Skip to content
Part 56 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

“Babu macen da zatace miki batason hutu Sa’adatu, ai an haliccemu ne dan mu huta, a killace mu a cikin gida a dauke mana duk wata dawainiya, amman idan wanda aka dorawa wannan nauyin sunyi tsalle gefe sunce so suke su ganmu a wahale ya zamuyi? Idan kika biyewa so bayan ya kwantar dake, binki zaiyi ya danne saikin daina numfashi, ki tattara Jabir din ki ajiyeshi a gefe yanda ya tattaraki ya fitar daga rayuwarshi, ki fuskanci karatunki da sana’arki, ki tsaya da kafafuwanki, ko ba Jabir ba, a gaba in kika jingina da wani namijin ba dan kin kasa tsayuwa bane, sai dan ki huta, ki maida numfashi, ko da ya matsa ba zaki fadi ba.”

Haka Badr tace mata, an kuma fada mata maganganu kala-kala, amman ai a cikin idanuwansu tana ganin fatan kowa, kuma ko rantsuwa tayi ba zatayi kaffara ba, idan yau Jabir yayi sallama yace ya mayar da ita zai zamana kamar addu’ar danginta ce Allaah Ya amsa. Idan ma zata fadawa kanta gaskiya, harda tata addu’ar da take da yakinin ta zarta tasu yawa. Jabir din dai yazo, sau ba adadi, amman a cikin zuwan nashi babu wata alama data nuna yana shirin mayar da ita din, kulawar nan tashi sai abinda ya karu, kulawar da yayi amfani da ita yana dorata akan keken bera tun daga farko, kulawar data mantar da ita dalilin aurenta da yayi sai da ya tuna mata da takardar sakin da har yanzun da take zuwa makaranta kullum idan taga takarda sai jikinta ya amsa. Idan ta kalli Abdallah, tausayinta da take gani cikin idanuwanshi saiya karya mata duk wani karfin hali da ta tashi dashi.

Idan kuma Jabir yazo ya tafi, ta shiga gida Fa’iza ta dinga binta da kallo kamar tana jiran taji tace Jabir din yazo ne harma yace ya mayar da ita sai wani yanayi marar misaltuwa ya dinga dukan zuciyarta.

“Fa’iza tace shi Jabir din yana yawan zuwa ma ko?”

Sauran Yayyenta kenan, inka cire Nabila da tace mata.

“Ki rike addu’a, idan akwai alkhairi a zamanku Allaah Ya dai-daita karya barki da dabararki.”

Sai kuma Badr, maganganunta sunyiwa Sa’adatu wata irin shiga da ta bata mamaki, saboda washegarin da sukayi wayar, ko da Abdallah ya bita da wannan kallon da safe, sai tayi masa murmushi, murmushin da take fatan ya dinga gani a fuskarta har saiya gane cewa ita din ba abin tausayi bace ba, musamman ma akan Jabir, tunda ai in dai aka zagaya aka kuma zagayo itace ta kai kanta, itace ta yaudari kanta idanma yaudararce. Yarjejeniya ce sukayi, kuma duk da ba karanta takardar tayi ba, tasan in yau aka dauko akwai maganar rabuwa da ita a ciki, kuma na rana daya Jabir bai taba bude bakinshi ya fada mata akasin hakan ba. Ko babu komai Jabir yasa ta gane burinta yana da iyaka, ko da ta dinga nemarwa kanta mafita, matsalolin nata ba masu yawa bane ashe, idan ta ga ‘yan uwanta cikin wadatar da suka fi karfin cin yau dana gobe, ta jita da kudin da zata ci duk abinda tayi marmari shikenan. Hango kanta a matsayin matar wani hamshaqi, keta hazo zuwa kasashen ketare, babban gida, wannan duk daga nesa ne take hangensu a wani abin azo a gani.

