Skip to content
Part 63 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

“Me ya rabaki da Baban Dinaar?”

Layi dayane rubutun, kuma sau daya ta karanta, ba zatace ga abinda takeji ba, tunda ai bashi bane ya farayi mata tambayar, ba dai tayi tunanin abinda zai fada ba kenan bayan yace mata

“Zanyi miki shisshigi Sa’adatu, zan tambayeki, amman idan ba zaki iya fadamun ba, ba zanji haushi ba, zamuyi kamar ban taba tambaya ba”

Ko da tunaninta yayi yawo, bai kaita wannan bigiren ba, batayi tunanin abinda zai tambayeta kenan ba, kuma me ta dinga cewa da aka sha tsareta da wannan tambayar?

“Babu komai, banyi masa komai ba”

Sai me kuma ta dinga fada? Ko sune suke fada tana jinsu

“Daman dan matarshi bata haihuwa ne, kuma yanzun ta samu ciki”

Akwai gaskiya a maganar, tayi shirune saboda sunyiwa gaskiyar kwaskwarima tayi mata dai-dai. Tunda ai tasan ko giyar wake tasha ba zata bude bakinta ta fada cewa daman auren kararre ne tun lokacin daya fara, ko Aisha ta samu ciki, ko bata samu ba, ita tana zaune ne cikin jiran lokaci. Kuma babu wanda yayi mata dole, itace ta zaba da kanta, ita ta kai kanta

“Kaddara”

Ta zabi ta rubuta, bai kuma dauki lokaci ba ya dawo mata da amsa

“Kaddarori da yawa suna zuwa da dalili Sa’adatu, nasan kaddara ce, dalilin da ban sani ba shisa na tambaya”

Taja numfashi, ta sauke, zuciyarta na wani irin tsalle, kamar maison yi mata wani gargadi data kasa fahimta

“Na aure shine saboda matarshi bata haihuwa, kuma zaman namu baiyi nisa ba ta samu ciki…sanda ya rabu dani baisan ina da ciki ba nima, sai daga baya”

Lokacin da Bashir ya dauka bata ga ko alamar cewa rubutu yakeyi ba yasa taji jikinta ya dauki dumi, ba kuma dumi irin na zazzabi ba

“Bani number dinki”

Batare da bata lokaci ba ta rubuta masa lambar, kuma cikin kasa da mintina biyu saiga kira ya shigo wayarta

Wani kira daya zame mata alkhairin da bata taba hangowa ba

Hannunta har bari yakeyi lokacin da ta daga wayar ta kara a kunnenta, bayan sallamar da yayi ta amsa, muryarshi ta sake dukan kunnenta da wata tambayar, tambaya ta biyu a yau, kamar ya shiryane tsaf dan ya birkita mata lissafi

“Kina son shi? Baban Dinaar? Kina son shi Sa’adatu?”

Babu wani daya tabayi mata wannan tambayar, ita da kanta batajin ta taba zama tayiwa kanta wannan tambayar, ko da ace tayita kuwa a cikin wani nisantaccen tunani ne da bata bawa muhimmanci ba. Haka shirunta na nazari ne, na rashin abinda ya kamata ta fadane, tambayar take sake nanatawa, yau, kuma a karo na farko ta bankado duk wata soyayya da ta taba yiwa Tahir, tana kokarin hadata da abinda takeji akan Jabir. Saita ga abu daban-daban ne, kamar so dai sunanshi so, amman yana zuwa da mabanbantan nau’i. Dan abinda takeji akan Jabir yayi hannun riga da wanda ta tabaji akan Tahir. Ba zuciyarta kadai takejin Jabir ba, gangar jikinta kanta mararin shi takeyi.

“Ina son shi”

Ta amsa cikin kalmomi uku, babu wani hesitation a muryarta ko kadan, ta amsane cike da yadda da abinda takeji din

“Mutumin kirki ne? Kin tabbata in kika koma masa zai rikeki da kyau? Ba zakiyi dana sani ba?”

