Skip to content
Part 66 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

“Ina kofar gida”

Jabir ya fadi tana daga kiran da yayi mata, bai kuma jira amsarta ba ya katse kiran. Ta duba agogo karfe tara saura. Dinaar tayi bacci, saita fito ta fadawa Fa’iza, kafin ta koma ta dauki hijabinta ta saka, tana tunanin abinda ya kawoshi, tunda washegari ne zata tare. Su Fa’iza sunje sunga gidan, tunda Jabir din yace aje a duba ko akwai abinda babu, kuma haka suka cikata da zancen haduwar gidan da yake a unguwar Sharada. Sunce yafi na farko inda ta zauna girma

“Me yasa ba zamu zauna a wancen gidan ba”

Ta tambayeshi lokacin da yace mata ana duba masa wani gidan ne, saiya amsa da fadin

“Wancen gidan naki ne Sa’adatu, abinda kike so zakiyi dashi”

Ta numfasa

“Idan inaso in zauna a ciki kuma fa?”

Dariya yayi sosai

“Kinga tunda Allaah Ya horemun, babu yanda za’ayi in kama haya, balle ince kiyi masa kudi in dinga biyanki duk shekara mu zauna a ciki. Nikuma banyi miki kama da mijin hajiya ba balle mu tare a gidanki”

Maganarshi ta karshe ta bata dariya

“To meye a ciki dan ka zauna gidana?”

Duk da baya gabanta tasan kai yake girgizawa

“Ki barni da maganar gidan nan Sa’adatu”

Sai kuwa ta kyaleshin. To ya samu gidan, sunje sun gani, yana kiranta a waya sosai tun da aka maida auren, amman yanda baice mata zaizo ba, itama bata bukaci ganinshi ba. Ya dai saka mata kudi masu nauyi, a cewarshi kar a dora ma Abdallah wahala tunda yanzun tana karkashin kulawarshi ne, ta jinjina kai kawai, to meye ma baya siya ya aiko dashi ko da bata auren nashi? Shi dai kawai ta kula mutum ne da baya gajiya da hidimtawa mutane da kudin shi. Da sallama ta bude murfin motar tana shiga ta zauna tukunna taja ta rufe, motar sai kamshin masu kudi takeyi. Jabir ya dago ya kalleta, sai yaga fuskarta tayi masa fayau, kamar ta kara haske, da yake ko kwalli babu a idonta, wanka ma tayi bata shafa mai ba, turare ma sai dai wanda aketa badeta dashi, shine inkayi dab da ita zakaji kamshin da takeyi mai sanyi.

“Na kasa hakuri ne, na koma gida na sake fitowa”

Ta kalle shi, wando ne da kadan ya wuce gwiwar shi, sai riga baka da alamu suka nuna ba zatayi nauyi ba, shigace dai da ba zaka takura ba

“Ina wuni”

Ta gaishe shi madadin amsar maganar da yayi mata

“Lafiya kalau, kunshi kikayi? Baki nuna mun ba”

Ya karasa yana kama hannunta hadi da fara jujjuyashi, zanen jan lalle ne akayi mata a tafukan, sai kuma yatsunta, sai baki da aka zana, kafar kuwa iya jan ne, da yake ya kwana ya turu sosai yayi kyau, ta fito a amaryarta

“Yayi kyau”

Ya fadi cikin wani yanayi da ta fahimta, yana lankwasa yatsunta a hankali cikin tafi hannun shi

“Har gobe zaki kai? Ni kuma fa? Ya zanyi?”

Yayi maganar can kasan makoshi yana saka idanuwanshi cikin nata, sai taji kamar an buge mata gwiwoyinta

“Dare nayi”

Ta iya fadi, sai ya kafeta da ido

“Korata kikeyi?”

Kai ta girgiza masa

“Kar Yaa Abdallah yaga na dade”

Ya sake dumtsa yatsunta yana murzasu a hankali

“Nafi shi iko dake a yanzun, idan naso daga nan gida zamu wuce kuma babu wanda zaice mun saboda me”

Kai ta daga masa cikin nuna ta yarda

“Kayi hakuri, ai goben da wuri zasu kaini idan Allaah Ya kaimu”

Saiya rausayar da kai

“Me yasa ba zanzo mu tafi ba?”

