Da akayi bikin Nana, bata dauka akwai wata boyayyar manufa a yanda Abida da yaranta sukayi tsaye don ganin komai ya tafi yanda ya kamata ba. Da akazo daukar Nana, tana ganinta a gefe, Abida ta rike, Abida ta rungume tana kuka kamar daga jikinta ta fito. Zatayi karya idan tace ranta bai sosu ba, da Uwani tace mata.
“Yanzun haka zaki zuba ido, idan nace miki Abida ta shanye miki yara sai kice kirkin da take musu ne.”
Shiru ta zaba, na ranar kawai, ta zabi shiru, saboda tana son jaddadawa zuciyarta kirkin Abida, tana son duba yanda ita da yaranta sukayi tsaye da karfi da kuma aljihunsu. Alhaji Salihu yayi mata kayan gado, da kujeru masu kyan gaske, haka kuma duk kayan abincin da akayi amfani dasu wajen bikin shine ya bayar. Gabaki daya kayan Kitchen din da aka kaiwa Nana, Abida ce da yaranta, Abdallah ya siyi labulaye, ko kudin hannunta data tara da gudummuwar da aka bata, satin bikin zuwa tayi ta mikawa Abida, tunda tasan ta fita sanin abubuwan da babu da kuma wanda ya kamata a siya. Abdallah ma, tana kula dashi, shigowa nawa yayi cikin hidimar bikin yana kiran Abida kamar akwai wani sirri da zasuyi. Bayan gaisuwa bata jin wata doguwar magana ta hadata dashi, yayi tsaye ne, yana barin shirun daya gifta a tsakaninsu ya sata sallamar shi, ya fice daga gidan.
Tasan a cikin yaran duka, shine babu shakuwar kirki a tsakaninsu ko lokacin da yake gidan, saboda tana yawan yi masa fada akan Abida da Sa’adatu, sai ya fara takaita maganar da take hadashi da ita, sai ya fara koyon yin shiru idan yana tare da ita, tunda ya fara hankali ba zatace ga ranar karshe da ya nufeta da wata matsala tashi ba, bayan rasuwar Habibu kuma, sai taga ya dauki wani girma ya dora a saman kanshi, girman da har a kasan zuciyarta tana son tayashi daukar nauyin shi amman bata san ta inda zata fara ba, da maganar aurenta ya taso, a cikin idanuwan shi taga kamar wata katanga ta ginu a tsakaninsu. Zata rantse ta sake rantsewa da duk rana da yanda Abdallah yake kara mata nisa, da yanda kuma take jin ya fito daga jikinta ne, idan ta kalle shi, idan wasu suka kalle shi zasu ga wannan alakar ta jini a tsakaninsu, amman bata sanshi ba, batasan waye danta ba.
Abida ta kwace mata shi, kamar su Nana, kamar kuma tazo duniya ne dan tayi wahala tsakanin rayuwa da mutuwa, ta haifo yaran da zata koma gefe tana kallonsu suna bautawa Abida. Da Uwani ta sake tayar mata da zancen haka tace mata.
“Ni banda wani kudi a wajena yanzun Uwani, kin dauka wai abin nan baya damuna?”
Sati daya a tsakani tazo mata da wani kullin magani kamar hoda, tace ta barbadama Alhaji Salihu wajen kwanciyar shi, ba zai mata musu ba inta nemi ta dawo da Sadiya wajenta. Ta karba, ba dan zuciyarta ta aminta da cewar maganin zai mata aiki ba, ta daiyi amfani dashine kawai. Bakinta har rawa yakeyi lokacin da ta gaishe shi da safe, duk wasu kalamai da ta dinga jerawa tunda ta karbi maganin ne taji sun rushe a cikin kanta.
“Daman…nace daman…”
Taji ta kwaso in’ina lokacin data bude bakinta, gashi ya kafeta da idanuwan nan nashi.
“Daman Sadiya ce, ita kadai ta rage karama yanzun…nace da zan rokeka ko zaka bari ta dawo nan wajena, ba zataji dadin zaman ba tunda ‘yar uwarta tayi aure.”
Ta karasa zuciyarta na lugude a cikin kirjinta,
“Ba damuwa…sauri nakeyi yanzun dai, mun karasa maganar idan na dawo.”
