Skip to content
Part 49 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

To Maryam Daiyabu Marmara. Allaah Ya gafarta miki Ya kyautata makwancinki Yasa jinyar da kikayi ta zame miki kaffara da daukacin musulmi. And to all cancer warriors, Allaah Ya baku lafiya Ya yassare muku. Amin thumma amin

*****

“Sa’adatu…”

Muryar Abdallah ta ratsa kunnuwanta tana kuma sakata kallonshi, tunda ta shiga gidan, Fa’iza ta kalleta tasan babu lafiya, ko daga kumburin da fuskarta tayi da idanuwanta da suka nuna alamar tayi kuka harta gaji, sai dai har hannunta ta kama cikin son ta zaunar da ita, ta kafe a tsaye, jingine da bango, tambayar kuma duk da Fa’izar tayi mata batace mata komai ba, shisa ta kira wayar Abdallah tace masa yazo gidan. Kuma sai akayi sa’a yana cikin unguwar. Ko mintina goma bai hada ba ya shigo.

“Bansan meya faru ba, ta shigo kuma batace mun komai ba.”

Cewar Fa’iza a maimakon amsa sallamar da Abdallah yayi, ta kuma karasa maganar ne cikin karyewar zuciya, hadi da saka hannu ta share kwallar data zubo mata. Zuciyar Abdallah akan labbanshi sanda ya furta sunanta, data kalle shi kuma, duk da rawar da kafafuwanshi sukeyi saida ya karasa inda take, ya kama hannunta yana zaunar da ita akan tabarmar tukunna ya zauna a gabanta shima yana lankwashe kafafuwanshi da ko takalmi ma bai cire ba.

“Meya faru? Menene?”

Ya tambaya cike da tarin taraddadi, saboda haka kawai yanayinta yake so yayi masa kama da wata safiya da zai bada rabin abinda ya mallaka idan za’a goge musu ita daga cikin rayuwarsu. Sa’adatu ta bude bakinta, ta mayar ta rufe, ta sake budewa amman ta kasa kwato kalaman, saboda yanayin da yake cikin idanuwan Abdallah din da yake karasa rusata. Me yasa bata hango yau ba? Me yasa bata ga komai ba kafin amincewa da Jabir banda miliyan biyar din da suka kira mata? Ta ina zata fara? Me yasa ma bata ga halin da Abdallah zai shiga ba? Ko wancen karin, ita da Tahir, har Abida ba zata nuna masa shiga tashin hankalin ba, yanda duk aka dinga fadawa Sa’adatu ta rame, sai bayan ta fara samun natsuwarta sannan ta ga tare da Abdallah sukayi jinyar sakin nata, kuma saboda shine ta nemo karfin gwiwa ta fara taimakon kanta

“Meya faru Sa’adatu?”

Abdallah ya sake tambaya yana katse mata tunaninta, sai wata kwalla ido daya ta ziraro mata, takai hannu da sauri tana dauketa, data bude bakinta wannan karin ta kwata kalmomi, wasu kalmomi da suka sa Abdallah yaji jiri ya kawo masa mamaya

“Sakina yayi Yayaa”

Fa’iza data furta

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Itace ta tunasar da Abdallah abinda ya kamata yayi kenan, ya nemi daukin Ubangiji, ya nemi natsuwa daga wajen Allaah a halin rudanin daya dirar masa. Saiya gashi ya zauna sosai, yana fadin Inalillahi yana sake maimaitawa har saida bugun zuciyarshi ya fara komawa dai-dai. Amman kuma ya rasa abinda ya kamata ya fara cewa, duk wani tsoron shine lokacin daya ji waye yake neman auren Sa’adatun ya dawo masa yanzun, tsoron da yan watannin da suka wuce ya fara dishewa ganin irin rikon da Jabir din yakeyiwa Sa’adatu, da kuma walwalar da yakeji a muryarta duk idan sunyi waya, irin wadda yake gani a fuskarta idan tazo gidan. Lokacin data fada masa tayi jamb kuwa shi kadai yana zaune murmushi yake kwace masa, burinta ne cigaba da karatu, burin da inda yana da hali shine zai cika mata shi. 