Wannan karin bata dauki lokaci ba ta amsa

“Mutumin kirki ne, wani irin kirki da ban taba sanin mutane masu matsayi irin nashi suna dashi ba, ko suna iya nunawa mutane irina, har yanzun yana kulawa dani duk da ni din ba dolen shi bace ba, kuma ko zamanmu na baya banyi dana sanin shi ba, bana jin zanyi na gaba idan na sake samun dama”

Bashir ne yayi shiru daga nashi bangaren, shirun da saida ta ciro wayar daga kunnenta ta duba taga kiran bai katse ba, ta sake mayarwa tukunna yace mata

“Bikin waye kike cemun za’ayi? Kince ‘yar uwarshi ce”

Murmushi tayi sosai

“Anty Badr”

Wani biki da take ta dokin zuwan shi da yake ba’a jashi da nisa ba, a daya daga cikin kwangilar da Badr din take samu nayin abincin manyan taro, wannan da yake bataso a samu matsala, harda ita akaje kai komai, ashe kaddarar haduwa da miji ce ta kaita, ba yaro bane ba, dan zaiyi arba’in da biyar, kuma itace matarshi ta uku, duk da ta biyu za’a kirata tunda dayar ta rasu, haka yana da yara bakwai, biyar na uwargidan shi, biyu na dayar da ta rasu, dan siyasa ne da ake damawa dashi, a gefe daya ga kasuwancin da yake tabawa, daka ganshi kasan kudi sun zauna masa har suna zabtare wani kaso mai girma na shekarun shi. Kuma da haduwar tasu da maganar auren ba’a dauki lokaci ba.

Haka wata uku kacal aka saka, sai Sa’adatu ta dinga ji kamar tafi kowa doki da murnar bikin, saboda har cikin zuciyarta take son Badr, take kallonta kamar wata ‘yar uwarta. Haka muhimmancin da Badr take bata, ‘yan uwanta ma saita hada ta janyosu cikin wannan mutuntawar da takeyiwa Sa’adatu. Nata ankon ma Badr dince ta siya, ta kuma zo har kofar gida ta dauketa sukaje shago aka aunata, ita ai ko iya Badr aka tsaya babu yanda za’ayi ta manta da Jabir tunda shine sanadin hadasu.

“Ki turomun katin events din ingani, kikuma tambayeta idan babu damuwa in zama +1 dinki”

Kawai sai Sa’adatu ta tsinci kanta da fadin

“Babu matsala ma In Shaa Allaah”

Tunda tasan idan ma mutum 100 zataje bikin dashi tana da wannan alfarmar a wajen Badr balle kuma mutum daya. Itama kuma sai taji tana son tambayar shi

“Matarka fa? Muna hira da kai da daddare sosai”

Dariya yayi

“Sai yanzun kika tuna da ita, kina tsoron ta kamani ta hadamu biyun ko?”

Ita ma dariyar tayi, a nutse Bashir yace

“Matata tasan ina magana dake, tasan duk wani wanda nake magana dashi mace ko namiji, kuma a halin yanzun bata kasar, taje yin wani karamin course daya danganci bangaren aikinta, amman ta kusan dawowa saura wata 7 In Shaa Allaah, akwai bambancin lokaci a kasar da take da nan, shisa nake magana dake harda daddare”

Kai ta jinjina cike da gamsuwa, daman ai Bashir din baiyi mata kalar mazan da zasu jingine matarsu ta gida ba su tafi gantalin hira da wasu matan har tsakiyar dare, sun dan kara taba hira kafin sukayi sallama bayan ya tuna mata ta tura masa katin bikin Badr. Tana ajiye wayar kuwa ta tura masa, da yake bikine na wayayyu, ga kuma kudi daga bangaren angon, haka itama Badr din tana da nata rufin asirin, tun daga ranar larabar satin bikin za’a fara shagali, bridal shower ne farko, sai kamu ranar alhamis, ranar Juma’a za’ayi mother’s eve, ranar asabar daurin aure da dinner. Haka suka shirya zasuje dinner din ranar asabar, karfe 8 za’a fara.

Babu abinda Sa’adatu takeyi a duka satin irin doki da shirin yanda bikin zai kasance, gate pass guda biyar Sa’adatu ta karba na kowanne event shima dan Badr din tace saita daukane da yawan nan. Amman ita wa zata ba? Daman sunyi niyya dai wajen Kamun zasuje ita da Fa’iza da Nabila dan suyi mata kara. Kunshi taje akayi mata na jan lalle a kafafuwa da hannu irin na zanen nan tun ranar talata, tunda wani irin hadi akeyiwa lallen sai yayi wata biyu bai fita ba, daman kudi ta ware sosai, Badr din tayiwa magana aka hadata da maiyin kwalliya. Itace harda su gyaran gashi aka yarfa mata kitso kamar itace amaryar. Fa’iza ce mai tayata sukayiwa kayan da zatayi amfani dasu turaren kabbasa, da turarukan Saffad sukayi amfani 07010137848 tunda Fa’iza ta zama babbar customer din Ummu Abdul, har tana maganar ma zatayi mata magana taji in bata da distributor a Kano.

