Ko da Sadiya tace mata Asabe zatayi aure, kwashewa tayi da dariya, sai da ta kalli Nana ta ga hawayen dake cike da idanuwanta, tukunna ta iya cewa.
“Wai da gaske kuke?”
Nana ta daga mata kai tana kasa magana sai hawayen da suka silalo mata. Zama Sa’adatu tayi, wani abu na matsewa a cikin kirjinta. Saita tsinci kanta da hasaso cewa Abida ce tace zatayi aure, lokaci daya wani duhu-duhu ya gifta ta cikin idanuwanta
“Wai akan me? Wanne aure kuma?”
Ta tsinci kanta da furtawa, kishin da bata taba sanin tana dashi a duniya ba ya taso mata yana sa murnar Facebook din da ta samu ta bude ya dishe mata, tama manta labarin data kwaso zata fadawa Nana, suka tarbeta da wannan bakin labarin. Ita fa har ranta aure ne karshen abinda ta hasaso Asabe ko Abida zasu sakeyi a rayuwar su, sun auri Habibu a duniya, sai ta dauka zasu jira lokuttansu ne, suna neman aljanna yanda zasu kasance matan shi acan. Kawai sai Asabe tazo rana tsakiya tace zata kara aure? Duka yaushe ya rasu? Ko dai bata son shine dama can? Cikin abubuwan da suke sata kuka da wanda take tunanin zasu sakata, bata lissafa da auren Asabe ba. Da gaske hawayen bakin cikine suke mata barazana.
“Hmm…”
Da Nana ta iya furtawa cike da nuna takaicin da take fama dashi sai Sa’adatu taji ta kara mata zafin da kirjinta yakeyi. Shisa ta bar dakin, ta kuma tsinci kafafuwanta a dakin Abida da take zaune tana lissafa kudin cinikinta na safe dan ta ware ribar.
“Kema auren zakiyi Amma?”
Sa’adatu jefeta da tambayar tana sakata daga kai ta kalleta inda take tsaye idanuwanta sun rine da hawayen da take kokarin hanasu zubowa. Tana jin labari, ta kuma san yara da yawa da suke kishin ace mahaifinsu ya mutu, mahaifiyarsu tace zata kara aure. Ko ita idan ace abin zai biyo ta kanta ta san ba zai mata dadi ba. Amman ta rasa dalilin da zaisa kishin yafi tsananta akan iyaye mata, sau nawa su matan suke mutuwa, anayin arba’in mijin ya sake wani auren, kuma babu wani da za’a samu ya daga masa magana kan haka. Ita mace tayi fama da yara, tayi fama da surutun mutane da basu san matsalolinta ba, amman sun dorama kansu lissafa lokacin da mijinta ya mutu da kuma ganin rashin dacewar tayi aure, kamar akwai wasu shekaru da al’ada ta dibarwa mace bayan mutuwar miji, da dole saita cika su kafin ta sake wani auren dan nuna cewa soyayyar da tayi masa ta gaske ce.
“Idan auren zanyi nima meya faru?”
Ta amsa ma Sa’adatu tambayarta da wata tambayar da tasa hawayen da take ta tarbewa zubo mata.
“Wai akan me? Saboda me? Me yasa zaku yiwa Abba haka? Kamar bakwa son shi?”
Ita abinma nema yake ya bata dariya. Sa’adatu na daya daga cikin yaran da in ta dauko aure zasuyi mata bore kenan. Ficewa Sa’adatu tayi daga dakin. Maganar kamar ta barta kenan, duk da ko gaisuwa ciki-ciki take yiwa Abida a kwanakin, Asabe kuwa dauke mata wuta tayi gabaki daya. Sai ga Amira ta kirata a yar Nokia dinta data ji jiki, dan an daure ma da kyauro ta tsakiyar. Murfin baya rufuwa. Da kuka kuma ta amsa sallamar da Abida tayi mata bayan ta daga wayar.
“La hawla wala quwwata illa billah… Amira, lafiya? Meya faru?”
Abida ta fadi cikin kidimewa. Dan tasan ko meye zaisa Amira kuka to ba karamin abu bane. Ita kuwa a halin da take ciki yanzun bata neman duk wani abu da zai daga mata hankali.