Rashin natsuwar da yake ciki game da aurenta saita dinga dishewa, ya daina jin faduwar gaba duk idan ya dawo gidan ya ganta, ya kuma fara bude zuciyarshi da tarin alkhairan Jabir a garesu, a maimakon da, idan duk yayi musu wata kyautar yana karbane cike da dari-dari da kuma zargi, yana ganin kamar Jabir din naso yayi amfani da kyautukan ne ya rufe musu ido daga ganin manufar auren Sa’adatu da yayi. Amman yaje gidan sau biyu, zai kai mata zobo da kunun aya. Duk da bai shiga ciki ba, a zuwa biyun kuma ya hadu da ‘yan uwan Jabir din mabanbanta, shi kanshi yanda suka karbe shi da girmamawa ba karamin kara masa natsuwa yayi ba, haka yanda suketa wasa da dariya da Sa’adatu, ya nuna yanda suka karbeta hannu bibbiyu, batare da kyamar inda ta fito ba.

Haka labaran da Fa’iza takan bashi da sukayi da Sa’adatu game da dangin Jabir din, dama mahaifiyarshi. Duka sai suka kara masa natsuwa, sai daya fara sakankancewa, ya bude zuciyarshi, ya rungumi auren da hannu biyu tukunna Jabir zai sako masa ita? To akan me? Harya gama samun abinda yasa shi aurenta kenan ko me yake nufi? Lokaci daya wani kunci ya fara mamaye guraben rudani da tashin hankalin daya saukarwa Abdallah

“Me kikayi masa?”

Ya tsinci kanshi da tambayar Sa’adatu data girgiza masa kai

“Babu abinda nayi masa”

Ta furta da sauri, saboda ai babu abinda tayi masa din banda ciki da bata samu ba, kuma inda ya barta ai zata samu cikin

“Haka kawai zai sakeki? Batare da kinyi masa komai ba?”

Cewar Abdallah yana kura mata ido, saboda so yake ya tabbatar duka laifin na Jabir ne shi kadai, so yake yaji da gaske Sa’adatu batayi masa komai ba, yanda zai tsugunna a gaban Allaah Ya kai karar Jabir hankalinshi a kwance

“Da gaske banyi masa komai ba…babu abinda nayi masa…”

Sa’adatu ta karasa maganar muryarta a karye, hawayen da take tunanin na yau sun kare mata suna zubowa, yanayin Abdallah na fito mata dasu. Shisa ta dora da.

“Matarshi ta samu ciki.”

Kalmomin na dukan tsakiyar kan Jabir, kafin su zauna masa kamar dama can akwai wajen dayake a bude yana jiransu. Sai kawai ya tsinci kanshi da mikewa, tunda daman takalmanshi na kafarshi, ya fice daga gidan batare daya san inda ya nufa ba. Ai daman yasan haka kawai maikudi kamar Jabir ba zai tsallake yaran masu kudi yazo yace Sa’adatu zai aura ba.

Wato aurenta yayi saboda matarshi bata samu ciki ba, to idan ta haihu sai yayi me? Ya sako musu ita ya karbe abinda ta haifa suje su rike shi da matarshi ko me? Tunda ai gashi yanzun matar tashi na samun ciki ya sako Sa’adatu tunda dalilin da yasa ya aureta din ya kare.

Wani irin tafasa zuciyar Abdallah takeyi kamar zata kama da wuta, inda ace yaushi wani ne me zai hanashi maka Jabir a kotu? Amman ko yanzun dinma ai ba zai bari a kwana ba, yanda ake kiran sallar magribar nan, masallaci zai shiga, bayan an idar da farilla sai yayi nafila saboda ya karawa takardun karar tashi armashi tukunna zai zauna yayiwa Ubangiji kirari har zuwa Isha’i, saima ya idar da Isha’i yayi shafa’i da wutr sannan zai mika sunan Jabir.

