Skip to content
Part 58 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Ko kadan baiyi niyyar fita kasuwa ba ranar, musamman yanda Na’im yayi kwance luf a kirjinshi yana bacci, shima da kira kan kira bai dinga shiga wayarshi ba baccin zaiyi. Kuma ranshi a bace, kamar wanda akayiwa dole haka ya shirya, Aisha nata yi masa dariya, bai kulata ba, kiran da suke tayi masa daga shagon takalmanshi ne, wani mutum ne yazo yana son magana dashi, ya kawo musu tallar takalma, yan kasar Italy ne, hoton takalman ne daya gani yasa shi shiryawa, dan takalma ne masu kyau sosai. Ya kuma ji dadin zuwan, tunda ido da ido ma takalman sunyi kyau matuka, sannan batare da fargaba ba suka fara ciniki, saboda mutumin ma sananne, Jabir din yasha jin sunan shi a bakunan mutane, kuma lokaci daya ko biyu ya taba ganin shi, sai yanzun dai wata mu’amala zata hadasu.

Sun gama cinikin ne, ya tura kudin, ana shigar da lissafin ne wayarshi tayi kara, saiya dauka sakon fitar kudin daya tura ne, shisa baima duba ba, har saida ya gama abinda yake, ya sake jin wani sakon ya shigo, ya fito da wayar, ta saman notification yaga Abdallah ne, zuciyar shi tayi wani tsalle, sakon layi dayane

“Muna gida, sun sallame mu.”

Suna wanne gidan? An sallame su daga ina? Su suwa ma kenan? Tambayoyin suka jeru cikin kanshi, saiya shiga ya bude sakon, ya kuma ga sakon farko.

“Sa’adatu ta sauka lafiya, an samu mace.”

Kamar yanda ya karanta sakon tana da ciki, haka ya dinga karanta na haihuwar yana sake maimaita shi, ta haihu fa yake gani, ita tata haihuwar haka tazo musu kenan?

Ta haihu
Sa’adatu ta haihu

Zuciyarshi ta maimaita kamar maison kwakwalwar shi ta fahimci wani abu. Saiya laluba aljihunshi, yaji mukullin motar shi yana nan.

“Sahal anmun haihuwa yanzun nan, ka kula da komai dan Allaah, idan akwai wani abin ka kirani.”

Jabir yacewa Sahal din, wani amintaccen yaron shi da yake alfahari dashi, baya kuma shakkar damka masa dukiyar shi komin yawanta. Harya karasa gidansu Sa’adatu gani yake kamar wani mafarki yakeyi, dan daya karasa dinma Abdallah Ya kira a waya ya fada masa yana kofar gida. Kuma ko mintina biyar ba’ayi ba tsakani Abdallah ya fito fuskarshi dauke da murmushi, murmushin da har suka gaisa da Jabir din bai daina shi ba.

“Bari inyi musu magana, saika shigo”

Abdallah ya fadi bayan sun gaisa, kai kawai Jabir ya iya daga masa, kuma ko daya dawo yace masa su shiga cikin gidan, haka yabi bayanshi kamar mai yawo saman ruwa, inda Abdallah ya cire kafarshi nan Jabir yake mayar da tashi, kuma da yake kanshi a kasa yake, batare daya kalli masu gaishe dashi suna masa barka ba yake amsawa da.

“Lafiya kalau, thank you. Nagode sosai.”

Har suka shiga dakin tare da Abdallah. Sa’adatu na zaune, kanta da hular data dan zame mata, kuma da alama kanta a kwance yake, ga gashi nan ya kwanta luf-luf, fuskarta tayi masa fayau, kamar kuma ta rame masa, doguwar rigace a jikinta mai dogon hannu, kuma a bakin katifa take zaune da kwano a hannunta, bai kai da ganin meye a cikin ba, amman dakin sai kamshin abincin yakeyi yana tayar masa da yunwar da bai shiga gidan da ita ba. Sai kuma yarinyar kwance a gefenta da alama bacci takeyi, ya kalli Sa’adatu, ta kalle shi tanayi masa murmushi, sai Abdallah ya fice yana bar musu dakin, kallon yarinyar yakeyi daga inda yake tsaye, kuma sai yake ganin kamar fuskar Na’im a tare da ita, abinda aka kwantar da yarinyar akai Na’im na da irinshi, cikin kayan da Aisha ta siyane.

