A ranar da ya tara mu da yarana a tsakar gida, na gama yanke haso cewa yanzu dai ba makawa sai na bar gidan. Na juya na dubi yaran, nan take na ji tausayinsu ya cika min zuciya. Na zauna a kasa sakwal, ina satar kallon fuskarsa cike da taraddadi. Sai ya ce. “Yau dai na gaji, fada min, su ma ki fada musu, wai mene yake faruwa ne?”
Gabana ya kara faduwa, da alama an zo wurin da ba lallai in iya samun wata mafita ba. Na kalle shi cikin marairaita na ce. “Wallahi ban san me na yi ba, amma don Allah ka yi hakuri.”
Sai na ji ya ce. “Ke yau fa ba ranar bayar da hakuri ba ce.”
Na ce, “Na shiga uku!” a cikin zuciyata.
Da na kara waiwayawa na dubi yaran nan, sai na ji muryar Umma tana kara karakaina a kunnuwana, tamkar yanzu take maganar: “Idan kuwa har kika yi ‘ya’ya da namiji, to yanzu masalahar yaran nan ita ta fi komai muhimmanci a wurinki.” Ban san lokacin da hawaye ya fara zarya a kan kumatuna ba!
Na yi mamakin jin sa yana cewa. “Haba Tawan, ai yau ba ranar kuka ba ce!” Na ga ya sa yatsunsa yana share hawayen da ke fuskata. Na kuwa tsaya cak cikin tsananin mamaki da rashin sanin tabbacin abin yi. Ya kara cewa. “Ki nutsu don Allah, yau so nake kawai ki fada min menene sirrin nasararki a zaman aure.”
Na bude idona sosai na kalle shi a wannan karon. Domin a raina ban fidda ran wataran za a yi min wannan tambayar ba, sai dai kawai ban zata shi din ne zai min ba. Ya ci gaba: “Na sha jin labarin mata masu bin aure, amma ban tava jin irin ki ba har yau! Tare da cewa ina sane da cewa lokuta da dama ina vata miki.”
Tsokokin fuskata ba su yi wata shawara da ni ba, na ji sun fara murmushi. Kafin in bude baki ya riga ni. “Na tabbata wannan ba yinki ba ne, domin wasu halayyar da kika fara nunawa tun kina amarya, ba su yi kama da halayen yara masu karancin shekaru irinki ba.”
Sai na ce masa. “Haka ne.”
Ya kuwa gyara zama “Yauwa, me ya faru ne don Allah?”
Ban wani damuwa da yaran suka kallon mu ba. Na turo daurin dankwalina gaba, na fara. “Lokacin da za a kawo ni gidan nan, kana sane da cewa Mahaifina ya dade a kwance ba lafiya. Don haka bayan an gama kai ni wurin duk wanda ake ganin ya kamata in yi bankwana da shi, sai aka kawo ni wurinsa daga karhe. Savanin yadda ni da sauran ‘yan rakiyata muka zata, bai yi min wata doguwar magana ba. Sai ya sa hannu a karkashin filonsa ya dauko wasu ambulam kanana guda goma sha biyu, ya miko min. Bayan na karva sai ya ce da ni:
“‘Kowane ambulam akwai lamba a bayansa, ki bi su a sannu kamar yadda lambobin suke: A watanki na farko a gidanki, ki bude wasika mai lamba daya ki karanta. Amma kar ki kara bude ta biyu, sai bayan kin shiga wata na biyu. Haka za ki ci gaba, idan kin bi su bisa tsari za ki kai har shekara guda kenan. Wadda da ina da lafiyata ni ya kamata in rika zuwa har gidanki ina yi miki wadannan maganganu, har tsawon shekarar.’
“Na fashe da kuka zuwa wani dan lokaci na daure na tsayar da kukan na kuma yi masa godiya da adudu’ar samun lafiya, sannan suka ja ni, mu ka yi gaba. Dukkan kayan da na zo da su kuwa babu wani abu da na yi wa kyakkyawan adani kamar wannan wasikun.
“Bayan mako guda sai na dauko mai lamba daya, na bude. Sai na ga an rubuta:
‘Yanzu sunanki Amarya, ‘yar gata, kyakkyawa, kuma mai ladabi. Ba za a ga mafiya yawan laifukanki ba. Amma kar ki rude, wannan lokacin zai wuce. Kuma ina fata wucewarsa ba za ta rikita ki ba!’ A daren wannan ranar kuwa ya rasu, ba na mantawa.”
Ya ce. “Allahu Akbar, Allah Ya jikan Alhaji.”
Muka ce. “Amin.” Sannan na ci gaba: “A wata na biyu, makon farko na bude mai lamba biyu. Sai na ga an rubuta:
‘Yanzu kun saba ko? Watakila ma kin lura da ya rage dokinki. Kar ki fasa komai kedai.’
Na kalle shi na ce. “A wannan ranar kuma na lura sam ba ka yi dariya ba, ba ka yi wanka ba, sai da rana da za ka fita!” Sai ya tintsire da dariya.