Sai dai duk wannan abin da yayi bai sama masa natsuwa ba balle ya rage masa tafasar da zuciyarshi takeyi. Saima bayan ya fito daga masallaci da wayarshi ta hau ruri, ya duba yaga Amira ce, bugun zuciyarshi saiya dawo, cike da rahar da bata kai ko ina ba, ta juye kuka suka kare wayar. Suma daren daga shi har Fa’iza babu wanda yaci abincin dare, balle kuma Sa’adatu, dan da yace ma Fa’iza taje su kwana tare da Sa’adatun, itace takiya, saboda tana son kasancewa ita kadai. Basu kuma matsa mata ba. Baccin kirki ma idan ka kalli fuskokinsu washegari zaka tabbatar babu wanda ya same shi, ko tara na safe batayi ba duka su Nabila suka cika gidan. Zuwa karfe shida na yamma har Amira ta itama ta diro Kano. Haka Sa’adatu ta dinga kallon yanda suketa kuka, ita yau ma data tashi sai taji idanuwanta a bushe kamar zuciyarta. 

Sai zazzabi kawai, yanda duk su Nabila suka dinga riketa suna kuka, da idanuwa kawai take binsu. Bayan bushewar da zuciyarta tayi, harda ma wani irin nauyi na daban, saboda yanda suketa kwashewa Jabir din albarka, musamman da Abdallah ya jaddada musu daman saboda matarshi ta kasa samun cikine yasa ya auri Sa’adatun, kafin Isha’i sai da Sa’adatu tasha paracetamol, bayan Amira ta tsareta tasa tasha fura dakyar. Tare suka kwanta a dakin Sa’adatun saboda duka su Nabila sun koma, tanajin Amirar nata kara kwashewa Jabir albarka tana kara mata zazzabin rashin gaskiya akan na rabuwa da Jabir din da take fama dashi. Saboda  tasan babu wani abu da Jabir yayi daya cancanci zagin da yake tasha tun safe. Idan ma akwai mai laifin to itace data amsa tayinshi tun daga farko, daga shi har Aisha babu wanda ya matseta yayi mata dole.

Ba Jabir bane ya jama ‘yan uwanta kunar ran da suke ciki, itace. Ita tayi auren yarjejeniya tun daga farko. Daga karshe kuma sai Amira ta riketa tana sake fashewa da kuka, zuwa safe harta fara hucewa. Sa’adatu najin tana yiwa Abdallah magana, tace masa zataje gidan Anty Talatu dan tasan halin da ake ciki, a kira Jabir din aji ko dai wani abu Sa’adatun tayi masa, tunda tace saki dayane yayi mata, kamar idan manya suka shiga cikin maganar za’a samu mafita. Shima Abdallahn duk yanda yake cike da jin zafin Jabir bai tankwabe shawararta ba, ko babu komai su dukansu basu da wani fata daya wuce ace Sa’adatu na zaune dakin mijinta kamar sauran ‘yan uwanta. Kar a fara kirga mata aure da kananun shekarunta. Babu wanda zaiso mata mutuwar auren nan gabaki daya.

Haka Amira ta shirya ta nufi gidan Anty Talatu, sai dai data fada mata, tare suka hadu suka sha kuka

“Anya babu sa hannun makiya a lamarin yarinyar nan Amira? Kinsan anga tana da sa’a, gashi yanzun kuma ta samu gidan hutu, harmu da muke nesa arzikin da take ciki yana samun mu.”

Jinjina kai Amira tayi

“To Anty waye zai saka mata hannu? Ita Sa’adatun nawa take da har wani zai saka idonshi akan lamarinta? Ina ma zata ga makiyan?”

Dan ta inda duk Amira ta hanga ita bataga yanda wani zai sakawa Sa’adatu ido ba. Ko Abida dai har ta rasu babu wanda zaice ga abokin fadanta, duk sharri irin na mutane kuwa, ba’a samu ko daya daya jefeta dashi ba, har gobe akwai makotansu na unguwar da suka taso da sukanzo gidan Abdallah, lokaci zuwa lokaci, cikin kuma mutanen Abidar ne da akayi zaman mutunci. To waye zai saka ma Sa’adatu hannu?

“Na rabaki da sharrin mutum, musamman yanzun da kai baka damu da lamarin mutum ba amman shiya damu da kai. Yau Malam da wuri ya fita, amman yana dawowa zanyi masa maganar sai asan yanda za’a bullowa lamarin.”