Ba zai manta ba, randa Sa’adatu ta bashi bracelet din nan, shi kanshi ba zaice ga a yanayin daya shiga dasu gidan ba, haka daya mikawa Aisha bayan ya amsa sannu da zuwan da tayi masa, sai ya kafe idanuwanshi akanta, ta bude akwatinan, wani kayataccen murmushi ya sauka akan fuskarta, ta bude baki, kafin tayi wata magana ya rigata da fadin

“Sa’adatu ce tace bayar, ita tace a kawo”

Sai Aisha ta mayar da bakinta ta rufe, ta kuma cigaba da juya bracelet din a hannunta, kafin ta daga net din katifar da Na’im yake ciki, ta ajiye bracelet din da akasa Hassan a jiki, ta kamo hannunshi ta daura masa wanda akasa Na’im din, sai ya zauna dam yanayi ma hannun nashi kyau, takai hannu ta shafa bracelet din, sannan da wani yanayi a muryarta tace masa

“An fada mata gender na abinda zata haifa?”

Tambayar tayiwa Jabir bazata, amman saiya amsa.

“Mace sukace”

Ta jinjina kai, har lokacin tana kallon bracelet din a hannun Na’im kamar mai neman wani abu a jiki.

“EDD dinta fa?”

Sake amsata yayi yana mamakin inda tambayoyinta suka dosa.

“Kace mata Na’im ya gode. Ka kuma ce mata anyi mana kyauta kala-kala, amman tata kyautar ta fita daban, nima nagode. Allaah Ya sauketa lafiya.”

Kuma sati biyu tsakani, ya dawo gidan, Aisha ta mike tana janyo wasu akwatina guda biyu ta ajiyesu a gabanshi.

“Ka kaiwa Sa’adatu. Allaah Ya kawo mana Baby cikin aminci.”

Ya kalli kayan, ya kalleta.

“Aisha…”

Ya kira, amman sauran kalaman sai suka makale masa.

“Ina da kishi Jay, ina da kishin da ban taba sanin girmanshi ya kai haka ba saida ya biyo takaina, amman ina addu’a, ba zan kuma daina addu’a ba, Allaah karyasa kishina ya taba tasiri akaina…”

Har lokacin Jabir ya kasa cewa komai sai kallonta da yakeyi

“Kuma watakila Allaah Ya duba alkhairina a gareta ya amsa addu’ata ta in rayu da kai ni kadai, tunda naji wa’azi, Malam yace ba haram bane yin irin wannan addu’ar.”

Sai Jabir yayi dariya.

“Allaah Ya saka da alkhairi.”

Dariyar tayi itama batare da tace komai ba, kuma yasan yawan kayan ne da abinda yake ciki saboda Sa’adatu, data kirashi bayan ta bude kamar zata fasa masa dodon kunne da murnarta, taga kiran ba zaiyi mata ba ta kashe ta kirashi video call, nan ma bai isheta ba, duk abinda ta daga indai yayi mata kyau saita dauke shi hoto ta tura masa, kuma bata daina damun shi da hotunan kayan ba har sai randa ya kai mata tashi siyayyar, kuma yaga takun da tayi, kafin ta koma baya, duka jikinta yaga alamar so tayi ta rungume shi, wani yanayi daya kasa mantawa har yau, har yanzun da yake so ko da bai rungumeta ba, ya sumbaceta, yayi mata godiya.

