Skip to content
Part 57 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

A zaune yake, amman ji yake idan yayi wani kwakkwaran motsi faduwa zaiyi. Yanajin sanyin tiles din asibitin da yake ratsa kafafuwan shi da babu takalmi, a yanayin yanda komai yake wuce masa, ya kasa tsayawa ya tantance waye ya ajiye masa silipas a kusa da kafarshi.

“Na gode.”

Ya furta, muryarshi na komawa cikin kunnuwanshi kamar ba tashi ba, takalmin kuma ya saka, yasha jin Mus’ab na labarin wani abokinshi inya shiga dakin tiyata, cikin wasu kayadaddun mintuna yakeyi ya gama, harma wadannan mintinan suka zama lakabin shi a cikin asibitin da suke aikin. Amman yanzun aishi yanajin kamar kwanaki aka shafe daga zuwansu asibitin.

“Shifa dan adam ba a bakin komai yake ba”

Wasu kalamai da Hajiya Hasina ke yawaita fadi, musamman idan taji labarin rashin lafiyar wani, sai yanzun gaskiyar maganganun take zauna masa. Kana yawonka hankali a kwance bakasan me yake shirin faruwa da kai ba, saima ka kalli agogo kana hasaso abinda zakayi da karfe kaza batare da kasan cewa cikar wannan lokacin zaizo maka da wani birkitaccen al’amari ba, su da safen da ai lafiya kalau suka tashi, harma daya tsaya yanawa Aisha dariyar maganar da tayi ta cewa

“Kasan ba cikin kowa bane yake irin girman da nawa yayi? Wancen watan da nace Antenatal, wata mata haka ta shigo, da yake hijab ne a jikinta kuma tana da dan jiki sai cikin yayi mata kamar tumbi, kuma anan nakuda ta taso mata, da yake Allaah Ya kawo mata gajeriya, kafin in gama abinda nakeyi akace harta haihu, na dinga mamaki daman tsohon cikine da ita? Ni kam ai tun yana wata shida ma, in zan fita daga mota shine yake fara yin gaba”

A safiyar kuma sai yaga cikin ya kara girma, in ba idanuwanshi bane ba, cikin yayi masa kasa sosai, tunda daya kama hannuwan Aisha yana taimaka mata ta mike saida yace.

“Cikinki kamar kasa yakeyi, ko nine nake gani”

Ta girgiza masa kai

“Ka manta jiya Edd dina ya cika? Yayi kasane saboda zan iya haihuwa kowanne lokaci.”

Sai ya jinjina kai, taya zai manta cewar lokacin da asibiti sukayi mata hasashen zata haihu yazo ya wuce, bayan ma ya fita lissafi, ko yanda take tashi ta kuma zauna dakyar, yanda in suka fita zagayen da likita yace ta dingayi yana taimakawa sosai zata dinga numfashi kamar mai cutar asthma, sai yaji tausayinta ya kamashi, sai ya kara jinjinawa mata, wato duk wadda kagani da danta kawai ka tayata godewa Allaah, ita kadai tasan wahalar da tasha kafin fitowarshi. Shi bayama son ya hasaso cewa shine dauke da wannan cikin na jikin Aisha.

“Nifa so nake in fita in mike kafata yau.”

Aisha ta fadi.

“Da yamma in rana ta sauka sai mu fita zagayen layi.”

Saita girgiza masa kai.

“Yawo fa, ba zagayen layi ba.”

Dariya yayi

“Ina zamuje to?”

Ta danyi jim, alamar tunani.

“Bari dai mu karya, yunwa nakeji.”

Tare suka nufi kitchen din, tare ma suka soya plantain da kwai, duk yawan wadda suka soya kuma Aisha fada masa takeyi ita kadai ma zata iya cinyewa. Cikin raha suka karya, da yake a tsakiyar falo suka zauna sai Jabir ya kunna musu tv, ya mika mata remote din, ta tsaya, tayi sa’a an saka wani india da ba zai tuna adadin da suka kalle shi ba saboda kaunar da Aisha takeyi masa.

