Skip to content
Part 65 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

SA’ADATU

“Wai da gaske ba zaki koma gidanshi ba Sa’adatu?”

Fa’iza ta tambayeta, dariya tayi mai sauti

“Zan koma matar Yaya, inaso in koma ai”

Kuma tun daga kasan zuciyarta takejin haka, tana son Jabir, babu wani kwaskwarima da za’ayiwa maganar. Shisa ta bawa kanta mamaki lokacin daya bukaci a mayar da auren ta kalli idanuwanshi tace masa bata da bukata. Kuma yanayin fuskarshi sai yasa dariya ta kusan kwace mata. Kawai saita rama wahalar daya bata, da zagayen da ya dinga saka zuciyarta nayi bayan yasan daga karshe zai mayar da ita, to me yasa zai barta shekara daya harda wani abu? Dararen da ta shafe tana juyi cikin bukatar shi fa? Ai duk saiya biyasu, yana dauka da wasa ta shiryawa janshi a kasa.

Kuma wasan ya dauki lamarin, sai bayan ya samu Abdallah yayi masa magana yace yaje su dai-daita da Sa’adatu, inta amince bashi da matsala tukunna hankalin shi ya fara tashi. Duk wajen wanda ya juya da yake tunanin abin zaizo da sauki saiya sake maida shi wajenta. Abdallah ne ma ya gayawa Fa’iza dan ita batayi maganar da kowa ba. Tun Jabir na damunta da sakonnin sai gashi yana binta makaranta, yana biyota gida, amsa daya kuma take bashi

“Nifa na hakura, idan don Dinaar ne dama can ai tsarin in haifa in mika muku ne, sai ka bari in yayeta kazo ka dauki ‘yarka, in kuma yanzun kake so hakan ma ba zai gagara ba, amman dan Allaah ka kyaleni”

Kai ya dinga girgiza mata

“Bafa saboda ita bane ba”

Saita tsareshi da idanuwanta

“To saboda me? Me yasa sai yanzun?”

Numfashi yaja tana kuma kallo yayi kokarin hadiye wani abu da kamar ya tsaya masa a makoshi

“Saboda ni ne, saboda ni nake so ki dawo, saboda sai yanzun nagane, inaso in zauna dake, inaso in karashe sauran rayuwata tare dake”

Saita tabe baki kamar duk abinda ya fada bai wuce har kasan zuciyarta ba

“Nikuma kaga banajin hakan”

Ya daga hannuwanshi yana saukewa cikin rashin madafa

“Bansan me zance ba, bansan me kuma kike so inyi ba Sa’adatu, idan gwadawa kikeyi kiga ko ina sonki kiyi hakuri kibari a maida auren sai in nuna miki a aikace, idan kuma so kike ki cigaba da gwada hakurina zan aro wani in kara akan wanda banma san ina dashi ba sai yanzun”

Daga lokacin ne kuma tunda ya tafi bai sake damunta da zuwa ba, zaiyi mata text ya duba lafiyarsu ita Dinaar kamar yanda ya saba, saida aka cika sati biyu cif tukunna ya sakeyi mata maganar

“In turo a maida aurenmu Sa’adatu?”

Ta karanta sakon, ta kafe wayar da idanuwa har hasken ya dauke, ta sake gyara kwanciyarta wani abu na dukan zuciyarta. Da gaske babu wanda yake wuce kaddararshi, kuma wannan kaddarar itace ta hadata da Jabir, amman in ba haka ba aiko a littafi sai anyi juyi kala-kala kafin mace mai matsayinta zata samu miji mai matsayin Jabir. Ta sani, ta kowacce fuska shi din yafi karfinta, sai ga kaddara ta hada tafiyarsu, harma ya sauke ajin nashi a gefe yake ta binta haka, ta dauki wayar

“Allaah Yasa mayar da auren namu shine alkhairi”

Kira ne ya biyo bayan sakon, kamar ba zata dauka ba, sai kuma ta daga ta kara a kunnenta

“In turo? Ki fadawa Yaa Abdallah zan turo”

Yayi tambaya yana kuma dorawa batare daya jira amsar da zata bashi ba

“Nagode…kiyi baccinki, sai da safe”

Da kai ta amsa tana sauke wayar. Batayi baccin ba, Bashir tayiwa sallama a twitter, akace kowanne mutum da zaka gani, kowanne mutum da wani abu zai hadaku, ko da bayan rabuwarku inka zauna saika samu dalilin wannan haduwar. Ita lokacin data hadu da Bashir, bakowa bane sai abokin Tahir, kuma bata taba zaton zai wuce hakan a wajenta ba, balle ta hasaso idan zata bada labarinta, zata zo wajen komawarta gidan Jabir saita hada dashi a cikin labarin

