Da gaske har zuciyarta, ta dauka duka unguwarsu babu wanda talauci yayi wa daurin goro irinsu. Saboda Sa’adatu bata kallon na kasa dasu sai dai wanda yake sama dasu, idanuwanta basu taba rissina kasa ba balle ta duba gidajen da suke cike a unguwar inda ake dora tukunya sau daya tal a rana, gidajen da sai mazajen sun fita sun nemo na sannan za’aci na safe, na rana harma dana dare, da kuma wanda sai an hada karfi da karfe tsakanin matar da mijin tukunna za’ayi dabarar abinda za’a saka a baki, dama gidajen da idan akaci yau gobe sai dai a wuni ana hamma. Balle kuma ta kalli yanayin gidan, wasu ginin kasane, wasu gidan hayar basu da karfin kamawa su kadai. Nasun da ta raina mai dakuna hudu harda wani a soron gidan inda Abdallah yake, yanda ko bayan da su Nabila sukayi aure, suka ragu a dakin, gani takeyi yayi musu kadan.
Inda zata same shi ita kadai zatafi so, ace kuma da bandaki a cikin dakin kamar yanda na Asiya yake, da makeken gado. Amman katifu ne guda biyu kawai da tun tasowarta take ganinsu, yanzun kuma fitinarta yasa yan uwan suka hakura suka bar mata guda daya ita kadai. Inma wani ya raba ya kwanta, to ba zai taba jin dadin baccin ba ranar, Sa’adatu ta dinga saka gwiwar kafa da ta hannu tana zungurin shi kenan, dan net din da aka daura saboda azabar sauro irin na garin Kano da ya gawurta ya raina kananun magungunan sauro, sai ta tashi ta kware, tace zafi ya isheta, haka sauron zai hadasu yaita gartsa. Karshe dole ka hakura ka bar mata katifar tunda a wajenta in dai bukatarta zata biya to zata jure komai. Rigima kuma a hana ido bacci a kwana anayu bakomai bace a wajenta. Idan ma dukane ba jinshi takeyi ba.
Kamar yanda ta taso cikin rufe ido daga abinda take dashi da kuma hangen wanda bata dashi, abin karuwa yayi yanzun da rashin Habibu ya fara tambayarsu tun bai rufa watanni shidda da rasuwa ba. Dan abincin da abokan arziki suka tara musu, fiye da rabin shi a wajen zaman makoki aka dafe. Kafin wani lokaci kuma ya kare musu. Naman da duk rintsi, lokacin da Habibu yake da rai, ba’a ko kwana biyar ba’a saka a miya ba, ko da kuwa yanka dai-dai ne. Idan bai samu ya aiko dashi ba, zai kunso dan balangu ko tsire kowa ya maida miyan shi. Balle kifi da in dai ya samu wasu yan canji saiya siyo ya taho musu dashi. Akwai sanda ta fara bacci aka tasheta aka bata nata kason, da ta ja siririn tsaki bayan ta haska taga irin kananun kifin nan ne da ake soyawa a bakin titi a bade shi da yaji.
“Yanzun akan wannan kifin magen aka katse mun bacci?”
Duk rashin magana irin na Nabila a lokacin sai da tace mata.
“Wai me yake damun kine Sa’adatu? Ke ba zaki taba karbar abu ko baiyi miki ba ki duba kokarin wanda ya siya, idan baki gode ba kija bakinki kiyi shiru? Dan ana saka miki ido baya nufin abinda kikeyi abune mai kyau.”
Tura baki gaba tayi, wani abu daya zame mata dabi’a.
“Karya nayi? Wallahi irin shine ake ba magen su Asiya.”
Kai Nabila ta girgiza tana fadin.
“Allah ya kyauta.”
To yanzun rabonta da jin dandanon kifi a bakinta harta manta, ba zatace bata saka shi a ido ba, tunda akwai masu suyar a hanyarsu ta makaranta. Rayuwar ji takeyi ta mata zafi fiye da kowa, saboda Hajiya kwanaki talatin da hudu ne tsakanin su da Habibu, tun wannan zazzabin daya saukar mata lokacin rasuwar shi, bata kara lafiya ba, ashe ma bana tashi bane. Wata mutuwa da ta daki Sa’adatu saboda gani takeyi kamar rashin Habibu, wannan dinma ita akafi yiwa. Kamar dai a dan tsakanin rayuwa ita ta zaba ta yiwa ruku’un dila. Sai su Hajiya ma suka tashi, saboda a yanda taji an bawa Baban su Asiya wani mukami ne, kasancewar gwamnatin da ta hau mulki tasu ce, shine ya samu ya karasa gidan su daya dauki shekaru yana ginawa a hotoro. Ai lokacin tashin, kowa yayi mamakin irin kukan da Sa’adatu tayi. Sai aka dauka shakuwar da sukayi da Asiya ce, har Hajiya nace mata.
“Ai dan mun tashi ba wai an yanke zumunci bajw gabaki daya Sa’adatu, in dai Asiya ce lokaci zuwa lokaci zansa a dinga kawota kuna gaisawa. Kuma kema ai wani lokacin zaki biyota idan ranakun da ba makaranta ne.”
