BASHIR
Zaune yake cikin mota, bama zaice ga abinda yake tunani ba, kafin aikin shi, inda za’aje masa zai iya zama haka yana jira batare da jiran ya gundure shi ba zai karyata, shi din da babu wani abu da yake ci masa rai irin jira, amman yanzun gashi ya zame masa jiki. Akwai wadatar hasken fitilu a wajen, da yake ya daga gilasan motan saboda AC dinshi a kunne take, sai wani yanayi yake ta dukan shi, cikin yanayin kuma yasan harda kewar matarshi, in ya rufe idanuwanshi wani lokacin sai yaji kamar hancin shi na zuko masa kamshin humrarta, in zaisa nama sau goma a bakinshi sai harshen shi yayi kewar dandanon girkinta.
Baisan ko sabo bane, shekaru tara ai ba wasa bane ba, tun bashi da komai take tare dashi, tun bashi da abinda zai bata, da yake ita suna da rufin asiri gidansu, sau nawa da yake makaranta zaiga ta saka masa kati, in kuwa zai koma, cincin, dambun nama saitayi masa kamar ibada. Idan yana Kano, sai yaga dama zaici abincin gidansu saboda bata gajiya dayi masa hidima, shisa tana cikin sahu na biyu bayan iyayen shi a lissafin shi na kyautata mata lokacin daya fara samu. Ya kuma yi kokarin ganin ya aureta dan ya tabbata ba karamar asara zaiyi ba idan ya rasata a matsayin mata.
Haka aka dinga ganin kamar ita dashi basu dace ba, kamar zamansu ba zaiyi nisan da ake fata ba saboda shi yana da zafi, itama kuma haka, suna fada bana wasa ba, sai dai da yake akwai girmamawa a tsakaninsu, ita tana kokarin tausasa nata kalaman, kuma su duka basu da girman kai in zukatansu sukayi sanyi, wanda duk yake da laifi baya sanya wajen karbar laifin harya bada hakuri ma. Bashir ya taso gidan yawa, yaga badakalar da ake sha a tsakanin matan baban shi, harda mahaifiyar shi ma, da girmansu amman in abin ya motsa ana taba kishi, ga kuma rashin hadin kai saboda suna fama da al’adar ‘yan ubanci. Shisa har kasan zuciyarshi mata biyu basu taba burgeshi ba. Har addu’a yakeyi inma an rubuta masa auren mata biyu to Allaah Ya canza masa abarshi da guda daya har karshen numfashin shi.
Shisa tunda yayi aure, ba zaice wasu mata basa masa kyau ba, ko kuma su burgeshi, ai akwai wanda suka fi matarshi kyau, kuma ba zai iya hana idanuwan shi ganinsu ba, sannan zuciyarshi da aka halittawa wajen mata hudu ma bai isa ya hanata motsawa lokaci zuwa lokaci ba, amman fa ko kusa basu taba burgeshi ya karasu ko a ‘yan matan rage lokaci ba balle kuma yaji marmarin aurensu. Kawai sai lokaci daya ya fara kula da comment din Sa’adatu a TL dinshi, kusan kullum in zaije shiga twitter sai yaga wani abu da yazo dai-dai da ra’ayin shi, inya duba sai yaga itace tayi engaging da wannan post din. Daya fara magana da ita zai iya cewa komai yazo masane kamar daman tunda can ya santa, ya saba da ita.
Mutum ne shi mai wahalar sabo, irin sosai, saboda yana da saurin fushi, shisa bai cika sakewa da mutane ba, bayan Tahir, sai tsirarun abokan da yayi sanadin aiki yanzun da kuma wasu lokacin makaranta, duk sauran mutanen sanadin Tahir ya sansu, shine kowa nashi, shine mai fara’a da saukin kai, kuma shine zakayi shekaru bakaga bacin ranshi ba. Ko da yaga yanda ya sake da Sa’adatu, ya dauki hakan a matsayin haduwar jini ne, da cewar da akeyi akwai irin wannan abin daman, akwai mutanen da zasu shigo rayuwarka tun daga maganar farko zaku sake da juna kamar dama can kun saba, bai hango zuciyarshi zata motsa mata ba. Sa’adatu ce fa, tsohuwar matar Tahir, abokinshi, amininshi, dan uwanshi. To ko mutuwa Tahir yayi anya zai iya auren matar kuwa? Balle Sa’adatu da shi shaidane akan irin soyayyar da Tahir yayi mata, soyayyar da har yau akwai birbishinta, da kuma yanda kaddara ta gifta musu.
