Skip to content
Part 13 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

“Fa’iza…”

Ta dauka hawayenta sun gama karewa, ta dauka a kowacce rana akwai wani adadi na hawaye da ake dibarwa kowa, kukan da tayi a ranar kuma, daga wayewar gari zuwa daren ya kamata ace hawayenta sun gama karewa. Yanzun kuma daya kira sunanta, cikin sigar nan dashi kadai yakeyi, ya kirata yana saka duk wasu sirrika da baisan yanda zai furta mata su ba, saiya sakata tunanin ko dai wannnan adadin hawayen na kowacce rana idan baka zubar dasu ba, wani waje suke samu su zauna, sai a ranaku irin yau din su tabbatar da hawayen zubarwa bai yanke maka ba

“Ko auren ‘yar uwarki da na samu isashen lokacin shirya masa, zuciyata bata natsu dashi kamar naki ba Fa’iza. Ina da tabbacin kina hannu nagari…”

Wasu a cikin maganganun Furaira suka dawo mata. Da Abdallah ya saka hannunshi ya riko nata, bugun zuciyarta ya karu kuma sai takejin da gaske akwai mutuwar da take zame maka alkhairi. Bata dai taba zaton irin wannan mutuwar zata gifta ta kaddararta ba, mutuwar Alhaji Nura, ba saninshi tayi ba, duk yanda Sa’adatu ta dinga kwatanta mata shi, duk kuma yanda ta laluba cikin kanta ta kasa samo fuskar Alhaji Nura

“Zaki ganshi Dattijo sosai, da farin gemu, muna fa wuce shi wani lokacin idan zamu Islamiyya, wanda in dai muka gaishe shi zaki ji ya amsa yana dorawa da Allah yayi albarka ya kara hasken ilimi?”

Ta tuna addu’ar, fuskar shi ta kasa tunawa, dan kallon mutane ba dabi’arta bane ba. Kallon mutanen ma gabaki daya, zata iya daga ido ta kalleka, amman in zaka tambayeta abu daya data kula dashi a tare da kai lokacin data kallekan zai wahala ta iya fadar guda daya. Abdallah ne mutum na farko data daga ido ta kalla, dukanshi ya samu wajen zama a tare da ita

“Abida tayi mun magana an bamu notis na wata uku, ko zamu sake kama wani gidan tare idan ina so. To daman Ladidi tana tayi mun maganar mu koma can Legas da zama, saboda Sakina ne nake ta kaucewa maganar…”

Wata irin bugawa zuciyar Fa’iza tayi, karar na toshe mata sauran maganganun da Furaira takeyi. Su koma Legas? Abdallah fa? Soyayyar da takeyi masa fa? Shikenan? Fatanta na ya waiwayeta wata rana ya ruguje?

“…Fa’iza…”

Taji muryar Furaira bayan ta tabata

“Kuka kikeyi? Menene? Komawa Legas dinne bakyaso?”

Hannu ta saka ta share hawayenta tana girgizawa Furaira kai a hankali, ganin yanda jikinta yayi sanyi. Fa’iza ta sani, wahalar duniya mahaifiyarsu ta sha dan ganin rayuwarsu ta inganta. Lokacin da iyaye da yawa suke dorawa yaransu talla don neman mafita, ita da kanta take fita tallar su ta turasu makaranta, ba zata manta Sakina data taba ce mata

“Ayya da kin dinga zama idan muka dawo makaranta mu sai mu fita, ki dinga hutawa dan Allah”

Dariya tayi, amman karancin shekaru bai hana Fa’iza ganin ciwon da yake cikin idanuwan Furairar ba

“Hutu Sakina? Ai hutuna ya kare daga ranar da kasa ta rufe idanuwan Abbanku, kawai dai ina da zabin da iyaye da yawa da suke dorawa yaransu talla basu dashi, ina da ‘yancin da zan fita a madadinku…”

Kuma komin gajiyar da zata kwaso, sai sunyi hira take kwanciya, sai ta tabbatar a cikin babu mai wata matsala, abu idan zasu nuna suna so, idan har baifi karfinta ba sai tayi musu. Yanda ta sake dasu, ta zama kamar wata kawarsu yasa komai fada mata sukeyi. Ko Abdallah abinda yasa Fa’iza ta kasa fada mata, dan tana ganin ita kadai take kidanta tana rawarta, da yace yana sonta da tuni ta fada, da yanzun tayi amfani da soyayyar da sukeyiwa juna wajen zame mata hujjar kin son komawa Legas. Yanzun idan ta bude bakinta ma me zatace? Su zauna ko zai dubeta wata rana? Ko da ta kwanta ma bata nemi bacci ba, dan tasan ba zai taba bata hadin kai ba, ta rufe idanuwanta ne tana barin fuskar Abdallah da takeyi mata yawo ta tayata hira har lokacin da ta saba tashi danyin sallolinta yayi kafin ta raba jikinta da katifar.

