Skip to content
Part 60 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Ba zata manta ba, bayan da Tahir ya furta mata yana sonta, zuwan shi na farko bayan hakan, tunda sukayi waya ya fada mata a lokacin zai fito daga gida, wasu igiyoyi da bata taba sanin da zamansu ba suka dinga zarge junansu a kasan cikinta suna hana mata zama, har zufa tafukanta suka dingayi, to yau idan aka tattaro duka wannan yanayin na baya, sai a ninka shi sau goma, tunda ai zufar bata tsaya iya tafukan hannunta ba, har a duka jikinta tanajin yanda zufa ke tsatsafo mata

“Kinga yanda kike zufa?”

Cewar Fa’iza, sai Sa’adatu ta numfasa kawai, dan bata yarda da daidaiton muryarta ba, idan ma ta bude bakin me zatace? Menene Fa’izar bata sani ba? Aita fada mata komai, tun washegarin hirarsu ta farko da Bashir, da kuma yanda suka dauki watanni shidda cif, a cikin watannin wata irin shakuwa sukayi ta ban mamaki, irin shakuwar da duk wanda yake kusa da ita yaji wani kaso na labarin Bashir

“Haka Bash yace…”

Ko

“Bash ma…”

Wani lokacin kuma

“Wani labari Bash ya bani…”

Dan Sa’adatu tayi kawaye, a Islamiyya da boko, amman duka kawayen a hankali suka dinga bin sauyin rayuwa, zuwa yanzun kuma zatace kawarta ma guda daya ce anan BUK, sai kuma Nasir Kabir da ba karamin dadin kasancewarshi abokin karatunta takeji ba saboda yanda take karuwa dashi, duk wani abu da zai shige mata duhu zai warware mata shi cikin sauki. Ba zata kira Badr da kawa ba, sai dai tace Yayarta, to zuwa yanzun kuma tanajin kusanci da Bashir fiye da su duka, saboda tanajin kamar ta dade da sanin shi, kamar tun tasowarta akwai shi cikin rayuwarta

“Wai ko dai Bash din nan ne sabon catch din da mukayi?”

Badr tace mata, kuma maganar ta Badr tayi mata dukan da batayi zato ba, ita wai? Bash? Ita da Bash? Haka ta dinga girgiza kanta kamar Badr din na gabanta, tana dorawa da fadar

“He’s just…”

Sai kuma ta dakata, kafin tace

“A friend?”

Ta karasa cike da rashin yarda da kai, ba kuma dan tana ma Bashir din wani kallo na daban ba, sai dan bata da sunan da zata kira alakar da take tsakaninsu, zatace yana da muhimmanci a wajenta, irin muhimmancin da take rasa sukuninta duk idan ba suyi magana ba a rana, idan bata magana to tana maganarshi da wani, idan babu daya a ciki tana tunanin abinda yakeyi tana kuma cika da dokin suyi magana dan ya labarta mata wadannan abubuwan, a wasu ranakun kuma sai taji kamar tana cikin rayuwarshi ta wani fanni da ta kasa misaltawa. Kuma wani abu da in zata fada tasan zai ba kowa mamaki shine yanda tun daga ranar farkon nan idan har sunan Tahir ya gifta a tsakaninta da Bashir to danshi ne, ba Tahir abokinshi ba, sannan babu wata rana da zasuyi magana ba zata tambayeshi yara ba, duka yaran, harda Hayatee a ciki. Haka idan zai turo mata hotunan yaran ko short video to harda na Hayatee yake hadawa ya turo mata, haka idan labarinsu zai bata.