Shiru tayi tana gudun ta fadi wani abu da zai sake birkita shi tunda taga yanayin shi, ta kuma san kiris yake jira ya saka mata rikicin da batasan ta inda zata fara ba, su wuce su tafi gida a daren nan, so yake ta kasa hada ido da ‘yan uwanta. Hannunshi da yake rike da nata ta dago ta sumbata

“Kayi hakuri, yaune kawai…”

Gyara zamanshi yayi

“In Shaa Allaah ba zakiyi dana sanin sake bani dama ba Sa’adatu, zan kula dake dai-dai iyawata, zan kyautata zamanmu, zan kuma rike aurenki har karshen rayuwata”

Kai ta daga masa, wani rauni na kawo mata mamaya

“Nagode…”

Ta iya furtawa, bai kuma kara mintina biyar ba sukayi sallama, ta koma gida ta kwanta, kafin bacci ya dauketa, ta dauka ma sai tayi mafarkin Jabir yanda ya samu waje ya manne mata a zuciya. Sai dai bacci tayi, irin baccin nan da bakasan a duniyar da kake ba. Washegari data tashi, ita da Fa’iza suka kara harhada yan abubuwan da take da bukata. Sai kuma kazar da Fa’iza ta sakata a gaba saita cinye, duk soyayyarta da nama, wannan kazar ta zame mata wahala, ko abinci bataci ba, har rana tana fama, dakyar ta iya cinyewa ta shanye romon. Ta sakeyin wanka tayi sallar la’asar, zuwa lokacin su Nabila harda Anty Talatu duk sunzo, gidan cike yake da ‘yan uwa. Anata raha, ita kuma jikinta duk ya mutu, kamar shine karon farko da tayi aure. Angama shiryata cikin laffaya ruwan toka, wata kyauta da Badr ta aiko mata dashi tun daga Abuja, saboda sunje yawon shakawatawa da mijinta, da suka dawo kuma sai suka sauka Abujar.

Kafin a fita da ita Abdallah ya shigo gidan, kuma kowa saiya fice yabarsu su kadai a dakin

“Wai dawowa nayi inyi miki nasiha, amman tun ina hanya nake hada kalmomin suna rushewa”

Murmushi Sa’adatu tayi, bata koyi kokarin dauke hawayen da suka zubo mata ba

“Allaah Ya zaunar daku cikin aminci Sa’adatu, Allaah Yasa mutuwace zata rabaku”

Ta dago tasa hannu tana daga mayafin daya rufe mata fuska, don tanaso ta kalli Abdallah sosai

“Allaah Ya saka maka da alkhairi Yaa Abdallah. Allaah Ya jikan iyayenmu, yara na zamewa iyayensu sadakatul jariyya ta hanyar kyawawan ayyukansu, Yaa Abdallah na tabbata kana daya daga cikin yaran nan…muna godewa Allaah da samunka a zuri’armu. Allaah Ya kula mana da kai ya bamu aron rayuwa mai tsayi da albarka tare. In Shaa Allaah zanyi kokarin ganin ban baku kunya ba”

Ta numfasa saboda muryarta da take kokarin karyewa

“Ina da sirrin da naketa riritawa Yaa Abdallah, sirrin da ban fadawa kowa ba game da aurena da Jabir na farkon, amman yanzun aure ne mukayi da fatan mutuwa ce zata rabamu”

Sosai Abdallah yake kallonta, shiru ya dan gifta kafin ya sauke numfashi

“Sirrin nan sanin shi zaiyi mana amfani dani dake?”

Cike da rashin fahimta take dubanshi

“Ina nufin yanzun idan na sani zaiyi mun amfani? Kema zaiyi miki?”