“Kinga yanda idanuwanki sukayi zuru-zuru? Baki da lafiya ne?”

Sa’adatu ta tambayeta tana kokarin hada idanuwa da ita, kamar zata iya ganin gaskiyar abinda yake damunta a cikin idanuwan

“Ke yanzun har kina iya ganin ramar da wani yayi?”

Sai Sa’adatu tayi ‘yar dariyar da Fa’iza tasan ta karfin hali ce kawai, kokari take da dukkan zuciyarta taga ta fara dawowa dai-dai, matsalar itace duk wani lalube da takeyi ta manta shi dai-dai din yanda yake, yanda ake jinshi, neman ranakun da ta taba tashi babu wani ciwo a cikin zuciyarta takeyi ta manta, yanda inta fitar da iska ta shaki wata batajin wani abu na rabewa a cikin kirjinta. Ranakun nan da bacci yake zame mata hutu ba wani abin tashin hankali ba saboda mafarkan Tahir, ta farka zufa ta jiketa kamar an kwara mata ruwa, numfashinta yana sama cike da barazanar daukewa, ko ta bude bakinta dan tayi gunjin kuka ko zata samu sauki, babu sautin da yake fitowa, sai wasu hawaye, batama sanin jikinta na bari wani lokacin sai taji Fa’iza ta dafata tana tofa mata addu’o’i.

Da rana kome zatayi tanajin Tahir a duk fitar numfashinta, abinda takeji akanshi ne a yanzun bata sani ba.

“Wayarki na wajena”

Abdallah yace mata, sai kawai ta daga masa kai dan ita har ranta ta manta da wata waya, dan bata ita takeyi ba, idan ta kunna me zatayi da ita? Tunda idan ta fito anyi aiki da ita, tayi kokarin yin hira, data koma daki banda kwanciya babu abinda take so tayi da rayuwarta har yanzun. Ta dai dauka ta gama kuka a gaban kowa, sai da ta fito da nufin zuwa wajen Abida, kafin ma ta taba labulen dakin da sallama, maganar Abdallah ta mantar da ita abinda tazo tambayar Abidar

“Kwanan shi biyu yau a unguwar nan Amma, a masallaci yake kwana inajin, yaki tafiya, nayi-nayi yaki tafiya, kinga babu abinda ban ayyana a raina ba, yanda zan manta shekarun da suke tsakaninmu idan na ganshi…ba dan yana dan uwana ba, Amma ina ganin shi, ina ganin yanda ya koma naji hawaye nayi min barazana…”

Abdallah ya karasa muryarshi na karyewa

“Idan na barshi ya ganta me zaice mata? Duka maganganun shi ba zasu canza komai ba…kar ganin shi…”

Bata bari ya karasa maganar ba ta ganta a tsakiyar dakin

“Yaa Tahir ne? Shine yazo?”

Kai Abdallah ya daga mata

“Yana waje?”

Kan dai ya sake daga mata, saita juya, ko mayafi batayi tunani ba ballantana takalmi, Abdallah yayi nufin bin bayanta, Abida ta hanashi, duka tausayi suke bata, zatayi karya kuma idan tace har yanzun kaddararsu bata saka hawaye zubo mata. Kofar gidan ta karasa, yana tsugunne a gefe ya hade kanshi da gwiwa, bata fita gabaki daya ba, bata kuma san ya akayi yaji tsayuwarta ba, ya daga kai dai, kafin yayi wata irin mikewa yana tsayawa a gabanta, kallonta yakeyi, idanuwanshi cikin nata. Bata taba jurewa kallon idanuwanshi irin haka ba, kamar yanda bata san ta hade girarta waje daya cike da taraddadi ba, idanuwanshi ne, amman kuma ba nashi bane a lokaci daya. Kamar yanda data kalli fuskarshi ta ga shine a idanuwanta, amman kuma bashi bane a zuciyarta. Ya canza fiye da ramar da idanuwa zasu iya gani

“Sa’adatu… Sa’adan…”

Sai ya kasa karasawa, ya sadda kanshi kasa, ya sake dagawa yana kallon Sa’adatun da gashi a gabanta amman idanuwanta sun nuna neman shi takeyi

“Sa’adatu…”

Ya kira muryarshi na sauka can kasa

“Duk wata tambaya da nake da ita ta bace mun, gaka a gabana Yaa Tahir amman me yasa babu abinda nake so in tambayeka sai inda kake? Ko kafin in furta tambayar batayi mun ma’ana ba, kaga dana furta sai ta sake hargitse mun… where are you?”