“Hum dil de chuke sanam akeyi kaga”

Kuma anan suka shiririce kallon ko bayan da suka gama karyawa. Yana zaune ya jingina bayanshi da kujera, Aisha kuma tayi matashi da cinyarshi yanata wasa da kitson daya gama yi mata dariyar girmanshi, biyu kawai aka raba kan ana kitse kowanne bangare.

“Kitson shiga fagen fama ne.”

Ta fada tana sake bashi dariya.

“Kamar fitsari nakeji Jay, ka taimakamun in tashi karya zubo.”

Aisha ta fadi adan rikice tana rikita shi shima saboda a kwance take a jikinshi, kokarin tashi takeyi kuma ta kasa, sai dai lokacin dashi ya mike tace masa.

“Ya zubo, inajin dumin shi, Jay nayi fitsari a jikina.”

Ta karasa maganar cikin yanayin rashin jin dadi da kidima kuma, sai dai kafin ya samu yace mata wani abu idonshi ya kai kan abinda ya birkita masa kai kuma har yanzun da yake zauna ma cikin wannan rikitar yake. Jini ya gani, ba don bai taba ganin jini ba, sai don ko ba’a fada masa ba yasan cewa matsala ce babba jini ya ballewa mai tsohon ciki kamar na Aisha. Shiya kamata saboda jikinta da yayi kamar tana jin nauyinshi fiye da ko yaushe.

“Jini ne”

Ta fadi, saiya daga mata kai

“Jabir…”

Ta kira cikakken sunanshi

“Babyna Jabir, kar in rasa babyna.”

Sai dai a wannan bigiren, itace ta fara zuwa masa kafin Babyn, Allaah ne ya basu a lokacin da suka fitar da rai, idan yaso saiya sake basu wani, amman ita kuma fa? Matar shi? Aishar shi, inya rasata ina zai samo irinta? Sai wani abu da yasan ba iska bace ya fara kadashi. Kuma har ya mutu idan za’a tambaye shi yanda ya iya saka Aisha a mota, ya jasu zuwa asibiti, wani labarine da baisan ta inda zai tattaro shi ba ballantana ya fara bayarwa. Da aka karbi Aisha ana shiga da ita dakin da za’a bata taimakon gaggawa, kuma likita ya fito yana fada masa zaisa hannu a takarda saboda za’ayi mata emergency C’s.

“Bugun zuciyar abinda yake cikinta yayi kasa sosai…”

Haka likitan yace, a maimakon ya amsa shi sai yace masa.

“Ko zan iya aron wayarka idan ba matsala?”

Saiya sa hannu a aljihu ya zaro karamar waya mai malatsai ya mikawa Jabir, daya karba batare da bata lokaci ba ya saka lambar Hajiya Hasina yana addu’ar ta zama kusa da wayar, yasan in dai tana kusa, ganin bakuwar lamba bazai hanata dagawa ba tunda lambarta ce da bakowa yake da ita ba, ringing na biyu sai kuwa ta daga da sallama

“Hajja…”

Ya kira sunanta

“Jabir?”

Ta fadi kamar da alamar tambaya

“Bugun zuciyar babyn yayi kasa sukace, wai za’ayi mata aiki a ciro shi, ni kadaine Hajja, ita sun shiga da ita wani daki.”

Jabir ya karasa maganar yana murza goshin shi, kanne gabaki daya yayi masa wani irin nauyi, kamar yana neman yafi karfin wuyanshi.

“In Shaa Allaah babu abinda zai faru, kayi duk yanda likitoci suka fada, yanzun zamu zo In Shaa Allaah, Aisha ce ko Sa’adatu?”

Numfashi ya sauke yana daga kai kamar tana ganinshi.

“Aisha”

Ya amsa

“Tam gamu nan In Shaa Allaah.”

Bai kuma ce komai ba ya sauke wayar daga kunnenshi yana mikawa likitan hadi da fadin

“Nagode. A ina zansa hannun?”

