Wasa yake da hannunshi akan kujerar jirgin da yake zaune, zaiso ace hannun Sa'adatu ne yake rike dashi, amman taja hannun nata da yake ta gefenshi ta dafe cikinta dashi, tun a hanyar komawarsu hotel daga asibiti, tayi wani irin sanyi, duk da ba zaice yasanta ba, amman anya tana yin sanyi haka? Yana daga cikin dabi'arta kuwa? Ga wani nisantaccen yanayi shimfide akan fuskarta kamar wadda aka daga aka jijjiga aka sauketa ta kai, sannan aka sake dagata aka ajiye saman kafafuwanta. Idan zai fassara kalmar da yakeji tana masa yawo cikin kai zai iya cewa Sa. . .
Allah ya kara basira
Thank you. More updates
Thank you
Allah ya qara basira