Mamaki ya sata kafewa a inda take harya fice bata iya ce masa komai ba, data ja kafafuwanta ta koma Uwani ta kira, muryarta dauke da mamakin da take ciki tana sanar da ita maganin yayi aiki. Da wannan mamakin ta yini, da dare kuma maganar da suka karasa da Alhaji Salihu saita wanke mata duk wani mamakinta, ta sake kunna mata wutar yarda da Malamin Uwani data jima da macewa a ranta. Abdallah ta kira tace masa Sadiyya zata zo tayi mata ko da sati ne tunda ana cikin lokacin hutun boko.
“Akwai Islamiyya fa…”
Abdallah ya fadi cikin son yi mata gardama, saida ta zage shi tas, tukunna cikin sanyi ya amsa da zata zo din. Bayan nan saida ta jera ma Abdallah kira kan wani kiran, duk da haka bata ga Sadiya ba sai ranar Alhamis, shima da kaya kala biyu a bakar leda, fuskarta kamar bata tabayin fara’a ba. Sai dai uwa dabance, kafin azahar harta sake suna kwasar dariyar wani fim din hausa da suke kallo, yau ita kanta Asaben zakaga saukin kadaici idan ka kalli fuskarta. Da yake Alhaji Salihu ba’a dakinta yake ba, har sha biyu saura basu kwanta ba daga ita har Sadiyyar, suna kallo suna hira, ga kayan ciye-ciye da ta baza musu. Bata hada kwanaki biyun ba, Asabe ta haska mata Sadiya wata rayuwa da bata taba mafarki ba balle ma tayi hasashen samu, ciki harda kwadaita mata samun shiga makarantar kudi kamar sauran yaran gidan, sai gashi ta tafi ta kwaso sauran kayanta tana yiwa Abida sallama, ko dawowar Abdallah bata jira ba.
Asabe ta dauka shikenan, Abdallah ne kawai, shima ko zai tsugunna Abida ta rika bi ta kanshi ba zai canzata daga matsayinta na mahaifiyarshi ba. Tana jin tunda Sadiya na kusa da ita, ga kuma Tahir da yake wanke mata zuciya ta hanyar kiranta duk safiyar duniya ya gaisheta da ita. Duk kuma juma’a tun bayan kammala makarantar shi sai yaje ya dubata, ba kuma zaije hannun shi na dukan cinyoyi ba, duk kuwa da yaga tana cikin wadata, ko da lemon zakine sai Tahir ya siya ya tafar mata dashi.
“Baki da wata matsala dai ko? Bakya bukatar komai?”
Baya gajiya wajen tambayarta, kamar in tana da matsala, ba zai nutsu ba saiya samo mata maganinta, kamar in tana bukatar wani abin zaiyi komai da yake karkashin ikon shi don ganin ya nemo mata abin nan. Tahir da yake kara tabbatar mata ko su hamsin ta haifa, arba’in da tara suka watsar da lamarinta, shi kadai din daya rage zai maye mata gurbinsu harma da doriya, shi kadai ba zai taba bari hawayenta su zuba ba, shi kadai ba zai taba gajiyawa da nuna mata muhimmanci a matsayinta na uwa ba. Koya ta tuno Abdallah na can yana bautawa Abida, idan ranta ya sosu, abu daya Tahir zaiyi, ya wanke mata zuciya tas, dan Abdallah, ta sallamawa Abida shi, ita da take da yaro kamar Tahir meye zai dameta?
Tahir da yazo ya zauna a kasa, saitin kafafuwanta yana neman ta saka masa albarka, babansu Bash ya samo musu aiki, duk da bakomai ta fahimta a bayanin ba, ta dai gane zai tafi can wajen da za’a horar dasu na tsayin wata shidda ne. Zuciyarta ta tsinke, ta kara tsinkewa da yace mata ba ko da yaushe zasu dinga samu suna magana ba, amman daya samu lokaci zai kirata, yace mata a Enugu wajen horarwar yake. Kallon shi tayi, sanyin shin nan yana kara bayyana. Sai taji so takeyi ta saka shi a daki ta kullo kofar ta zauna a bakinta tayi gadin shi har karshen rayuwar shi, kar wani abu ya taba mata shi, duk wahalar da take jin ana fada ana sha a wajen horarwar nan, zuciyarta taki kwantawa.
“Anya Tahir? Babu wani aikin sai na kaki? Naji ance horarwar akwai wahala.”
Murmushi yayi.
“Mama kiyi mun addu’a, ai FRSC ne, bai kai na sojoji wahala ba.”