Tayi shiru kafin ta girgiza masa kai a hankali, tunda da gaske ne babu wani amfani, inta fada masa aurensu na farko na yarjejeniya ne, tunda yanzun sunyi na tsakani da Allaah babu amfanin hakan

“To ki cigaba da adana shi tunda Allaah Ya sirranta muku, banajin akwai wasu ma’aurata da basu da sirri a tsakaninsu Sa’adatu. Ke dai ki tsarkake zuciyarki yanzun, ki kuma saka Allaah a dukkan lamarinki”

Ta daga masa kai da sauri, shiya kamata, kowa kuma ya bar masa, da kanshi ya sakata a mota, yayi tsaye duk ‘yan uwanta suka shiga motocin, bai kuma koma gida ba saida yaga sun bace masa, cikin zuciyarshi ya bisu da addu’ar sauka lafiya da kuma ta zaman lafiya mai dorewa a zaman auren Sa’adatun.

*

Kuma Sa’adatu na da yakin addu’ar ‘yan uwanta, dama yanda itama da karfafawar Fa’iza bata sake wasa da ibada ba, musamman salolin Nafila da kuma azumi duk sanda ta samu halin yi, suna daga cikin abubuwan da suka taka rawa matuka wajen tafiyar da rayuwarta a shekarun nan biyar. Godiya ga Allaah kuwa kullum cikinta take ta hanyar yawaita yin sadaka ga mabukata. Tana zaune cikin rufin asiri, ta kammala karatunta, aikin da Jabir ya nuna kamar bashi da ra’ayin tayi shine abinda yasa ta yanke shawarar dorawa da karatun nata har zuwa inda taji ta gaji da kanta, wannan kuwa kai tsaye ya amince mata.

Ta sake haihuwa, ta kara samun yarinya mace da taci suna Hasina, suna kiranta da Noor. Kawai a shekarun abinda yake bawa Sa’adatu mamaki shine kishin Aisha, ita a yanda take karantawa a labarai da kuma yanda takeji, haka akace kishi a gidan talakawa aka fi samun shi, sune suke da lokacin batawa akan kishiya, ko kuma tada jijiyar wuya akanta, masu kudi basu da wannan lokacin, to kana da kudinka da wani kasuwancin ko kuma aikin, ina kake da lokacin wata kishiya, balle kuma ace gidan kowa daban. Sai ka manta ma da kana da wata kishiya balle kayi lokacinta. To ita dai a yanzun zatace bata da matsalar komai banda ta Aisha lokaci zuwa lokaci, shima kuma ba zatace Aisha kai tsaye ba, zatace Jabir da yanda yake nuna mata bambanci tsakaninta da Aishar.

Da yake haihuwa ta budewa Aisha, ita yanzun yaranta ukune, kuma dukansu maza, bayan Na’im ta haifi Naadir sai yanzun tana goyon Mashhud. Kuma a yanda take ta rashin lafiya Sa’adatu tasan zaiyi wahala ace ba wani cikin take dashi ba tunda Naadir ya cika wata na goma yanzun. Laulayi takeyi mai zafi duk cikin da zatayi, haka Jabir zaizo ya dinga daukarta da sunan ta duba Aishar, bayan ba wata tarbar kirki take samu ba, haka zatayi kicin kicin da fuska tana amsata dakyar. Amman idan itace bata da lafiya sai dai yace Aisha na gaishe ta da jiki, wanda tasan ko bata fada ba shi zai iya cewa.

Babu abinda yafi mata ciwo ma irin batun yara, ko yanzun ma Jabir na dauke mata kai akan abinda take da gaskiya. In dai zai kwaso yaran yazo gidanta dasu Aisha taji suna nan sai tasa ya mayar mata da yaranta, amman fiye da rabin rayuwar Dinaar acan gidan Aishar takeyinta. Ranar ma ya fita dasu siyayya ne, saiya biyo ta gidanta, taji ya amsa kira yana rufewa da

“Yanzun zamu dawo fa”

Da yake Dinaar tayi bacci sai yabarta ya maida Na’im da Naadir. Zuwa yamma sai gashi ya dawo daukar Dinaar

“Aisha tace ya ban dawo mata da yaranta duka ba, nace mata Dinaar bacci tayi banason motsata, zata tayarmun da rigima, nace bari inzo in dauketa”

