Skip to content
Part 67 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Allaah Ya gafartawa Baba (Ibrahim Aliyu) Allaah Yayi masa Rahma, Allaah Ya kyautata namu karshen. Amin thumma amin

*****

JABIR

“Babu fa yanda za’ayi ace bikin Badr bamuyi attending kowanne event ba, kaima ka sani kuma”

Haka Aisha tace lokacin data fito masa da kayan da zaisa

“Nifa banajin fita ko ina ne”

Kuma har cikin ranshi hakan ne, ai yasan Badr ce, idan akwai wanda yafi kowa cancanta ayiwa hidima to tana cikin lissafin nan, babu wanda zaice bashi da wani abu a gidanshi ko dakin shi da in aka tambaya ba zaice Badr bace ta bashi, tana da kirki, kuma ya tabbata zuwan shi ba zai ragewa bikin armashi ba, akwai tarin mutanen da ba ‘yan uwanta ba da yasan zasu nuna bajintarsu a bikin fiye dama yanda su zasu nuna, tunda kirkin Badr a jininta yake, ita din ta mutane ce, ba zabe takeyi ba idan ta tashi. Bata huta ba, shima bata barshi ya huta ba saida taga ya shirya, kayan da ta saka kalace da bature yakewa lakabi da wine, shikuma sai ta bashi yadi ruwan kwai mai haske, shi da kanshi sai yaga sunyi kyau, musamman da ta rike Na’im, haka ya kasa boye murmushin shi.

Sai da sukayi hotuna sosai kafin suka fita, data bashi Na’im baiki ba, ya zagaya ya zauna, ita kuma ta zauna a mazaunin direba, tunda haka sukeyi yawanci, idan bayason fita ta matsa, to itace takeyin tukin. Ba wata hira sukayi ba, saboda kasalar da Jabir yakeji tana bin gabbanshi, sai sautin karatun Qur’ani da yake tashi a hankali, Aisha tana bi da sanyin muryarta, ya dai gyarawa Na’im zama, shima kuma ya gyara, a hankali sautin muryar Aisha yake shigar shi yana tuna masa safiyar ranaku masu yawan gaske da zai kwanta yana saurarenta tana rera karatunta mai dadin saurare. Har sakashi takeyi yanajin kamar wasa yakeyi duk lokacin darussan Tajwid saboda yanda take bawa kowanne harafi hakkin shi

“Ina son karatunki, ina son muryarki in kina karatu”

Ya sha fada mata, kuma duk wani karatu da zaiji a kunnuwanshi a bayan na Aisha yake, yana da recordings da yawa na karatun nata da batama san yayi su ba, ko da suka karasa wajen sai yakejin inama ace gida suka isa, kuma da sun shiga kwanciya zasuyi, ya riketa a jikinta yanajin karatun nata har bacci ya dauke shi. Zaice ko da suka shiga wajen taron zuciyarshi gida take son zuwa, kuma cikin karamci da girmamawar da Badr bata gajiya dashi ta taso tana zuwa har inda suke suka gaisa kafin ta koma mazauninta bayan anyi musu hotuna tare. A yawon da yakeyi da idanuwanshi ne suka sauka kan Sa’adatu, wani abu ya hargitsa masa yana dawo masa da kuzarin daya rasa tun fitowarsu, kafin zafi ya maye masa gurbin komai. Wani irin zafine da tunda yake bai tabajin irinshi ba, ya gane wanda take tare dashi, shine na rannan, kuma daga inda yake, da shigar da sukayi, inda baisan Sa’adatu ba zaiyi zaton saurayinta ne.

“Menene? Me ya faru?”

Aisha ta tambaya, kuma yasan yanayin fuskarshi da yakejin ta canza ce tasa tayi masa wannan tambayar

“Sa’adatu ce”

Ya amsa batare daya dauke idanuwanshi daga kanta ba, yana dorawa da

“Ita da wani kato…”

Sauran maganar ya fito a kausashe

“To madalla”

Cewar Aisha da wani bacin rai yake taso mata ganin yanda Jabir din ya hargitse lokaci daya. Mikewa yayi a zabure har saida ya tsoratata

“Hannun shi, hannun shi…”

Ya fadi

“Ka zauna kafin kaja a fara kallonmu”

Sai kuwa ya zauna din, amman ba zatace ga ranar karshe da ta ga irin bacin rannan a fuskarshi ba

“Tashi mu tafi”

Dariyar takaici tayi

“Akan wanne dalili?”