Baya taba rasa labari akan Hayatee kamar yanda bai rasa sababbin hotuna da videos dinta ba, kawai zatace Bashir abokin Tahir data sani ta sanadin Tahir daban, wannan Bashir din abokin Tahir data hadu dashi a manhajar twitter daban, mutum daya ne, amman alakar ta bambanta, yanda wancen ya mu’amalanceta daban da yanda wannan yakeyi. Watakila hakan ne yasa suke rayuwarsu batare da sun sakko Tahir a cikin hirarrakin nasu ba. A duka watannin shidda kuwa, sai jiyan da yace mata

“Gobe zan shigo Kano, so nayi inyi shiru sai dai in baki mamaki, sai kuma na kasa hakura”

Kafin zuciyarta dake tsallen murna ta dawo cikin natsuwarta ya kara da abinda ya canza salon tsallen zuciyar zuwa wani abu da har yanzun din nan a cikin shi take, wani abu da ya girmi ta dora shi akan kalamai.

“Ni da Tahir ne”

Hanjin cikinta ya kada

“Yana son ganinki Sa’adatu, it’s not my place to say this, amman ina rokar masa alfarma, karkice a’a, nasan ku duka kuna da wasu kalmomi daya kamata ace kun digawa aya, bakuyi hakan ba. Idan har kin amince zamuzo gobe bayan sallar isha’i In Shaa Allaah”

Saita jinjina kanta, tunawa da tayi baya ganinta yasa ta amsa da

“Ok”

Tana kuma kasa cewa komai, kamar hakan Bashir ya fahimta yayi mata sallama. Cikin dabara ta zame Dinaar da tayi bacci a jikinta ta mike tana samun Fa’iza ta fada mata, ita kanta saida ta jinjina al’amarin, cikin sanyin da jikinta yayi har da muryarta tace

“Allaah Ya kawosu Sa’adatu, ko ciki zaku shigo to?”

Kai Sa’adatu ta girgiza mata

“Bari mu zauna a soro, sai in saka mana darduma”

Kuma washegari Fa’iza da kokari, bayan dambun naman da ta sakata a gaba sukayi, suka samu robobi guda biyu matsakaita aka zuba a ciki, tunda sunsan ba lallai su iya ci anan ba, gara a basu su tafi dashi, zobo da kunun aya kuwa ko zasu zo ko ba zasuzo ba wannan dole ayi shi, nasu na musamman aka karawa kayan hadi, haka Fa’izar bayan ta kara kalkale ko’ina na soron gidan da daman a tsaftace yake, ta dauko kwandon sharar da yake bayan kyauren ta shiga dashi cikin gida, itace harda janyo kofar gidan ta kunna turaren wuta a ciki, ta kuma soka na tsinke a kusurwa har biyu. Ko yanzun da Sa’adatu take shirye tsaf, ta kuma saka hijabi ruwan kwai, fuskarta fayau duk yanda Fa’iza tayi fama da ita, ko hoda bata saka ba.

Wacce hoda zata shafa tana ta fama hada gumi? Ai ta tabbata sai fuskarta tayi jirwaye, sai kuma data duba wayarta ta tuna a tsayin watannin nan, ko na rana daya Bashir bai tana tambayar lambar wayarta ba, balle a tsallaka batun waya. Bata kai da tunanin yanda za’ayi ba idan sunzo yaro yayi sallama, kafin ita ko Fa’iza su amsa yace

“Ana kiran Sa’adatu, inji Bashir”

Wani abu ya ruguje a cikin kirjin Sa’adatu

“Kace su shigo soro gata nan”

Fa’iza ta amsa tana mikewa kamar babu goyon Dinaar a bayanta, da yake Abba da duhu ya fara in dai ba’a gama abinci da wuri ba sai anyi da gaske yake cin na dare, yama jima da yin bacci, itama yau Dinaar din mai hirar dare tunda ta rage kuka, baccin takeyi. Manyan darduma ne guda biyu, su kansu kamshi sukeyi mai sanyi, ta mikawa Sa’adatu data karba, sai taji sunyi mata nauyi fiye da kowanne lokaci, cikin jan kafa ta karasa soron gidan, ta shimfida darduma daya, tana shirin shimfida dayar daga gefe taji sallamarsu, a tare sukayi, amman hakan bai hanata jin muryar Tahir ba, muryar shi da lokaci bai tafiyar mata da ita ba kamar yanda tayi zato.