“Yanzun aure zakiyi Amma?”
Taji maganar kamar daga sama. Sai da tayi dariya.
“Ke kuma waya fada miki?”
Ta kuwa ce mata Sa’adatu ce, sosai Abida tayi dariya tukunna ta fada mata ita ba aure zatayi ba, bama shi bane a gabanta. Duk da kai tsaye batace musu ba zata kara aure ba, idan tana da bukatar hakan, su basu isa su hanata abinda Allah ya halasta mata ba. Kamar yanda ta fadane, ba aure bane a gabanta, ta rufin asirinta, Sa’adatu da Jidda da suke gabanta take, gasu duk mata. Sa’adatu maganar aure na iya tasowa kowanne lokaci. Ga zuciyarta ma, ta ina zata fara rayuwa da wanin Habibu? Yaushe har zasu fahimci juna balle su gina irin rayuwar da sukayi ita dashi? Rashi kam tayi shi ta sani, kuma har karshen nata numfashin ba zata daina kukan shi ba.
Bata gama mamakin Amira da Sa’adatu ba, Nabila tazo gidan da turtsetsen cikinta, haihuwar yau ko gobe. Da yake tunda tayi auren, data samu cikin sai ya zube, sai yanzun wannan ya zauna. Duk da ba kuka tayi ko hayaniya ba, amman cikin sanyinta Abida ta karanci itama ba zata samu goyon baya daga wajenta ba inda auren ta rakito.
“Ki cigaba dayi mana addu’a Amma, abinda muke dashi zamu cigaba da hadawa muna kawowa, asiri zai cigaba da rufuwa da yardar Allah”
Ta karashe bayan tayi mata maganar auren, da tayi mata bayanin cewa ba aure zatayi ba tana ganin numfashin data sauke.
“Ke ba zaki daina yawo ba, sai kin haihu a hanya.”
Dariya tayi sosai. Sanusi ma dakyar ya barta ta fito din. Yana ta fada kamar zai ari baki, ganin bata taba nace masa kan zuwa unguwa ba sai wannan lokacin shisa ya barta. Ita kuma tunda Sa’adatu ta fada mata hankalinta ya tashi, har kuka tayi tana tuno Habibu. Ta kira Amira suka sha kukan su ta waya suna jinjina al’amarin tare sa jajantawa juna. Aikuwa ranta kal ta bar gidan. Ko da ta fadawa Sa’adatu cewar Abida ba aure zatayi ba, Sa’adatu ta jitane kawai, amman a ranta ta yarda Abida aure taso yi, ganin duka basu bata goyon baya ba shine ta bullo musu da wannan dabarar. Asabe dai data share kowa, haikan maganar aurenta ta kankama. Ta dinga shiri da tattara kaya. Ta fita harkar yaran nata da suke ta sha mata kamshi. Da yake abinda duk baizo ba, to ba’a saka masa lokaci bane ba. Sai ga satikan da aka diba, ranakun da ke cikinsu sun wuce har ranar tazo.
Bayan isha’i kuwa aka karbi sadakin Asabe aka daura mata aure da Alhaji Salihu Danbatta. Kuma kamar almarar da ta zamewa yaranta gaske ranar data tsayar ta tarewa tazo, tuni daman duk wani shirinta ta gama yin shi. Sai ta tsinci kafafuwanta da takawa dakin Abida, jikinta yayi mata sanyi bayan ta shiga, ta soma juya kalamai tana neman daidaita su dan su fito mata yanda take so, sai abu ya faskara, tafi mintina biyar ta rasa ta cewa, sai Abida ce tace.
“In dai yara ne karki damu Asabe, wallahi zan rike su iyakar kokarina, zan kuma zauna dasu da amana. Har gaban abada jinin Habibu yafi karfin komai a wajena. Ina miki fatan alkhairi da zaman lafiya a gidanki.”