Ta karasa da turanci ko zaifi fahimtar abinda take son tambayar shi, ko ita da kanta zata gane abinda take so ta tambaye shi

“Bansani ba, bansani ba Sa’adatu, watakila ina tare dake din dana raba da kaina…bansani ba, numfashi nake babu gargada, gani da alamar rai a jikina amman banajin rayuwa tare dani…”

Kai ta jinjina tanajin ta fahimce shi, ta fahimci duk wata kalma daya fadi, sai dai fahimtar ta saukar mata da wata irin gajiya marar misaltuwa

“Shikenan ko? Ni da kai…shikenan ko?”

Ta tambaya da wani nisantaccen yanayi a muryarta, tana ganin yanda yayi da fuska kamar taji masa ciwo da makami

“Ina so in tafi ne, in ganki kafin in tafin, kinga yanzun dana ganki sai nakejin babu wata sauran tazara da zan saka a tsakaninmu fiye da wadda nayi…”

Numfashi taja ta sauke tana sake jan wani ta sauke shi da fadin

“Kaje kawai, ka tafi Yaa Tahir, Allah ya sama maka sauki a tafiyar”

Saiya jinjina mata kai, ta ina zata fara jin haushin shi bayan ya koma haka? Taya zata ga laifinshi bayan tuhumar da yakeyi ma kanshi tayi girman data kashe hasken da bata taba ganin idanuwanshi babu shi ba, wacce tambaya zatayi masa kuma? Sun nemi sauki, sun samu sauki a tare da juna na dare daya kawai, yanzun kuma ya zame musu dole su nemi sauki batare da juna ba. Yanda duk take cikin kunci, yanda ta dauka kaddara da ta gama wasan kura da ita jefota tayi a maimakon ta ajiyeta a hankali, Tahir bata ga alamar kaddarar ta jefar dashi ba har yanzun balle ya numfasa ko yaya ne

“Nagode…Nagode da komai. Ina maka fatan alkhairi Yaa Tahir”

Wani abu yayi da fuska da yake kama da kwatanta murmushi

“Bankwana kike mun ko Sa’adatu?”

Sai ta dan daga kafadunta, hawaye na zubo mata

“Meya rage?”

Ta tambaya, kai ya girgiza yana hadiye wani abu da yake jin yafi karfin makoshin shi. Ya saka hannuwan shi duka biyun yana rufe fuskar shi, idan kuma Sa’adatu ba zatayi karya ba zatace tana juyo hucin fitar numfashin shi, kafin ya sauke hannuwan yana kallonta, idanuwan shi sunyi mata wani irin wayam fiye da dazun, a hankali ya furta

“Babu…nima nagode”

Juya zatayi yayi saurin fadin

“Bari in fara tafiya…dan Allah”

Sai ta daga masa kai, tana kallo ya juya, duk wani taku na kara nisanta mata shi daga zuciyarta, ta rasa nisa yayi mata ko hawayenta ne suka dishe mata ganin shi da wuri. Ta saka hannu ta goge tanajin yanda da gaske komai ya kare, kamar daman zuwan Tahir din take jira ya tabbatar mata da karewar komai. Da ta shiga gida, Abdallah ta samu a tsakar gida sai kai kawo yakeyi, yana ganinta yayi saurin karasowa inda take, saita kauce masa, taje ta dauki buta ta wanke fuskarta, sannan ta dawo

“Sa’adatu…”

Ya kira, tasan kome yake son fada mai muhimmanci ne tunda ya kira sunanta

“Komai ya wuce fa Yayaa…na maka alkawari komai ya wuce daga yau. Ina wayata?”

