Skip to content
Part 59 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Sanarwa

Dan Allaah ina neman afuwar duk wanda ranshi ya baci sanadin rashin update daga gareni. Especially Habiba A Gurai. Ayi hakuri, a yafe mun, a kuma taya ni da addu’a da daukacin musulmi gabakidaya. Allaah Ya bamu lafiya mai dorewa. Na gode kwarai

*****

“Matar Yaya ko dan daga cikin har nakuda sunzo mun cikin sauki shisa Allaah Yake jarrabani ta fannin nan? Su Yaa Nabila sunce haka nayi kukan nan da ina karama, haka Amma ta dinga fama?”

Sa’adatu ta tambayi Fa’iza tanajin kanta na gab da rabewa gida biyu, ga makaranta tana da ita washegari. Daga haihuwa, ya dauketa kwanaki kusan sittin, ba zatace ta dorar da wani abu na soyayyar da takeyiwa Dinaar ba, to yaushe ma ta samu lokacin bayan ko a cikin zaman jegon tana lekawa makaranta, wani abu da sukayi tashin hankali da Jabir akai, dan suna tare da direban daya ajiye mata ya karbo masa wani sako lokacin data kirashi, kwana goma da haihuwar dan yaje ya kaita makaranta, sai dai a maimakon shi data ji tsayuwar mota a kofar gidansu ta saka hijabinta, tana goye da Dinaar, hannunta kuma rike da jakar yarinyar da duk wani abu da su biyun zasu bukata, ta fita waje, sai da zuciyarta ta buga ganin Jabir a tsaye, ya jingina bayanshi da motar tashi, hannuwanshi harde a kirjinshi.

Kuma ko da tayi saurin sauke fuskarta, taga idanuwanshi, taga fuskarshi gabaki dayanta

“Ina kike tunanin zuwa?”

Ya tambaya tun kafin ma ta karasa inda yake, muryarshi tayi kasa sosai, da hankalinta duka ba’a kanshi yake ba, ba lallai taji maganar ba, ta aro jarumta ta yafa

“Makaranta”

Ta amsa a takaice

“Idan kuma nace ba zakije ba fa?”

Wani abu ya tokare wuyan Sa’adatu, kamar kuka abin na neman ya danne mata shakkar Jabir, ta daga kai tana sauke idanuwanta cikin nashi

“Saboda me?”

Saiya raba jikinshi da motar kamar mai niyyar karasawa shiya sameta

“Saboda Dinaar batayi kwarin da zaki fara wannan jigilar da ita ba.”

Duk da batasan meta tsammata ya fito daga bakin Jabir din ba, saida maganar ta taba zuciyarta. Hakane fa, komai yanzun saboda Dinaar ne, kulawar shi, damuwar shi, da sauran abinda ya rage a tsakaninsu, ba saboda yau kwananta goma da haihuwa ba, ba saboda jikinta a danyace yake da jegon da take ciki ba, ba saboda al’adar datayi mata hani da fita ko’ina in bai zama dole ba saita gama wanka , to Jabir ma bai duba dan zaman da sukayi da wahalar da tayi na rainon ciki ba, ina zai duba wata al’ada, idan ma ba bata lokacinta da zatayi ba, ai gabaki dayanshi ma bai tabayin wani abu da yake mata nuni da ko yasan al’ada ya damu da ita ba. Saboda haka ta jinjina masa kai, ta dago da jakar hannunta ta bude, ta ciro yar karamar jakar da kudinta yake ciki da waya, sai kuma takardunta na makaranta, ta mayar da jakar ta rufe, tana karasawa ta mikawa Jabir da duk da bai fahimci me yake faruwa ba yasa hannu ya karbi jakar.

“Dan rike mun…”

Cewar Sa’adatu, tana sake mika masa takardun da yar jakarta, ya kuma karba, saita saka hannu tana kwance goyon Dinaar da kamar jira take a saukota ta wage baki da duka muryarta tana canyara kuka babu ko jan numfashi, saida Jabir ya dan zaburo jin kukan da ta saki, tunda da ba a gabanshi Sa’adatu ta kwantota ba, zai iya cewa wani abin akayi mata ta saki ihu haka, gyara mata zama Sa’adatu tayi a hannunta, kafin ta mika dayan hannun tana karbe takardu da karamar jakarta, ta kuma tattara Dinaar da ko alamun tsagaita kukanta batayi ta mikawa Jabir daya tsaya yana kallonta.

“Zan makara dan Allaah ka karbeta.”

Kallonta kawai yake yi, idan ma akwai abinda ya kamata ya fada to ya bace masa.

“Abban Na’im mana.”

Cewar Sa’adatu a kagauce.