“Alhamdulillah. Ma Shaa Allaah Sa’adatu. Allaah Ya tabbatar muku da alkhairi”

Bashir ya fadi bayan ta gaya masa. Sunyi hira sosai, yanata tsokanarta. Bacci tayi sosai a daren, ta tashi da safe, kafin tayi shirin makaranta ta fadawa Abdallah

“Ma Shaa Allaah. Zamuyi magana dashi In Shaa Allaah. Allaah Yasa hakan ne mafi alkhairi”

Wani sanyi ya ratsata, lokacin da ‘yan uwanta suka fara kiranta daya bayan daya, kowa farin cikin shi yake nunawa, amman hakan bai hanasu karawa da addu’ar tabbatuwar alkhairi ba, kuma da duka zuciyarta take amsawa da amin, tanajin bambanci mai yawa a wannan auren da ma wancen din. Kuma da daren ranar ne ta samu kira da bakuwar lamba, kira biyu kafin ta daga da tunanin masu order din zobo me ko kunun aya, sai taji muryar Tahir, wani abu ya tsirga mata

“Bash ke fadamun zaki koma gidan Baban Dinaar shine na kira in tayaki murna”

Ya karasa da wani yanayi a muryarshi

“Yaa Tahir”

Numfashi ya sauke da taji sautin shi ta cikin wayar

“Bansan sau nawa zanyi miki sallama ba a rayuwata Sa’adatu. Ina fatan wannan ta zama ta karshe…”

Ta rufe idanuwanta, yanayi kala-kala na gifta mata, anya kuwa? Kamar akwai wani bangare a cikin zuciyarta da Tahir ya zauna, tashin shi kuma baisa wani ya taba cike wajen ba

“Yaa Tahir…”

Ta sake fadi tana kasa dorawa da komai

“Kiyi farin ciki, farin ciki mai yawa. Allaah Yasa yayi miki ninkin soyayyar da nayi miki, ya zauna dake fiye da zaman da nayi miki tanadi…Allaah Ya sadamu da alkhairi”

Ta amsa da

“Amin…”

Muryarta a karye, daya katse wayar kuma saita ajiyeta hawaye na zubo mata. A hankali tayi ma Tahir addu’ar alkhairi, ta kuma dora da rokawa Asabe gafara da Rahmar Allaah, a ganinta hakan na daga cikin hanyoyin da zata iya saka wani kaso na daga soyayyar Tahir. Zuciyarta kamar anyi kwalema an cire mata abubuwan da suka danneta haka ta kwanta sakayau da ita. Kuma badan Dinaar ta taba rikici ba tasan da wuri zatayi bacci. Da safe Abdallah baice mata komai ba, lecture daya gareta, tun azahar ta dawo gida, da Fa’iza ta kalleta saita fara washe baki

“Matar Yayaa anya akwai mai sona da Jabir kamanki?”

Dariya Fa’iza tayi

“Yasan darajar mutane ne Sa’adatu, sannan danginshi duka suna sonki, hakan abune mai matukar wahalar samu a wajen mace”

Numfashi ta sauke, itama shaidace, tunda ai ta gani wajen Abida, harta koma ga Allaah tana fama da kiyayyar dangin miji, da gaske hakan abune mai matukar wahalar samu. Ita ta kamawa Fa’iza aikin sukayi tuwo miyar danyar kubewa. Sosai taci tuwon don yayi mata dadi, yasha naman rago. Tayi alwalar sallar isha’i da batayi da wuri ba, sun zauna kallon wani film ita da Fa’iza tunda an bar wuta. Saiga Abdallah ya shigo yanata doka murmushi, hannunshi rike da wata leda daya mikawa Fa’iza, ta bude, alawace a ciki, dabino sai wani irin goro manya-manya, fari da ja

“Sa’adatu…”

Abdallah Ya kirata, ta fito rike da hijabinta a hannu, yasa nashi hannun a aljihu ya ciro damin kudi ya mika mata

“Ga sadakinki, an maida aurenku da Jabir yau bayan sallar ishai…”

Zuciyarta tayi wani irin tsalle, kudin suna mata nauyi a hannu

“Alhamdulillah Yaa Rabb… Alhamdulillah”

Cewar Fa’iza

“Kai Alhamdulillah, Ma Shaa Allaah”

