Skip to content
Part 62 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

JABIR

Me zaice ya nema ya rasa? Duka rayuwarshi, tun tasowarshi ma, haihuwa ce abu na farko daya fara sanin ya nema ido rufe, kuma lokacin daya fara cire rai, sai Allaah Ya dubeshi ya azurta shi da samun har guda biyu. Yazo gabar daya kamata ace matsalolin shi basa wuce irin wanda kowanne mai iyali yake fuskanta, mai iyalin ma wanda yake da rufin asiri irin nashi, sabanin da ba’a rasawa a kowanne gidan aure, rashin lafiya da kudi basu isa su tare ba, sai yan kananun abubuwa, ya kamata ace yanajin shi complete, amman daga ranar da ya mikawa Sa’adatu takardar nan yakejin wani rami da ta tafi tabar masa. Ta shigo rayuwarshi da manufa daya ne, sai kuma ta zame masa wani bangare da bai taba sanin yana bukata ba.

Kamar ace tunda ya tashi iska kala daya yake shaka, tare da kowa kuwa, idan yace kowa harda Aisha a cikinsu, yanayin rayuwarsu iri dayane, bambancin da yake tsakaninshi da Aisha na halayyane kawai, kuma shima a cikinsu sunyi tarayya a abubuwa da dama, idan sukaji sun gaji da rayuwar waje daya, dan canjin da zasu nema shine su shirya wata tafiya zuwa wata kasar suyi wasu kwanaki su dawo, to shima yanzun wasu kasashen maimaici ne sukeyi, kullum cikin neman wani abu da zasu sabunta zamantakewarsu sukeyi. Ta bangarenshi sabuntar saita zo masa tare da Sa’adatu, tunda ta shigo rayuwarshi yaji hakan, amman lokacin dashi ya shiga rayuwarta, sai komai ya kara canza masa, dan abu kadan da zaiyi saiya burgeta.

Idan zasu fita da Aisha, a siyayyar kayan sakawa, ko wani abu da zasuci, kafin ya zaro katin shi da nufin biya ta mika nata, yasan tana kokarin yi masa godiya da nuna mata jin dadin shi duk idan yayi mata abu, sai dai yasan duk kudin da zai bata ba zasu burgeta yanda suke burge Sa’adatu ba, duk inda zai kaita wajene da zata iya zuwa da kudinta, wajene da watakila tasha zuwa tun kafin ma ta aure shi. Abubuwan da zaiyi ya burge Aisha basu da yawa, amman Sa’adatu yana kula da ita, ko turanci yayi burgeta yakeyi, ko fita sukayi cin abinci tana da tambayoyi sama da hamsin da takeyi masa akan abinda zasuci din. Haka bata rasa wata tambaya da zatayi masa in suna hira ko idan yana bata labari.

Sa’adatu a wajenshi kamar ace yayi shekara da shekaru ne cikin daki, yana shakar iska iri daya, saiya fito waje, yayi sa’a lokacin da akayi ruwa ne aka dauke, iska ta kada, kamshin kasa ya taso ya wuce cikin hancinshi a lokaci daya. Haka yake jinta.

“A breath of fresh air.”

Inji bature, Sa’adatu ce wannan sabuwar iskar a rayuwarshi, kuma baisan yanda ya saba da ita ba sai da tayi masa nisa, sai yakejin baya numfashi yanda ya kamata. A hankali yake ta sabawa da rashin nata, duk da wani lokacin saiya tashi yaji babu abinda yake so irin ya jita a jikinshi, ya zauna tare da ita, suyi hira kamar yanda suka saba, idan ya dauki wayarshi da nufin ya kirata saiya kasa, to idan ya kirata me zaice mata? Bayan ya kula baya-baya takeyi dashi, duk wata hira in ba ta Dinaar bace bata hadasu, da sun gaisa zatace masa ga Dinaar din nan, ko tana bacci ko tana dariya, ta dora da.

“Bari in tura maka video.”

Wata rana ma bata jira ya amsa sai dai yaji ta kashe wayar. Idan kuma ta tura masa da video din shikenan, koya ce wani abin ba lallai ta amsa shi ba, sai idan tazo sake tura masa wani video din saita hada ta amsa da wancen sakon, da wannan halin ko in kula din da take nuna masa yaga layin data shata a tsakaninsu, idan ita, a shekarunta zata iya tsayawa a tsallaken layin data gindaya musu, sai shine ba zaija girmanshi ya bata waje ba? Idan sako ma ya tura mata, zatayi masa godiya, yawanci ta text ne, shikenan. Dinaar kuwa data mika masa ita take komawarta cikin gida, Abdallah ne ya siya masa mutunci daya taba zuwa ya same shi zaune a cikin mota da Dinaar din yace masa ya shiga ciki, in yazo ganinta ya dinga shiga ciki, haka ya dinga murmushi, washegarin ranar ya shirya, sabon yadi ne ya dauka yasa, ya kuma hada harda hula.