Sannan tun farko ita daman fatan nata bata jingina shi da kowa ba, so tayi ta tsaya da kafafuwanta, sai Tahir ya shigo rayuwarta yasa ta ajiye komai, bama jingina ba, kwanciya tayi a jikinshi, kaddara ta zare shi tana barinta akan turbaya. Data mike kuma, batajin ta gama kakkabe jikinta tas-tas ta karbi tayin Jabir. Maganganun Badr kamar sun dauraye mata fuskane bayan ta tashi daga dogon bacci, sai taji ta wartsake.

Sai dai anya Jabir na cikin jerin mazan da za’a tattara a watsar?

Sai dai ai ance labarin gobe abarwa Allaah.

Da yake akwai son karatun a ranta, kuma da gaske ta daura damarar yinshi, ga Jabir daya saukaka mata komai ta hanyar bada mota, da kuma direban da zai dinga sintirin kaita yana kuma zuwa daukarta lokacin da ta gama.

“Ba makaranta ba kawai Sa’adatu, duk inda zakije ki kirashi ya kaiki, ya zauna ya jiraki kigama ya mayar dake gida.”

A makarantar ma Jabir ca yayi ya dinga zama yana jiranta ko da wuni zatayi, itace take ce masa yayi tafiyarshi inta gama abinda takeyi zata kirashi. In banda rikici irin na Jabir ya za’ayi ta saka mutumin da a kintace ma ya girmi Abdallah ya zauna wuni guda yana jiranta? Yanda dai duk tayi zaton karatun zaizo mata da sauki sai take ta cin karo da akasin haka, karatun aikin jinya ba karatu bane na ragwaye, koma tace makarantar kacokan saika shirya kowanne bangare zaka zaba kuwa. Balle kuma nata da wata rana mutane zasu yarda da ita da majinyatansu. Ranar farko da taje ta dinga kallon wani matashi da yake ta faman yi mata murmushi tana tunanin inda ta sanshi, harta karasa kujerar gefenshi ta zauna suka gaisa ta kasa tunawa, har saida taji wani ya kira sunanshi tukunna ta tuna

“Nasir Kabir Getso”

Ta maimaita cikin zuciyarta, shine wanda ya sai mata ruwa. Bata godewa Allaah da haduwa da Nasir ba sai da suka ci wata biyu cikin watanni shida na zangon farko a shekarar, saboda alamu duka sun nuna Nasir din na cikin dalibai idan ma bai kasance wanda zai ja ajin ba gabaki daya. Kokari gareshi ba kadan ba, da kuma wata irin fasaha ta iya koyar da mutum cikin sigar da zai fahimci bayanin fiye da yanda wasu a cikin Malaman nasu sukeyi. Gashi cikinta daya fara fitowa yasa Nasir din na bata wani girma na daban kamar yanda mazan ajin sukeyi, tunda a zatonsu tana da aurene. A mata kuma zatace kawa daya tayi Fati Baba, ba don komai ba, sai dan yanzun tana jin bata da lokacin tara tarkacen kawaye, kuma ta kula itama Fatin ta bangarenta hakane.

Tunda Jabir ya ajiye mata direbanta, sai kuma ya dauke kafarshi, zai kirata a waya, wannan ma ya zama dan kullum, daya kula sanda zai kira da safe yawanci tana makaranta, bata cika dagawa ba, saiya koma kiranta karfe takwas na dare, ba doguwar magana sukeyi ba, ranaku da yawa cikin kasa da minti daya sunyi sun gama

“Kuna lafiya? Babu wata matsala?”

In kuma ranar taje awo ne zai kara da

“Me sukace a asibiti? Basu ce ana bukatar komai ba? Babyn lafiya kalau? Kefa? Kema basu ce wani abu na damunki ba, ko ki dinga cin wani abu?”

To ita meye za’a ce ma ta dinga ci da bataci? Ba laulayi takeyi ba, banda cikinta da yake kara girma da kuma canjin da takeji a jikinta, babu wani abu da yake damunta, ba zatace tana fama da wannan kwadayin da wasu masu cikin suke magana akai ba, ko ta ga sunayi, idan ma za’ayi maganar gaskiya tunda can ko wata mai cikin ba zata nuna mata kwadayi ba. Ba zatace kwadayinta bane ya karu tunda akwai shi tun kafin cikin, cin abincinta ne ya karu, sosai, dan kamar ma bata koshi haka take jinta, baka taba raba jakarta da danginsu chips da biscuits kala-kala a makaranta. Banda zirga-zirgar makaranta, da kibar da zata narka sai kowa yayi mamaki. Ta kuma yi duhu, inma da ciki harda dai wahalar karatu ta sakata yin duhun.