Sai lokacin ya kalleta

“Saboda ina so inje gida”

Kai ta jinjina masa

“Saboda dai ba zaka iya ganinta da wani ba, nikuma babu ta inda hakan ya shafeni, idan umarni kake bani in tashi mu tafi, ba zanki ba…”

Sosai yake kallonta, itama taki janye nata idanuwan daga cikin nashi saboda a shirye take da duk wata rigima da yakeji da ita

“Ni tafiya zanyi”

Kafadu ta daga masa, kuma yaga alamar bata da niyyar cewa komai, saiya mike. Bai tuna cewar da mota daya suka fito, kuma mukullin na hannun Aisha ba sai bayan ya fita yaje wajen motar. Bayason komawa ciki, direba ya kira ya tsaya ya jirashi, wata zuciya na ce masa ya koma ciki ya sako Sa’adatu a gaba su fito tare ya sauketa gida. Duk wata addu’a da tazo bakinshi ita ya dinga karantawa domin neman samun salama. Ko da direban yazo gidansu yace ya kaishi, in yayi sallama lokacin shiga to sabone bawai dan ya tuna da hakan ba, ya shiga kwadawa Hajiya Hasina kira

“Jabir, lafiya? Me ya faru?”

Ta tambaya a rikice bayan ta fito, ta riga tasan shine, babu wani tashin hankali da zai faru da daya a cikin yaranta suzo suna mata wannan kiran, Jabir ne kawai, abu karami ko babba, ko da babu komai ma zai iya zuwa yana kiranta tun daga bakin kofa

“Banganki bane ba”

Zai amsa inta tambayi dalili, bayan bai shiga ciki ya dubata ba

“Sa’adatu, inaso in dawo da ita”

Maganar ta fito masa kai tsaye, sai Hajiya Hasina tayi murmushi tana dorawa da

“Ma Shaa Allaah…”

Shima murmushin ne ya kwace masa

“Saiki fadawa su Babban Yayaa suje gobe, banaso a dauki lokaci”

Da murmushin a fuskarta tace masa

“Harkun dai-daita kenan? Sune sukace aje goben?”

Kai ya girgiza mata

“Banma yi mata magana ba tukunna”

Wannan karin murmushi tayi mai sauti

“To kaje ku fara magana da ita, inta saka maka lokaci sai ka fadamun”

Duk da mamaki ya nuna a fuskarshi saiya daga mata kai, yayi mata sallama yana ficewa yaje wajen motarshi ya bude ya shiga, yana fadawa direban ya kaishi gida, a hanya yake tunanin dalilin da zaisa Hajiya Hasina tace yaje yayi magana da Sa’adatu bayan wancen karin babu wanda yace masa haka, kowa ca yayi ya mayar da ita, amman zaiyi yanda sukace din, tunda inda son samunshi ne kar a wuce gobe ba’a mayar da aurensu ba sai yaga yanda wani kato zai dinga fita yawo da ita. Daya koma gida ya rage kayan jikinshi ma ya kwanta saiya kasa bacci, yanata juyi ranshi na baci batare da wani takaimamen dalili ba, baisan iya lokacin daya dauka a haka ba Aisha ta shigo da sallama a bakinta, ya amsa, saida ta fara kwantar da Na’im kan gadon shi, yana kallonta ta shiga bayi, ruwa ta watsa ta fito.

Ta gama duk wani night routine din data saba kafin kwanciya, kafin ta hau gadon, tayi addu’a ta tofa a jikinta ta juya masa baya

“Bakiyi mun ba”

Ya furta yana matsawa jikinta, batace masa komai ba

“Bakiyi mun addu’ar ba yau”

Ya sake fadi, saita ture shi tana zame jikinta ta matsa gaba, sake matsawa yayi yana janyota, wannan karin yayi mata rikon da ba zata iya zamewa ba, in tayi addu’a zata tofa musu ne, ko bacci yakeyi yakan jita lokutta da dama

“Banajin dadi fa”

Ya fadi, shiru tayi batace masa komai ba, haka ya dinga magana

“Ni nake magana kina shareni Tasha?”

