remote yana neman tasha kafin ya tsaya kan wata da aka saka wani fim din amurka.
Taga suna dai “Nerve”. Rashin wani abu daban da zatayi yasa ta nutsar da hankalinta, sai kuma fim din ya soma yi mata dadi fiye da zatonta. Tunda tafi son india, sai taga wadannan din ba wani dadi garesu ba sosai. Lokacin da aka gama yayi dai-dai dana magriba, sai suka tashi, shiya fara shiga bandaki, ita kuma ta zauna bakin gado ta jira shi, daya fito ta shiga, falo ta koma tayi sallarta acan. Data idar ta dauki remote tana kara maganar tv din, neme-neme ta shigayi har saida ta samo india sannan ta bar tashar.
Jabir ya jima kafin ya fito daga dakin.
“Me zakici da daren nan?”
Hade gira tayi cike da tunani, bataso tace a koshe take tazo yunwa ta dameta cikin dare, gara dai ta samu wani abin ko bataci ba, zuwa can cikin dare in yunwa ta tasheta tana da abinda zataci.
“Kai me zakaci?”
Kai ya girgiza.
“Da wuya, sai dai wani abu mai ruwa haka.”
Da dare bai cika saka abu mai nauyi a cikinshi ba, yau kuma ya rigada ya ci abinci da yamma sosai.
“Ko zakici nama?”
Ya fada ganin ta rasa me zatace masa.
“Komai ma.”
Ta fadi a sanyaye, wuceta yazo yayi.
“Kizo ki kulle dakin, zan kwankwasa idan na dawo.”
Tashin tayi kuwa taje ta rufe kofar ta koma ta zauna ta cigaba da kallonta. Tana daiyi tana duba lokaci, tayi isha’i ta sake zama da kyau. Karshe ma sai taje ta watsa ruwa ta saka kayan baccinta ta dawo ta zauna, jiyama duk boyon data gama ai yaganta a cikinsu, karshema gado daya suka kwana. Bai dawo ba sai tara saura, ya mika mata ledojin da suke hannun shi yana wucewa batare daya amsa sannu da zuwan da takeyi masa ba. Ta tabbata da cikin talakawa yazo babu abinda zai hana ko ba’ayi masa rukiya ba a hayaka masa maganin jinnu, mutum yanzun fuska a sake, zuwa anjima kuma kaman wanda ya hadu da abokan gaba? Ai dole za’ayi zaton yana da mutanen boye. Matar shi na kokari ta tsinci kanta da fadi, na yan dakika kuma tunanin Aisha da dalilin da yasa suka taho babu ita ya dan tsirga mata, data bude leda daya kuwa, dan taji dayan lemuka ne da ruwa masu sanyi sosai, duk da taga kamar akwai wata ledar a ta ruwan, sai ganin wani irin tsiren hanta ya mantar da ita komai, ciki harda koshin da tayi na yamma.
Taci fiye da rabi, tana godewa Allaah daya nufeta da samun dadi irin wannan,ko da kuwa na dan lokacine, idan ta rufe ido zata dinga tuno tayi rayuwa irin wannan kuma taji dadinta. Ta janyo dayar ledar ta bude, ta dauki ruwa ta bude tasha, tayi koshin da babu wani lemo daya burgeta. Sai kuma ledar datayi kama da kwaline a ciki taja hankalinta, ta dauka ta bude, tana zarowa, kwalin wayane, waya irin ta Jabir, zuciyarta tayi wata irin dokawa, batasan ta mike da kwalin a hannunta ba, ko kwankwasa dakin batayi ba balle kuma sallama ta tura kofar, yana tsaye da dogon wando da singileti a jikinshi, bata ma lura ba, hakoranta kusan gabaki dayansu a waje suke take daga masa kwalin wayar.
“Taki ce.”
Ta fadi a takaice, wani irin ihun murna tayi daya saka shi runtse idanuwan shi, tayi tsalle, ta kuma ruga tana masa rungumar da tayi masa bazata, duka ta farune a cikin dakika, ta rike shi ta sake shi ta cigaba da tsallen da takeyi, ta kuma fice daga dakin da gudu kamar yarinyar yar shekara hudu da kayiwa kyauta da abinda ta dade tana fatan samu. Tabar shi a tsaye da iskar da yaji gabaki daya ta sake masa tun shigowar Sa’adatun, saiya samu waje ya zauna gefen gadon, rungumar da Sa’adatu tayi masa tasa shi jin kamar guduma ta saka ta buge masa gwiwoyin kafafu. Dole ma su tattara su koma gobe, yana bukatar samar da tazara a tsakaninsu, da sauri. Da yaji vibration din wayarshi sai da zuciyar shi ta buga, Aisha ce, mantawa yayi da fushin da yake ya kai hannu ya janyo wayar ya daga kiran ya kara a kunnen shi yana sauke mata numfashi mai nauyin gaske.
“Nayi kewarka, fushi kake mun har yanzun ko?”
Ta fadi batare data jira yayi magana ba, wayar ya gyarawa riko kamar hakan zaisa ya riko Aisha ta cikinta, ya ganta a gabanshi, ko bata tuna masa dalilin da yasa yake tare da Sa’adatu a Abuja ba, to ta zama wata katanga a tsakaninsu, saboda yanajin gab yake da kasa mallakar kanshi akan yarinyar da ya bawa kusan shekaru goma
Tsoro ne yaji ya tsirga masa