“Sannu Sa’adatu”

Ya fadi yana rankwafawa ya dauki yarinyar da taketa bacci, yana mikewa, kafin ya kai fuskarshi saitin kunnenta dan yayi mata huduba, Sa’adatu ta kalle su, komai nayi mata kama da mafarki. Tunda ta tashi da safen take jin jikinta kamar ba nata ba, ga cikinta da yayi nauyi sosai. Dakyar tayi sallar asuba, anan kan dardumar ta kwanta. Bacci mai nauyi ne ya dauketa, kuma a cikin baccin taji kamar an kwada mata wani abu, ta bude idonta babu shiri, sai dai ta kira sunan Allaah ne, saboda neman ko waye ya kwada mata abinda ya kwada mata takeyi, tunda ai ga zafin nan tanaji, ta kasa tantance daga ina yake fitowa ne. Kuma ko za’a dora mata wuka a wuya zata rantse da bayanta ya amsa sai da taji yayi wata kara, karar ce kuma ta sakata kwalawa Fa’iza kira, da gudu ta rugo dakin kamar bata goye da yaro a bayanta

“Sa’adatu”

Ta kira cikin kidima

“Matar Yaya wani ya shigo gidan nan, ya kwadamun wani abu a bayana, bayana zai karye.”

Kuma da Fa’izar ta gane abinda yake faruwu, sai dariya ta kwace mata.

“Yaushe wani ya shigo Sa’adatu? Ina fa tsakar gidan tun dazun ina wanke wake, tashi mu tafi asibiti nakuda kike.”

Kai Sa’adatu take girgiza mata

“Ina bacci naji an kwadamun abin na tashi…ma…”

Wani murdawa da abinda yake cikin nata yayi sai gata a tsaye babu shiri, da yake daman ba wani abu zasu dauka ba, Abdallah kawai Fa’iza ta kira, sai ma yace mata yana cikin unguwar, shiya taho da mai adaidaita suka nufi asibiti. Cikin ikon Allaah ko mintina sha biyar basuyi da zuwa ba, tunda Abdallah nata kokarin siyan kati ta banki network ya hanashi, saiya fita wani shago daya gani a wajen asibitin ya siyo, ya dawo kenan yana gama saka katin, bai kai da lalubo lambar Nabila ba aka fito akace musu ta sauka lafiya, ta samu mace. Haka ya dinga kiran ‘yan uwa da karsashi yana fada musu kyakkyawan labari. Sunce zasu rike Sa’adatu zuwa yamma dan ta huta, amman da yake ta dawo hayyacinta, kuma ba wata doguwar nakuda tayi ba, sai take jinta garau.

Wata irin yunwa ma taji, ita shayin da aka hada mata bai kai mata ko ina ba duk da kaurin shi kuwa, kuma so take taji ta a gida. Wanne bacci zata kwanta tayi a asibiti tunda Allaah Ya sauketa lafiya? Sai kawai ta kafewa likitar kan cewa itafa in dai babu wata matsala a sallamesu, zata huta a gida. Haka kuwa aka sallamesu, tunda Jabir ya jima da biyan kudin komai, shine ma yake da canji a wajensu. Fa’iza ce ta goya jaririyar, tana kwance Abba daga bayanta taba Abdallah shi ya sabe a kafada, napep suka kara dauka zuwa gida. Suna shiga Nabila tana zuwa itama, itace ma ta dorawa Sa’adatu ruwan wanka. Ita kuma ta shige daki, Fa’iza ta bita da yarinyar tana kwanceta ta mika mata, itama ta fita zuwa tsakar gida.