Tana jinta ta shige daki tana daukar wayarta da take ringing

“Allaah Yasa alkhairi Sa’adatu. Allaah kuma Yasa mutuwace zata rabaku”

Idanuwanta cike da hawaye ta kalli Abdallah

“Ka ajiyemun kudin to”

Bai musa ba ya karbi kudin

“Banyi sallah ba, bari inyi sallah”

Kai ya jinjina mata fuskarshi dauke da fara’a. Sallar tayi, tana dorawa da nafilar godiya ga Ubangiji daya sake lullubeta da Rahma irin ta aure batare da ita din ta kasance wata ba. Ranar ta amsa wayar ‘yan uwa kamar me, musamman Amira da tace mata washegari zata baro Bauchi, farin ciki ya cika zuciyar Sa’adatu. Sai dai duk wannan farin cikin da rakeyi bata kai Jabir ba, duk wata nasiha da ake tayi masa bama ganewa yakeyi ba sosai, ji yake kamar yayi fuka fukai ya same shi a gaban Sa’adatu ya kamata ya rungumeta, yayi kewar jinta a jikinshi, yayi kewar wannan igiyoyin da suka dauresu waje daya.

Igiyoyin da yanzun ya rike gam yake fatan banda mutuwa babu abinda zaisa ya sake wasa dasu. Daya karasa gidanshi kuwa saiya tsinci kanshi da takawa ya rungume Aisha sosai, data raba jikinshi da nata saita sa hannu ta dauke kwallar da take mata barazana, da kanshi ya fada mata zai dawo da Sa’adatu, ya kuma fada mata za’aje nemar masa aurenta a karo na biyu kowanne lokaci. Amman yanda take ta ganin status din ‘yan gidansu na taya shi murnar maida auren yanzun nan, wani na bin wani, harda masu sake posting din hotunan wancen bikin na farko sai suka bata mamaki, ko tunanin zata gani babu wanda yayi, ko da yake ance naka naka ne ai, Jabir kuma nasu ne, bai kamata ace tayi mamaki ba duba da yanda yake da muhimmanci a wajensu.

Ta tabbata kaunar da sukeyi masa da son farin cikinshi ne ya shafi Sa’adatu, zai kuma cigaba da shafar duk wani abu da zai rabi Jabir din. Amman zuciyarta nayi mata zafi sosai, bata kuma san yanda zatayi da wannan zafin ba, balle yanzun daya shigo ya rungumeta yana son ta tayashi raba farin cikin mayar da auren

“Allaah Yasa hakan ne mafi alkhairi garemu duka”

Nashi hannun yakai yana share mata hawayen daya zubo mata, batare daya amsa ba, sai sake rungumeta da yayi

“Ina sonki, babu wani abu da zai canza hakan”

Tabe baki tayi, maganganun basu wani shigeta ba, wacce soyayya kuma? Wanne canjin yake magana akai, ai ya riga da ya canza komai daga lokacin daya hada shimfida da Sa’adatu yana raba mata komai nashi, maganar soyayya kam ai ajiyeta za’ayi a gefe, soyayyar da tayi kadan ya zauna su rayu su kadai? In dai wannan ce Allaah Ya amfana. Shima kamar ya kula kalaman nashi basu wani shigeta ba, shisa ya fara janta da hira yanayi mata kame-kame

“Zakaci wani abune? Inaso in kwanta”

Don hirar ta gundureta, shi kanshi ba wani jinshi takeyi ba a halin yanzun

“Naci abinci a wajen Hajja”

Kai ta jinjina masa, harta yunkura zata mike saita fasa ta zauna

“In roke ka wani abu?”

Da sauri Jabir ya daga mata kai

“Bani da matsala da aurenka, bani da matsala da matarka. Dan Allaah kayi mun alfarma daya, karka tilastamun zumunci da ita, Dinaar da duk wasu masu zuwa a gaba idan Allaah Ya bamu, kofata a bude take a wajensu, amman banda matarka, ta zauna a inda duk zaka ajiyeta kabarni in zauna inda nake nima”

Kallonta Jabir yakeyi sosai

“Banaso kuyi gaba da juna Aisha”

Kai ta girgiza masa

“Ba gaba zamuyi ba, inta kama wani dalili ya hadamu zamu gaisa, amman bayan hakan banyi maka alkawarin komai ba, dan Allaah karka takuramun”

Saiya jinjina mata kai

“Nagode”

Ta fadi tana tashi tabarshi a wajen. Yanda ta saka Na’im a tsakiyar gadon yau, shima saiya kwanta a gefe. Ta fannoni da dama yau zaiyi mata uzuri, ai mata ma suna kokari akan lamarin kishi, shi wani ya gani da Sa’adatu, amman da wani abu kamar icce ya tsaya masa a kahon zuciya bai sauka ba sai yau da aka mayar da aurensu, hankalin shi ya kwanta yanzun.