Akan hakan tayiwa Anty Talatu sallama, kuma batayi mamaki ba, dan saida ta koma ta fadawa Abdallah yanda sukayi tukunna ya fita daga gidan shima. Zuwa bayan Isha’i kuwa, wajen karfe tara na dare saiga kiran mijin Anty Talatu din, magana sukayi sosai da Abdallah, ya nemi lambar Jabir din, yana cewa duka sunyi ragwon azanci da basuyi musayar lamba da ko mutum daya a cikin wakilan Jabir din ba, da aisu za’a nema kai tsaye, a maimakon Jabir din. Haka sukayi sallama, Abdallah yace zai tura masa lambar

“Sai dai zuwa gobe in tuntube shi tunda yanzun dare yayi…Allaah Ya kyauta Ya kuma sa zaman bai kare ba.”

Abdallah Ya amsa da amin. Sai dai me, kwana biyu aka jera ana kiran Jabir bai daga wayar ba, da yake mijin Anty Talatun ya danyi boko, saiya tura masa da gajeran sako yana gabatar da kanshi a matsayin wakilin Sa’adatu da kuma dalilin kiran, saboda Anty Talatu ce ma ta bashi wannan shawarar

“Kasan masu kudin nan na daga lambar da basu sani ba sukeyi, gara ka tura masa sako.”

Sai kuma yaga ai hakane, tunda ma Jabir din zai iya tunanin cikin masu damunshi da maula ne, watakila shisa yaki dagawa. Zuwa dai kwanakin hatta Anty Khadi ma an sanar da ita maganar sakin Sa’adatun, kuma ita da Abdallah ne suka hadu suka saka Amira a gaba da saita koma Bauchi.

“Zaman me kikeyi? Zaki baro yara da mijinki kizo nan ki tare, zamanki dai babu abinda zai canza, addu’a ce kuma ko daga can ma zaki iya yi mata…”

Haka su Nabila, tace kar wanda ya sake zuwa gidan, tunda da sunzo din sai sunyi kuka, a cewar Anty Khadi, suna karawa Sa’adatu damuwa ne kawai, tunda shi aure daman ai rai gareshi, yanda kuma duk aka kai ga tattalinshi idan kwananshi ya kare babu wanda ya isa ya hanashi mutuwa. Su cigaba da addu’a, idan akwai sauran zama a tsakanin Jabir da Sa’adatu, kuma zaman da alkhairi a ciki, Allaah Ya dai-daita su, idan kuma babu Allaah Yayi mata musanya da wanda zai zame mata alkhairi. Nasihar ta Anty Khadi ta shigesu matuka, harta dan ragewa Abdallah kunar zuciyar da yake ciki. Ita dai Sa’adatu sai raba idanuwa a tsakaninsu, dan tun washegarin ranar da abin ya faru hawayenta sukayi tsaye. Tana dai jin nauyin da kirjinta yayi mata, ga rashin bacci ya saka kullum da ciwon kai take tashi, wani irin sama-sama take jinta. Shisa kome za’a ce sai dai ta daga musu kai, zuwa yau dinma ta daina musu akan cin abinci, abinda duk aka miko mata saita karba tayi kokarin ganin ta tura shi ta cigaba da hadiyewa har sai ta soma jin alamar zatayi amai.

Har akayi kwanaki bakwai, Jabir bai nemi mijin Anty Talatu ba, bai kuma daga kiran daya dingayi masa ba bayan wannan sakon daya tura masa. Sai ga bawan Allaahn nan ya tako da kanshi ya samu Abdallah, yana sa kima da darajar shi na karuwa a idanuwansu gabaki daya

“Yaron nan bai amsa kirana ba har yanzun Abdallah, har sako na tura masa, gashi lamarin masu kudin nan sai Allaah, balle inje in same shi.”

Da sauri Abdallah yace

“Ai Kawu ka rabu dashi kawai, karka sake kiran shi dan Allaah, mu bari muga iya gudun ruwan shi, tunda dai shi yayi sakin, kuma tace shine ma ya daukota daga can gidan nasu ya sauketa har nan kofar gida…”

Dan idan mutumin nan yaje ya samu Jabir yayi masa wani wulakancin Abdallah baisan halin da zuciyarshi zata sake shiga ba.