Sai dai ita ba nisa da Asiya bane matsalarta, dan abinda take samu daga wajen Asiyar da zai yanke shi take yiwa kuka, tun bayan rasuwar Habibu sai tausayinta ya sake baibaye Asiya, dan har karin safe takan miko mata. Tun da suka tashin kuma sai cin abincin gidan nasu da ta kara rainawa a yanzu ya zame mata dole. Ko dan yunwa data fara neman yi mata lahani. Idan tuwo ne, sai ta yayyanka shi ta kwada da manja, sai da Abida ta fito mata ta bayan gida ganin irin barnar man da takeyi mata. Ranar ma tayi kuka har saida ran Abida ya sosu.
“Da Abba na nan babu abinda zai sakani cin tuwo kin sani Amma…”
Ta fadi hawaye na zubar mata. Da Habibu na nan itama da ba zata hanata dibar manjan ba. Bayan wainar filawa, harda taliyar hausa take hadawa yanzun da safen, da kuma wake da shinkafa da rana. Duk dan su samu abinda zasu rufawa kansu asiri, ita ba ‘yan uwa gareta masu hali ba, ko suna dashi babu wannan zumuncin na taimakon marar shi, yarta tilo da take da yakinin in tana dashi ba zata jigata ba, itama nema suke. Duk da a halin rashin da suke fama, duk juma’ar duniya sai tayi mata aiken kayan miya, ko da bashi da yawa, wata ranar harda naira dari ko dari biyu, garin tuwo idan ta samu halin hakan, tun bayan rasuwar Habibu. Tana kara tuna mata shi aikin alkhairi ba sai kana da wadata ba, tunda ba kadan yakeyi ba.
“Ya kamata mu shawarta sana’ar da zamu fara don mu rufawa kanmu asiri, kinga maigidan nan wata shidda ya kara mana, mu zauna kyauta kafin mu cigaba da biyan kudin haya, ga hidimar makarantar yara, ga abinda za’aci, ga kuma yanayin rayuwa da take cike da kananun bukatu da manya.”
Abida ta cewa Asabe bayan sun fita takaba, sai ta rushe da kuka kamar ta rufeta da duka tana fadin.
“Na shiga uku, mutuwa mai tonon asiri, yau ni Asabe rashin Habibu na neman tozartani.”
Ta dinga fada tana maimaitawa, kafin ta kekashe kasa tace ita bata ga wata sana’a da zata iya ba. Fatarta ba kalar da zata kusanci murhu bace ba, tunda ko da Habibu na da rai a gawayi sukeyin girki, Abida ce kawai in tuwo ne sai taga gara ta hada itace sai yafi mata sauri, ko yara su hada, to itama Asaben nata yaran kanyi haka. Basa kuma damuwa da zagin da take hawansu dashi inta gani, cewar wai jikinsu zai lalace, zasu zo suyi baki suna kaurin hayaki. Haka ta linke hannayenta, sai dai abinda ‘yan uwanta da suke da tsananin hadin kai duk kuwa da talaucinsu suka harhado mata suka kawo. Sai kuma Abdallah, da tun kafin rasuwar Habibu yayi jamb, bai ci ba, sai Habibun yace ko da Polytechnic ce ya fara ko FCE, idan ya gama sai ya jona ya cigaba a jami’ar, da yake yana da burin ganin Abdallahn yayi karatu, burin da mutuwa ta gifta a tsakani.
Yanzun shi da kanshi ya danna wannan burin can kasan zuciyar shi, da kanshi ya zagaya bayan layinsu ya samu Malam Yusha’u ya roke shi akan yayi wa babban danshi da kowa yasan yana da garejin gyaran motoci ne acan wajen Zoo Road, don ya fara zuwa koyon aiki. Tunda daman burin shi akan karatun bangaren gyaran motocin ne. Da yake kuma anyi zama na mutunci, Malam Yusha’u ba mutum bane mai manta alkhairi, gyaran motar da dan nashi yakeyi, yake rike da iyalin shi dama su iyayen shi, silar shi Habibu ne. Ba zai kuma manta ba, Tasi’u sanda yaki makaranta yaso ya lalace ne ta hanyar bin abokanan banza, Habibu kuma na daga cikin mutanen da Tasi’u yake mutuntawa, shi ya dauke shi ya kai shi wajen gyaran mota, a lokacin ya biya yace a koya masa. Sai akayi sa’a ya zama sanadin shiriyar shi, da yake kuma yana da rabo a harkar harya samu daukaka.
Duk da Abida bataso wannan lamari ba.
“Yanzun shikenan batun karatun Abdallah?”
Murmushin karfafa gwiwa yayi mata
“Duka bamu hango rayuwar zatayi wannan juyin da mu ba Amma, kinga ko hayar gidan nan, kudin zaune suke, balle azo maganar abinci da sauran bukatu…”
Kallon shi Abida tayi, tun rasuwar Habibu tana kula, wata irin natsuwa ta sake shigar shi. Girman daya haushi ya bayyana har akan fuskar shi. Idan kasan Asabe, ka kuma yi zaman yini daya da Abdallah, kamanni ne kawai da kuma jini da baya karya zai hanaka musun cewa ba daga jikinta ya fito ba. Sai dai kuma duka yaranta babu wanda yayi halinta, jinin Habibu yayi rinjaye akan nata. In da nauyin bai yiwa Abida yawa ba, da ba zata barshi ya hakura da karatun shi ba, ko yanzun kuma ita a zuciyarta wannan burin bai mutu ba. Saboda bayan asusun da sukeyi ita dashi na kudin hayar gidan, tana yin wani daban da take fatan kafin shekara ta zagayo sunyi taruwar da zasu siya masa form din makaranta, su kuma isa biyan kudin, sauran tana da yakinin Allah ba zai hana musu ba.