Tun a asibiti aka bata yarinyar dan ta shayar da ita, ta kuma yi hakan, tanata kallonta, so takeyi taji irin abinda ake misaltawa a litattafai, ko kuma take gani a fina-finai duk lokacin da ka haihu aka saka maka abinda ka haifa a hannunka, wannan kaunar, wannan shaukin, banda kanta da yake mata nauyi da mamaki inta kalli yarinyar ta kasa jin komai, gani take kamar wani zai daga labulen dakin yace ta mikota, kamar kowanne lokaci za’a iya karbarta, ko a tasheta daga mafarkin da takeyi. Har yanzun da tayi wanka da taimakon Nabila, ‘yan uwanta da suke gari suka fara cika gidan, ita ma yarinyar akayi mata wankan, wannan yanayin bai barta ba. Har kuma Abdallah ya shigo yana sanar dasu cewa Jabir yazo wani sama-sama take jinta. Ga farfesun da Fa’iza ta dumama mata na kayan ciki aka miko mata duk ya bude dakin da kamshi.

Lokacin da Jabir ya gama yiwa yarinyar huduba saiya tsaya yana kallonta, abinda zuciyarshi ta dinga so kwakwalwar shi ta gane dazun sai yanzun ta fahimta, damar shi ta gama karewa akan Sa’adatu, ya rasa wannan damar, aurensu ya karasa karewa da haihuwar nan da tayi, sai yaji kafafuwanshi kamar suna rawa, hakan yasa shi tsugunnawa.

“Ga kafet can ka dauko.”

Sa’adatu tace masa, saiya girgiza mata kai.

“Tafiya zanyi ma ban gayawa kowa kin haihu ba.”

Saita jinjina masa kai, tasa cokali ta soma shan romon farfesun a hankali, tanajin kamar an sabunta mata kafofin dandanonta, harshenta ya bude yana karbar dadin farfesun, jiya da daddare ashe babu abinda ta fahimta.

“Baki tambayi sunan yarinyar ba.”

Jabir ya fadi yana kallon Sa’adatu, kuma da yake yanzun akwai shamaki a tsakaninsu, sai yake jin tana fisgarshi, dararensu suna dawo masa kamar lokacin suke faruwa, sai ga idanuwanshi suna tsallakawa wajajen da yafi so a jikinta, ya lumshe idanuwanshi, ya sake budesu yana sauke numfashi. Yanayi ne da Sa’adatu ta sani, yanayi ne da tasha gani a tare da Jabir.

“Kina so ki kure jarumtar da ban taba ce miki ina da ita ba ko Sa’adatu?”

Kalmomin shi suka dawo mata, dama wasu da yakan rada a kunnenta, har a cikin kanta kuma suna da nauyin gaske, sau nawa ya sha ce mata shi ba jarumi bane ba, sai dai tayi dariya kawai. Raunin nashi yana bayyana sosai a irin wannan yanayin harma ya kasa mallakar kanshi, a irin wannan yanayin ne kuma ya kan zabtare shekarun shi ya dai-daita da nata ya biyewa duk wata tabara da zata dasa masa. Kawai sai taji itama jikinta ya fara amsawa.

“Abban Na’im.”

Ta kira da rawar murya, daman mace da namiji idan suka kebe ai na ukunsu shaidan ne, tunda jaririyar da take hannunsu zata tare musu jin busar shaidan ne? Jabir ya sauke mata kasalallun idanuwanshi cikin nata.

“Sunan, baka fada mun sunan ba.”

Saiya mike daga tsugunnan da yayi, ya karasa ya kwantar mata da yarinyar da take bacci har lokacin.

“Kausar, sunanta Kausar, zaki iya kiranta da duk lakanin da yayi miki dadi, sunan mahaifiyata ne.”

Batasan tsakanin yanayin da yayi maganar da kuma raunin daya mamaye ilahirin jikinshi wanne bane ya karya mata zuciya. Amman sai hawaye suka soma yi mata barazana.

“Kausar?”

Ta maimaita, Hasina lakani ne kenan? Sai Jabir ya daga mata kai.

“Daman sunan Hajja lakani ne?”

Wannan karin shiya kalleta, kuma ya girgiza mata kai.

“Ba Hajja bace mahaifiyata.”