Sai gashi ita kanta da ta zauna kusa da kayan sanda ake turarasu wani irin kamshi mai kwantar da hankali takeyi, irin kamshin nan da sai anzo gab da ita za’aji shi, ba kuma karamin kyau tayi ba ranar bridal shower din, doguwar rigace ta wani material ruwan kwai, make up din da akayi mata baiyi hayaniya ba, haka daurin ya zauna sosai a kanta, sai Dinar da ta sakawa fararen kaya, da yake keyar a sude take babu gashi sai tayi mata amfani da turban, ba karamin kyau ta karaba data sakata a baby bag daga gaba. Da yake a gida tabarta taje wajen make up din, direba ta kira ya kaita, ya sake dawowa da ita, yanzun kuma zai sauketa inda ake bridal shower din

“Kai Ma Shaa Allaah Sa’adatu, baki ga yanda kikayi kyau ba”

Itama ta ga kyan da tayi, a bakin kofa suka hadu da Abdallah

“A kula sosai Sa’adatu, banda rawar kai kinji ko?”

Murmushi tayi tana daga masa kai, yana ta mata addu’ar dawowa lafiya da jaddada mata kar tayi dare, idan kuma Badr ta tsayar da ita taga tayi dare ta kirashi sai yaje su dawo tare

“Direba zaije ya daukoni ya dawo dani Yaa Abdallah, ba zanyi daren bama In Shaa Allaah”

Sai gashi dai har bakin mota ya rakata, tana kuma ganinshi yayi tsaye saida suka bace masa tukunna ya koma gida. Kuma bama ita bace batayi daren ba, karfe hudu aka fara, anayin magriba aka tashi, daga ita, babbar kawar Badr din da tazo daga Abuja sai wasu cikin yan uwanta aka bari, duka suka koma gidansu Badr din tare, sukayi sallar magriba, taso tafiya a lokacin Badr ta hana, da yake itama hirar tayi dadi, duk da sun girmeta basu nuna mata ba ko a fuska, sosai suke janta da hira zaka rantse daman can sun santa ne. Da akayi isha’i  kuwa zata tafi saida tayi mamakin tarin ledojin da Badr ta hadata dasu, da wayarta tayi ringing kuwa mikewa tayi tunda a zatonta direban ne ya iso, wata kanwar Badr din Asma’u ta tayata daukar ledojin tayi musu sallama, mamakinta ya karu da taga Jabir ya fito daga cikin motarshi yana takowa inda suke.

Kananun kayane a jikinshi, wani wando ne da kai yasa Sa’adatu bitar duk wata kala data sani amman ta kasa samun wadda zatayi dai-dai data wandon, sai riga mai gajeran hannu, plain ce baka. Duk da Jabir ba haske ya cika ba sai taga rigar ta kara masa haske sosai ta kuma amshe shi, kamshin da yakeyi na ‘yan gayu ya daki hancinta, ta kara godewa Allaah da itama in dai ya matso kamshin ‘yan gayun takeyi da turarukan Saffad emporium. Ledojin da suke hannunta ya karba hadi da amsa gaisuwar da Asma’u takeyi masa, ya bude mota ya saka, ya karbi na Asma’u kafin tayi musu sallama tana shigewa cikin gidan tabar Sa’adatu a tsaye tana kallon Jabir daya rufe bayan motan, maimakon ya zagaya bangaren direba ya zauna saiya sake dawowa inda take.

Sosai ya matsa har saida zuciyarta ta buga a cikin kirjinta, hannu yasa ya shafi kan Dinaar da take bacci kafin ya dan rage tsayi yana sumbatar kan nata, wani abu daya ke neman daukar Sa’adatu ya watsata wasu darare da labban Jabir din akan nata goshin sukan sauka, rufe idanuwanta tayi ta budesu a hankali wani yanayi na tsirga mata, kuma kamar yasan abinda take tunani saiya kalleta yayi murmushi

“Kinyi kyau”

Ya furta yana dorawa da

“Sosai”

Bayan ta wanke kwalliyar, daurin ma irin ture kaga tsiyar nan ne tayi bayan ta idar da sallar isha’i, sai mayafinta data rataya a kafada

“Nagode”