Wannan nauyin ne yasa Abdallah ya rage hidimtawa Sa’adatu, tunda kudin makarantar su yana kan shi, ga kuma Asabe data nade hannayenta. Itama duk abinta Sa’adatun, tausayin shi takeji, duk yayi wani iri, kamar bashi ba, yayi wani duhu da wahala ce kawai take saka shi. Ga wani gashi daya fara cika masa fuska. Tun bakwai ya fice daga gida, dan yana rigansu, kuma baya dawowa sai bayan isha’i. Wata rana ma har tara na dare yana kaiwa, ko kowa ya shige daki, ita tana nan tsakar gida, ta baza litattafan makaranta ko da ba zatayi komai ba kuwa, dan ta ga shigowar shi
“Yaa Abdallah”
Ta kan fadi a madadin sannu da zuwa, kamar yanda kiran sunan nashi yake maye mata gurbin abubuwa da yawa, kuma ya zama wani mutum guda daya da take jin ya rage wanda yake fahimtar ta, a tare dashi bata bukatar kalamai masu yawa. Yanayin muryarta kawai zata canja wajen kiran sunan nashi zai fahimceta.
“Bakiyi bacci ba Sa’adatu?”
Shine amsar shi ko karfe nawa kuwa ya shigo, ko da zai ga sauran a tsakar gida, ita kadai zai ware yayi wa wannan tambayar.
“Yanzun zan kwanta Yayaa.”
Kuma ba karya bane ba, tunda dawowar shi lafiya ne abinda take son gani.
“Ko akwai wata damuwa?”
Tambayar da take sanyaya ran Sa’adatu, tambayar dashi kadai yake yi mata, kamar yanda shi kadai ne bata iya tunkara da damuwar a yanzun ko da kuwa tana da ita. Saboda nauyin da take ganin yayi masa yawa, saboda in har ya samu sarari sai ya bata kudi. A cikin wannan tsakanin ne kuma tunanin da bai taba zuwa kanta ba yazo, saboda matsin da take jin kamar ita kadaice a ciki. Tunanin fara kula samarin da take ganin ko kyallinta basu kai su hanga ba balle su tsaya waje daya da sunan zance. Wanda ta kwallafa rai a kanshi, Haris din gidansu Asiya, ko da basu tashi daga unguwar ba, Asiya tace mata anyi maganar auren shi, yana dawowa za’ayi, da ‘yar abokin Baban su da suka fara soyayya tun yarinta. Maganar da ta kwana biyu tokare da kahon zuciyar Sa’adatu, bawai son Haris takeyi ba, tunda ko ganin shi bata tabayi ba, amman tana son hutun da take hangowa a tare da samun shi.
Ta kuma ji haushin Asiyar sosai a lokacin, sanda ta ware bakinta ta fara bata labarin Haris din, me yasa bata hada da cewar yana da mata a hannu ba? Sai da ta zauna ta dinga shirya hanyoyin da zata bi don ta samu shiga a wajen shi? To sunma tashi, balle har inya dawo, abokan shi suka fara sintiri gidan, itama tabi sahunsu ko zata dace. Illar da take jin tashin su Asiya tayi mata ba karama bace ba, don ta wuce yankewar samun abinci, harda wasu daga cikin burukanta. Su Asiya ne wani zare guda daya da take dashi na haduwarta da masu kudi. Tana ta baza ido ta ga ta inda Asiya zata bullo ne ko yanzun, tunda tana jin unguwar da suka koma ta masu kudi ce, tazo din dai, ta kuma dauketa taje taga gidan nasu da unguwar ma gabaki daya.
“Ance ana sallama da Sa’adatu.”
Wani yaro ya fadi bayan yayi sallamar da bai jira an amsa ba.
“Kace ina zuwa.”
Sa’adatu ta fadi, tana sa Abida da take zaune kan dardumarta bayan idar da sallar Magriba, don ta rigada ta saba, sai anyi isha’i ta gabatar da ita, ta karasa azkar da adduo’inta sannan take mikewa ta nade dardumar. Da ta ga Sa’adatu ta dauki hijabi tana fadin.
“Ana kirana a waje Amma.”
Sai da ta sauke numfashi, saboda ranar ce karo na farko da aka aiko kiran Sa’adatun ta fita, amsarta daya ce.
“Bata nan.”
Idan kuma Abida tayi mata magana zata ce.
“Amman tarkacen samarin nan ne fa da zasu zo su isheka da shegen surutu.”
Sanin in ta matsa mata, ranta ne zai baci a banza tunda Sa’adatu bata lankwasuwa, sai ta kyaleta, ta dai cigaba da yi mata addu’ar da duk a cikin yaranta babu wanda yake samun kamarta, tunda a ganin Abida tafi sauran bukatarta. Daga farko, lokacin da ta fara tasawa, Abida ba tayi zaton Sa’adatu zata gama aji uku babu maganar auren wani akanta ba, ba dan tafi kowa kyau a gidan ba, sai dan komai na Sa’adatu na nuna cewar ita din mace ce, komai nata na nuna zai wahala idan ba’a halicceta a duniya don maza su bauta mata ba. Ko wanne motsi nata yana nuna cewar ita din macece. Kuma hakan na kara tabbata da yanda zai wahala rana ta fito ta fadi ba’a aiko ana kiranta ba. Fitace batayi, sai yanzun. Sai dai me? Ba’a hada wata daya ba, murnar Abida ta koma ciki, saboda babu ranar da ba za’ayi sallama da Sa’adatu ba, ba kuma mutum daya ba. Kowa yazo fita takeyi, ta dawo da ledoji ko kudi.