To shikuwa wanne irin tsautsayi ne zai kaishi? Shi da kafin Tahir yayi aure yafi kowa kokarin ganin mai sunan Sa’adatu ma Tahir baiji ba balle hakan ya fama masa da ciwon da yake yawo dashi. Har kokari yakeyi in suna chatting da Sa’adatu ya takaita murmushin fuskar shi, yaji bata burgeshi ba, bata kuma sa a karon farko yaji yana son rayuwa da wata mace bayan matarshi ba. Ranar daya rako Tahir kuwa, akwai wani rauni a yanayin da ta kalli Tahir dashi da yasa shi ya kusan karasawa gabanta ya kareta daga ganin Tahir din ya kuma zame mata karfin da yaga tana bukata a lokacin, shisa bai tsaya sun gaisa ba ya koma motarshi. Kuma baisan ko zuciyarshi da take cike da fata iri-iri akan Sa’adatu bane yasa yake ganin kamar akwai birbishin abinda yakeji game da ita akan shi.
Idan tayi dariya, idan tayi murmushi, murmushin nan da kunya ke haskawa cikin idanuwanta, akwai wani abu tare da Sa’adatu da bai taba gani a tare da kowacce mace ba, kuma bawai da gangan takeyi ba, halittarta ce a haka, duk wani motsi da zatayi cike yake da alamar da take nuna ita din macece, musamman raunin da bata gajiya da nunawa, raunin da cikakkun maza irinshi zasuji suna son yin duk wani kokarinsu wajen ganin sun zame mata bangon da zata dafa. Sai gashi ya daga hannuwa bayan sallar Wutr din daya idar yana rokon Allaah Ya fitar dashi kunyar Tahir Yasa karya kasance cikin jerin mutanen da ba zasu bar halal domin kunya da zaman tare ba.
Kuma a washegarin alamar daya fara gani na Allaah Ya amsa addu’ar nan shine tarin soyayyar Jabir da Sa’adatu take kokarin yakicewa, haka tsananin kishinta da Jabir din ya kasa boyewa sai daya bashi dariya, daya kalli Dinaar, ya tuna da irin rayuwar kadaici da rashin mahaifiya da Tahir ya dinga fama dashi lokacin kuruciya duk kuwa jajircewar mahaifinsu akansu, sai tausayin yarinyar ya kamashi, in har da wannan soyayyar da yake gani me yasa ba zasu sake ba auren nasu dama ta biyu ba? Wani lokacin sai an rabu, an bawa juna iska ake sanin muhimmancin juna, dole Sa’adatu zatayi wani auren, kuma Jabir baiyi masa kama da wanda zai bar ‘yarshi agolanci a wani gidan ba.
Sai yaji wannan kariyar dayake son ba Sa’adatu ta canza salo, yaji yana son bayan tayata da addu’ar daidaituwar komai tsakaninta da Jabir in akwai alkhairi a zamansu, yayi duk wani kokarin da zai iya wajen nunawa Jabir abinda zai rasa idan yayi wasa.Don alamu sun nuna masa Jabir din irin mutanen nan ne da suka saba samun komai da suke so cikin sauki, shisa duk tarin kishin Sa’adatu da yagani a tare dashi ya kasa yin wani kwakkwaran motsi akan mayar da ita rayuwarshi, kamar mai jiran ita ta fara yin wannan yunkurin, shikuwa in dai yana nan ba zai barta ba, zai tayata wajen ganin ta daga daraja da kimarta a idanuwan Jabir yanda sai ya kawo kanshi, sai taja shi a kasa kafin ta koma.
Kuma kamar tasan tunanin da yakeyi a dai-dai lokacin ta fito daga studio din da aka gama mata kwalliya, shirye tsaf cikin kayan da basu matse ba, asalima irin rigunan nan ne da ake yayi yanzun. Bashir dai yasan ba atamfa bace a jikinta, ba kuma lace bane ba, wani kalar abune da baisan sunan shi ba. Abu daya ya sani, ya karbeta, yayi mata kyau, daurin da akayi matane kawai abinda zai bambantata da amarya. Da yake ya samu yakice duk wani tunani akanta sai ta tsaya ayi masa kyau kawai
“Kasha jira ko? Matar nan bata cikamun alkawari ba, na samu tanayiwa wata kwalliyar ne, da yake babbar macece sai na hakura aka gama mata tukunna, kayi hakuri dan Allaah”
Ta karasa maganar tana zama hadi da jan murfi motar ta rufe”
Kai ya girgiza
“Lost in my own thoughts, banga dadewar ba”
Yayi maganar yana jan motar ya hau titi, akwai ‘yar tafiya tsakanin wajen da akayi mata kwalliyar da kuma event centre din, lokacin da suka isa dakyar Bashir ya samu wajen da ya ajiye motarshi saboda yawan motocin da suke harabar wajen. Haka suka taka suna ‘yar hira shi da Sa’adatu, data ciro gate pass dinma sai ta mika masa ya nuna suka shiga wajen, kuma idanuwan Sa’adatu ya yango musu wajen da zasu zauna, kafin wata da ta kasa shaida fuskarta ta karaso tana mata alama da su biyota, duk da mamakin da tayi bata musa ba, suka bita har can gaba-gaba inda aka tanadi wani wajen zaman na musamman, suka zauna.