“Allaah Ya kyauta, ita Sa’adatun dai ku kara tausarta…”

Haka suka rabu bayan ya kara yiwa Abdallah nasihar da kalaman da yake fatan zasu kwantar masa da hankali, duka yaran tausayi suke bashi na halin maraicin da suke ciki, gashi babu wani dangin uba namiji tsayayye akansu, haka daga bangaren mahaifiyarsu, sai dangi da zumunci yayi matukar rauni tun iyayen ma na raye balle kuma yanzun da kasa ta rufe musu ido, watakila dai da ace su din masu kudine, to da dangi na kusa dana nesa suna nan zagaye dasu. Da Abdallah ya shiga cikin gida, Sa’adatu na daga daki taji yana fadawa Fa’iza anata kiran Jabir bai daga ba, ta jinjina kai kawai, daman me yasa zai daga? Ai wahalar da kansu kawai sukeyi, ita kuma bata da karfin gwiwar ce musu su daina duk wani kokari da sukeyi, aurenta ita da Jabir ba abu bane da zasu iya gyarawa, amman idan tayi magana ai zasu tambayi dalilin, ita kuma babu yanda za’ayi ta iya bude bakinta ta fada musu.

Fa’iza ma da safen saida ta sake ce mata

“Kinsan zaki iya fadamun komai Sa’adatu, mu kashe mu rufe mu biyu ba sai wani yaji ba, idan akwai wata matsalar da kika kasa fadawa Yayanki mu tattauna a tsakaninmu ko zamu samo mafita”

Sai tayi mata wani busashen murmushi tana fadin

“Babu wata matsala matar Yayaa. Iya abinda na fadane, kuma da kanshi ya fadamun matarshi na da ciki kafin ya furta mun sakin.”

Sai Fa’izar tace

“Hmmn…”

Tana mikewa tabarta, tasan su duka suna cikin damuwa ne, amman me zata iya musu? Sai dai tabarsu lokaci yayi aikinshi akansu. Ita yau ma da tunanin wayarta da bata dauko ba ta tashi, haka kawai taji tana son ta dauko wayar. Tunda safen take taso tayiwa Abdallah magana ta rasa ta inda zata fara. Haka ta kwana da abin a ranta, washegari kuma saita dauki wayar Fa’iza, batama san ta haddace lambar Jabir ba saida taga ta rubutata babu gargada, ta tura masa gajeran sako.

“Sa’adatu ce, ban dauki wayata ba.”

Saida ta ga shigar sakon tukunna ta goge shi daga kan wayar, ta mayar ta ajiye. Wajen karfe sha daya, Fa’iza ta gama yi mata mitar data sa taje ta sauke Abba da take goye dashi tunda ya jima dayin bacci.

“Sai kirjinki yayi ciwo, karkije ki sauke shi ki huta.”

Ita duk korafin nauyin yaron da Fa’iza takeyi bataji ba, ko dan daman kirjin nata dauke yake da wani nauyi da yafi na Abban shisa. Saiga yaro yayi sallama wai ana kiran Hajiya Sa’adatu a waje.

“Je kace waye…”

Inji Sa’adatun, saiga yaron ya sake dawowa

“Sakone inji Alhaji Jabir.”

Hijabin da yake rataye akan igiya Sa’adatu ta dauka, ta fita, sai kuwa taga direbansu ne daya gaisheta cike da ladabi, yana kuma bude mota ya mika mata wata yar leda da wayarta da kuma cajar wayar

“Nace sauran sakon bari sai in shigar miki dashi ciki.”

Da mamaki ta daga masa kai kawai tana wucewa ciki, ga mamakinsu daga ita har Fa’iza cefane ne daga dangin kayan miya dana lambu, kifi da kuma nama masu yawa, sai kayan shayi. Haka suka dinga kallon kayan

“Ikon Allaah…”

Cewar Fa’iza, Sa’adatu kuwa daki ta shige tanajin nauyin da zuciyarta tayi ya karu, ita ai wayarta kawai tayi masa magana, me yasa zai aiko da wadannan kayayyakin? Me zatayi dasu? Ya damu da abinda zataci ko tasha ya saketa?

<< Tsakaninmu 48Tsakaninmu 50 >>

4 thoughts on “Tsakaninmu 49”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×