“Wacce dabi’ace kike son dorawa kanki Sa’adatu? Zagi kike so ki jamun a unguwa?”
Baki ta turo tana kada idanuwanta.
“Idan nace ba zan fita ba kice ba kyau wulakanta mutane, yanzun kuma ina fitar shima ya zama abin magana Amma? Ni komai nayi banyi dai-dai ba? Bafa ni kadai nake fita zancen nan ba a cikin gidan nan.”
Binta da ido Abida tayi.
“A cikin wanda kike maganar wa kika ga a rana tana fita fiye da sau daya? Wa kika ga tana shigowa da wannan kayan da kike shigowa dasu? Ke ko tsoron samarin zamanin nan bakyaji? Idan kika zo baki aure su ba sukace a biyasu wannan hidimar da sukeyi miki fa?”
Sam maganganun Abida basu shigi Sa’adatu ba, tunda ba rokonsu tayi ba, su da kansu suka kawo mata, tana bukata sai tace ba zata karba ba? Ko asirin da ake cewa Samari nayiwa ‘yan mata a zuba a abu a kawo musu, ita bata taba aminta da wannan shirmen ba, wanda duk ya kawo sai ta karba. Idan ya tashi ya dade baice sai an biya shi ba, ko su da suka zo wajen nata, ai sun ganta, sun san ita din ba kalar aurensu bace ba. Rage dare sukeyi da ita, abinda suka kawo kuma kamar siyen tsadadden lokacinta ne. Har zaunar da ita Abida tayi tana mata wata nasiha ganin fadan da hargagi yaki shigarta, a cikin nasihar ne taji ta hado mata da maraicinta da ko kadan Sa’adatu bata ga alakar shi da samarin da ta fara samun saukin kuncin da suke ciki ta sanadinsu ba. In ba data fara tara su ba, yaushe rabon da ko kamshin nama taji? Amman yanzun har ‘yan uwanta in an kawo tana sammusu.
Tunda ada inta boye taci ita kadai, ta san suna da Habibu da duk rintsi zai nemo ya kawo musu. To yanzun in bata sanadinta ba, basu da mai basu. Shikenan sai Abida ta labe bayan wasu hujojji da bata ga tushensu ba tace ta daina tsayawa da Samari? Ganin taki ji yasa ta fadawa Abdallah daya sami Sa’adatu yace mata.
“Wannan samarin bana son inji ance kin kara tara su, in akwai wanda kike so a cikinsu, ki tsayar dashi, shi kadai ya dinga zuwa, in kuma babu duk ki sallame su kafin Allah ya kawo wanda zai kwanta miki.”
Idanuwanta cike da hawayen takaicin daya turnuqeta tace,
“Yaa Abdallah”
Nashi idanuwan da suka yi mata kama dana Habibu ya saka cikin nata
“In dai na isa kenan, in kuma ban isa ba zaki iya yin abinda duk kike so”
Ya karashe da wani yanayi a muryar shi da yake tasiri akanta a ko da yaushe. Bataji haushin shi ba, saina Abidar data san ita ta hadota dashi. Shisa ta dauki gaba da kowa a gidan.
“Yar sarakan bakin hali, Allah ya yaye miki.”
Asabe ta bita dashi wata safiya da take tambayarta abinda take sakawa alalenta in zatayi takeyin ja sosai. Ta amsata can kasan makoshi.
“Abinda na taso naga kuna sakawa”
Ta gyara zaman jakar makarantarta a kafada ta fice. Ba shiri Asabe takeyi da kowa ba, ciki harda yaranta da take takaicin rashin kishinta da basayi har suke girmama Abida, gidan duka babu wanda ya tsiri daga tijararta inta tashi. Sun sabane shisa baya damunsu, sun dai fi rashin jituwa da Sa’adatu, kuma duka gidan babu wanda ya ci jibga a wajen Asabe kamar Sa’adatu, ko yanzun in dai tana kusa da ita, to sai ta kai mata masga. A lokacin da kowa yake zabar shiru idan tijarar Asabe ta biyo ta kanshi, to Sa’adatu sai ta tanka. Ko da bayan dukan da Asabe zatayi mata, Abida zata kara mata da wani. Aiki kuwa idan na Asabe ne, kuma Sa’adatu ta saka, ba zata taba ganin dai-dai ba, ko wanke wanke, nata kwanonin ne take bari karshe, saita tsoma su a ruwa ta dauraye mata babu ko omo, da gangan saita saka duka kofuna a cikin tukunyar miya dan su nadi maiko sannan zata saka su a ruwan ta dauraye.
Idan tazo tana fada sai Sa’adatu tayi kwal-kwal da ido tana fadin
“Amma wanke-wanken da nayi yau bai fita ba dan Allah? Ke kinga maiko a kofunan ki? Ko kinga sauran kanzo a jikin tukunya?”