Turaren daya feshe jikinshi dashi harda na Aisha ya kara, ko babu komai dole Sa’adatu ta zauna tare dasu idan a cikin gida ya shiga, kamar ranar da suka dawo Asibiti, ai yaga gidan, karami ne, dole dakin Sa’adatun za’ace ya shiga. Kuma ko daya kira Sa’adatu yace mata gashi nan, haka tace masa tana zuwa, ta fito da hijab a jikinta tace ya shigo, inda Allaah ya rufa masa asiri baiyi zakal din wucewa gaba ba, saura kiris dai data tsaya a cikin soron gidan shiya karasa ciki duk kuwa da yaga darduma a shimfide.

“Ga waje ka zauna, ina zuwa in dauko maka ita.”

Sa’adatu tace masa, kuma yanda jikinshi yayi sanyine yasa shi zama, gabaki daya duk wani doki da yazo dashi ya nema ya rasa, haka ta miko masa Dinaar, ta gaishe dashi sama-sama tana koma ciki, ya zauna da yarinyar da taketa bacci, kuma kamar da gayya, masu siyan zobo suka dinga zarya kamar ana tunkudosu, har wani yaro daya kwaso da gudu da wata roba daya huda tsakiyar murfin yana matsawa ya matsawa Jabir a fuska yana sakashi mikewa babu shiri har Dinaar na shirin kubcewa daga hannunshi, ya gyarata yana kwalawa Sa’adatu kira, ta fito a firgice jin yanayin kiran da yakeyi mata.

“Ungota ki bani ruwa da sabulu, wani abu yaron nan ya watsomun.”

Sai yaron da yayi tsuru-tsuru da ido ya soma kwaso ban hakuri.

“Wallahi ban ganshi bane ba, ruwa ne, me kyau ne, a rijiyar gidansu Halliru na dibo…kin gani?”

Ya karasa maganar yana nunawa Sa’adatu robar ruwan, kai ta jinjina masa.

“Na gani…”

Tana maida kallonta kan Jabir da yayi kamar yana jira ne yaji fuskarshi ta kama da wuta.

“Ruwane a ciki baban Na’im, bari in sallame shi ina zuwa.”

Ta shige ciki tana barin shi, dole ya fita da Dinaar din a hannunshi ya karasa wajen motarshi yana dauko robar ruwa ya wanke fuskarshi, ya koma ya kirata ya bata Dinaar yayi mata sallama ya tafi ranshi na tafasa. Da gaske Sa’adatu takeyi ta shata layi mai girman gaske a tsakaninsu, tun lokacin kuma ya kara kaffa-kaffa, yana kokarin ganin baiyi wani abu da zai zubar da girmashi a idonta ba, Dinaar tunda da car seat dinta, in yazo ganinta ta bashi ita sai ya sakata yaja motarshi, suyi yawonsu, koya tafi daya cikin shagunanshi da ita, har gidama yana zuwa da ita, kuma haka Aisha zata karbeta ta hada da Na’im taita fama. Haka ya cigaba da lallabawa, duk yanda kewarta zata dameshi saiya danne, koyaso tura mata wani sako da zai nuna mata haka saiya nemi wani abin da zai dauke masa hankali.

A kwanakin nan ne ma idan yaje gidansu saiya dinga musu hirar Dinaar, yana nuna musu hotunanta, har daukarta yayi ya kaima Hajiya Hasina ita, a tsayin rayuwarshi bai taba ganinta da goyo ba, sai gashi tace a goya mata Dinaar din, amman data tashi ta fara kuka, dakyar ta bari cikin kannenshi suka rakashi aka mayar da ita, da ca tayi sai dai aje da ita, daya tashi kuma saiya koma can gidan bai nufi gidanshi ba, ya dinga zama a falon Hajiya Hasina, bayan tambayar ko Dinaar din tayi shiru bata dora masa da komai ba, batayi masa maganar Sa’adatu ba, babu wanda yakeyi masa maganar Sa’adatu, wanda duk sukayi masa zancenta a baya yanzun kowa yaja bakinshi yayi shiru, haka kawai yake jin kamar da gayya sukayi masa haka, yanzun sun gane yanaso ayi masa maganarta, yanason wani abu da zai boye a bayanshi yayi abinda zuciyarshi take ta kissima masa, tunda shi a karan kanshi bashi da kwarin gwiwa.

