Domin kuwa karatu na musaman Umaima ta shiga karantawa Widad akan Shuraim, ta nuna mata kamar yadda yake fada musu ya yi sa'ar mata , to haka ita ma ta godewa Allah ta yi sa'ar miji , domin kuwa akwai dubban mata dake fatan burin samun miji me rabin-rabin irin kulawar da Shuraim yake ba ta, amma basu samu ba, haka kuma ta nuna mata irin matan da suka dinga rubibinsa amma Allah ya zabeta ya mallaka mata shi dan haka ta nutsu ta rike mijinta .
Hajiya Widad kuwa karatun nan ya zauna dam a kwakwalwarta domin a yanzu. . .