Haka kawai sai Asabe taji kwalla na neman zubo mata, yanda duk take tarbeta kuma abin ya faskara. Ga mamakinta Abida ma saita kama hawayen. Sun sani, ba wani zama sukayi da zasu ce zasuyi kewar shi ba, asalima sun shafe zaman ne Asabe na neman duk wata hanya da zata takaleta da fada, duk wani abu da zata kuntata mata dashi. Amman a zaman nasu sun hada wani abu da suke tsananin kewar shi, sun hada Habibu, kuma gurbin ido ba ido bane ba, su duka sunsan ko akwai namiji irin shi to sai an tona za’a samu, tono ba dan karami ba. Sai gasu suna sabunta ma kawunansu kukan rashin shi da sukayi. Dan ita Asabe haka ta tashi ta fice batare data iya cewa komai ba. Ta bar Abida da tayi kuka ranar kamar ba zata daina ba, duk wata kewar Habibu da takeyi ta sake dagowa sama ta dawo tana danneta.
Tafiyar Asabe sai tayiwa Sa’adatu dadi kuma, saboda gidan ya kara musu girma. Su Nana sun koma kwana dakinta. Jidda daman a wajen Abida tafi kwana. Saiya zamana dakin nasu ya zama nata ita kadai. Yan kudinta yanzun rabi wajen turo fim suke karewa, ta samu ta karbi wani earpiece a wajen Abdallah. In ta shige daki yanzun shikenan, kallo ya dauke mata hankali. Tahir dai ya samar musu wata al’ada ta kiranta karfe takwas dai-dai, sukan shafe mintina goma ko fiye da haka kuma suna hira. Hirar da takeyiwa Sa’adatu dadi fiye da tunanin mai tunani. Har duba lokaci takeyi idan ya kara ko da minti biyu ne akai sai tayi masa mita.
“Yaa Tahir inata duba agogo tun dazun.”
Sai dai yayi dariya yace mata.
“Nutsuwata na tare da kiran nan Sa’adatu…dole ne inyi shi.”
Duk kuwa da ba ko yaushe take gane kalaman shi idan yayi su a dunkule haka ba, ita dai tana jin dadin kiran nashi. Da sun gama ne zatabi gado tana kallon fim din da take dashi a cikin wayar, wata rana sai taji idanuwanta na mata yaji ne take hakura ta ajiye. Tana dai kula kamar rayuwar kara tsananta take a gidansu kullum, daga shinkafa yar gwamnatin da suke ci an koma cin ‘yar hausa. Haka zasu sha tsinta tana kallon su,ko magana batayi ba, saboda babu wanda ya taba nufarta da maganar ta tsince shinkafa. Abida bata taba sakata ba, gasu Nana nan, aiki kafin ma tace suyi sun san meya kamata. Ko ranar da shara zata zagayo kan Sa’adatu, ran Abida sai ya baci yanzun da waya take dauke fiye da rabin hankalin Sa’adatu. Idan ranakun karshen makone da cinikin wainar filawa yafi da safe, sai t kwace wayar ta soka a habar zani sannan zata samu kan Sa’adatu.
Suna cikin wannan rayuwar ne da ake ta fafutukar neman rufin asiri duk rana. Suka tashi wata safiya, Jidda ta dauki buta da nufin shiga bayi dan tayi sallar asubar da ta rasa saboda ciwon cikin daya addabeta, ta yanke jiki ta fadi a tsakar gidan. Haka suka rude gabaki dayansu, Musamman Sa’adatu da tafi kowa kuka, gani takeyi ma kamar Jiddar ta mutu. Daman tana yawan fama da ciwon ciki. Suna zuwa asibiti, gado aka basu, data farfado daga suman da tayi dole akayi mata allurar bacci saboda ciwon cikin daya sake taso mata kamar hankalinta zai kara barin jikinta. Bayan gwaje-gwaje aka tabbatar musu da tsakuwar ciki ce (Appendix). Kuma samun saukinta shine ayi mata aiki a cire. Fadar tashin hankali da kaduwar da sukayi ma bata bakine.
Musamman wata doguwar takarda da aka baiwa Abida, mai dauke da abubuwan da ake bukata, magungunan da zata sha dan ya taru waje daya da kuma kudin aikin, sai taji wani jiri na shirin dibarta. Duk kuwa da Abdallah na ta kwantar mata da hankali.
“Kasan ba wasu kudi muke dashi a ajiye ba, banda na hayar nan da ko rabi ba sukai bama.”