“Duk idan zanzo dinner sai bikina ya dinga dawomun, sai inajin wani yanayi da bansan sunan shi ba”
Cewar Bashir bayan sun zauna, yana saka Sa’adatu yin dariya
“Baka sha wa’azi wajen Yaa Tahir ba?”
Shima dariyar yayi
“Toshe kunnuwana nayi fa, dan Allaah ya gani Madam ta cancanci duk wani abu da ta roka a wajena, kuma sai nima naji dadin Dinner din fiye da yanda nayi tunani”
Ko da aka fara shirye-shiryen da aka tsara na Dinner dinma hira su Sa’adatu sukeyi suna dariya kamar su kadaine a filin wajen, a jikinta Sa’adatu taji ana kallonta, irin kallon nan da zakaji kamar idanuwan mai yinsu na yawo a ilahirin jikinka, hakan yasa ta raba hankalinta daga kan Bashir ta tafi neman wanda yake mata wannan kallon da dalilin shi, sai kuwa suka sauka akan Jabir da yake zaune daga nesa da ita, amman kujerar shi tana fuskantarta ne, kuma bashi kadai bane a teburin nashi, da alama tare yake da Aisha
“Baban Dinaar ne ko?”
Bashir ya tambaya, sai ta daga masa kai
“Ki sauke idanuwanki, kiyi kamar baya wajen”
Sai kuwa tabi umarnin Bashir, duk da jikinta yanata yi mata gardama, yaki bata hadin kai wajen haduwa su share kallon Jabir. Da yake an ajiye musu tarkace kala-kala a gabansu, saita kai hannu ta dauki lemon gabanta ta zuka da straw din ciki ko zata hadiye abinda yake neman taso mata, a lokacin data ajiye lemon, taja numfashi, Bashir ya miko hannu yana dan taba gefen dankwalinta, sai ya nuna mata wani dan karamin zare a hannunshi, zuciyarta ta buga da karfin gaske, lokaci daya idanuwanta suka sauka akan Jabir daya tashi tsaye, abinda take gani cikin idanuwan shi yasa tayi saurin sauke nata, data kara kallon shi sai taga ya zauna, alamu kuma sun nuna magana yayi da Aisha da suke tare, kafin ya sake mikewa, bai kara kallonta ba yadan ja kujerar shi baya dan taga hakan, tukunna ya mike yana bin hanyar da zata fitar dashi daga wajen gabaki daya.
“Ya tafi fa”
Sa’adatu tayi maganar cikin wata irin murya, sai Bashir yayi dariya mai sauti
“Good, sai mu maida hankalinmu kan bikin”
Haka tayi kokarin yi, tayi canjin kudi yan naira dari bibbiyu da zatayi liqi dasu, kuma Jabir ma ya bada an kawo mata na dubu dai-dai, a ranta take cewa bata ga dalilin da zaisa ta likasu ba, amman lokacin da Badr ta fito filin bayan MC ya kirata, Sa’adatu ta tashi taje don tayi mata liqi, Badr din kuma ta miko hannu ta kama nata ta dan matsa hadi dayi mata murmushi
“Yaushe kikazo?”
Ta furta akan labbanta
“Tun dazun, kinyi kyau sosai”
Cewar Sa’adatu tana daga mata hannu cikin alamar dake nuna komai yayi, sai Badr tayi dariya, taja hannun Sa’adatun zuwa gefenta, ta kuma yiwa daya daga cikin masu daukar hoton alama daya dauke su, babu bata lokaci ya shiga haska su, ta kuma ce ya daukar mata Sa’adatun ita kadai, ai da aka gama yi mata batasan lokacin data zaro kudin nan ta fara zubawa Badr ba. Bayan ta koma ta zauna kuwa, basu kara dadewa ba, Bashir ya nuna mata lokaci
“Dare ya farayi Sa’adatu…”
Kuma a lokacin ne wayarta ta fara kara, data duba taga Abdallah ne, saita kashe ta tura masa gajeran sako
“Akwai hayaniya Yaa Abdallah, yanzun zan dawo In Shaa Allaah”
Bata kuma nemi tayiwa Badr sallama ba, dan tasan haka zatace ba zata tafi ba sai an tashi, a wajen fita daga ita har Bashir kowa an bashi manyan ledoji guda bibbiyu, duka Bashir ne ya rike musu har wajen motar shi, sai da suka hau hanya ta fara jera hamma, yana mata dariya
“Jiya fa banyi bacci ba da kyau, saboda inata dokin dinner din nan”
Kai Bashir ya girgiza mata
“Ko kuma kina tunanin zuwa kiga Baban Dinaar ba”
A kunyace ta kalle shi
“A’a Allaah, ni to in ganshi inyi masa me?”