Itama shi take kallo, tana jinjina yanda zaka san abubuwa da yawa game da mutum kuma a lokaci daya kaji bakasan komai ba. Irin abinda takeji kenan, sau nawa ta rike Jabir a jikinta? Shi sau nawa ya riketa a nashi jikin? Sau nawa taga rauninshi? Sau nawa ya kirata kamar yana shirin fashe mata da kuka? Jabir, Jabir din da yake tsaye a gabanta a yanzun. Amman da kalmomi hudu kacal yana neman rusa duk wani sani da take tunanin tayi masa.

“Bansani ba.”

Ta iya furtawa, ta hadiye wani abu daya tokare mata wuya, kafin ta dora da.

“Sai menene ban sani ba?”

Saiya juya mata idanuwanshi kawai, ko shisa take ganin kalarshi ta fita daban data sauran ‘yan uwanshi? Sai dai kuma ai yana kama dasu, sosai take ganin fuskarshi cikin ta sauran ‘yan uwan nashi.

“Har yanzun baka fadamun yarenka ba”

Yar dariya Jabir yayi

“Sau nawa zance miki dan Nigeria, bahaushe kamarki.”

Saita girgiza masa kai, kafin tayi magana ya rigata da fadin

“Dinaar…zan kirata da Dinaar. Saboda itace yarinya mace ta farko dana samu, saboda sunanta Kausar, saboda zan kalleta da fuska biyu, zan kalleta a matsayin ‘yata, zan kuma jingina soyayyar da nakewa mahaifiyar da hotonta kadai nasani…”

Ya danyi jim, kafin yayi wani gajeran murmushi da ya karya wani abu a cikin kirjin Sa’adatu, wani abu da ta tabbata ba zuciyarta bace ba, tunda ai ance zuciya bata da kashi.

“Zinariyata ce wannan, mai tsadace sosai. Ki kulamun da ita…”

Ya karasa kamar yaso ya dora da wani abu amman ya zabi hadiye kalamanshi

“Ita kadai?”

Sa’adatu ta tsinci kanta da fadi, tana saurin dorawa da

“Bansan abubuwa da yawa ba akanka.”

Saboda batason ya amsa tambayar farko, bata son ya dora kalamai akan yanayin da yake fuskarshi sam, tagani, ba saiya furta mata ba.

Yana cewa
“Ki kula daku.”

Ya hada harda ita a cikine saboda a lokacin yarinyar shi na cikinta, yanzun ta fito, sauran kulawar da take tsakaninsu ta karasa yankewa. Ko shisa ma ta kasa jin wannan shaukin da ake fada akan yarinyar? Ko shisa take jin kamar za’a kwace mata ita kowanne lokaci?

“Bari inje Sa’adatu”

Cewar Jabir, saboda bayason amsa ko daya a cikin tambayoyin nata, ta ina zai fara? Dukansu tambayoyine da amsarsu bata da sauki a wajenshi, tambayoyine da suke masa nuni da layin karshe da sukazo a tsakanin shi da Sa’adatu

“Dinaar din fa?”

Wata murya ta tambaya a cikin kanshi

“Allaah Yasa mutuwa ce zata rabaku, Allaah Yasa kai da Sa’adatu har abada.”

Addu’ar da Hajiya Hasina take yawaita yi musu kenan. Daman tun a wancen lokacin Amin din tashi saita dinga makalewa a makoshi, yau kuma saiya kalli Dinaar da take gefen Sa’adatu, sai abu biyo suka zo masa. Har abada din da Hajiya Hasina ta roka musu ta amsu, ba a tsakanin shi da Sa’adatu ba, har abada din akan Dinaar ta fada, itace zaren da zai cigaba da hadashi da Sa’adatu tunda ya cika yarjejeniyarsu ya datse igiyar data kullasu waje daya.

Sai dai waye zai hada kwarin zare da igiya?
Anya kuwa addu’ar nan ba lilo takeyi ba?

<< Tsakaninmu 57Tsakaninmu 59 >>

7 thoughts on “Tsakaninmu 58”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×