Yanata lallabawa ne, jiya da asuba ya jima a masallaci yana rokon Allaah Ya sassauta masa yanda Sa’adatu ta manne masa a kwanakin, mafarkinta yayi, ya tashi a wahale, yaji dadi da Aisha tana hutun sallah, bai tasheta ba, ya wuce masallaci, kuma daya fitone ya tura mata sako, a maimakon ta amsa masa sakon ta text saita tura masa da video din Dinaar.

“Kefa, ke ya kike Sa’adatu? Bakya kewata ko?”

Ya tsinci kanshi da furtawa a hankali yana shafa wayar. Yau kuwa sai yayi ma kanshi alkawarin zaije ya duba Dinaar dan itama ya ganta, kuma ba zai bari tayi biris dashi ba, dole suyi hira ko kadance. Shi yaso yaje makaranta ya dauketa shisa ya kira Direbanta ya fada masa data kirashi tace tagama da makaranta ya kirashi ya fada masa. Haka kuwa akayi, sai dai lokacin kuma aka kawo musu wasu kaya da ake bukatar saka hannunshi, sai yace direban yaje ya dauketa, amman yana kaita gida ya kira. Ya gama da shagon ya fito direban ya kirashi yana fada masa wai Sa’adatu tace masa ya tafi kawai akwai wanda zai mayar da ita, bata gama ba.

Wani abu da baiyi tunani ba ya tsirga masa har tsakiyar kai, aikuwa direban ya fara balbalewa da fadan da tunda ya fara masa aiki bai taba sanin ya iyashi ba. Ya kashe wayar ya fara kiran Sa’adatu, amman ga mamakin shi bata daga ba, ya jera mata kira biyar, karshe yaji wayar a kashe, daya shiga mota hanyar makarantar ya dauka kafin yayi tunanin ai ko yaje ma ba lallai ya sameta ba, gara yaje gida ya jirata yaga wanne katon ne yake da karfin halin daukota a mota ya kawota gida. Kuma ko a yanda yakeji din ya dauka a cikin yan ajinsu ne, tunda yasan rawar kai irin ta matasa, shisa daya hangosu ta mudubin motar da yake zaune ya tsaya yaga fitowarta, sai yaga an bude mazaunin direba, wanda ya fito din kuma ba matashi bane ba, babbane da ya isa ya tsaya da Sa’adatu kuma ta biye masa.

Shisa baisan lokacin daya fito daga motarshi ba, balle da suka kara matsowa sai yaga babu wani abu da zai nunawa Bashir ta bangaren kyau ko cikar halitta, asalima shi da yake namiji yake kuma cike da zafin kishi yasan Bashir bashi da makusa, balle kuma mace, ko da yaso amsa sallamar da Bashir yayi masa ba zai iya ba, idan ya bude bakinshi tabbas kashedi zai yankawa Bashir din, hakan kuma ba karamin zubar masa da girma zaiyi ba, tunda ai shiya bada damar da har wani zai iya samun kwarin gwiwar dauko Sa’adatu ya dawo da ita gida. Kuma ko yanzun daya dauki hanyar gida abinda yake tunani kenan, inda bai bada wannan damar ba, ina Sa’adatu zata shige gida tabarshi a tsaye kamar sakarai? Duk dama ta samu, har ta bata masa rai irin haka.

Yanayin yanda ya shiga gida yasa Aisha bin bayanshi da sauri tana riko hannunshi, ya zame.

“Tasha please…”

Saboda bayajin yin magana, saita sake kamo hannun nashi tana sumbatar tafin, ta sumbaci bayan kafin ta saki ta fice daga dakin tana bashi space din daya nuna yana bukata. Kwanciya yayi kan gadon, ya lumshe idanuwanshi, sai yaga Sa’adatu da dariyar da ta kwashe da ita, kome ya fada mata? Watakila ma shiya zaga, abin yayi mata dadi tunda haushin shi takeji. Babu shiri ya tashi zaune, yaja numfashi ya sauke, saiya lalubo wayarshi daga aljihu, batare da tunanin komai ba ya danna mata kira, wannan karin ta shiga, dan ta dauka.

“Baban Na’im”

Ta fadi.

“Ni kika wulakanta Sa’adatu? Saboda wani? Ni ko?”

Ya furta kamar karamin yaro.

“Wulakanci? Yaushe? Ya za’ayi inyi maka wulakanci Baban Na’im? Dan Allaah kayi hakuri, wallahi bansan me nayi ba.”

Ta fadi, yana jin rikitar da take cikin muryarta, shisa yace,

“Hmmm…na gode.”

Yana kashe wayar, sai gashi ta biyo bayan kiran, wani dadi ya kurdo ta tsakiyar bacin ran da yake ciki, yana kallon wayar harta yanke, ta sake kira tukunna ya daga.

“Dan Allaah kayi hakuri.”