Abida tayi maganar cikin sanyin murya.
“Su din za’a dauko Amma, Allah zai kawo mana wata hanyar.”
Su din kuwa ta dauko, da abinda su Nabila suka harhado akayi hidimar jinyar. Cikin ikon Allah akayi komai cikin nasara harta samu sauki aka sallamo su. Hankalin yaran ya kwanta, banda na Abdallah da Abida da suke tunanin kudin hayar gidan har dubu tamanin. Yanda duk suka so, ko dubu ashirin taki samuwa, ga shi har sun jara sati biyu a lokacin da ya kamata su bada kudin. Danma Alhaji Nura mutum ne mai tsananin tausayi, sai dai su duka basu ga laifin shi ba lokacin daya sa aka kira masa Abdallah yayi masa maganar kudin hayar yace masa suna karasa harhadawa ne. Yaso yayi ma Abida maganar ko zasu nemi karami ne su koma, amman yasan ba karamin tabasu hakan zaiyi ba, saboda sana’ar Abida data samu karbuwa a cikin unguwar.
Bayan kwana biyu Alhaji Nura ya sake kiran Abdallah, sai dai wannan karin maganar da yayi masa daban, magana ce kuma da ko bayan ya koma yayiwa Abida ita saita ji sanyi a ranta, dan ya basu mafita ne a saukake.
“Ko zaku saki dakuna biyu a cikin gidan ne Abdallah, kaga a maimakon dubu tamanin sai ku dinga biyan arba’in. Akwai matar da akazo mun da maganar tana neman gida, amman daki biyu take so, itama mijinta ya rasu, da marayunta, in dai kuna so sai ku sakar mata dakunan.”
Ai kuwa Abida tace masa zasu saki dakunan. Daga ita sai yaran mata, daki biyu ya ishe su, shi yana da nashi a cikin soro daman. Kuma da yake Alhaji Nura dan albarka ne, da suka bashi dubu ashirin karba yayi, yana yi musu lamanin cikon da sun karasa hadawa. Habibu mutumin kirki ne, dan kasa ta rufe masa ido, ba zai taba wulakanta iyalin shi ba. Sai lokacin hankalin Abida dana Abdallah ma ya kwanta. Washegari kuwa yaran na dawowa makaranta, kafin suce zasu tafi islamiyya tace su tayata su kwashe sauran kayan dake dakin Habibu, sai kuma su kwashe na dakin da Asabe ta bari su mayar nasu dakin ta dora dayi musu bayanin dalili.
“Yanzun dan gidan nan ne har zamu raba zaman shi da wasu Amma?”
Sa’adatu ta fadi wani malolon bakin ciki na turnuqe ta, wato su maimakon abubuwa suyi musu sauki. Kara jagulewa ma sukeyi. Meye amfanin tashin asubar da sukeyi su kamawa Abida ayyuka kafin su tafi makaranta? Da sun dawo su tusa wani kafin lokacin Islamiyya, su ba wani abinci me kyau suke ci ba, balle ace nan kudin suke tafiya. Ba kudin kashewa take basu ba, rabonsu da sabon kaya tun na waccen sallar, shima kuma Hajiyar su Asiya ce kafin ta tashi ta sai musu atamfofi ta basu. Ragon layya kuwa da wayanta dai ba zatace ga sanda aka yanka shi a kofar gidansu ba daman. Sai dai Habibu ya siyo musu nama da kaza idan ya samu sararin hakan. To waccen sallar kaza sai ta miyar abincin gidansu Asiya. Sai kuma wadda Tahir ya kawo mata. Akan me za’a kuntata su yanzun? Sai da ta fara sabawa da zaman dakinsu ita kadai. Kuma shikenan yanzun bandakin da suke maneji dashi da wasu zasu kara rabawa, wacce irin rayuwa ce wannan?
