Mami tace "haka na zama me Yara biyu domin duk da na yaye Amar duk inda yake sai yazo gurina Kuma Bai San wata uwa da wuce ni ba, to haka Shima Safwan Kuma a wannan lokacin ne hankalin Malik ya tashi akan lamarin matar Dan nasa yace indai baza ta iya shayar da yaranta ba gwanda ya rabu da ita , shi Kuma duk da haka yana matukar San matarsa.
Haka na yaye Safwan shekara biyu da kusan rabi sai ga wani cikin , wannan karon tasha abun zubar da ciki Allah ne yayi sai an haifi Safna ita ma tana. . .