Murmushi Bashir yayi, hankalin shi na kan tukin da yake duk kuwa da babu motoci sosai saboda sha daya tayi
“Ki motsa masa kishin shi mana, ni kuma ki sakani wasa da rayuwata”
Dariya Sa’adatu tayi mai sauti
“Ai sai bayan munje ma naga wautar da nayi, tunda na tabbatar wajen cike yake da ‘yan uwanshi, idan yazo ya kamani da kokawa nace zan rama taron dangi zasuyi mun”
Sosai Sa’adatu take dariya harta kasa magana, saboda da gaske ne, idan dambe za’ayi tsakanin Jabir da Bashir a wajen taron nan, tana da yakinin kaf ‘yan uwanshi, harda Badr a ciki kuwa taron dangi zasuyiwa Bashir, a dan zaman da tayi dasu ta gane suna da hadin kai.
“Ai ba zan bari ba”
Ta fadi tana cigaba dayin dariya, sai Bashir ya harareta kafin ya koma ya kalli titin, hira sukeyi sosai harya sauketa, sai da tayi masa sallama, ta kuma dauki ledojinta, ta fito daga motar tukunna ta kula da Abdallah da yake tsaye ya jingina bayanshi da jikin kofar. Gajiya da baccin ne shimfide a fuskarshi, wani yanayi daya nuna mata cewar ya jima a tsaye a kofar gidan, sai taji wani yanayi ya rufar mata, ita kuwa bayan yafiya zata iya daga hannuwa ta rokarwa Abida gafara batare data hada da Asabe ba? Saboda hanyoyin da zatayi amfani dasu wajen kamanta kulawar Abdallah a gareta batajin suna da yawa, inta hada da yiwa mahaifiyarshi addu’a kamar zata kamanta ko ba da yawa ba
“Yaa Abdallah…”
Ta kira cikin karamar murya, hamma yayi a maimakon ya amsata, ya kuma mika hannun shi ya karbi ledojin, da kai yayi mata alamar ta wuce, babu musu ta shige gidan, yana biye da ita, yayi addu’a yana rufe kofar. Ya mika mata ledojin har bakin kofar daki
“Sunyi bacci, in Dinaar ta farka za’a miko miki ita”
Kai ta daga masa, ya shige dakinsu, itama ta shiga nata, saida ta fara sake kayan jikinta ta dauki wipes din Dinaar ta goge kwalliyar fuskarta, duk da haka bataji tayi mata yanda take so ba, shisa ta fita tsakar gida ta wanko fuskarta, ta duba ledojin, abinda zai iya lalacewa taje ta saka a fridge, tukunna ta samu ta kwanta.
Wayarta ta dauka da nufin turawa Bashir text din godiya da kuma fatan ya karasa gida lafiya, bata ma ko cire lock din wayar ba kiran Jabir ya shigo, ga mamakinta, bawai tana tsammanin kiran bane ba, kawai zuciyarta a nutse take, bataji wannan tsallen ba, haka babu zumudi ko wani fata ta daga kiran ta kara a kunne hadi dayin sallamar da Jabir bai amsa ba, sai huci da yake sauke mata a kunne
“Me kike so dani?”
Ya tambaya, kuma da dukkan gaskiyarta ta amsa shi
“Bangane…”
Kuma a maimakon ya fahimtar da ita saiya sauke numfashi hadi da kashe kiran
“Ikon Allaah…”
Cewar Sa’adatu, mamakin da batayi ba da taga kiranshi yana dirar mata yanzun, da taga inta tsaya tunanin abinda Jabir din yake nufi wahalar da kanta zatayi saitayi abinda ta dauki wayar domin shi tun da farko, da kuma taji ya sauka lafiya, sukayi sallama saita
yi addu’ar bacci tana gyara kwanciyarta
Zuciyarta wasai
Batare da sanin abinda wayewar garin zata zo mata dashi ba…