Daman kalaman da yake son fadi din sunki haduwa, ko da yake ta juyasu, karshen su tambayar ko tana lafiya ne sai kuma karfafa mata gwiwa kan cewa komai zaiyi dai-dai. Kallonta yakeyi kamar bai yarda da ita ba, sai tayi dariya

“Baka yarda dani bane Yaa Abdallah…kasan ko zanyiwa kowa karya banda kai”

Numfashi ya sauke yana jinjina kai, ya yarda da wannan, tun tasowarta, ko barna tayi aka titsiyeta tace ba ita bace, shi idan ya tambaya zata fada masa ita dince, tana kara girma tana kara gina wannan gaskiyar a tsakaninsu. Ko ta boyewa kowa banda shi ya sani

“Komai ya wuce…Kuka, damuwa, babu wani abu da zai canza wannan kaddarar Yayaa…”

Kai ya jinjina mata

“Damuwarki ce bana so daman…”

Dariya ta sakeyi

“To ai na daina damuwar In shaa Allah”

Kai ya sake jinjinawa, ko dan ya kwana biyu baiji dariyarta bane shisa yake jin sautin yayi masa wani iri. Tafiya yayi ya dauko wayar daga daki ya mika mata, data karba saita budeta tana ciro batirin sannan ta zare sim din ta mika masa

“Ka siyomun sabo…”

Karba yayi

“Zan taho miki dashi In shaa Allah…”

Bata amsa shi ba ta wuce dakinsu

“Fa’iza ana goge account din Facebook a sake wani sabo kuwa?”

Kai Fa’iza ta daga mata

“Sosai ma…”

Sai ta zauna

“Yawwa, anjima zamu goge tsohon nawa in sake bude wani…”

Da idanuwa Fa’iza take binta ganin sauyin da yake tare da ita yau din. Sauyin da su duka sukaki yarda dashi daga farko, sai da sukaga wannan ramar da tayi ta fara bacewa, dan Abida sai da tace zatayi tuwo taji Sa’adatu tace

“Tuwo kuma Amma? Mai da yaji mukaci fa da rana, ni wallahi bana cin tuwo, dari zaki bani a siyomun indomie in dafa…”

Tukunna ta yadda ko da Sa’adatu bata dawo dai-dai gabaki daya ba, to ta fara. Sai dai yau kallonta Fa’iza takeyi tana mamakin karfin hali irin nata, ba zatace bata jinjinawa kokarin Sa’adatu ba. Yau dai da inta tuna zatayi nisa da Abdallah taji kamar ana kokarin zare wani zare da yake nannade da tsokar zuciyarta, sai taji tana so taje ta kama hannun Sa’adatu taja ta daki tace tambayeta inda ta samo karfin halin cigaba da rayuwa bayan Tahir ya barta. Ita fa bama wata soyayya sukeyi da Abdallah ba amman tanajin kamar karshen duniyarta yazo. Da Abdallah ya shigo sai tayi saurin wucewa daki ko gaishe dashi batayi ba, saboda bata yarda da kanta ba  ko kadan. Shikuwa daya gama gaisawa da Abida, aka zuba masa abin karin kumallo, yana ci idanuwan shi na neman Fa’iza a tsakar gidan, harya gama jan jikin shi bata fito ba, dole ya tashi ya tafi.

Daga makaranta kuma saiya wuce gareji saboda tun yana makarantar ake kiran shi. Shisa sai dare ya koma gida, ruwa ya fara watsawa kafin ma ya nemi abinci, ga wata gajiya da yake ji har cikin kasusuwan jikin shi, da yaci abincin ya gama ya fitar da kwanonin ne Abida ta kirashi

“Gidan ka samar mana madaidaici da zamu iya zama mu kadai…”

Bai barta ta sauke maganar ba ya tare da fadin

“Su Fa’iza fa?”

Kallonshi takeyi, yanda duk ya rikice, shisa ta kasa gaya masa da safe

“Tace tana tunanin zasu koma Legas…”

Abincin da ya gama ci yake tunanin ya natsa masa ne yaji yana hautsinawa tare da barazanar dawowa

“Legas? Su duka? Harda Fa’iza? Ni kuma fa? Ya zanyi kenan Amma? Idan ta tafi ya zanyi?”

Tambayoyin suka kwace masa batare daya san a fili yake furtasu ba, mikewa yayi ya fice daga dakin, Abida ta bishi da kallo, ita kuma yaranta har biyu soyayya ce kaddararsu. Kofar dakinsu ya tsaya ya kai hannu da nufin kwankwasawa, sai ga Sa’adatu ta fito, shayine Fa’iza ta dafa musu, ta fito daukar cokali

“Yaa Abdallah…”

Ta kira da mamaki

“Ina Fa’iza?”