Kawai inta duba mudubi bata ganin tayi kyan nan da ake cewa masu ciki nayi, kuma ta gani akan Fa’iza dan wani irin kyau tayi duk da bakar wahalar da tasha, ramar ma sai tayi mata kyau lokacin, fuskarta tayi wani irin fayau. Ita kuwa data duba sai taga kamar kibar daya kamata ace tana rarrabuwa zuwa wasu sassan jikinta ce take tattarowa tana samun wajen zama a hancinta da zata rantse yayi ribi biyun na da, har wani budewa take ganin kofofinshi sunayi

“Matar Yaya hancina baya miki kama dana botorami dan Allaah?”

Abba daya tashi daga bacci Fa’izar take ba ruwa lokacin, saida kofin ya subuce daga hannunta saboda dariya.

“Bafa abin dariya bane, wallahi ko ban duba mudubi ba inajin nauyin shi akan fuskata.”

Dariyar dai Fa’iza takeyi, ko kadan hankalinta bai kai kan hancin Sa’adatun ba saida tayi wannan maganar, data kalleta sai wata sabuwar dariyar ta taso mata, da yake ko babu ciki ma Sa’adatu ta iya tsokana, ita dai idan kayi mata sai nan da nan ta hau, balle kuma ance mai ciki da saurin kulewa, ai sai ta cika fam, har tana mirginawa ta mike

“Yi hakuri, haba Madam…”

Cewar Fa’iza har lokacin tana dariya, sai Sa’adatun ta shige daki tana barinta a tsakar gidan. Data kwanta a katifa, saita dauki wayarta, idan karatun ya danyi mata sauki, bata da aikin gida mai yawa ko kuma ta gama, takan dauki wayar ta shiga kafafen sada zumunta, musamman twitter da yafi komai daukar hankalinta a yanzun din. Dan harma takan yi comment a wasu post din, yau tana shiga da post din Officer AB ta fara cin karo, video ne na sakanni goma kacal, kuma ko da bata bude ba, ta riga da tasan kazace, hakan dai bai hanata budewar ba, kazarce kuwa, gasashiya, sai dai ya mika hannu zaija ledar da kazar take ciki aka buge masa hannu. Duka abin ya farune a cikin sakanni goma.

Amman wasu sakanni cikin gomar nan sunsa abinda yake cikin Sa’adatu juyawa kamar mai neman sake waje, har saida takai dayan hannunta tana dafe cikin hadi da kiran sunan Allaah, ta kusan dakika biyar tana maida numfashi kafin ta sake duba wayar tana kuma kara replaying din video din. Ai shekaru biyu da doriya kamar basu isa ace sun goge mata duk wani abu daya danganci Tahir ba, kuma a jerin mutanen da take da yakinin ko a cikin duhu inta laluba zata ganesu, Tahir zai shiga cikin wannan jerin. Mutum ne shi mai tsananin riko da addini, kafin daurin aurensu sau daya zatace ya rike hannunta, shima kuma su duka suna cikin rudadin da Asabe ta jefasu ne, amman ai idanuwanta sunfi sauka kan hannuwanshi fiye da fuskarshi saboda yanda kunyarshi da take ji kanyi mata shamaki da kare masa kallo yanda zuciyarta takan raya mata.

Shisa tasan hannun nashi, har wasu kananun tabbai da suke jikin hannuwan Tahir ta sani, ko yanzun kuma ta rufe idonta tsaf zata lalubo hoton hannuwan shi inda ta binne, kuma in dai ba fuska bace kadai ake iya kama da ita, harma da hannuwa za’a iya samun na wasu suyi kama da na wasu, hannun Tahir ne ta gani, harso ta dingayi ta saka pause dai-dai saitin hannun nashi, ta kasa

“To idan hannun Tahir ne sai me?”