Kuma kafin wani lokaci saida wani lokaci sun zama abin kallo a cikin asibitin saboda yanda suka cika shi, daga danginshi harna Aisha da basu hana masa jin kamar shi kadai yake zaune a gabaki dayan asibitin ba, daga shi sai dakin da aka shiga da Aisha mintina kadan da suka wuce, jikinta da kayan da suka sake mata, wasu kaya da ya kasa tantance asalin kalarsu, ko yace tashin hankali ya binne masa sunan kalar

“Awa nawa yanzun Hamma? Bai isa ace sun fito ba?”

Ya fadi duk da bai daga kai yaga waye kusa dashi daya dafa masa kafada ba

“Duka mintina goma ne da shigarsu Jabir, yanzun zasu fito In Shaa Allaah.”

Kuma daga maganar bayajin ko an duba an kara wasu mintina sha biyar din kukan jariri ya daki kunnuwansu, kukane da yakeyi kamar an ciroshi duniyar ne bada son ranshi ba a yanda ya bude duka murya yana kwala shi, a tsakanin kukan nashine kuma Jabir yake jin muryoyi daban-daban,amman a lokaci daya, wasu na Hamdala wasu kuma suna Kabbara cikin kara mika wuya ga Ubangiji. Sai Jabir yaji wani yanayi yana dukanshi, bugun zuciyarshi na karuwa ninkin wanda ya tako asibitin dashi, kukan jaririn na shigarshi, a lokaci daya kuma zuciyarshi na budewa da wani sabon shafin kauna da bai taba sanin akwai irinta a duniya ba. Har lokacin bakajin komai sai kukan jariri, sai kuma fara’ar da take kan fuskokin kowa. Bai san ya akayi ba, sai ganin Hajiya Hasina yayi ta nufo shi rike da jaririn da aka nade cikin showel fari kal, fuskarta dauke da wata irin fara’a.

“Namiji aka samu Jabir, namiji ne.”

Ta fadi da kyallin hawayen farin ciki a idanuwanta, Allaah Mai kyauta da kari, yau itace rike da gudan jinin Jabir.

“Hajja bari in zauna karmu fadi.”

Dariya tayi mai sauti, wasu na tayata.

“A zaune kake ai.”

Saiya mika hannuwanshi da yakeji suna rawa ya karbi yaron, kuma kamar ya fahimci abinda yake faruwa da Jabir din ya girmeshi saiya zabi wannan lokacin yanayin shiru, Jabir ya kura masa ido, ya daga kai ya kalli Hajiya Hasina.

“Kayi masa huduba.”

Kai Jabir ya iya daga mata, ya kai bakinshi saitin kunnen yaron yanayi masa kiran sallah a hankali, yabi hakan da adduoin nema masa albarka da kariya daga fitintinun duniya. Sai dai lokacin daya dago dabinon Ajwa ne aka miko masa, ya balli kadan ya tauna yana saka danyatsan shi ya fito dashi ya lalubawa yaron a baki, sannan muryarshi na rawa yace

“Hassan, Hassan Jabir Hassan Paki…”

Yana dorawa da

“Na’im”

Hajiya Hasina ta jinjina kai kawai, abinda takeji ya shake mata wuya ya hana magana.

“Allaah Ya raya mana shi cikin aminci da salama, Yayi masa albarka.”

Cewar Farhana data tako ta karbi yaron dan ta mikawa mahaifiyar Aisha data koma gefe cikin kawaicinta, ko da ta mika mata shi ma sai tace mata.

“Ai da kin basu sun ganshi tukunna.”

Farhana tayi mata murmushi.

“Hajiya shima fa baice yanayinki ba balle kiyi masa yanga.”

Dariya tayi tana karbarshi da sunan Allaah a bakinta, duk da babu abinda take sonji irin labarin ‘yarta, ba’a dauki wani lokaci ba likitan da yayi mata tiyatar ya fito da murmushi dauke a fuskar shi.