Yace mata, sai ta dan kalli dakin batare da ta amsa mishi ba

“Fa’iza…”

Ya kira yana sa shayin Fa’iza ta kurba bin wata hanyar daban, tari ta soma yi, tana mikewa, da hijabin da tayi isha’i a jikinta bata cire shi ba, kafin ta karaso Sa’adatu ta koma cikin dakin, ita kuma ta fito tana samun shi tsaye a bakin kofar. Tarin da takeyi ta nema ta rasa lokaci daya, kafin wata shakkuwa ta maye mata gurbin tarin lokacin da Abdallah ya kama hannunta yana soma janta, saida sukaje soron gidan da yake haske da kwan lantarki tukunna ya tsaya, har lokacin yana rike da dantsen hannunta, inda takejin dumin nashi hannun yana ratsa ko’ina na jikinta

“Legas zaku koma? Me yasa? Ni kuma fa?”

Yake tambaya yana saka idanuwanshi da suke dauke da wani maiko daya girmi na hawaye a cikin nata, ta ga bangarori da yawa nashi, har kuka ta ganshi yanayi, sai dai bata taba ganin wannan bangaren ba, tsaye yake a gabanta kamar dan karamin yaron da ake son kwacewa abu mafi muhimmanci a rayuwar shi, tsaye yake ta bude mata wani abu da takejin inta tsaya kare masa kallo zata nutse a cikin shi

“Yaa Abdallah…”

Kai yake girgizawa, ba sunanshi yake so yaji a bakinta ba

“Dan bance ina sonki bane zaki tafi? Bani da komai ne Fa’iza shisa, idan nace ina sonki inda kalmar zata kaimu nake hange da nisa sosai, ina rike da kafadun Amma har yanzun, ban tsaya da kafafuwana ba, idan na saketa nace in rike ki faduwa zamuyi tare…”

Runtsa idanuwanta tayi saboda yanda ya kara karfin rikon da yayi mata kamar zai karyata, duk yanda ake fadin karamin jikin da take dashi ita bata cika gani ba, amman yanzun a gaban Abdallah ji takeyi ta kara kankancewa, kalamanshi kuma nema suke su batar da ita gabaki daya

“Dan Allah karki tafi…karkiyi mun nisa, ba zan iya jurewa ba”

Saita tsinci kanta da daga masa kai, dayi masa alkawarin da batasan yanda zata iya cika masa shi ba, tana ganin ya sauke wani numfashi, ya runtsa idanuwanshi ya bude su yana sake sauke numfashi, kafin ya daga mata kai yana sakin hannunta ya fice daga gidan gabaki daya. Data koma sai ta tsinci kafafuwanta a dakin Furaira da take zaune tana cin abinci

“Ayya…”

Ta kira muryarta na rawa

“Dan Allah karmu koma Legas”

Kallonta Furaira tayi

“Nasan bakyason tafiyar, kin daiki fadamun dalili ne”

Wani abu ta hadiye tana tattaro duk wani karfin hali

“Saboda Yaa Abdallah…”

Da mamaki Furaira take kallonta wannan karin

“Abdallah dai? Yaron nan gidan?”

Kai Fa’iza ta daga mata cike da fargaba, sai Furaira ta hasketa da wani kayataccen murmushi. Allah ne shaidarta, ko auren yaranta biyu da fargaba tayi musu shi. Gara ma Ladidi, iyayen mijin duk sun rasu, ‘yan uwanshi kuma duka maza ne, su da nasu iyalin suna nan arewa, shikuma yana kudu. Babu wani wanda ya daga maganar rashin danginta, amman Sakina duk da bata fada tasan dangin mijin ba sonta sukeyi ba, mahaifin yaron ne daya tsaya ya goya masa baya har aka samu akayi auren, kuma sai da suka ga ya kara aure sannan hankalinsu ya kwanta. Duk dare kuwa da tunanin inda Fa’iza da Asma zasu fada takeyi. Musamman Fa’iza da sanyinta da kawaici, idan bata shiga hannun nagari ba rayuwarta zata tagayyara.