Wani sashi na zuciyarta ya furta mata yana sakata fita daga Twitter dinma gabaki daya. Saboda ai da gaske, idan hannun shine meya faru? Meye hadinta dashi a yanzun? Ita da take fama da kanta ma. Kamar matsalolinta basu isheta ba saita gayyato wata tsohuwar matsalar. Kwanciya tayi duk da yamma tayi, amman haka kawai zuciyarta ta rasa sukuni. Kuma ko da Jabir ya zabi wannan yammacin bayan daukar wajen wata daya bata saka shi a idonta ba, ya kirata a waya tana dagawa kafin ma tace wani abu ya rigata da.

“Ina kofar gida.”

Sam ta kasa jin zuwan nashi ya canza mata rashin sukunin daya mamaye mata zuciya. Haka ta dauki hijabinta ta saka tana fitowa ta samu Fa’iza da take tsaye tana yanka albasa.

“Jabir ne yazo.”

Tayi maganar muryarta na fitowa cike da kasala, kamar wadda ta fara bacci aka tasheta ko take shirin farawa.

“Ki daukar masa zobo da kunun aya mana.”

Bata tankwabe tayin Fa’iza ba, in dai Jabir nema zai iya sakata komawa ta dauko masa, gara kawai ta fita dashi. A zaune ta same shi cikin mota, ta karasa ta bude ta shiga ta zauna, ta fara ajiye robar zobon da kunun aya, tukunna taja kofar tana dan kallon shi da fadin

“Ina wuni.”

Cikin kasala da rashin walwalar da take ciki.

“Lafiya kalau, ya kuke?”

Ya amsa yana nazarinta

“Alhamdulillah”

Yanda tayi maganar tana kumbura fuska sai yasa Jabir yaji yanaso ya mika dan yatsa ya latsa kumatunta da sukayi masa kiba yaji ko a idonshi ne yake ganin kamar zasuyi laushi. Amman ai in neman rigima da mai tsohon ciki akwai riba a ciki ya sani, saima yayi amfani da hannun yana daukar robar kunun aya, kafin ya jama kanshi rigimar da baisan ranar karewarta ba. Babu ciki ma Sa’adatu abin kuka ba wahala yake mata ba ballantana yanzun.

“Ya makarantar? Babu wata damuwa ko?”

Kai ta girgiza masa.

“Daman zan dubaku ne.”

Kamar hakan take jira kuwa ta kama murfin motar tana budewa.

“Ina zaki?”

Tambayar ta kwacewa Jabir, sai Sa’adatu ta kalle shi tana rasa amsar da zata bashi, tunda ai shi yace daman zuwa yayi ya dubasu, tunda ya gansun kuma saita dauka shikenan. Zata iya tafiya abinta, ganin kuma bata da niyyar bashi amsa yasa shi fadin.

“Ba wata matsala dai ko?”

Kai Sa’adatu ta girgiza masa, wata alamar ta bata dai cikin yanayin son magana, kuma sai hakan yasa Jabir jin babu abinda yake so irin yasa ta maganar, a lokaci daya kuma damar daya rasa ta riketa a jikinshi ta dirar masa tana saka shi cikin yanayin rashin walwala kwatankwacin wanda Sa’adatun take a ciki.

“Ki kula da kanki dan Allaah.”

Kuma wai sai yanayin yanda yayi maganar da kuma canjin da taji a muryarshi lokaci daya yake nema ta danne duk wani hali da take ciki, kafar da ta daga da nufin saukewa waje ta gyarawa zama a cikin motar, tare da yanayin zamanta yanda zata fuskance shi sosai.

“Me nayi?”

Ta bukata kai tsaye, sai ya girgiza mata nashi kan

“Banfa yi komai ba, babu abinda nayi.”

Ta fadi ganin gabaki daya duk wata walwala ta dauke daga fuskarshi.

“Ni ma bance kinyi wani abu ba ai Sa’adatu.”