Numfashi ta sauke.
“Allah ya tsare mun kai ya baka nasara.”
Murmushin ya sake kawata fuskarshi da shi, har bakin gate ta raka shi tana kara bin shi da addu’a. Duk da haka ran daren da zai tafi sai daya kara komawa yayi mata sallama.
“Ni da Bash ne Mama, nace bari in kara ganinki.”
Idan wani ta tambayeta, ya watanni shiddan nan suka zo suka wuce mata, abinda zata iya dorarwa ba mai yawa bane ba. Zancen duk da zatayi karshen shi zai kare ne da yanda tayi kewar danta kamar shi kadai ta haifa. Randa zai dawo kuwa, ita da kanta ba zata iya kirga yawan kiran da tayi masa ba. Tun satin take fadawa Alhaji Salihu zata fita unguwa, yace a kaita kamar ko da yaushe, bata damu da mamakin direban ba da tace tashar unguwa uku zasu je. Akan idanuwanta motar su Tahir ta tsaya, rungumar bazatan da yayi mata yana dagowa dauke da murmushi a fukarshi ya kauda mata tunanin duhu da kuma ramar da yayi. Babu komai a zuciyarta sai farin cikin sake ganin shi. Batare da ta hango Abida na can tana shirya yanda zata kwace mata shi ba.
Tabbas ta shammace ta, tunda bata hango ba, ko da Tahir ya tsugunna a gabanta, ba sabon abu bane ba, saida ya bude bakin shi da fadin.
“Bansan ta ina zan fara ba Mama, amman ina so in fara fada miki ne da kaina, za’aje tambayar aure na…”
Wani tsalle zuciyarta tayi, batasan murmushi ya kwace mata ba, duka yaushe ne take zancen a zuciyarta, idan ya kara natsuwa, zatayi masa maganar aure, tunda me yake jira? Gara ta ga auren shi tunda ranta.
“Alhamdulillah Tahir, kace da labari mai dadi kazo yau.”
Sai ya takaita mata farin cikinta.
“Sa’adatu ce Mama…”
Tayi kokarin mikewa, kamar yanda take gani a fina-finai idan aka fada maka wani labari daya girgizaka, saika mike tsaye, har wani kidan tashin hankali ake saki a bayan fage, sai dai ta kasa mikewar, babu kuma wani sauti bayan na bugun zuciyarta, dakyar ta iya bude baki, a tsakanin tashin hankalin da take ji ya rungumeta tace.
“Wacce Sa’adatun?”
Tana dora duka fatanta akan amsar da zai bata, ya kasance wata Sa’adatun daban, saiya tabbatar mata, yana rusa wani abu da bata san yana tsaye a tare da ita ba. Tun a lokacin kuma tayi masa tashin hankali, ta fadi maganganun da ko za’a tsareta ba zata iya maimaita su ba, saboda batajin tana cikin hayyacinta. Kanshi a kasa har tayi ta gama, hakuri kawai ya bata ya tashi ya fice. Ta dauka bayan mutuwar Habibu babu wani abu da zata sake yiwa kuka irin wannan, babu wani abu da zai shiga tsakaninta da baccin dare, yanda taga rana haka taga daren ranar, babu tunanin da batayi ba kafin wayewar gari, da ta tashi da kiran wayar Tahir ta fara sai ta jita a kashe. Ta zauna tana jiran ya kirata, dan ko karin safe ta kasa, Sadiya ma bata ko gaisheta ba, tayi shirin makaranta ta fice, tunda ta sameta tana risgar kuka taji dalili.
“To ai daman sun dade tare fa, tun kina gidan ma, Sa’adatu ce ba wata bare ba Mama, ke da zakiji dadi ma bai kwaso mana wata can ba.”
Bata san ta kai mata duka ba.
“Shanyayya marar zuciya da bata san ciwo na ba…”
Ta fadi tana dorawa da zaginta, ko da tabar mata wajen ma bata daina sirfa mata zagi ba. Tahir bai kirata ba, kuma yinin ranar duka wayar shi a kashe. Bata son ta kira Uwani, kafin ta tayata nemo mafita saita gaya mata maganar da zata fara kona mata zuciya. Karya tayiwa Alhaji Salihu na cewar matar Kawunta ba lafiya ta wuce gidan Abida, ta sameta a tsakar gida tana bare maggi, ko sallama batayi ba, dan daga kai Abida tayi tana kallon yanda Asaben take huci kamar kububuwa. Daman ta san za’a rina, babu yanda za’ayi Asabe tayi na’am da wannan auren, Allah ne shaidarta, babu kalar addu’ar nema musu zabin da zaifi zama alkhairi da batayi ba, ba kuma Tahir bane bata so, tijarar Asabe take tsoro.