Abida bata amsata, tunda tasan kadan ne cikin abinda zata iya aikatawa. Akan dole in dai Sa’adatu ce tayi wanke-wanken gidan sai Asabe ta sa an sake wanke mata, idan ma tana kusa zatace kar Sa’adatu ta taba mata kwanoni.
“Da ban haihu ba da takaicinki ya karni Sa’adatu, to Allah ya bani nima.”
Idan Sa’adatu na son tunzurata sai ta biye mata tana fadin.
“Haba Mama, yanzun ladarki ne bakya so in samu? Ko so kike kija Amma tayi mun fada duk yanda nake kokarin gujewa bacin ranki.”
Ai sai ta cigaba,tana fadin in dai ladarta ne Sa’adatu ba zata taba samu ba, ko duba yanda Sa’adatun ke kunshe dariya batayi. Musamman yanzun ma, ta mayar da Asabe kamar wata kakarta, duk da batama cika wuni a gidan ba, babu wanda ya san inda take zuwa, tana iya ficewarta tun safe har dare. Idan ta dawo kuma ko ta shige daki, in dai zata fito Sa’adatu na tsakar gida saita takaleta, in kuma tana tsakar gidan ta shigo itace gaba wajen saurin yi mata sannu da zuwa tana dorawa da,
“Me aka kawo mana a leda ne Hajiya Mama? Inzo in amshi kaso na?”
Bata damuwa da hararar da take zabga mata, ko amsar
“Tunda uwarki ta aikeni ai sai kizo ki amsa”Saboda ko ya ranta ya baci in ta batawa Asabe nata ran sai taji sanyi. A haka ranar asabar din da ba zata manta ba, an aiko kiranta bayan Magriba, ta dauki hijabi saboda a bakin kofa taje zubar da shara taci karo da yaron, tasan harta dawo Abida bata fito daga daki ba. Bakinta kuwa yaki rufuwa ganin Tahir da dukkan nutsuwar shi zaune akan mashin din da yazo dashi
“Yaa Tahir.”
Ta kira cike da mamaki saboda bata sa ran ganin shi ba, a lissafinta sauran sati biyu yazo.
“Baki san waye bama kika fito ko?”
Yayi maganar wani kishinta na tasowa daga kasan zuciyar shi, musamman kyan da tayi masa. Idanuwan nan nata kamar sun kara haske, duk da yaga tayi duhu a hasken lantarkin daya haska unguwar. Ita dai fara’a kawai takeyi tama rasa abinda zatace masa.
“Wai duk murnar ganin nawa ce haka?”
Kai ta daga masa tana sake kallon shi bayan ta karasa kusa dashi ta tsaya
“Ka shammaceni ne, ni da nake ta lissafi ina kirga kwanaki wajen sha biyar”
Dariya yayi
“Jarabawar ce aka saka mana ita lokacin da bashi muke hasashe ba.”
Ta jinjina kai, koma meye ita sun gama mata komai tunda gashi a gabanta, ta tabbata kafin lokacin komawar shi abubuwa zasuyi mata sauki.
“Kun kusan gamawa ai ku huta”
Numfashi ya sauke, kalmar sun kusan gamawa nayi masa dadi har ranshi, karatu akwai gajiya, kowanne dalibi zai shaida hakan.
“Saura shekara daya In shaa Allah”
Ya karasa maganar yana saukowa daga kan mashin din da yake zaune, kamshin turaren ah mai sanyi ya daki hancinta, tana kallo ya daga inda ya tashi yana ciro abu a leda, zuciyarta ta fara tsalle cike da zumudi, dan tasan ko meye ma nata ne. Sai dai daya juyo ya kalleta, akwai wani yanayi a cikin idanuwan shi daya dishe dokin da takeyi kadan, musamman daya kira sunanta yana dorawa da,
“Dan Allah daga Amma sai Abdallah zasu san kyautar nan daga wajena ta fito, kinfini sanin halin Mama…”
Kai take daga masa tun kafin ma ya kai karshen maganar, ya mika mata ledar hannun shi.
“Ina son duk sanda nake son magana dake in samu yin hakan kai tsaye ba sai na biyo ta hannun wani ba.”
Ta tabbata da idanuwan shi akan kirjinta suke babu abinda zai hana shi ganin bugawar da zuciyarta tayi tana fada mata waya ce, waya Tahir yake bata. Da sauri kuwa tasa hannu ta karba tana rasa abinda ya kamata tace masa, ta ina zata fara masa godiya da cika mata mafarkin da ta fara tunanin ko a cikin bacci yayi mata nisa balle kuma ido biyu?
“Ki fara shiga gida, zan biyo bayanki.”
Batayi masa musu ba, ta juya ta shiga gidan, ta kuma tsinci kanta da wucewa dakin Abida kai tsaye ta samu waje a gefen bango ta zauna tana jingina bayanta, batare data cire hijabin jikinta ba, ta tura mata ledar, tana sakata kallonta.
“Yaa Tahir.”
Kawai ta fadi, Abida ta kama ledar ta kwance tana fito da wayar a cikin kwalinta, Nokia X2. Wayar da su duka basu san tarin abubuwan da Tahir ya hakura dasu na watanni dan kawai ya mallakawa Sa’adatu wayar ba, ko shi wadda take hannun shi bata kai wannan din ba. Da bugun zuciya Abida take kallon wayar, sannan ta kalli Sa’adatu, wayar na tabbatar mata da zargin da takeyi na Tahir na son Sa’adatu, tana kuma hasaso mata tashin hankalin da hakan zai haifar tsakaninta da Asabe.
