Bayan fitar kowa ta dago suka hada ido ta gaisheshi tana sunkuyar dakanta , ya amsa yana dubanta ransa na kinmsa masa irin zallar kyan Widad , zai iya cewa acikin nikabi tafi kyau kamar wata balarabiya, gyaran murya yayi yace” naji ance wasu a mota sun dauke ki , amma Allah ya taimaka kin kubuta , naso zuwa duba lafiyarki amma kiran gaggawa daga mahaifina ya dakatar dani , ina fatan basu taba lafiyarki ba ko?” ta daga masa kai , yace “kuma ina san zan turo iyayyena zuwa gobe ko jibi domin baban mu yayi min Magana akanki , kuma ina ganin mun fahimci juna. . .