Daki ta koma, bata tayasu kauda ko tsinke ba, babu kuma wanda ya kulata. Duk masifar da ta dinga yiwa su Nana, ko wani dan abu ya fada kan katifar data mallake a matsayin tata sai ta dauka tayi cilli dashi tana binsu da kashedin karsu takura ma rayuwarta da kuma kananun maganganu. Kamar yanda suka saba da fadan Asabe, haka suka saba da halin Sa’adatu, sai tayi musu abu hamsin basu kulata ba, radio dinma da suka sa Abdallah ya sai musu suka kunna suka koma kan katifa daya suna sauraren wani shiri da akeyi a gidan radio Kano, suka barta tana gyara kwanciya, ranta cike fal da kuncin da bata san ta inda zata samu saukin shi ba. Kuncin da a ranar ba ita kadai bace a cikin shi, harda Asabe a gidan Alhaji Salihu Danbatta da zaman shi yazo mata da wani abu daban da wanda ita da Uwani suka tsara.
Matan shi biyu, itace ta shiga a ta uku, kuma duka a gida daya suke, sai dai kowa bangaren shi daban, kuma bangare hudu ta gani, da alamar yana da tsarin hada mata hudu ne tunda jimawa. Sai dai ko a ido har zuwa yanzun bata saka matan shi ba, ta dauka zai hadasu yayi musu nasiha yanda Habibu ya hada ita da Abida yayi musu a lokacin daya auro ta. Sai baiyi hakan ba, ya dai ce mata.
“Matana basu da tashin hankali, idan baki shiga bangaren su ba, ba tare da wani dalili ba, ba zasu shigo naki ba, ni mutum ne da kwanciyar hankalina take da muhimmanci a wajena, bana son wata fitina tunda ke ba yarinya bace ba.”
Kuma gaskiya ya fada mata, basu taba takowa inda take ba har yanzun. Gashi da wani irin kulle na ban mamaki, wani abu da sam bata saba dashi ba. Ya hanata zuwa ko ina, kudin da take hango zata dinga samun su, ya kama bakin aljihun shi ya datse. Sai dai akwai abinci me kyau, duk sati za’a zo a kawo mata kayan miya, nama na rago dana kaza, harda kifi. Abinda kuma duk tace masa tana so zaice za’a kawo. Kudine dao ta kula ba zai dauka ya bata ba. Wayar daya bata, kusan duk kwana biyu saiya saka mata kati a ciki. Ta tattauna matsalar da Uwani.
“Idan nace miki rayuwa ya canza, yanzun ba’a zama haka sai kice waye-waye, ke mai kudi irin wannan, kin dauka matan shi sakarkaru ne da zasu zauna haka? Ke dai ki kwanta ki hangame baki… karki tashi ki nemarwa kanki ‘yan ci.”
Babbar matsalarta da Uwani kenan kuma, duka mafitarta sai ta hado da Malamai, wani abu guda daya da zuciyar Asabe ta kasa aminta dashi. Bawai zurfin ilimin addini tayi ba, kawai tana tsoro ne. Amman matsin ya fara mata yawa, shi dai ba hira suke zama suyi ba, ranakun girkinta sai wajen karfe tara na dare yake shigowa. Ba ko da yaushe yake cin abincin da zata ajiye masa ba, zai tambayeta ko akwai abinda take bukata da za’a kawo mata. Da baya sauke hakkin aure sai tace bata san dalilin da yasa ya aurota ba. Da safe kuma da yayi wanka, ba tsayawa yake ya karya ba zai mata sallama ya fice. Kadaici take ciki da kayan kallon da ya hada mata ya kasa debe mata. Ga yaranta tunda tazo babu wanda ta saka a ido. Shi kuma ya hanata fita balle taje ta gansu. Tana da yakinin hankalinsu a kwance yake tunda suna tare da Abida, nata hankalin daine yake a tashe da taga wautarta a fili yanzun, sai ta tattara yara ta sallamawa Abida?
Abida fa da tunda can duk wata hanya da zatabi taga yaran suna karkashin ikonta shi takeyi. Sai rana tsaka wani abin duniya da take hangen zata samu ya sa tabar mata su ta taho. Yanzun gashi bata hango samun wannan abin ba, yaran kuma na neman subuce mata. Ko a waya Abdallah bai nemeta ba. Tahir ne kadai ya kirata kusan sau biyar yana jin lafiyarta, tare da yi mata alkawarin yana zuwa daga makaranta zaizo ya dubata, karatu ne yayi musu zafi. Aminu ta dai san ya fara bautar kasa, ya gama bai gama ba, bata sani ba, idan ta ganshi ko kafin tayi auren nan, to Tahir ne ya janyo mata shi, idan tayi masa mita zaice.