Danma saiya fara neman gidane tunda wancen ya rigada ya mallaka mata shi. Dole zai samu wani da zai ajiyeta, ga kuma su siyan furnitures da sauran abubuwa, amman bashi da matsala da wannan hidimar yana da masuyi masa, zai dai dauki akalla sati daya ko fiye da haka, anyi mai wahalar, to sauran shirin zaiyi shi a tsanake batare da gaggawar komai ba. Haka ya fadawa Sa’adatu daya kirata washegari tunda yanaso yaji nata tsarin

“Kabani sati hudu don in shirya a nutse”

Kai ya girgiza mata

“Sati biyu dai, kiyi komai a sati biyu dan Allaah”

Saita kasa yi masa musu. Tunda kamar yanda Amira ta fadane, ta iso kano da yammaci, sun kuma hadu da sauran ‘yan uwa inda suka shirya yar walima, Sa’adatu ta basu kudi wadatattu daga cikin wanda Jabir ya bata na hidima. Ga Sadakinta ma a account Abdallah ya saka mata, shisa suke ta hidimar cikin wadata. Duk da kunyar da takeji bai hanata karbar duk wani kayan gyara da ake bata ba, daman ga fatarta ta murje saboda shower gel din da Aisha Lame tayi mata recommending da ma wasu mayukan da suka dace da fatarta 07036662633. Ko da ake maganar yi mata dilka ma, scrub ta siya a wajen Aishar sai akayi mata amfani dashi, turaruka kawai aka siya, sai gashi ta fara kyallin amarci.

“Kinyi kyau kanwata, kamar bake ba. Allaah Yasa mutuwa ce zata rabaku, dan Allaah ke ma karkiyi wasa da addu’a”

Amira ta fadi muryarta na karyewa

“Amma zatayi farin ciki inda zata ganki yau”

Cewar Nabila, sai su duka suka fara hawaye, kewar Abida na dukansu

“Aikuwa saina fadawa Yaa Jabir kunsa amaryarshi kuka”

Nana da take share nata hawayen ta fadi, tana sakasu dariyar da basu shirya ba. Duk da zuciyoyinsu sun danyi nauyi haka suka cigaba da hidimarsu cike da karsashi. Kwanan Amira biyar, kamar karta tafi, Sa’adatu harda hawayenta ranar da zata koma

“Gaskiya auren nesa bashi da dadi, ke kadaice kikayi mana nisa haka”

Cewar Sa’adatu

“To ai auren kenan Sa’adatu, babu inda baya kai mace, ko ina ne kuma fatan zama cikin aminci da girmama juna akeyi, in aka samu wannan sauran abubuwan duka masu sauki ne, zan sake dawowa In Shaa Allaah, a gidanki ma zan sauka idan nazo”

Turo baki gaba Sa’adatu tayi

“Ai banma kama zancen nan ba Yaa Amira, kece zaki kwana a gidana? Tafdin…ke dai Allaah Ya dawo mana dake lafiya”

Amira tayi dariya kawai. Da yake mai adaidaita sahun dan unguwar ne Abdallah yayi masa magana tun dare, harda Fa’iza aka tafi rakata, itama Sa’adatu taso zuwa sukace saita tambayi Jabir, ta kira shi bata shiga, dole ta hakura. Ta koma gida ta zauna, ta dauki wayarta saita rasa abinda zatayi da ita, saboda tun ranar da aka maida aurenta da Jabir, ta fadawa Bashir yayi murna sosai saiya rufe da fadin

“Ina miki fatan alkhairi a rayuwar da zaki fara. Allaah Ya kula da duk wani motsinku. Nagode da karamcinki, Allaah Ya sadamu da alkhairinsa”

Ta karanta sakon yafi a kirga, kuma saida ya kwana tukunna ta iya amsawa tana hada masa da godiya. Ya bude, tagani, amman bai dawo mata da amsa ba, tasan sallama ce yayi mata tunda ta zama matar wani, babu yanda za’ayi su cigaba da magana.

Amman zuciyarta tayi mata wani iri, ta tabbata zata kwana biyu kafin kewar hirar da suka saba ta saketa.

Shikenan

Bashir ya shigo rayuwarta ya taka rawar da zaiyi

Gashi har lokaci ya tafi dashi

<< Tsakaninmu 64Tsakaninmu 67 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×