“Bangane in karbeta ba.”

Ya samu ya fadi.

“Eh saboda ni zanje makaranta, ita kuma kaga batayi kwarin da zanyi zirga-zirga da ita ba, idan na dawo saika kawota, in kuma kayanta za’a hado mata sai kayimun hakuri in dawo, ko in shiga gida inyiwa Matar Yaya magana.”

Mamakin shi a bayyane yake yanzun.

“Ni kike fadawa magana Sa’adatu?”

Jabir ya tambaya tsakanin mamaki da kuma bacin ran da yake taso masa.

“Ka dai rantse sai kasa na makara, in ba haka ba yaushe na fada maka magana daga baka ‘yarka?”

Tayi maganar tanakin yarda su hada ido, ya dauki yan mintina yana kallonta.

“Idan nace ba zakije ba me zai faru?”

 Ya sake tambaya.

“Zakace banji maganarka ba.”

Ya jinjina kai.

“Saboda sai kinje.”

Ta daga masa nata kan, sun jima a haka, kukan Dinaar na shiga har tsakiyar kanshi.

Zuciyarshi ce take fada masa bai kamata ya biyewa Sa’adatu ba, harda kuruciya take damunta.

“Tana kuka.”

Sai lokacin ta hada ido dashi

“Zata daina, ka karbeta lokaci nata tafiya.”

Yaja numfashi ya sauke.

“Ki shiga mota mu tafi.”

Yanayin da take gani a fuskarshi yasa murmushi ya kusan kwace mata. Inda ma ya kwantar da hankalin shi, da zatazo da kanta ta bashi labarin wahalar da tasha a ranar, da yanda Dinaar din bata barta ta dorar da komai na karatun ba saboda kukan data dinga canyarawa. Sai dai wasu a cikin Malaman nasu, masu mutuncin sukan bata damar rubuta attendance sannan suce ta fita daga ajin, wasu kuwa lamarin babu dadin ji.

“Allaah Ya sakawa iyayenmu da gidan aljanna.”

Take fadi tana karawa, duk lokacin da Dinaar zata isheta da kuka wannan addu’ar take tsintar bakinta da furtawa babu kakkautawa. Wata rana kuma saita dinga tunano dararen da zata fito fitsari, ko in tana rashin lafiya ta kwana dakin Abida, yanda zata farka ta ganta tanata jero sallolin Nafila, yanzun sai take tunanin ko dai tun kukan daren data dingayi ne tana hanata bacci yasa harta saba da tashin dare? Gata nan dai yanzun tama fi samu tayi abubuwa da yawa cikin daren fiye da yanda take samu tanayi da rana, tun tana ciwon kai da safe na rashin wadataccen bacci harya zame mata jiki yanzun. Yau dai dakyar ta samu tayi raka’a biyu, jikinta takeji a mace, sai dai ta koma ta kwanta, idanuwanta sun bushe, saita dauki waya, da kallo tayi nufin yi, haka kawai ta koma bude Twitter, tanata scrolling, sai taci karo da wani posting daya dauki hankalin mutane, dan ga comments nan sunfi dubu.

Kafin ma ta karanta, daga yawan comment din tasan ba zai wuce wani bane ya yaudari wata tazo ta kawo maganar twitter. Kara gyara kwanciya tayi dan ta tabbata zata sha dariya. Sai akasin hakan ya faru, ganin post din watace sukayi fada da wata, take mata gorin yawan aure-auren da tayi, to hankulan mutane ma yafi karkata ne ga aurenta na hudun da bai karasa shekara daya ba, da yake sunyi dinner, kuma ta watsa zafafan hotunan da akayi na dinner din, shisa mutane da yawa sun san da anyi auren, labarin karewar auren ne dai sai yanzun ya fito fili, kowa kuma yake ta samun damar tofa albarkacin bakin shi, wanda duka yanke hukunci ne da dorawa ita macen laifi. Sai kawai Sa’adatu ta dingajin wani abu na dukan zuciyarta. Duk kuma comment din da zata karanta da yake magana akan daman wasu matan haka suke, kila abinda taje nema a auren ne bata samu ba, wasu na kiran auren kwadayi ne daman, sai takejin kamar da ita wasu suke.

Zuciyarta har tsalle takeyi idan ta karanta wani comment din, saita fara hasaso idan nata labarin ne aka baje a titin twitter din kowa na tofa albarkacin bakinshi ya zataji? Me ma zasuce idan sukaji cewa aurenta na farko kwananshi daya, washegari da safe mijin ya damka mata takardarta a hannu, a cikin takardar kuma ya rubuta kalaman da suka datse duka igiyoyin auren, wani abu da ta zabi ta toshe kunnenta daga jin dalilan da suke ta yawo har a tsakanin ‘yan uwanta, har yau din nan kuma ko a tunaninta batason ma dora wani dalili akan rabuwarta da Tahir, sunyi aure, sun rabu, shine kawai, tunda ai ance shima auren kamar mutuwa yake, in lokaci yayi babu tsumi balle dabara, saiya kare, amman yau posting daya da taci karo dashi na neman ya sata tunanin da ta hanama kanta a yan shekarun.

