Tana shiga gidanta ta fara kuka mai tsuma zuciya me yasa zasuyi mata wannan munmunar fahimtar, tabbas tasan Hisham yaso Widad amma ba halalin sa bace , ko dan basu san haramci za'a aikata ba ne, Innalillahi Wa'inna ilaihi raji'un.
Munira tana zaune cikin dakinta daga ita sai daguwar rigar baci irin me nanewa a jikin nan taji an banko kofa.
Daddyn tane da wani murtikeken danko a hannunsa fuskar nan tasa kamar ta mayunwacin zaki dake cikin tsantsar fushi da yunwa.
Idonsa a rufe ya fara dukanta ta ko Ina bayan ya rufe kofar da key yasa. . .