Amman Abdallah, tasan ba Abida ta haifeshi ba, amman yanzun din bashida wata uwa data wuceta, kuma Abida surika ce da kowa zaiyiwa yaranshi fatan samu

“Fa’iza ai da kin fadamun, in dai Abdallah ne ko yanzun ya shirya zan bashi ke”

Wata kunyace ta rufe Fa’iza, da gudu ta fice daga dakin, zuciyarta na wata irin bugawa, ko da ta koma dakinsu ma kwanciya tayi tana jin jikinta har rawa yakeyi, kamar farin cikin da take ciki yafi karfin daukarta. Daga wannan daren zuwa kwanakin da suka wuce bayan shi, wasu kwanaki da suka bace a lissafin Fa’iza, saboda babu komai a cikin tunaninta daya wuce kalaman Abdallah da take ta juyawa tana kara juyawa, a cikin kwanakin ne Furaira da Abida sukayi magana

“Idan nace miki nafi kowa maraba da wannan hadin ba lallai bane ki yarda Furaira. Abdallah yarone nagari mai kyakkawar zuciya, ance karka cika baki akan dan yau, ni kam bani da haufi akan Abdallah, ina da yakinin zai rike miki Fa’iza da amana. Sai dai dan makaranta ne yanzun, banda garejin da yake zuwa, bashi da wata hanya ta samun kudi…shisa ba zanso kaina ba ince ta jirashi alhalin bai shirya ba…”

Murmushi Furaira tayi

“Nasani Abida…ni inda za’a rikemun Fa’iza nake so, in dai zai rikemun ita da dukkan zuciyar shi, na bashi Fa’iza, ya hada iya abinda Allah ya hore masa na Sadaki, inda zasu zauna, in dai sana’ar shi zata isa suci abinci yazo a daura musu aure”

Wasu hawaye ne suka ciko idanuwan Abida, tasan Abdallah da zurfin ciki, da kuma kunya, amman a kwanakin nan idan ya shigo cikin gidan, idanuwanshi basa gajiya da yawon neman Fa’iza, daman ita Fa’izar ba tun yanzun ta kula da son da takeyiwa Abdallah ba, yanzun haka Fa’iza ta daina sakewa da ita. Ko da Abida ta fadawa Abdallah yanda sukayi da Furaira kanshi ya sunkuyar kasa

“Amma anya kuwa? Inajin tsoro…yanzun duka haukan soyayya ne yake dibarmu, kar zama yayi zama ta kasa hakuri da yanayin rayuwar da zamu iya tsintar kanmu a ciki…talauci ba kaddara bace mai sauki…”

Ta fahimce shi, shisa tace masa

“Kayi magana da ita Fa’izar dai”

Bai kuwa jira ta kara wani abu akai ba ya mike yana kiran Fa’iza, tayi masa kyau cikin hijabinta kalar ruwan kasa mai duhu, sai yaji babu abinda yake so saiya roketa ta aure shi da talaucin shi dan ba zai iya jure rashinta ba

“Ina sonki, na fada miki ko?”

Kai ta daga masa a kunyace

“Har abada wata tafiya ce mai nisa Fa’iza, bani da komai, karatun nan, idan na kammala banda tabbacin wani aiki daya wuce koyarwa idan Allah ya sa ina da rabo, duk idan na hanga bana ganin zan sama miki rayuwar da ba zaki nemi komai ki rasa ba…ko da nace ki jirani in sami aiki, samuna dai lallabashi zamuyi, ba zamu taba fin karfin bukatun yau da kullum ba…ga kannai ina dasu, ga Amma, ko aure sukayi in dai suna cikin bukata suna da kaso a duk samuna Fa’iza…”

Numfashi yaja, kafin ya cigaba ta katse shi da.

“Zaka kula dani?”

Kai ya daga mata

“Zaka rikeni da amana?”

Kan ya sake daga mata, wannan karin ita ta sauke numfashi

“To muyi addu’a, Allah ya rufa mana asiri mufi karfin abinda zamuci yau da gobe, idan rashin lafiya ta gifta mana ya hore mana halin abin jinya… Ka kula dani dai-dai karfin ka, ba zan tabayin korafi ba”

Kallonta yake kamar yana neman tabbatar da gaskiyar kalamanta

“In nemi aurenki?”

Kai ta daga masa

“Duk da bani da komai?”

Kai ta sake daga masa

“Ina sonki ne fa karshen kalaman soyayyar da nakejin na iya…kin tabbata zaki iya zama dani a haka?”

Dariya tayi a hankali, sautinta na nutsar masa da duk wani abu da tunanin nisa da ita ya daga masa

“Nagode… Nagode Fa’iza”

Ya fadi a fili, a zuciyarshi kuma yana jera wasu alkawurra a gefen inda take zaune.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.4 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 12Tsakaninmu 14 >>

2 thoughts on “Tsakaninmu 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×