“Alhamdulillah…”

Ya fadi yana sakasu yin hamdala shima, kuma sanda aka fito da Aisha daga dakin tiyatar idonta biyu ma, Jabir kadai aka bari ya bita dakin yana riko hannunta.

“Sunce mun namiji ne.”

Ta fadi muryarta na fitowa cike da nauyi, saboda bacci ya fara neman cin karfinta.

“Namiji ne Tasha, ki huta dan Allaah, sannun, nagode. Nagode sosai.”

Ya karasa yana matsawa sosai ya sumbaci gefen kuncinta.

“Na’im…”

Cewar Aisha tana rufe idonta.

“Na’im”

Jabir ya maimaita mata, sai dai bacci ya rigada ya dauketa. Shima saiya dora kanshi a gefen gadon bakinshi dauke da hamdala, ita ya cigaba da maimaitawa har saida yaji duk wani firgici ya bar jikinshi, farin ciki na maye masa gurbinshi, natsuwa na saukar masa. Ga matarshi ta fito lafiya, ga kuma danshi can a waje, lallai Ubangiji Mai yawan Rahma ne.

*****

Jabir ya hana a sallami Aisha bayan kwana uku, duk da likita ya tabbatar masa cewa babu wata matsala, yace su dai barta a asibitin sai tayi sati, saboda inta koma gida mutane ba zasu barta ta huta ba. Ya kuwa yi gaskiya, dan ko bayan da suka koma gida, haka aka dinga tururuwar zuwa tayasu murna. Jabir mutum ne da abin hannun shi bai rufe masa ido ba, daga shi har Aisha basa kyashin hidimtawa duk wanda yake tare dasu balle kuma ace dangi. Basa duba kana dashi ko baka dashi, in dai sun tashi zasuyi maka alkhairi dai-dai iyawarsu. Shisa zai zama bata lokaci ma fadin irin bajintar da mutane sukayi musu, balle shi kanshi uban gayyar wato Jabir.

Haka akayi suna cikin aminci aka gama, sarai Jabir yaga sakon Sa’adatu na tayashi murna da addu’ar fatan alkhairi ga Aisha da abinda ta haifa, da yake shima ta sakon ya sanar da ita haihuwar. Bai samu ya kirata ba dai sai yau, kuma yanayin yanda yaji muryarta na fita, duk da tace masa lafiyarta kalau sai ya kasa samun natsuwa. Da yayi sallar Magriba saiya tsaya ya siyi gasassun kaji da manyan jarkokin yoghurt da yasan Sa’adatun naso tukunna ya kama hanya, da yake ya fada mata yana hanya, da taga kiranshi sai bata dauka ba, hijabin data sakama na Fa’iza ne, ruwan toka mai haske, kamar ko yaushe idan yazo saida ta daukar masa zobo da kunun aya ta hada masa da ruwan robar da yanzun baka rabasu dashi tunda Jabir ya rantse ba zata sha kowanne ruwa ba sai shi, kafin wani ya kare ya sake sawa anzo an kawo mata wasu.

Yau har sallama tayi masa, ya amsa kafin ta gaishe dashi tana dorawa da

“Abban Na’im”

Zuciyarta daya, har kasan ranta ta tsinci kanta da tayashi murna tun ranar daya fada mata, da kuma ya tura mata hotunan Na’im din, haka taje tana nunawa Fa’iza, sunata yaba kyan yaron da yanda ya burgesu. An saka masa kayan yan gayu, ya fito tas, yana kwance akan wani bargo mai gashi-gashi. Kuma da yake ya fada mata sunan yaron dama yanda zasu dinga kiranshi saita tsinci kanta da sake masa suna har a jikin contact dinshi. Dariya kawai yayi, da inya ga daga haihuwa mata sun sakewa mazajensu suna sai abin ya dinga masa wani iri, sai yaji kamar in hakan ta faru dashi zaiji tsufan duniya ne ya hau kanshi. Ko kadan abin baya burgeshi, Aisha ma tasani, tunda dawa zaiyi maganar in ba ita ba? Amman da Sa’adatu ta kirashi da hakan, sai ya tsinci kanshi cikin wani irin nishadi marar misaltuwa.