Ta furta muryarta na rawa.

“Hmmm.”

Ya sake fadi, ta nanata masa kalmar yayi hakuri harya bace kirga, kuma da duk kalma daya da zata fada din da yanda yake jin saukin bacin ran da yake ciki, sai dai daya hango dariyarta da murmushin Bashir sai wani abu mai duhun gaske ya taso yana neman lullube masa komai.

“Shikenan.”

Ya fadi a dakile yana sake kashe wayar kafin ya tambayeta waye Bashir, meye hadinta dashi, meye kuma dalilin daya sa zai daukota ya kawota gida. Da yake yana tsoron kar zuciyarshi ta rinjaye shi saiya tashi ya fita falo inda ya samu Aisha kwance akan doguwar kujera tana danna wayarta, Na’im kuma yana cikin abin zamanshi yanata juyashi, da alama ma baccine yake shirin daukarshi. Ya tsaya daga baya yana dara habarshi daga jikin majinginin kujerar, Aisha ta sauke wayar tana nazarin fuskarshi.

“Me zan samu? Inajin yunwa.”

Ya fadi, saboda tun abincin safe rabon daya saka wani abu a cikinshi.

“Fried rice nayi da kaza…ina da frozen samosas.”

Ya dan yatsina fuska.

“Dankali nake so, da kazar idan ban takuraki ba.”

Kai ta jinjina masa.

“Babu matsala, ka zauna da Na’im.”

Saiya zagayo yana fadin.

“Mu biki kitchen din to mu tayaki hira.”

Bata musa ba, tana fere dankali ne, batare data kalle shi ba tace.

“Are you ok?”

Numfashi Jabir yaja yana saukewa, a hankali ya girgizata mata kanshi alamar a’a.

“Abinda yake damuna abune da ba zan iya tattaunawa dake ba.”

Wani murmushi Aisha tayi mai dauke da ma’anoni kala-kala, duk daren da zata tashi tayi nafila saita roki Allaah Yasa ta rayu dashi ita kadai, to amman a kasan zuciyarta sai wani irin rauni ya dinga nukurkusarta, duk idan ta gama addu’ar sai taji kamar shakkun da zuciyarta take ciki zatayi ma addu’ar katanga wajen amsuwa, wani abu na rashin jin dadi saiya mamayeta, a maimakon ta samu salama a cikin ibadar data aikata, satin daya wuce saita gwada canza akalar addu’ar, idan akwai rabon ta raba Jabir da wata, Allaah Ya saukaka mata kishinta, Yasa karta sarayar da lahirarta a sanadin kishi, itama waccen din yasa karta cutar da ita, ranar farko da tayi addu’ar tsoro ne ya dinga tsirga mata, rana ta biyu haka taji tana son yin kuka, ta kuwa dinga rerashi a sujjadarta, amman tayi bacci bayan nan.

Saiya zamana duk da ciwon da takeji in tayi tunanin Jabir da wata macen, sai taga ya tsaya a hakan, a ciwon da babu yanda za’ayi ace an raba kowacce mace dashi, amman bata zafafa ba, shisa yanzun maganarshi batazo mata a bazata ba, harma tayi karfin halin cewa.

“Sa’adatu ce ko?”

Kuma shirun daya biyo bayan tambayar yasa ta juyo ta kalli Jabir da yayi saurin sauke kanshi kasa.

“Allaah Ya zaba mana abinda yafi zama alkhairi.”

Tayi addu’ar da dukkan zuciyarta.

Ko ba komai, ai akace fata nagari lamiri.

Kuma taji “amin” din da Jabir ya furta a kasan numfashin shi, to ita kuwa wanne labarin karfin hali irin na namiji za’a bata? Tunda aka halatta masa hudu, ai kuwa babu wani abu daya kamata mace tayi da wuce tsananta addu’a da neman sauki akan lamarin kishi, kuma saukin zata cigaba da nema, ai daman ta tabajin ana hirar a wajen aikinsu, ba zata manta ba, matar ma kabila ce.

“Duk namijin daya dandani zama da mata biyu fa, zaiyi wahalar gaske ya dawo ya zauna da daya, ko dayar ta fita to zai hango wata ya karo.”

Ita kuwa a yanzun daya hango wata, gara ya dawo da Sa’adatu, ko babu komai ta fuskoki da yawa babu wani abu da Sa’adatun zata nuna mata daya wuce kuruciya, kuma batayi mata kama da wadda zata cutar da ita ba, ta sauke numfashi. Tana jin yanda idanuwan Jabir suke bin duk wani motsinta, shisa taqi yadda ta sake juyawa balle kuma su hada ido taga abinda bata shirya masa ba.

 

<< Tsakaninmu 61Tsakaninmu 63 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×