To balle kuma a tsallako auren Jabir, ko da ita takai kanta, kuma tasan daman kararre ne tun lokacin daya fara, amman sai karewar tayi mata wani irin duka da bata tsammata ba, watakila bandashenta zasuyi.

“Wanda ma zai sake kwasarta shi nake tausayawa.”

Wani comment kenan da Sa’adatu ta karanta tanajin kalaman kamar an yarfa mata mari, har batasan lokacin da ta amsa da

“Kamar yanda za’a tausayawa duk wadda tsautsayi yasa ta fadawa shi wanda yayi sakin ko?”

Bata kuma tsaya nan ba, sai da ta dinga bin duk wani comment tana amsawa da bakar magana, kafin wani lokaci comment section din ya hargitse, har wani yaji-yajin bacin rai Sa’adatu takejin idanuwanta nayi, ta saman notification ta ga alamar anyi mata magana a dm dinta, taja wani dogon tsaki, haka kawai kuma sai wani abu ya dinga mintsininta akan taje ta duba Dm din taga ko wani ne ya bita can, dan daidai take jinta da kowa yau, kilan tsautsayi da rabon tayi masa zagin alakoro ne yasa shi binta Dm. Ko sunan bata tsaya dubawa ba ta bude sakon, sallama ce sai kuma aka dora da umarnin daya bata mamaki.

“Karki sake kula kowa a comment section din can.”

Ta karanta, ta sake karantawa, ko sallamar bata damu data amsa masa ba ta rubuta.

“Akan me?”

Tana dorawa da.

“Ina ma ruwanka.”

Zata fita taga alamar kamar yana rubutu saita tsaya

“Nima mamakin da nakeyi kenan, babu ruwana. Kawai dai karki kara kulawa.”

Ga mamakin Sa’adatu dariya ce take neman kwace mata

“Sannu da karfin hali to.”

Ta amsa, tana duba sunan shi, Officer AB, sai taji zuciyarta tayi wani irin duka daya mantar da ita karfin halin shi

“Yawwa. Danma ina tsoron ki watsomun nawa rabon da nace ki hada harda goge duka comments din da kikayi”

Sai dai zuciyarta da taci gaba da dokawa har jikinta na amsawa yasa da ta karanta abinda yace bata ma fahimta ba sosai, saboda babu abinda take gani ko tace yake dawo mata sai wannan video din da ta gani a shafin shi, yanzun ma fita tayi daga dm din tana shiga profile dinshi ta koma wajen media ta sakeyin kasa ta gano video din, kuma ko da zuciyarta zatayi mata karya, kwakwalwarta ba zata yaudareta ba, hannun Tahir ne tagani, dan ko wankin kwakwalwa akayi mata ba za’a wanke mata da wannan sanin da tayi masa ba, kafin ta tsaya wani dogon tunani ta koma Dm din tana kuma yi masa tambayar da sai bayan ta tura ta karanta sannan zuciyarta tayi wani shiru na jiran tsammani

“Kasan Tahir?”

Kalmomi biyu ne kacal

Amman tanajin tsayinsu har bayan zuciyarta

Shima kuma ga alama nan ta rubutu yakeyi, ya dauki mintunan da ko da bata kirga ba tasan sun kusan tasarma biyar, kafin ya dawo mata da amsar data kara tabbatar mata da abinda ta sani

“Sa’adatu? Sa’adan Tahir?”

Sai kawai taji kamar hawaye na son kwace mata

“Kasan Tahir”

Ta rubuta wannan karon babu alamar tambaya, saboda ta fadane cike da tabbatarwa

“Bash ne”

Shima ya amsa

“Bash din Tahir”

Wasu hawaye data kasa tarbewa suka zubo mata, a lokaci daya kuma sai da tayi murmushi, to ita dashi waye na Tahir din kenan? Ko da yake su dukansu babu yanda zasu bada labarin rayuwarsu batare da Tahir ya shigo ciki ba, duk da ita a yanzun ai shafukan labarin da yake ciki ya jima da karewa, idan aka zagaya aka kuma zagayo Bash din shine na Tahir

“Hmmm…”

Ta tsinci kanta da furtawa

“Kina ina?”