“Abubuwa ne suka sha mun kai Mama, yanzun ba gashi nazo ba.”
Kuma fadanta da ta gwada akan shi randa yazo ya riko cefane, ya hado da Abida. Mikewa yayi ko sallama baiyi mata ba, ya saka takalman shi yayi gaba. Sai da ta kusan wata shidda bata saka shi a ido ba, da Tahir ya janyo mata shi tayi masa maganar haka yace,
“Ai kar inzo in bata miki rai ne.”
Shisa take gudun yi masa fada. Ba halinsu daya da sauran yaran nata ba. Ko Abdallah da take gani da sanyin hali, a fuskar shi tana hangen rashin jin dadi idan tayi wani abin. Banda Tahir, da a tsakanin kowanne fadanta, murmushin fuskarshi baya bacewa. Kuma zaiyi kokarin bata hakuri, hankalin shi baya taba kwanciya sai ya ga ta huce ko kuma tace masa abin ya wuce. Tana son yaranta, fiye da yanda zata misalta, amman Tahir halayen shi da kulawar da yake nuna mata na saka shi samun wani waje daban a zuciyarta. Duk da shi kadai ba zai maye mata gurbin sauran ba, dole suma tana bukatar su. Bata nemi Uwani ba kamar yanda ta shareta kwana biyu tunda taki daukar shawararta, sai da taji kamar hayaniya ranar wata alhamis, ta leka ta window din dakinta ta hangi wata hamshakiyar mace, da samari matasa da kuma ‘yan mata zagaye da ita suna ta raha.
“Hajja yanzun sati biyu zakiyi? Gaskiya zamu sha kewa.”
Wata budurwa ta fadi.
“Ni dai wayata Hajja, kar a manta da ita”
Matar tayi dariya tana kallon matashin da yai maganar
“Matsalarka kenan, wato ba zakayi kewata ba”
Ko da ta dawo ta zauna, sai zuciyarta take ta damunta da tambayoyi, da yake itace da girki ranar. Sai da ta kasa hakuri da Alhaji Salihu ya dawo tace masa
“Yau dai kamar naga wata a cikin matar gidan”
Kai ya jinjina yana tabbatar mata
“Hajiya Safina ce, ta tafi Dubai yau, zatayi sarin kaya. Itace uwargida na”
Sai Asabe taji wani abu ya dirar mata da ba zata iya fassara shi ba. Da gaske Uwani takeyi da tace mata ita kadai ya maida sakarai, yake kullewa a cikin gida. Sauran matan shi suna fita duk inda suke so, ga wata nan yawon bai tsaya a cikin garin Kano ba, kasar gabaki daya ta bari. Kuma da bakin shi yake ce mata sarin kaya zataje. Kenan kudi yake dauka yana bata. Abinda Asabe bata sani ba shine, Hajiya Safina ce silar karin habbakar kasuwancin Alhaji Salihu, mahaifinta shima dan kasuwane babba, kuma daya rasu ya bar musu dukiya ba yar kadan ba, kasancewar su uku kacal ya haifa, mata biyu, sai namiji da yake karaminsu. Kuma rabin nata gadon shi ta mikawa ya kara a cikin tashi kasuwar, data nemi zata fara nata kasuwancin bai hanata ba, har yau, Hajiya Safina bata taba yi masa maganar wannan kudin data bashi ba, dan ko basuyi kan da kan wajen dukiya ba a yanzun, ko zai fita to da kadan ne.
