A.B BALLAH. ne gaban mahaifiyar sa hajiya mamah, yana fada mata labarin Safna bai boye mata komai ba akan rayuwarsu.
Ta dago ta kalleshi tace " kasan wannan ba abune mai yiyuwa ba . Kana dan babban gida kace zaka auro almajira, kuma almajirar ma mara asali da tushe 'yar mace. Toh tun wuri ka rufe zan chanta".
Shiru yayi hankalinsa ya tashi ya fara ma magiya amma fafur taki sauraransa, ya riko kafafunta yana kuka mai sosa zuchiya, dole ta tsaya tana kalonsa.
Ta sani Abudullahi mutum ne mai hakuri a iya rayuwar da tayi da shi tunda ta haifeshi. . .