Sa’adatu ta tsira masa ido kawai tana kallon karfin halin shi

“Ai ka mayar mata da iya yaranta fa, kabarmun yarinya babu inda zataje”

Sai ya kalleta kamar ta aikata wani babban zunubi

“Bangane me kike son fada ba”

Ta jinjina masa kai

“Su Naadir basu taba kwana a gidan nan ba, ko yini basu tabayi ba, daka shigo dasu kamar zan gutsiresu zata fara kiranka a waya, amman ni tawa ‘yar sai tayi wata a wajenta”

Saiya fara fada kamar zai ari baki har yana fadin

“Yara nawa ne Sa’adatu, babu kuma wanda zai rabamun kansu, ina da ikon in daukesu in kaisu duk inda nake so”

Kuma haka ya dauki Dinaar ya tafi da ita, sai dai ya barta da share hawayen takaici. Kamar hakan bai ishe shi ba, kwana biyun da yayi a wajenta yana ta dauke mata kai, haka ya gama kwanakin ya tafi. Ita kuma ta tattara shi ta watsar. Da yake in dai wata matsala ce bata da abokin tattaunawa a yanzun daya wuce Fa’iza saikuwa Badr. Sai ta fadawa Badr din

“Saifa kin kara hakuri Sa’adatu, dan Allaah karki sake masa magana akan yara, har ita Dinaar din”

Sai tace

“Hmm…”

A fili, saboda a kasan ranta tunanin da takeyi daban ne, ta dai amsa Badr da duk wasu shawarwari data dinga bata, sai dai Jabir na zuwa gidan saita kasa hakuri ta kalleshi tace

“Ka kwace Dinaar ne gabaki daya?”

Da rashin fahimta yake kallonta, tasa dan yatsa ta dauke kwallar data taru a idonta

“A yarjejeniyarmu daman idan na haifeta baku zanyi, idan karbarta zakayi duka ka fadamun dan Allaah”

Da sauri ya karasa inda take yana riketa a jikinshi

“Wacce irin magana kikeyi haka Sa’adatu? Dan Allaah karki sake tayarmun da maganar yarjejeniya, Aisha nason Dinaar sosai, haka itama tanajin dadin zaman can saboda su Na’im, bawai don komai ba, amman idan kinaso in dawo da ita nan sai inyi hakan, dan Allaah karki sake wannan tunanin”

Kai ta jinjina masa kawai, amman har kasan ranta takejin ta haifawa Aisha Dinaar ne, duk kuma wani abu da Jabir zai fada ba zai canza wannan tunanin ba. Shisa ranar bata kare ba saida ta turawa Abdallah kudin da taketa ajiya shekara da shekaru

“Ka siyi gida dashi Yaa Abdallah tunda kaqi zama acan kasa an zuba ‘yan haya. Kudine da naketa ajiya. Dan Allaah karkace wani abu, gidan da sunanka zaka siya”

Dakyar ya iya ce mata

“In Shaa Allaah”

Sakon godiyar shi sai daga baya ya iso, gara tasan tayi abinda tayi niyya da kudaden, inma ya dauke Dinaar dinne gabaki daya shiya sani, ba zata dai sake tayar masa da maganar ba, wannan alkawari ne tayiwa kanta. Lokacin da sukaje tarewar su Fa’iza a sabon gidan kuwa, fara’a bata bar fuskarta ba

“Alhamdulillah…”

Ta furta, sauran ‘yan uwa na tayata, nima kuma ina tayata ta hanyar ajiye alkalami na anan.

NAGODE

To every single reader, wanda na sani da wanda ban sani ba. Allaah Ya saka muku da alkhairi for always supporting me. Allaah kuma Ya sadamu da alkhairinsa.

 

<< Tsakaninmu 66Tsakaninmu 65 >>

1 thought on “Tsakaninmu 67”

  1. Tammat bi hamdulillah
    Sannu lubna
    Well done
    Thank you very much for sharing tsakaninmu with us all.
    Allah ya jiqan iyaye ya saka miki da alkhairi

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×