Matar shi ta biyu, yanda yake zaune da Asabe haka yake zaune da ita, babu abinda take siyarwa. Shi bai saba ya dauki kudi ya bata ba, duk abinda take so zai sa a kawo mata, ko Hajiya Safina ma ba zai tuna ranar karshe daya dauki kudi ya bata ba. Haka al’adar shi take, hudubar Uwani ce tayi ma Asabe tasiri. Harta kirata tace ta karbo mata taimakon da tace zata karbo mata, sai da ta gama yi mata shakiyancin ta ga uwar bari, tukunna tazo ta kawo mata, rubutune da garin magunguna, wani ta zuba masa a ruwan wanka, da inda zai taka, da kuma abinda zai sha. Haka ta karba jikinta nata rawar tsoro da rashin sabo. Abinda ita da Uwani basu sani ba shine, tun lokacin da Kawun Alhaji Salihu ya nemi kassara shi akan dukiyar daya zage ya nema da gumin shi, ya daina sakaci da addu’a, azkar na safe da yamma bai taba wuce shi ba, kusan shekara sha biyar kenan, sannan duk juma’ar duniya akwai masu kosai da wainar da cinikin su kaf na ranar shine yake yi musu shi, a rarrabawa almajirai a matsayin sadaka, kamar yanda akwai mutanen daya bama kwangilar yin wake da shinkafa duk safiya ana rabawa mabukata.
Zagaye yake da kariyar Allah, da in ba wata kaddarar ba, zai wahala kananun bokayen dake saka rigar Malunta suyi nasara akan shi. Da Bismillahi ya kwankwadi zobon data hada masa yana sa sanyi ratsa ranta. Har tana jin fiye da rabin matsalarta ta kusan zuwa karshe. Yaran ne take son yiwa Uwani zancen su, bata so ta kara tabbatar mata da sakarcin da tayi, tunda sun tsayane da maganar zata kai su Nana gidan Kawu, sai suka ki amincewa. Har ranta kuma yanzun kyashin morar yaranta da Abida takeyi ne yake damunta. Idonta ya rufe daga ganin bautar da Abida takeyi musu kamar daga jikinta suka fito. Yanda ko na rana daya, tun barin Asabe gidan bata taba bambanta tsakanin su Nana dasu Sa’adatu ba. Dan in yanzun kaje gidan ma zaka dauka su duka nata ne. Shisa ko Furaira data tare a gidan bata san ba yaranta bane ba.
Da yaranta mata guda biyu tazo, Fa’iza da kuma Asma’u da suke kira Ma’u, Faiza zata bama Sa’adatu kusan shekara uku, dan ta kammala karatunta na sakandire, Ma’u kuma tana aji biyu a sakandire. Sai dai Fa’iza irin mutanen nan ne masu karamin jiki da zai wahala ka canki shekarun su dai-dai in ba fada maka sukayi ba. Ayya suke kiran Furaira, mace mai san hira, kuma da alama ba zatayi matsala ba. Ta cewa Abida yaranta hudu, Ladidi tana aure a garin Legas, sai Sakina tana garin Katsina, yanzun kuma sai Fa’iza da Ma’u da suke gabanta. Ita da mijinta duka sun taso sunga kansu a gidan marayu ne, kafin suyi aure, yanzun da Allah yayi masa rasuwa shekaru takwas kenan, ita da yaranta ne dangin kansu, basu da kowa da zasu nuna su kira nasu. Rasuwar shi tasa ta kama sana’a kala-kala dan ta tallafi yaranta, kafin ta fara siyar da gwanjo, kuma itace sana’ar data karbeta, yanzun sari akeyi a wajenta sosai. Musamman da Ladidi tayi aure, kuma sana’ar mijinta ce, tunda a wajen sarin gwanjon ne ma suka hadu dashi. Daga can ake aiko mata.
Ko Sa’adatu da ta dauki zafi da dawowar su sai gata ta sake dasu. Musamman Fa’iza da cikin kankanin lokaci take neman maye mata gurbin Asiya da tayi mamakin yanda ta watsar da ita. Kuma su Fa’izar suna da rufin asirin su dai-dai gwargado, tunda Furaira na kama kudin da bata da abinda zatayi dasu daya wuce ta kashe musu. Itama Fa’iza da babbar wayarta. Sai dai maimakon kallo kamar yanda Sa’adatu takeyi, Fa’iza na son karance-karance.
“Kinsan da ina da kwakwalwa da tuni na zama marubuciya, amman na sha gwadawa ko rabin shafi sai in kasa rubutawa.”