“Yace ke kadai zan fadawa shi ya bani dan kar Mama taji.”
Bugun zuciyar Abida ya karu, shi kanshi Tahir din ya san wannan abin dai-dai yake da tashin hankalin kowa idan Asabe ta sani, shisa yake son su hadu su rufeta. Wani abu da batajin zata iya, saboda ita macece da take son yin abubuwanta kai tsaye, hankalinta ba zai kwanta ba, saboda gani zatayi ko yaushe Asabe zata iya sani, boye matan zai kara zama wata fitinar ta daban. Kafin ta kulla abinda zata fada Tahir yayi sallama a bakin kofar, dan bai samu Asabe ba, ta fita. Ta kuwa ce ya shigo, bayan sun gaisa ba bata lokaci tace masa.
“Yanzun Sa’adatu take nuna mun waya…Tahir wannan wayar ai tayi girma, kuma me yasa za’a boyewa Asabe? Bakasan komai da sanin iyaye yafi albarka ba?”
Kallon razana Sa’adatu tayi mata, inda Tahir baya dakin, da ta mika hannu ta dauki wayar sai taga yanda za’a kwashi yan kallo idan akayi kokarin rabata da ita. Kuma duka maganganun Abida taga wannan bigiren suke dosa. So take tace ba zata rike wayar ba, ko kuma a fadawa Asabe ta tashi bala’i tace saiya karbe. Lokaci daya kwalla ta fara taruwa a idanuwanta. Tana neman dalilin da zaisa Abida ta dinga kokarin gina katanga a tsakaninta da abubuwan da suke sama mata saukin kuncin rayuwar da suke ciki.
“Amma yanzun duk wata kyauta da Abdallah zai yiwa Sa’adatu sai da sanin Mama yake yinta? Idan albarka ce kema zaki iya saka mana. Dan Allah karkice tayi girma, ko saina fadawa Mama kafin in bata, in dai nima ina da iko akan kanwar tawa kamar yanda Abdallah yake dashi.”
Har yanzun zuciyarta ta kasa natsuwa, amman kalaman shi sun daureta, yanda yayi su kanshi a kasa cikin sanyin murya sun tabata. Inda Asabe na duba halayen yaranta, da ta kasance cikin godiyar Allah da kyautar su da yayi mata.
“Allah yasa albarka ya bar zumunci.”
Murmushin da yayi ya sake kawata fuskarshi da take cike da kwarjini. Yayi mata sallama ya mike, yana fadin.
“Saida safe kanwata.”
Kai kawai Sa’adatu ta iya daga masa, yana sakin labulen ta kai hannu ta jawo kwalin wayar tana fara zazzageta. Shikuma fita yayi daga gidan gabaki daya, ya hau mashin din da yazo dashi, wanda na Bashir ne, mutum daya da zai kira aboki. Sai ga Asabe ta bullo, hakan ya sashi saukowa daga kan mashin din ya tarbeta da fara’ar shi. Sai dai yau nata farin cikin yayi nisa, ranta a jagule yake.
“Yanzun nazo akace kin fita, daman zan gaishe dake ne”
Murmushi ta kakalo tayi masa.
“Ka kyauta ai, Allah yayi albarka, ka gaishe da dan uwanka da mutanen gidan.”
Ya kula yau bata son doguwar magana tunda harta sallame shi da wuri haka. Shima sai yayi mata saida safe ya wuce kawai. Ita ta shige gida, ta nufi dakinta ta zauna kan ledar dakin tana tunanin mafita. Da wani yace mata zata sake marmarin yin aure a watan daya wuce zata karyata. Da gaskene taso Habibu, tana kuma son shi har yanzun, tana jin babu wani namiji da zata mikawa zuciyarta haka. Ko da Uwani, kawarta tayi mata zancen wani auren dariya tayi.
“Wanne aure kuma Uwani? In kai ‘yan matan da suke gabana ina?”
Da take ce mata har yanzun batayi girman da zatace wai zata zauna ta tallafi yara ba, yaranma da suke da hankalin da zasu iya kula da kansu. Da kuma take fada mata tana da kyawun da masu kudi zasuyi rububinta in ta basu dama duk jin zancen kawai ta dingayi.
“Nifa har gobe banga me kika gani kika auri Habibu ba wallahi, da kyanki kikaje kika dinga irin wannan rayuwar.”
Maganar data sosa ranta kenan ta sakata yiwa Uwani sallama a ranar, wannan kushen da take yiwa Habibu tun suna ‘yan mata da Asabe ta dauki son duniya ta dora shi akanshi, shiyake hadasu fada. Kuma cikin ikon Allah, a wajen hidimar bikin Asaben da Alhaji Hashimu, Uwani ta hadu da nata mijin, wani matashin dan kasuwa maiji da kudi, abokin dan uwan Alhaji Hashimun ne da sukazo taya shi murna. Kuma yana mata wani irin so da zai baka mamaki. Kusan abinda duk take so ita da yaranta shi akeyi a gidan. Duk kuwa da dangin shi basa sonta, musamman da hasashen su akanta ya zamana gaskiya. Uwani macece da idonta yake a bude tunma kafin tayi aure, bayan tayi din ta hadu da gogaggun abokai, da sun girme mata, amman haka ta shiga cikinsu, su suka koya mata shige-shige, harta hada da son da mijinta yake mata wanda bahu algus a ciki da kuma wanda ta nema ta samu a wajen Malamai, tayi katanga tsakanin shi da ‘yan uwan shi, daman iyayen sun jima da rasuwa.