Wata tambaya da Bash din ya jefo mata

“Kano”

Ta amsa shi, haka kawai taji ta dora da

“Kano, ina BUK ina karantar Nursing, nayi aure ina da yarinya (Dinaar) amman yanzun banda aure.”

Kuma sai taji kamar babu wani dalili da zata fada masa haka.

“Dinaar…gold kenan ko? Sunan yayi mun dadi”

Hannu tasa tana share hawayenta.

“Kausar sunanta, haka muke kiranta.”

Ta rubuta tana gyara kwanciyarta ta kalli Dinaar data motsa kamar tasan maganarta akeyi, amman kuma bata bude ido ba, bacci takeyi sosai

“Duka sunayen sunyi mun dadi. Allaah Ya bani mace nima, yarana biyu, kuma duka maza ne.”

Ta jinjina kai

“Yaa Tahir fa?”

Ya dan dauki lokaci, kuma a shirun nashi sai taji tana fatan amsar shi tazo mata da cewa Tahir yana nan baiyi aure ba.

“Hayatee”

Ta karanta sunan, ma’anarshi na zagaya mata

“Macece, sunanku daya.”

Kafin kuma maganganun su gama zauna mata, saiga hotuna guda uku, na farkon ta bude, yarone kyakkyawa da kai tsaye ba zatace ga shekarun shi ba, hudu watakila, daga kasan hoton ya rubutu Tahir sai na biyun ma namiji ne Ahmad. Sai na ukun daya ya rubuta mata Hayatee, yarinyar ba fara bace ba, tana da duhu, amman kyakkyawa ce, batasan lokacin da murmushi ya subuce mata ba, saita shafa hoton, gashin da iya gabane akayiwa dabara akasa ma ribbon yafi komai bata dariya, ta sake komawa tana kallon yaran Bashir din kamar mai neman fuskarshi a cikin tasu, ta sake yo kasa tana ganin hancin Hayatee irin na Tahir ne, amman idanuwanta da bakinta watakila na Mamanta ne, hakama duhun da take dashi, dan Tahir farine kamar Asabe.

Bata samu rubuta komai ba, Bashir ya rigata

“Sai dai wannan Tahir din bashi da hakuri”

Dariyar da tayi mai sauti ce

“Kai ya biyo kenan?”

Ta tsinci kanta da amsawa

“Wacce karyar Tahir ya fada miki kika hau kika zauna?”

Ba a fili kawai tayi dariya ba, harshi ta turawa kawunan dariyar

“Ba fadamun yayi ba, gani nayi”

Dan ba zata manta yanda ya balbale wani abokinsu da fada ba bayan daurin aurenta da Tahir, sun shigo cikin gidan lokacin za’ayi hotuna, kuma data daga kai ta kalle shi sai tayi saurin sauke idanuwanta saboda yanda yanayin shi ya bata tsoro, kuma a duk ganin da tayi masa, ko da bakinshi baya motsi, to alamunshi na nuna ko dai wani ya gamayiwa fada, ko yana shirin yi, ko ranar farko data fara ganin shi, duk da ya danyi kokarin sakin fuskarshi, idanuwanshi a harzuke suke, sannan in suna waya da Tahir ai ba zatace ga adadin ranakun da taji muryar Bashir din a hasale ba

“Bash ne ko?”

Idan ta tambaya sai Tahir yayi dariya

“Kinsan zuciyarshi a tsakiyar kai take, baya raina abin fada”

Amman yanzun sai cewa yayi

“Sharri dai zakiyi mun, amman labarin hakuri na ai abin kwatance ne”

Abu daya zata iya fadi lokacin da Bash yace mata

“Baki da makaranta gobe ko? Ina da aiki nikam, idan na tsaya zanje ina gyangyadi a Office, bari in gudu kafin kisa oga yace a jefani a cell”

Data duba agogo, sai tayi mamakin lokaci, yau ta fahimci me ake nufi idan akace akwai mutanen da zakayi magana dasu a ranar farko yanayinsu yasa kaji kamar ka jima da saninsu, a duka hirar da suka dingayi da Bash ba zatace ga takaimaiman abinda suke hira akai ba, amman tayi dariya, tayi murmushi, ta sake darawa, ta jita cikin nishadin da ta manta rabon da tayi irin shi, sannan bayan itama tayi masa sallama, sai wani tunani ya dirar mata

Akwai wata kadaici da take ciki wanda mutanen da suke zagaye da ita suka kasa cike mata gurbin shi

Kadaicin da yau Bash ya rage mata wani kaso daga cikinshi

Da kuma ta rufe idonta sai taji tana fatan budesu dan ganin me gobe zatazo mata dashi…!

 

<< Tsakaninmu 58Tsakaninmu 60 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×