Ta cewa Sa’adatu, ita kuma karatu ba damunta yayi ba, duk da tana ganin ‘yan ajinsu na fama, duk ‘yan kudinsu wajen masu bada hayar littafi suke tafiya. Ita kuwa gara taji dandanon bakinta ya canja.
“Nifa cacar kudin hayar littafine ba zan iya ba wallahi.”
Dariya Fa’iza tayi.
“To waye yace sai kinyi haya? Bayan da wayarki a hannu, kuma yanzun ana samun su a guruf din marubuta na manhajar Facebook, gasu nan kala-kala, kullum da wanda za’a turo…”
Ita ta nuna mata inda zata shiga, yanda zata zakulo tsofin shafukan da aka jima da wallafawa. Sai ga Sa’adatu tsumu-tsumu a harkar karatu. Duniyar rubutu na haska mata abubuwa da yawa da sukayi dai-dai da rayuwar da take yiwa kanta fatan samu. Furaira ba wuni takeyi a gidan ba, ita Fa’iza ta gama makaranta, Islamiyyar su Sa’adatu kawai ta shiga. Daga ita sai Abida ake bari, a wannan zaman ne Abida ta kula da Fa’iza bata da kwiya, kuma yarinya ce mai hankali. Sosai take kama mata ayyuka, tun tana hanata harta soma kyaleta tunda ba ji takeyi ba, sai tayi dariya tana fadin.
“Idan na kama sai kiga mun gama da wuri Amma.”
Haka kuma suna aikin suna hira, zai wahala kayi zaman yini daya da Fa’iza bata shiga ranka ba, baka kuma yi dariya ba. Tana daya daga cikin irin mutanen nan da komai raha ne a wajen su. Ko da abin bacin raine to sai sun sakaya shi da raha yanda zuciyar kowa zatayi sanyi, raharta saita hadu da kirkin Abida da kuma kula irin ta Abida da take ganin yanda idanuwan Fa’iza suke bin duk wani motsi na Abdallah da gaisuwa ce kawai take hadasu. Tunda suka zo gidan, bayajin idan ya hadu dasu a hanya zai gane fuskar Fa’iza, bai taba kallonta kai tsaye ba.
“Ina wuni.”
Ta kan gaishe shi cikin siririyar muryar da a farko ya dauka iyayi ne irin na mata. Sai da yaji ko magana takeyi haka dai muryar tata take fitowa, da wani amo da ya sha saka shi son ya daga ido ya kalli fuskarta sosai. Sai dai shiga sabgar mutane ba halin shi bane ba, Idan ya samu sararin siyo abu yanzun dai, cikin karamcin da ya taso dashi, sai ya hado da su Fa’iza.
“Allah ya saka da alkhairi.”
Din Fa’iza cikin muryar nan tata yana sanyaya ranshi. Randa ya fara kallon fuskarta, ya dawo da wuri ne, yana kiran Sa’adatu da zai ba gugar wata rigar shi, Nana tace masa tana sallah, saiya juya kawai tunda yasan inta idar zata neme shi.
“Yaa Abdallah…”
Fa’iza ta kira shi tana saka shi juyowa, saboda bata taba kiran sunan shi haka ba.
“Ayya aka gyarawa fridge dinta, shine na fara zobo, gashi kasa albarka.”
Ta karasa maganar tana mika masa robar zobon daya sa hannu ya karba, ya kuma kalli fuskarta da kwan fitilar da ya haske gidan ya haska masa ita sosai, komai na fuskarta madaidaici ne, kamar yanda kai tsaye ba zaka kirata da fara ba, haka ba zaka kuma ce mata baka ba. Ta tsaya a tsakiyane kamar kowanne a cikin kalar na son yin rinjaye.
“Allah ya kawo ciniki mai albarka.”
Ya furta yana dorawa da.
“Nagode”
Sanyin zobon na ratsa tafin hannun shi.
Tare da wani sanyi na daban, wani sanyi da ba shida kalaman fassara shi.
Allah ya yafe kurakurenki ya jiqan iyayenki
Damu baki daya
Allah ya yafe miki kurakuran ciki ya sa mu amfana da abunda ke ciki. Allah ya gafarta wa iyayenki
Allah yajiqan iyaye yaqara basira sister