Zaune ta tashi, kishin da take ta kokarin dannewa na taso mata

“Me kake so dani? Me zance maka? Muje waje tare, ka baroni saboda kaga tsohuwar matarka, kuma in dawo ba zaka barni inyi bacci na cikin salama ba, me zance maka? Sau nawa nace maka in kana sonta ka dawo da ita?”

Daga kwancen yake kallonta cikin hasken dakin da bai wadata ba

“Zan dawo da ita”

Ya furta a hankali, sai Aisha taji kamar ya mareta, lokaci daya wani hawaye ya dinga kawo ma idanuwanta ziyara tana kokarin maida shi, dakyar ta iya mallakar kanta ta koma ta kwanta, amman saida suka zubo, anya akwai wani abu da yakai kishi wahalar da mata? Ta tambayi kanta, taji dadi da Jabir bai sake ce mata komai ba, don bacci sai barawo ne ya sace ta, ga jikinta yayi mata nauyi balle ta tashi ko da sallah tayi ta roki Allaah sassaucin zafin da zuciyarta takeyi.

Washegari da wuri ta shirya tace ma Jabir tanaso taje gidansu, fatan dawowa lafiya yayi mata. Shima kuma shiryawa yayi, akwai ayyukan da yake son ya kammala da wuri don yaje wajen Sa’adatu. Itace ma daya kirata tace masa tana makaranta sai yamma zata koma gida. Dole ya cigaba da zagaya stores dinshi yana karasa duk wani abu dayake ta turewa gefe don yaga saurin lokaci.

Ya kasa saka wani abin kirki a cikinshi, sai milk shake yake ta kwankwada, sai kuma apple da yaci guda biyu. Ba kuma yunwar bace bayaji, wani abune cikin cikin nashi kamar kaya yayi masa tsaye, yasan kuma ba zai warware ba sai yayi magana da Sa’adatu. A hanyar gidansu ya tsaya yayi sallar magriba, haka kawai sai zuciyarshi take bugawa, kuma bai gane dalilin da yasa zuciyar tashi take masa wannan bugun ba sai bayan Sa’adatu ta fito yace mata

“Daman inaso ki fadawa Yaa Abdallah su Babban Yayaa zasu zo a mayar da aurenmu”

Ta saka idanuwanta cikin nashi na wasu dakika tace masa

“Nope, Allaah yayi mana zabin alkhairi, banajin komawa ni kam”

Kuma har tayi masa sallama ta shige gida mamaki ya hanashi motsawa daga inda yake, banda

“Nope…”

Babu abinda yake maimaitawa cikin kanshi, wata kalma da tayi masa ciwon da bai taba zato ba, saboda ta isa kunnuwanshi tattare da wani raini da bai zata zai gifta a tsakanin shi da Sa’adatu ba. To me ma take nufi? Bata son shi? Bata son sake zaman aure dashi? Haka ya kwanta ranar, ga yunwar da yakeji na kara bacin ranshi, kuma Aisha ko magana batayi masa ba balle ta tambaye shi dalilin da yasa yace bayacin abinci.

Farfesun kayan ciki ne da wainar da baisan inda ta samo ba, ta zauna taci, harda karfin shan lemo take dashi, siririf din da takeyi da abin zukar lemon ne ya karasa kure hakurin shi

“Kin cikamun kunne Aisha, babu yanda za’ayi ki baro dining area kizo inda nake kwance ina hutawa kice zaki dameni”

Dariya tayi

“Ikon Allaah, to kayi hakuri yallabai”

Ta mike da kofin lemonta tana sake siririf din taja stroller din Na’im suka wuce suna barin shi a wajen. Hakan kuma ya kara kular dashi, daya kwanta a dakinshi sai kadaici, yunwa da bacin rai suka hade masa waje daya. Dole ya tashi ya nufi dakin Aisha, bacci takeyi sosai, shisa ya shige jikinta yana neman dalilin da zatayi masa gardama ko fadane suyi ko zaiji sauki, amman saita karbeshi cike da kulawar data saba.