Akwai wuta, soron ko allura ka yadda zaka dauki abinka, ko da babu wuta kuma kwan irin mai cajin nan ne. Hannunta na rawa ta karasa shimfida dardumar, kuma batare da wani dogon tunani ba ta lalubi waje ta zauna kafin ta amsa sallamar muryarta na rawa, ta daga kai tana kallon su biyun. Tahir ta fara kallo da yake sanye da bakin yadi wuluk, kuma ko gugar da yasha ce shisa taga har wani kyalli kyalli yakeyi, da hula akan shi itama baka, idanuwansu suka sarke cikin na juna, wani abu da batayi tsammani ba ya tsirga mata, taji kamar tana son yin kuka

“Yaa Tahir”

Ta furta a hankali, kafin ya amsa Bashir yace

“Ina zuwa”

Sai lokacin kuma Sa’adatu ta raba idanuwanta daja Tahir, sai dai harya juya, bayanshi kawai tagani, sai kuma yadin jikinshi da yake fari, kuma shi kanshi babu hula. Kan dayar dardumar Tahir ya cire takalminshi ya zauna, ya kafa mata idanuwa kamar yana son idanuwan nashi su lalubo masa duk wnai abu da yake son sani, a gefe daya kuma su isar masa da sakon da yake dauke dasu

TAHIR

“Babban abokin ango zai bada tarihin ango”

Haka Mc ya fada a wajen taron kamun bikin shi, wani taro da har lokacin da yake zaune ya kasa gasgata cewa wai shi Tahir ne yake zaune a wajen taron bikin shi, kuma shine za’a daurawa aure nan da kwanaki biyu. Sakina, yar uwarshi ce, ta bangaren mahaifinshi, kuma zai iya cewa ta jima tana son shige masa, shine bai bata fuska ba. Idan yace bayajin sonta ma zaiyi karya, kawai komai ne yake zuwa masa da wani irin yanayi mai wahalar misaltuwa. Haka ya dinga kallon Bashir din daya fara da bada tarihin makarantun da yayi, zuwa halayen shi da wasu ma baisan yana dasu ba sai yanzun da yakeji a bakin Bashir din, harya gama kuma bai daina kallon shi ba. Iya abinda zaice kenan? Wannan kalmomin daya fada yana nufin su kenan a tarihin shi? Kamar fa ya bude littafi ne saiya zabo yan shafuka a ciki bayan tambayar da akayi masa kamar tana bukatar duka shafukan da yake cikin littafin ne.

Sai kuma yake jin ai idan shi aka ba filin ma bai san ta inda zai fara ba, shin zai fara daga tushe ne? Yanda mahaifiyarshi ta fita tabarsu a hannun matan uba? Yanda tun tasowarshi yasan cewa duk yanda mahaifinshi yayi tsaye wajen ganin rayuwarsu bata shiga halin tagayyara ba yanajin wannan rashin na uwa a tare dashi, sau nawa za’ayi masa abinda ya kamata yana shigowa gida ya nufeta ya labarta mata amman bai samu hakan ba? Ko kuma zai fara daga dai-dai inda ya mallaki hankalin shi ya dauki kafafuwanshi ya nemo Asabe? Da ya nemota din kuma sai yasan cewa tabbas yana daga cikin mutanen da Allaah Ya sake jarabta ta hanyar mahaifiya. Idan duk ya tsallake wannan zuwa haduwarshi da Sa’adatu, soyayyarsu, ai dole dai ya sake komawa kan Asabe.

Wanne kalamai zaiyi amfani dasu? Wa zai cewa mahafiyarshi ta kauce hanya saboda kawai ta rabashi da Sa’adatu akan dalilin da kwata-kwata bashi da tushe? Ko zaice yanaso a bashi dama guda daya a rayuwarshi, damar da zai zabi Asabe yabar Sa’adatu ko dan kar lahirar ita Asaben ta kasance cikin halin kila wa kalan da yanzun yake farkar dashi tsakiyar dare. Duk soyayyar da yake yiwa Sa’adatu bata kai ba, ba zata taba kaiwa rabin wadda yakeyiwa Asabe ba, uwa ai tafi karfin wasa. Lokacin Bashir Kaduna akayi posting dinshi. Daya tattara kayanshi kuma tare suka wuce Kadunan da Bashir, bayan yayi tsaye anyiwa Tahir din takardar asibiti na cewar bashi da lafiya aka bashi hutun sati daya. Satin daya kasance wani sati da ba zai taba manta ranakun cikinshi ba, abinci ma sai sun kai ruwa rana shi da Bashir tukunna yake tashi ya sha ruwan shayi.