“Bokanki yayi kadan Abida, wallahi wannan karin ke baki isa ba, Abdallah dana bar miki bai miki ba? Sauran yarana da kika shanye duka bai isa ba? Sai kin hada da Tahir? Ko babu mata a duniya gara in saka shi a gaba ina kallo da in barshi ya auri Sa’adatu…gara tun wuri, tun ba’aji kanmu a gari ba wannan maganar ta watse, wallahi, kinji na rantse, zan kuma kara rantse miki Abida, wallahi baki isa ba, kome zai faru sai dai ya faru, amman wannan auren ba mai yiwuwa bane ba”
Bata fasa bare magginta ba, duk da itama mamakin hannuwanta da basa rawa takeyi, har Asabe ta kare tijararta, tana da yakinin har makota suna jinta, danma gidan babu kowa, duk sun tafi makaranta, daman ita da Fa’iza ne, to itama ta fita kasuwa, Asabe na fita ta sauke numfashi, zuciyarta sai bugawa takeyi, lokaci daya taji hawaye ya cika mata idanuwa, ta sa hannu ta dauke su, amman kamar ta bama wasu kofar fitowa. Da daddare taja Sa’adatu daki, taso ta fahimceta, batama bari ta karasa maganar da ta fara ba ta katse ta da
“Mama tazo gidan nan ko? Ai Yaa Tahir yace mun zaije ya fada mata za’azo tambayar aure, daman nasan wallahi sai tazo gidan nan tace zatayi rashin mutunci, dan Allah Amma karki ma saka zancenta a ranki, ita bata isa ta hanani auren Yaa Tahir ba…”
Wannan dalilin ne yasa tun dazun take godewa Allah tana karawa da Asabe bata sami Sa’adatu a gidan ba, tasan halin Sa’adatu, ba zata duba matsayin Asabe da ya sauya a wajenta ba, ajiye komai zatayi a gefe ta biye mata. Sai dai in kasheta zatayi daga baya ta kasheta
“Ni dai tashin hankali ne bana so Sa’adatu…”
Kai Sa’adatu take girgiza mata
“Dan Allah Amma kiyi mana addu’a kawai…dan Allah, in ba shi Yaa Tahir din bane yace ya fasa ni hargagin Mama ba zai dameni ba.”
Ta karasa maganar tana mikewa ta fice daga dakin batare data bari Abida tace mata ta gama magana ko bata gama ba.
Wata daya
Wata biyu
Wata uku
Wata hudu
Wata biyar
Wata shidda…
Tasan rayuwa guda daya ce, rukuni gareta kala-kala, a shekarunta kuma tana tunanin idan aka tambayi Sa’adatu zatace a cikin wannan rukunnan rayuwar, ta san rayuwa kafin Tahir, ta san rayuwa tare da Tahir, har sai tayi da gaske take iya tuna wata rayuwa da tayi batare dashi ba. Yayi mata wani irin sabo da bata fahimci girman da yayi ba sai da yazo yi mata sallama, ta kafe kanta a kasa tana kallon abinda ba zatace gashi ba.
“Sa’adan Tahir”
Ya kira a tausashe, wani suna daya makala mata, wani suna da duk idan ya fada tasan maganar da zata biyo bayanshi mai muhimmancin ce, wani suna daya kira yau yana jera kalaman da taji suna dafata a inda take tsaye.
“Kiyi mun magana mana, daga yau fa zuwa gobe idan Allah ya kaimu, idan naji muryarki bansan yaushe zan kara samun dama ba…”
Babu wani yunkuri da tayi, tabar hawayen da suke tayi mata barazana zubowa, kafin ta daga kai tana sauke idanuwanta akan fuskar shi, tana so yaga duk wata tambaya da take yawo a cikin zuciyarta. Ta ina zata fara? Tashi muryar kuma fa? Muryar da bayan ringing din wayar da yakan tasheta daga bacci duk safiya, ringing din da yana katsewa ta daga wayarne ta kara a kunne, muryar shi ce zata dirar mata, kafin kiran sallar asuba, shine kararrawarta.
