Washe gari jaririyace ta tashi kowa a gidan sai kuka take Safna ta toshe kunne tana " wayyo!!! Mammy babinki zata hana mu bacci ".
Fauzan ya shigo yana mutstsika ido "mammy!mammy me ya samu bebinki? yaya Safna ce ta zaune ta ko "?
Iyah ta mike tana cewa "sannuh, wato har kasan a zaune mutum yan biyu"?
Yayi dariya, tace "maza kuje kuyi sallah asubah tayi ".
Haka suka cigaba da zama a gidan Iya tsohuwa har suka kwana shida. Ita kuma bebi kwananta biyar a duniya kenan .
Iya bata nuna ko da wasa tana san jin labarin Aisha da yaranta ba. . .