Wuni yake mirgina akan katifar dakin Bashir din, hawaye kuwa sai dai ya dinga jin zubarsu cikin kunnuwanshi, sallah ma a dakin yake yinta

“Kasan matsayin wanda ya kashe kanshi a musulunci ai Tahir, kuma ka dauko hanyar kashe kanka idan har ba zaka daina wannan damuwar ba, haka kuma kasan babu abinda damuwar taka zata canza, Sa’adatu ba zata dawo maka ba, abinda ya faru ya riga ya faru”

Bashir ya fada kamar zai mareshi

“Haka kuma Mama ba zata dawo ba? Haka babu yanda zanyi da wasa da tayi da lahirarta”

Sai Bashir ya girgiza masa kai

“Nifa ban yadda da wannan tatsuniyar ba, kawai Allaah Yayi ba kuda rabon zama da Sa’adatu, wani Ya isa yayi maka abinda Allaah Bai kaddara ba?”

Wannan karin shi Tahir dinne ya jinjina nashi kan

“Dan Allaah kayi mun bayani to Bash, ka fadamun dalilin da zaisa ni da hannuna in saki Sa’adatu washegarin aurenmu bayan duk wahalar da na sha kafin in aureta”

Sai Bashir din yayi shiru, ya kuma san bashi da abinda zai fada masa, ranar daya kamata ya koma Kano saboda aikinshi tana cika kuwa ga mamakinsu daga shi har Bashir din saiya mike, ya shirya tsaf, ya kuma hada shayi da kanshi yasha. Haka duk wani mai sonshi ya dinga tayashi murnar ganin ya hakura, ya dangana, amman ai shi kadai yasan irin ciwon da yake ji a zuciyarshi, ya hakura da gaske, saboda babu yanda zaiyi, hakuri a wannan bigiren abune daya zame masa dole. Wata irin rama ya dingayi da yasa mahaifinshi zaunar dashi da kalamai masu taushi

“Kayi hakuri Tahir, rayuwar ma gabaki daya ai lokaci take jira ta kare balle kuma wani abu da yake cikinta”

Kuma wannan kalaman na daga cikin kalaman da sukayi tasiri a kanshi, harya fara dawo da walwalarshi, sune kuma sukayi masa jagora lokacin da Sakina ta dawo rayuwarshi da karfinta, tana matakin karshe a jami’a a lokacin, kuma kowa ya dinga nuna masa goyan baya, shisa bai tankwabeta ba, ya dinga mamakin gaggawar da aka dingayi a maganar auren, duka daga tasowar abin da auren, wata shida aka saka. Duk da ya saka musu sharadin da sukace sun amince, na ba zata tare ba har sai transfer dinshi ta fito, sai su tafi gabaki daya, suma iyayenta kuma suka rokar mata alfarmar ko da transfer din ta fito, yayi mata hakuri ta karasa rubutu jarabawarta ta karshe, ya kuma ce bashi da matsala da halan. A lokacin ya cigaba da  cuku-cukun yanda za’ayi a mayar dashi Lagos, haka kawai yakejin zaman Kano ya fice masa a rai.