To me yasa zai dinga mata magana da wannan sigar? Tunda batayi komai ba.

“Kije ki huta, idan akwai wani abu ki kirani ko kiyi mun text.”

Ta numfasa zatayi magana wayar Jabir din ta fara kara, kuma sanin wacce wayace a cikin wayoyin yasa shi mika hannu gaban motar inda ya ajiye wayar yana daukota, Aisha ce, har zai kashe tunda ai daga nan wajen Sa’adatu gidan zaije, sai wani alkawari daya daukarwa kanshi akan Aishar ya dawo masa yana sakashi daga wayar ya kara a kunne.

“Kana ina?”

Aisha ta fada tana sauke numfashi cikin kunnenshi, ya danyi jim kafin ya amsa da.

“Nazo duba Sa’adatu.”

Tunda ai a rikicin da tayi masa, rikicin da ya dauke su kusan wata daya maganar ta mutu, haka ta dinga maimaita masa

“To meye na boyemun? Na isa in hanaka abinda kake sonyi ne ko kayi niyya? Ai daman ban sakawa raina zan rayu da kai ni kadai ba.”

Kuma da yayi lallashin, ya bita kamar zai kwanta mata tana botsarewa sai a satikan ta koya masa tattarata da rigimarta ya ajiye gefe daya saboda ta gajiyar dashi, ta kaishi wani mataki da shima yakejin halin da take ciki din ko kishinta sun daina daga masa hankali, kuma yayi alkawarin in dai akan Sa’adatu ne da lamarinta ya daina yiwa Aisha shamaki, ya daina tunanin ko ranta zai baci, ko zataji babu dadi.

“Aina dauka mun wuce matakin da zamu tsaya yiwa juna boye-boye ko wani zagaye.”

Haka ta kara masa, shi zaice ma suna fada, kala-kala kuwa, amman ai koya zata bata masa rai, yana da yakinin Aisha na tausasa harshenta, tana zaban abinda zata fada masa, amman a wannan dan tsukin kusan duk abinda tayi niyya saida ta fade shi. Ta dinga sakashi tunano duk wani labari da yaji yan uwanshi mata nayi akan mazajensu da suka kara aure, da kuma suma mazan abinda suka fuskanta daga wajen nasu matan a lokacin da zasu kara aure, yanata dauko abubuwa yana aunasu da abinda Aisha takeyi masa. Kuma da ace bai dinga hadawa da irin nashi kishin yana mata uzuri ba, tabbas da sun samu gagarumar matsala. Tunda ya kula itama din tana da wani irin kishi da batasan dashi ba.

“Amman yanzun zan taho. Lafiya dai ko?”

Jabir ya dora dashi jin shirun Aisha da yayi yawa ta dayan bangaren, sai numfarfashin da take sauke masa cikin kunne.

“Take your time.”

Ta fadi tana katse kiran, kuma ai shi ba yaro bane, yasan gatse, ya jishi a muryarta. Daya kalli Sa’adatu data kafa masa ido, ga mamakinshi saita gyara zamanta cikin motar sosai.

“Kasan mun kusan shiga test week, gani nake kamar bamu wani dade muna karatun nan ba, ga semester din farko na neman karewa”

Sa’adatu ta fadi, tana nemo duk wasu labarai na makaranta, ai tasan Aisha ce tun daga yanayin yanda yayi kafin ya amsa wayar. Har ca yake mata yanzun zai tafi, wani abune ta dinga ji yana mintsininta, lokaci daya ta nemi rashin walwalar da take ciki ta rasa, babu komai a ranta yanzun sai son taja Jabir da labari ya bata lokaci a wajenta. Ya tafi yanzun yaje yayi me? Saurin me yakeyi? Ita matar tashi in tayi hakuri ai a gefenta zai kwana.

Yanda kuma Sa’adatu ta dage tana kwaso masa labari sai kawai yasa shi jin dariya na neman kwace masa.

Ko da aka rarraba halaye a tsakanin mutane
mata sai sukayi tarayya a wajen kishi.

<< Tsakaninmu 55Tsakaninmu 57 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×