A wata na uku, da na dauko mai lamba uku, sai nag a:
‘Yanzu an zama jiki ko? Watakila ma kina zargin ya dena wasu abubuwa na kyautatawa. Ki lura da kyau, ke ma ai kin dena da yawa.’
Da na dubi kaina na gan ni busu-busu da daurin kirji, ni kadai sai kunya ta kama ni. A lokacin a kalla na tuna kusan abubuwa biyar da na dena.
A wata na hudu, da na dauko mai lamba hudu na bude, sai na ga an rubuta:
‘Ya jiki? To duk rintsi dai ki zama mai tsafta.’
To ai daga wannan lokacin ne na dena ajiye wannan gwangwanin. Ya ce. “Na tsani gwagwanin yawun nan naki dama wallahi.” Duk muka yi dariya.
A wata na biyar kuwa da na bude ta biyar, babu komai a ciki sai:
‘Ki ba shi hakuri. Wannan mutumin a duniyarki babu wani mai muhimmanci kamar sa!’
Shi ne fa ranar da ba ma maganar nan ka ga katsam na same ka a falo ina ta yi maka kuka. Ya ce. “Ikon Allah! Tabbas na tuna tuna.”
Watarana bayan na gama sharvar kukana, na bude mai lamba shida sai na ga:
‘Yanzu tuni an dena soyayya ko? Kar ki damu, idan kin jure za ta dawo sabuwa.”
Ina gama karantawa na kama kuka, na manta rabon da na ji kalmar soyayya ma ni lokacin.
A wata na bakwai da na bude mai lamba bakwai sai na ga an rubuta:
‘Watakila yanzu in kika ji ko kika ga yadda wasu ma’auratan suke yi, sai ki dauka kamar ke ce ba ki yi sa’ar miji ba ko? To kar ki rudu da wannan, kowane gida da irin tasa matsalar.’
A ranar da na gama karanta wasikar na roke ka, ka bar ni in je gidan Farida. Saboda kaf kawayena babu wadda suka yi zuzzurfar soyayya kafin aurensu kamar ta. Abin mamaki da na je sai na ji tasu matsalar ta ninka tamu!
A wasika ta takwas babu komai sai:
‘Ki yi hakuri, ibada kike!’
Daga nan da na shiga wannan rashin jinyar, ban samu damar bude ta watan tara ba, sai a watan goma bayan na haifi Anwar ma. Da na zo sai na debo biyu, a ta taran an ce. ‘Sannu, Allah Ya ba ki lafiya’ A ta goman kuma aka ce. ‘Kar hidimar da ta shagaltar da ke ga barin ta miji. ’
Sai da na yi waige-waige a cikin dakin nan, ko zan gan shi yana kallona. Sannan na ci gaba da kuka ina yi masa addu’a.
A watan sha daya, da na bude sai na an rubuta:
‘Duk abin da yake so yanzu kin sani, haka wanda ba ya so. Idan ba ki kyautata zamanku ba, ke kika so!’
Tun daga wannan ranar ne na ware littafi guda, wanda a cikinsa nake rubuta dukkan abubuwan da na fahimci kana so, a kowane fannin mu’amularka. A vangare guda kuma wadanda duk na san ba ka so.
Ta sha biyun ce…” Dariya ta kwace min a wannan gavar. Ya ce. “Yaya dai?” Na ce. “Ta sha biyun ce na yi yin duniya in daure sai watan sha biyun ya kama, amma na kasa. A ranar ashirin da daya na watan sha dayan na kara bude ta. Sai na ga:
‘Ki sani, mamaci yana iya samun labarin ayyukan iyalansa, bayan rasuwarsa. Kuma idan da wani aiki da za ki yi don ki faranta min, bai kai ya biyyyar aure ba!’
Sannan na kura masa idanu, na ce. “To daga wannan ranar sai na mayar da biyayyarka tamkar sauran rukunan ibadar da ba ni da zavi sai na lazumce su. Kamar yadda don na zame na fadi a wurin alwala, ko na gurde na ci da ka yayin ruku’u, ba zai sa in dena sallah ba. Haka kuma dukkan wani laifi da za ka iya yi min, ba zai sa in bar biyayya gare k aba!”
Da ya dago kai, sai na ga ashe idanunsa cike suke da hawaye. Sai bayan wani dan lokaci ya goge, sannan ya ce min:
“Ke bayan ma Uwargida na kara miki da Uwardaki!”
Nice one 👍
Masha Allah
Masha Allah
Dakyau. Labari ya ƙayatar matuƙa. Allah ya ƙara hazaƙa.
#haimanraees
Ma shaa Allah
Allah ka bamu mata nagari muma kasa muzama nagari a wajensu amin ya Allah.
Jinjina ga Dawakin hikima. 👍👍
Ma sha Allha, very nice Allah ya Kara basira da juriya da jajircewa
Mashaa Allah, labarin ya kayatar! Allah Ya kara basira, Dawaki.