Babu kuma yanda mahaifinshi da Bashir basuyi ba akan ya fara zama anan Kano din, Sakina ta tare, ya kafe. Ita kam ta bangarenta bata damu ba tunda Tahir din take so, kuma ta same shi. Haka suka tattara shi da Sakina suka koma Lagos, abubuwan da yake gujewa a zaman Kano suka bishi har Lagos din, tunda ko bayan darensu na farko da Sakina din, bacci na daukarshi sai fuskar Sa’adatu ta dingayi masa yawo, sai kuma safiyar da yayi mata sakin nan, sai ta Asabe ta maye masa gurbinta Sa’adatu, ya ganta daure cikin wasu irin sarkoki, babu wannan farin, tayi duhun da in da ba mahaifiyarshi bace ba zai taba ganeta ba, haka ya farka a firgice bayan yaji Asabe ta kira sunan Sa’adatu, har saida ya tashi Sakina, ganin yanda jikinshi yake rawa yasa ta rungumeshi

Kuma sai ya kasa tsaida hawayenshi, bata tambayeshi me yake faruwa ba, ta rikeshi harya samu natsuwa, ta rikeshi har yayi bacci a jikinta, ta cigaba da rike shi duk dararen da mugayen mafarkanshi suka hana masa samun baccin kirki, Sakina ta zame masa wata rumfa da baisan yana bukatarta ba saida ya sameta, kuma a hankali halayenta, yanda take kaffa-kaffa dashi suka siya mata tarin soyayya a wajenshi, suka kara daga darajarta a idonshi, harya tsinci kanshi wata rana da bata duka labarinshi, labarin da yasan ta tsinta a cikin dangi, amman ai kowa zai kara abinda yake so ne akai, kowa zaiyi masa kwaskwarima, shine kawai ya fada mata shi a yanda yake

“Ka roketa mana, ka roki Sa’adatu ta yafewa Mama, a yanda ka fadamun kana da wannan alfarmar a wajenta…”

Sakina ta fada masa

“Ba zan iya ba Sakina, banda karfin halin da zan kalli Sa’adatu inyi mata wannan maganar, da zan iya da nayi tun ranar da naje na ganta”

Yanda bai sake kawo maganar ba, haka itama Sakinan, kamar yanda kuma yasan ta toshe kunnuwanta daga duk wasu surutan mutane lokacin daya karbi ‘yarsu a asibiti bayan ta haihuwa, ya mika mata ita da fadin

“Sa’adatu, sunanta Sa’adatu”

Haka ta sake kauda kanta daga

“Hayatee”

Da ya fara kiran yarinyar harma tana tayashi, shisa baya kyashin duk idan yana zaune cikin abokan aiki ana hirar mata da halinsu ya bude nashi bakin ya yabi tashi matar da halayenta, duk da kamar kowa suna samun sabani, tunda duk halayenta macece ita da bata iya boye fushi ba, kuma idan ya bata mata sai dai su haura sama, daga baya wani a cikinsu ya fara saukowa, amman sai tayi magana, a zamantakewarsu zai iya cewa hakurin shi ya dara na Sakina, amman ai ita ta siyawa kanta wannan alfarmar a wajenshi da kyawawan halayenta. Shisa zaman yake musu dadi, sun fahimci juna. A wani zuwa da yayi Kano ne yakejin labarin Sa’adatu tayi aure, ga mamakinshi sai yayi murmushi

“Allaah Yasa wanda zai rikeki da amana ne, Allaah Yasa abokin rayuwarki ne daga nan har aljanna”

Ya fada a kasan numfashin shi, wata nutsuwa da baiyi zato ba ta shige shi, sai kuma yaji ya kara sakin jikinshi da Sakina, kamar akwai wani bangare da yake rikewa, wani bangare da rashin auren Sa’adatu yake rike dashi. Haka rayuwar ta cigaba da tafiyar masa da wani irin cigaba, abu dayane yakan datse masa duk wani farin ciki dayake ciki, wannan abin kuma shine hakkin Sa’adatu da yake kan Asabe, hakkin da yake son sauke mata amman ya rasa ta inda zai fara shi, kawai sai

rana daya suna waya da Bashir ya fada masa wasu kalmomi da yaji suna neman juya masa kai

“Munyi magana da Sa’adatu, Sa’adan ka”

 

<< Tsakaninmu 59Tsakaninmu 61 >>

1 thought on “Tsakaninmu 60”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×