Da ta tashi tayo wanka ta dawo ma baccin ta sake komawa tana barin shi, daya fito daga nashi wankan yaso ya tasheta ta hada masa shayi, sai kuma yayiwa kanshi fada ya tashi ya hada shayin da kanshi, ya kuma shanye a kitchen din kafin ya koma dakin, ya kwanta a gefenta yana fatan bacci ya dauke shi. Amman abin ya gagara, kan kunnenshi aka kira sallah, yayi alwala ya fita masallaci, saida ya dawo tukunna baccin ya fara daukarshi, shima rigimar Na’im ta tashe shi duk da Aisha ta daukeshi sun fita daga dakin, bayan ya koma baccin ya tashi, kanshi yayi nauyi, ba ciwo yakeyi ba, yanajin kamar babu iska ne a ciki, yayi masa wani irin dumm. Baiki tayin Aisha na karyawa ba, dan yunwa yakeji sosai

Doya ce da kwai, sai sauce din nikakken nama

“Babu kifi a gidan?”

Kai ta girgiza masa

“Sai danye, in zaka jira sai inyi maka, me kake so? A gasa?”

Kan ya sake girgiza mata

“Karki wahalar da kanki…”

Murmushi tayi masa

“Allaah sai inyi maka tunda kanaso”

Ruwan shayin ya kurba, yayi masa dadi yasha kayan kamshi

“Kibari sai da daddare”

Numfashi taja ta sauke

“Allaah Ya kaimu daren, gasawa za’ayi?”

Ya daga kafadunshi

“Duk abinda kikayi mun inaso”

Yaci doyar fiye da yanda yayi zato, ya goge hannun shi, ya sumbaci Aisha a labbanta, ya karasa ya sumbaci Na’im da yake bacci a gefen fuskarshi tukunna yayi mata sallama. Akwai takalman da aka kawo musu yanaso ya duba yagani, lokacin da yaje shagon ma, Amiru, da shine yake kula da bangaren sadarwa na shagon, wato duk wata cinikayya da zasuyi ta online, shine yake kulawa da wannan, yana ta aikin daukar takalman a hoto, sunyi ma Jabir kyau, dan saida ya dauki wasu bakake

“A account din shago zakasa kudin oga”

Cewar Amiru

“Kai Amiru, kaman zan gudu”

Jabir ya fadi yana dariya

“Ai dan karka manta azo lissafi ne a samu gibi”

Dariya Jabir ya sakeyi, yayi musu transfer din kudin, tunda daman haka sukeyi, duk wani abu da zau dauka ko ya aiko wani ya dauka, to zai biya kudin daga personal account dinshi. Sai bayan ya dawo sallar azahar tukunna ya kira Sa’adatu, sai tayi rejecting tana tura masa gajeran sako cewar tana aji, shima sakon ya tura mata cewar zaizo in anyi magriba

“Idan ‘yarka zaka gani Allaah Ya kaimu”

Shifa mamakin Sa’adatu yakeyi

“Ke zangani”

Ya tura mata, bata dauki lokaci ba wajen amsa masa

“Zanyi karatu, ina da test gobe idan Allaah Ya kaimu, bani da lokaci”

Murmushi mai sauti ya subuce masa duk da baya cikin nishadi

.

“Wai Sa’adatu ni kike yiwa haka?”

Ko haske wayarshi tayi saiya duba, amman bata sake cewa komai ba. Sai yayi dariya yana fadawa kanshi kawai so takeyi ta rama yanda ta dinga rokonshi ya ture, shima zai jure duk wani jan aji da zatayi masa. Idan kuma yaga zata bata masa lokaci saiya samu Abdallah yayi masa magana kai tsaye. Wannan tunanin ne kuma ya dan sama masa nutsuwa, kamar yanda tace bata da lokaci bai matsa ba, daga shagon saiya wuce gida abin shi, wani film ma suka kalla shi da Aisha, ga kifin data gasa yayi masa dadi.

Saiya tsinci kanshi da ture Sa’adatu gefe, sukayi nishadin da kwa

na biyu basuyi irinshi ba, tunda ai shine, yaushe yake saka ma ranshi yin abu ya gagare shi? Zaije ya samu Sa’adatu ko da a makaranta ne, su karasa magana

Abinda bai sani ba, hausa sunce wasa farin girki…

<< Tsakaninmu 67

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×