Ta amsa muryarta can kasan makoshi, kuma dan kawai ya kara kashe mata jiki saiya bude mata murfin motar yayi tsaye rike dashi, haka ta taka ta shiga ya mayar ya rufe, tukunna ya zagaya ya shiga nashi bangaren yana kunna motar yayi corner suka kama hanya. Lokaci zuwa lokaci yakan dan saci kallonta, kyau tayi masa sosai, musamman janbakinta daya fara dishewa kamar wadda ta saka wani abin ta goge shi, kamar kuma ranakun da shine yake zama sanadin da jambakin duk da zata sa yake komawa haka. Daya kalli hannunta data tallafe Dinaar dashi da jan lallen daya turu sosai sai yaji yana son ya rike shi, ya murza kamar yanda ya saba, yaji zufar da tafukanta sukeyi duk idan yana rike dasu, kaman hakan nason nuna masa tasirin da yake dashi a wajenta, ya bude bakinshi ya rufe sau ba adadi, so yake ya fadi wani abu da hira zata balle a tsakaninsu amman ya rasa abinda zaice

Yawanci idan suna tare duk itace tafi jan akalar hirar tasu, amman yau kamar wadda takeyi masa rowar muryarta sai tayi shiru tana kallon titi, masu kayan marmari ya hango

“Mu tsaya mu siyi fruits?”

Data kalli wajen mai fruits din sai taji babu wani abu daya burgeta, ko jiya haka Abdallah yazo musu da lemon zaki, kankana da ayaba mai yawa. Ko yanzun suna da ragowa a cikin fridge.

“Sai dai in kai, amman muna da a gida”

Ya jinjina mata kai

“Bakya bukatar wani abu?”

Ita ledojin da suke jibge a bayan motarshi ma tasan fiye da rabinsu a fridge zasu kwana, kuma zai wahala akwai wani abu na kwadayi da zatayi tunani a yanzun da ba zata samu a ciki ba, shisa ta girgiza masa kai

“Yanzun dai kam babu komai”

Haka kawai sai takejin wani rauni na shigarta, wai itace yau akeyiwa tayin siyawa wani abu amman tayi tunanin duk wani abu na kwadayi amman taji bata bukata, kenan ta kawo matakin da tafi karfin abubuwa da yawa? Daman rayuwa zata kawota irin yau? Kuma da tazo yau din sai ya zamana inta juya babu Abba, babu Ammanta da zata raba wannan rayuwar jin dadin tare dasu

“Yaa Abdallah ga wasu kudi fa sun taru ko akwai inda za’a jefa su”

Tace masa satin daya wuce, ga kudin cinikinta, ga wanda Jabir yake yawan turo mata, ga kuma wancen miliyoyin da taketa juyawa ta rasa ta inda zatayi masa maganarsu

“Sai dai ki ware wani abin ayiwa su Amma sadaka”

Hakan kuwa tayi, ya kuma zaburar da ita da irin projects din Angry Ustaz da take gani a twitter, dan haka a lokacin taje shafin nashi tunda tana following dinshi sukayi maganar ko nawa ne zai isa a gina rijiyoyi irin wanda taga sunayi tanaso ta ginawa su Abida. Ya tura mata, nan take tayi masa transfer, baccin da tayi ranar na daban ne, har wata iska ta dingaji tana shigarta, shisa yanzun ma bataji wani abu na rashin jin dadi ba sai ma

“Alhamdulillah”

Data furta a kasan numfashinta tana cigaba da maimaitawa a hankali, saboda tasan babu wani abu da ya kai musulunci dadi, saboda ya bata damar da zata raba duk wani abu najin dadi da zai sameta tare dasu Abida ta hanyar adduo’inta da kuma yin sadaka da niyyar ladan ya kai musu

“Nagode”

Tace tana kallon Jabir, saboda ai ko babu komai duk wani abu da takeji dashi yanzun sanadin shine ta samu, haka wanda zata samu a gaba ma idan ta waiga dole wani kaso daga ciki na jingine da Jabir din, da yake ya dan tsayane inda ake bada hannu, saiya kalleta sosai, yana so ya tambayeta godiyar me takeyi masa, amman yanayin da yake cikin idanuwanta da fuskarta yasa shi amsawa da

“You are welcome Ammin Dinaar”

Murmushi tayi mai sauti batare da tace komai ba. Haka suka karasa gidan kowa da abinda yake tunani, saida ta fara kai Dinaar tukunna ta dawo ta dauki ledojinta tana shiga dasu gida, biyun da suka rage data dauka tayi masa saida safe, ya amsa hadi da dorawa da

“Ki kula mun daku”

Ta jinjina kai ta shige gida, shikuma yaja motar s

hi yana ficewa daga layin

Yau

Su duka sunajin akwai kalaman da suketa shawagi an iska a tsakaninsu suna neman agaji, amman duk suka zabi su kauda kai…

<< Tsakaninmu 62Tsakaninmu 64 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×