Yanzun haka kasuwanci takeyi na atamfofi da leshina, har Legas tana zuwa sari. A shekarun baya kawancen nasu da Asabe yayi sanyi, saboda yanda take yawan yi mata magana kan zuwa wajen Malamai, in dai Abida ce da yaranta sai sun zama ‘yan kallo a cikin gidan. Amman Asabe bata da wannan ra’ayin, tana da fada, mita da neman magana. Amman ita kanta tasan Abida bata da muguwar zuciya, na rana daya bata taba yiwa yaranta mugunta ba. Daga nesa in ba an fada maka ba, ba zaka tantance waye nata ko na Asabe a cikin yaran ba. Haka kuma bata taba nuna mata cewar ita matar so bace a wajen Habibu. To me yasa zataje ta mikawa wani Malami kudadenta? Bayan bata da wani dalili mai karfi nayin hakan. Kuma ko babu wannan tana da tsoro sosai.
Kawancen ya fara dawowa ne bayan tazo mata gaisuwar Habibu, ta kuma dawo, ta sake dawowa duk da bata da wani abu da take kara Uwani dashi. Sai itama ta cigaba da zumunci da ita, har ta dinga kwadaita mata sake yin aure, aure bawai don so ba, aure kuma ba irin na Habibu ba, aure na hutu, arziki taci, na kusa da itama suci. Tun batajin zata yarda da maganar har yau da gobe, halin da suke ciki, maganganun Uwani suka fara zauna mata, musamman da ta ce.
“Ko dan ‘yan matan dake gabanki ai kin tashi ki tsaya da kafafuwanki Asabe, idan maganar aurensu ta taso dame zakiyi musu kayan daki? Tunda ubansu ba wani abu ya bari ba, ba kuma ‘yan uwan da zasu huce miki takaici gareki ba.”
Ranar data koma gida haka ta kusan kwana tana juyi, da gaskene, ita batama taba kawo wannan tunanin a ranta ba, ganin cikin rufin asiri, kuma dai-dai karfinsu akayi bikin su Nabila. To yanzun Habibun da zasu jingina dashi babu. Akwai yaron da yake zuwa wajen Nana, duk da shima karatu yake, ko da za’a tsaida magana saiya kammala, amman wa take dashi da zai bata idan lokacin ya taso? ‘Yan uwanta suma karfin haline sukeyi wajen taimaka mata, hidimar aure kuwa ba abu bane mai sauki.
“Akwai Alhaji Salihu da nake sarin atamfofi a wajen shi, idan kina so wallahi zan hadaku, kinsan ‘yan Kano da farar mace, mai kudine na gaske…”
Uwani tayi mata tayin data kasa tankwabewa. Duk da jikinta yayi sanyi bayan ta ganshi. Wani mutum da yake hararo sittin, bakikirin dashi, guntu da tumbin da zaka fara hange idan kwana zai shawo kafin sauran jikin ya biyo bayan shi. A haduwar farko ya fallo kudi har naira dubu goma ya danka mata.
“Ke yanzun ai kin wuce yin aure dan so ko wani abu, ki daiyi don rufin asirinki dana yaranki.”
Maganar Uwani ta fado mata, kuma ga dukkan alamu asirin nata zai rufu idan ta amincewa auren Alhaji Salihu. Data shawarci ‘yan uwanta ma kowa ya bata goyon bayan sake yin aure tunda bata wuce hakan ba. Saita kara samun kwarin gwiwa, sai dai batayi zaton kai tsaye zaice mata ba zai rike mata su Nana ba. Ta dauka yana da arzikin da idan yaran sunfi haka ma zaice ta tattaro ta taho dasu. A cikin wannan tashin hankalin take, gashi yace yana so a tsaida magana. Habibu bashi da ‘yan uwa maza da zatace ta dauke su ta mayar dasu can. Uwani tace ta tuntubi cikin nata ‘yan uwan, ita da zata fara kama kudi, in dai tana basu wani abu, babu wanda zai ki rike mata. Hawayen rashin Innani saida suka zubo mata. Inda tana da rai, komai sai yazo mata da sauki.
Ko kadan duk satin bata samu natsuwa ba, har saida Kawu Ila yace su Nana su koma gidan shi, tunda shima yana hango samun na cefane daga wajen Asaben. Tunda tace Alhaji Salihu Danbatta ne, yaji wani abu ya tsirga masa. Don ya sanshi a kasuwa, babu ma wanda yake harkar atamfofi a kasuwar da zaice baisan Alhaji Salihu Danbatta ba. Shisa batayi tunanin yaran zasu kalleta kamar tana neman rayuwarsu dan tace zata sakeyin wani auren ba.
“Duka yaushe Abba ya rasu?”
Nana ta fadi tana kallonta da hawaye cike taf a idanuwanta.
“Ni wallahi ba zan bar gidan nan ba, babu inda zan koma”
Cewar Sadiya itama kuka na kwace mata. Zagin duk da tayi musu kamar ma kara tunzura su takeyi dan da gudu Sadiya tana kuka ta fice daga dakin ta samu Abida da take alwalar la’asar a tsakar gidan tana fadin.