“Yan mata”

Ya fadi, dariya Sa’adatu tayi, dariya sosai, ita yanzun a halin da take ciki, yanda take jin ta zama wata iri, ai tafi dacewa da a kirata Gwaggo.

“Bari yan mata suji ka.”

Dariyar yayi shima.

“Kina da son girma Sa’adatu, yar yarinya dake.”

Kai ta jinjina har lokacin da murmushi a fuskarta.

“Nice yarinyar? Shekaru ashirin, nafa yi rabin arba’in Abban Na’im, mu yanzun ai mun shiga sahun manya”

Banda dariya da

“Allaah Ya shiryamun ke.”

Baisan kuma mai zaice mata ba, yaji dadi sosai ganin lafiyarta kalau, duk da ta shiga sati na talatin da shida a lissafin asibiti, amman a nata lissafin da tace masa Fa’iza ta tayata sunyi ta wuce hakan, amman ai daga lissafin nata harna asibiti hasashe ne, sanin asalin kwanakin cikin sai Allaah, karshen lissafin dai shine fatansu na ta sauka cikin aminci. Hira suka danyi har aka fara kiran sallar Isha’i tukunna yace mata zai tafi.

“Akwai abinda nayi…”

Sa’adatu ta fadi tana saka idanuwanta cikin na Jabir

“Abinda nasa akayi…akayiwa Na’im.”

Tayi maganar kamar mai tsoro, kuma zuciyarta bugawa takeyi. Itama a Instagram taci karo da shafin matar, tana saida azurfa, tanayin irin customized din nan, sai taga tanayin abin hannu na yara dana manya wanda ake rubuta suna a jiki na azurfa, da yar sarkar da za’a zagaya a daura. Bracelet ne da yayi matukar burgeta, ko kadan bataji komai ba na kudin da matar ta cajeta, kamar yanda bata tsaya dogon tunani ba tasa tayi mata har guda biyu, daya aka rubuta Hassan, dayan kuma Na’im. Sai dai bayan an kawo kuma sai ta dinga tunani kala-kala, to idan kuma Aisha tace bataso fa? Me ma take tunani, ita dai kawai taji kamar ya kamata tayiwa Jabir din wani abu da zai nuna tana daga cikin masu tayashi murna.

“Ya kamata fa muyiwa Jabir wata kyauta, sai dai mu ba masu kudi bane Sa’adatu, meye zaka siya kaba irinsu Jabir idan anyi musu haihuwa wanda basu rigada sun siya ba? Dama ace kishi bai hadaku da matar ba, tsakaninki da Jabir ne kawai sai in daka yaji insaka a robobi in bashi ko mutane ta rabawa.”

Dariya Sa’adatu tayi, batajin ma yaji na daya daga cikin abinda zasuyi maraba dashi, bambancin da yake tsakaninsu ba’a kudi kawai ya tsaya ba a tata mahangar, anya suna wani rabon yajin jego?

“Sai mu bisu da addu’ar fatan alkhairi Matar Yaya.”

Kuma da wannan ta rufe bakin Fa’izar, ita dai ta zagaye ne ta siyi bracelet din, a makaranta ma aka kai mata ta biya kudin delivery din.

“Nasa anyi ne kawai, amman bansan ya zaka karbi abin ba, watakila ba zataso ba, zan fahimta idan bataso.”

Ta karasa tana ciro dayan hannunta daga aljihu ta mika masa yan akwatina guda biyu masu matukar kyau da aka sako mata bracelet din, karba Jabir yayi, ya bude na farkon da akasa Na’im, ya jima yana kallon abin tukunna ya kalli Sa’adatu ya furta.

“Thank you. Tasha ba zataki karba ba, mungode sosai Sa’adatu, Na’im ma ya gode.”

Saita jinjina masa kai, yanda ya sauke murya na motsa zuciyarta, a lokaci daya kuma yana sakata yin fata kala-kala.

<< Tsakaninmu 56Tsakaninmu 58 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×