“Sa’adatu…”
Ya kan kira cikin muryar shi.
“Yaa Tahir, na tashi…”
Shine amsarta, kuma tasan muryarta na isa kunnen shine dauke da baccin da bai gama sakinta ba.
“Kiyi mana addu’a…bari in karasa masallaci.”
Ba kullum yake jira ta sake cewa wani abu ba yake yanke kiran, kafin kuma ta tafi makaranta, karfe bakwai idan bai sake kira ba, bakwai da kwata saiya kirata, ya jaddada mata tayi addu’a kafin ta fita daga gida. Zai wahala ka yini da Tahir baka fahimci yanda yake ba addini muhimmanci ba, tunda ta san shi, doguwar magana ta fara hadasu, idan zasuyi tsayuwar minti biyar, a lokacin da ita take amsa shi zata ga labbanshi sun motsa, kamar yayi magana a kasan numfashin shi da sautin daya tsaya a zuciyar shi kawai, ko waya sukeyi kuma zata ji yanayin yanda ya sauke numfashi kamar yayi magana, sai da sukayi sabon da zata iya tambayar shine yace mata.
“Yafiyar Allah nake nema Sa’adatu.”
Da ta kula kuma sai taga motsin labbanshi.
“Astagfirullah”
Shine abinda yake fada.
“Kinga lokacin tafiya yakeyi, tare da kwanakin da aka rubuta mana, shisa na sabawa kaina neman yafiyar Allah, kar ya wuce ban rabauta da komai ba.”
Kwana wajen hudu ta jera itama tana gwadawa, a tunaninta zata iya sabawa a kwana biyu ma, sai taga ba karamin wahala bane ba, tunda in tayi shiru tunani ne yake maye mata gurbin magana, in kuma ta bude bakinta hira zasuyi da Fa’iza ko da wani dai, kara lokacin wata ibadar da bata zama wajibi ba abune mai matukar wahala, kai zai amfana, tun a duniya ma, kafin kuma aje lahira, amman abune mai wahala, sai dai idan ta tuna, abin ya fado mata a rai, zatayi ta neman yafiyar Allah, da ta manta kuma shikenan.
“Kince mun fa ba zaki sakeyin kuka ba…”
Tahir ya fadi cikin wata murya da ta kara fito da hawayenta.
“Dana dawo maganar auren mu za’ayi, ko kin manta? Kullum zaki dinga ganina sai kingaji…”
Murmushi ya kubce mata duk da hawayen da basu daina zubowa ba.
“Kuma da na samu dama zan kiraki, calendar din dana kawo miki jiya zaki dinga duba mana ke dai, kullum ki soke rana daya, sai kiga har sunzo, ga kuma jarabawar ku ma, kinga tsakanin karatu, zuwa makaranta, aikin gida, da soke mana ranaku a jikin calendar, dan wanda zai rage na kewata bashi da yawa…ni ya kamata ma in fiki damuwa.”
Murmushi tayi sosai, da Fa’iza take ce mata.
“Ni ba zan biye miki ba, dan baki san so ba.”
A lokacin gani take duk zance ne, menene so din? Bayan wanda take yiwa kanta, bayan kuma son samawa kanta rayuwar hutu da jin dadi, sai kuma soyayyar iyaye data ‘yan uwa. Babu wani so bayan wannan, ko aure ma baizo mata a layin so ba, a mataki zata ajiye shi, matakin da take fatan ya zame mata tsanin da zata cimma jin dadi. Sai Tahir ya leka kanshi cikin nata kan, ya saka baki ya bushe duk wani tsarinta, ya bar filin sannan ya fito, ya fara dorata akan wani tsarin tare dashi a ciki. Sai matakin auren ya canza a wajenta, daga hanyar da zata cimma muradinta na samun rayuwar hutu zuwa hanyar da zata sakata raba sauran kwanakinta tare da Tahir, sannan sauran abubuwan su biyo bayan wannan.
Haka ya bita da kalaman shi, har saida ta saka hannu ta goge hawayenta. Bai bar kofar gidansu ba saida yaga tanata dariya tukunna. Ko a waya har ya sauka Enugu, duk maganar da zasuyi karshenta da dariya sukeyin sallama. Yace mata zai kirata daya kara bakin kofar camp din kafin su shiga sai suyi sallama, bai kira ba, sako ya tura mata.