“Amma dan Allah karki kore mu daga gidan nan idan Mama tayi aurenta, zamu cigaba da tayaki sana’arki muma saimu samu wadda zamu dingayi, dan Allah ki barmu mu zauna dake.”
Maganganun suka daki Abida harta manta alwala takeyi ta tsaya tana kallon Sadiya da take kuka. Asabe kuma ta rufo mata baya, sai dai tayi tsaye ta kasa karasowa balle ta wanka mata marin da tayi niyya na wannan tonon sililin da ta fito tanayi mata, duk da tasan dole Abida taji, amman ai bata wannan sigar tayi niyya ba, kuma Abdallah ma tasan anan zaice zai zauna, shi bata damu ba tunda namiji ne.
“Kinji Amma…”
Sadiya ta fadi hawaye na sake zubo mata.
“Nan ai har abada in dai ina cikin shi gidanku ne Sadiya.”
Juyawa Sadiya tayi tana ma Asabe wani kallo dake fassara bata taba tunanin zataci amanarsu haka ba. Kafin ta wuce dakinsu, Abida ma alwala ta sake tana wucewa nata dakin. Hakama Nana bar mata dakin tayi bayan ta koma, suka saka mata taraddadin tarbar Abdallah da maganar, idan su mata sunyi mata tawaye haka shi kuma da yake namiji fa? Sai kuma ya bata mamaki, duk da ya dauki wajen mintina biyar baiyi magana ba, yana sa zuciyarta tsananta bugun da takeyi.
“Amman su Sadiya ba zasu biki ba?”
Ya fadi da wani tabbaci daya haska har a cikin idanuwan shi, bai isa ya haramta mata abinda Allah ya halasta mata ba. Kishin kuma daya turnuqe zuciyar shi yasan ba Hujja bace ba, dan tayi zaman aure da Habibu baya nufin yanzun da kasa ta rufe mishi ido ta cigaba da zama a haka. Dalilinta na son sake yin auren nema bayason ya fara lissafowa. Kannen shi dai in yana da rai ba zasuyi zaman agolanci a wani wajen ba.
“Da gidan Kawu nace….”
Bai ma bari ta karasa ba ya katseta
“Amma ba zataki rike mu ba, zamu zauna anan tare da ita, tunda nasan zata zabi ta rikemu akan ta kara wani auren.”
Ya karasa dacin da yakeji na bayyana har a muryar shi, bai kuma bari ko juya maganar ta gama ba ya mike da fadin.
“Allah yasa alkhairi”
Yana bar mata dakin. Kwalla taji ta cika mata idanuwa har saida ta zubo. Sai taji son auren na neman fice mata a rai. Haka ta kwanta da tunani barkatakai a ranta, da safe da taje gidan Uwani saita kara mata karfin gwiwa
“In dai yarane ki watsar da batunsu, kishin babansu ne ba wani abu ba, da sunga da gaske kinyi auren, kuma suma shine mafitarsu zaki ga sun hakura, da kansu zasu nemeki”
Ta yarda da kalaman nan, tunda su Tahir ma da kansu suka nemota. Suma da sun gama fushin zasu nemota ne. A kwana biyu ma saita fita batunsu saboda Alhaji Salihu da aka tsaida masa aurenta, aka kuma saka sati hudu. Wani irin barin kudi yake yi mata.
Wani aure da alkhairin shi yake tare da jirwaye.
Wani aure da dalilin shi yake jingine da kaddarar da ta rantse tsakanin ahalin Asabe dana Abida.
Maa shaa Allahu BarakAllah Allah ya sanya Albarka a cikin wannan tafiyar Allah yasa ki Gama da hannunki
Mashaa Allah
Allah ya biyaki ya yafe kuskurenki da namu gabadaya Allah yajikan mahaifanki muma Allah yabamu ikon yiwa namu biyayya
Allah jikan magabata yakara haskaka makwancinsu, Amin
Ya ake subscription din?
Ki shiga ta menu (yana sama ta hagu, wasu zane uku) akwai wajen da aka rubuta ‘subscribe’ ki latsa shi. Za ki ga subscription packages daban-daban sai ki zabi daya, bayan haka ki bi process din har karshe, wurin da aka baki bank account details. Sai ki yi making payment ki turo mana da shaida a email namu ko Whatsapp number mu.
Allah ya yafe miki kurakuranki damu baki daya
Aslm sister’s Dan Allah amun Karin bayani gani nayi register Amma baya budemun tundaga babi na ukku yaki budewa,amun bayani Yaya zanyi
Badiyat kin yi subscription kuwa?
Masha Allah Allah ya kara basira
You’re one of the writers I’ve always wished to read their books,kina qoqari Sosae,Allah ya qara basira..Ameen
Masha Allah
Masha Allah
Allah yakara basira
Ma sha Allah
Ma sha Allah. Allah yafe mana baki daya
Masha Allah
Ya zanyi subsscribing
Ki duba menu, akwai wurin da aka rubuta ‘subscribe’ ki latsa. Next page zai baki subscription packages namu, ki zaba. Ki bi process din har karshe, wurin da aka bada bank account details, ki biya sai ki turo mana da receipt a email namu ko whatsApp number mu.