“Zanyi kewarki da yawa Sa’adatu, nayi sallama da kowa, amman dana tuna harda ke a cikin mutanen da ba zan gani ba tsayin wata shiddan nan sai inji zuciyata ta karye. Ina son ki, ba zanyi karya ba idan nace tun daga ranar dana fara ganinki a cikin gidanku zuciyata ta fara doka miki. Nayi ta ririta soyayyar ne ina jiran lokacin da zai dace in bayyana miki, inajin da na fada miki da wuri, wannan kusancin da muka gina a tsakanin mu, dana kara samun na wasu lokutta, watakila daya rage mun girman filin nan da nake ji na rashin ki da zanyi…”
Numfashin da take rike dashi tun fara karanta sakon ta saki tana sake jan wani tare da wata iska da taji ta ratsa ko ina na jikinta.
“Idan na kiraki kuka zakiyi, bana son ace ba zan iya sake magana dake ba sai bayan wata shidda, kuma kukanki ya zamana abu na karshe da kunnuwana zasuji, gara idan na rufe idanuwana inji dariyarki ta dazun…”
Kukan ne kuwa ya kwace mata.
“Ba zance ki kulamun da kanki ba, saboda na roki Allah ya kulamun dake, ya kare mun ke, ya kuma dauke idanuwan maza daga kan matata. Zan kuma cigaba dayi kullum, I know you will be fine Sa’adan Tahir. Sai Allah ya dawo dani, ina son ki…sosai.”
Gabaki daya ta zama wata iri, kamar ba ita ba, akan Tahir, daman wannan ne son? Soyayyar kenan? Ka susuce, komai ya kwance maka, ka sauka daga kan duk wani abu da ka sani ka sani kamar ba abu bane mai wahala, sai ka koma kan sabon tsarin da soyayya ta shimfida maka kace zaka sauka daga kai zaka gane wahalar da take cikin hakan. Ko abincin dare bata iya ci ba ranar, har karfe sha daya tana gwada wayar Tahir amman a kashe take, ta san a kashen zata jita, kawai da sun fara surutunsu kuka yake kara kwace mata. Da asuba ma data bude ido dai-dai lokacin daya saba kiranta, wayarta ta janyo kamar tana son duba dalilin daya sa bai kirata ba, saita tuna, hawaye masu zafi suka cika mata idanuwa.
Bata taba tunanin akwai ranar da zata zo taga nama, nama ya ganta, bataji zuciyarta tayi mata fari kal ba sai a tsakanin watannin nan, duk wani abu da take so, shi Abdallah yake kokarin ganin ya samu ya siyo mata.
“Kanwata bana son wannan rashin walwalwar taki…”
Murmushi kawai ta iya yi masa, duka duniyar takejin batayi mata dadi, har tayin zuwa asibiti yayi mata, saboda yaga tayi zuru-zuru. Damuwar da take gani a tare dashine yasa da taji ya shigo gidan take aro walwala ta dora akan fuskarta. Ta jashi da hira kamar yanda suka saba. Amman ita kadai tasan halin da zuciyarta take ciki, sai da taji kamar ba zata kai watannin nan ba, lokaci ma daina ganin saurin shi tayi.
“Sa’adan Tahir.”
Shine abinda ya fara fadi bayan ta fita, ko takalmi sai daga baya ta kula wari daya nata ne daya silipas din Abdallah. Hijabin ma ba sakawa tayi ba, yafashi tayi,dan ba wayarta ya kira ba, aike yayi.
“Ance Sa’adatu tazo inji Tahir.”
Dan aiken kuwa a wani waje hanyar fita tayi karo dashi, ta hankade shi gefe ta riga shi fita tana sauke numfashi kamar tayi tseren gudu, sai dai maimakon ta amsa shi, kuka saiya kwace mata, kafafuwanta na kasa daukarta, tsugunnawa kawai tayi a wajen tana sakin wani kuka tare da duk wata kewarshi da tayi, yana tsaye yana kallonta, har saida ta tsagaita da kanta, ta goge fuskarta ta dago sannan yace,
“Nima nayi kewarki…da yawa.”
Randa ta fara ganin shi, bata san zata so shi ba.
Da ta fara son shi, bata hango zata daina don wani dalili ba
Kaddara ce ta miko mata Tahir, tasa hannu ta karba
Ita da kaddara kuma sunfi karfin Asabe da hargaginta…
Allah ya yafe miki kurakuran ki ya gafarta wa iyaye ya baki zuri’a Dayyaba