Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Tsantsar So by Khadeejarth Sabi'u Yahyah

“Ita ce fa wannan Budurwar jikar Mai martaba Sarkin mu da tazo daga ƙasar waje kwanaki biyu da suka wuce.”

Ya yi maganar wa abokin nasa da ya yi masa tambayar gaba ɗayansu kowanne yana kuma hangame baki wurin kallon kyakkyawar fuskarta da kuma haɗaɗɗiyar surar da Ubangiji ya azurtata da shi.

Outfit dake jikinta normally Jean’s ne sai kuma Riga Top white ta ɗaure rigar sanyi a ƙugunta ƙafafunta sanye da Boots irin na fita training na safe ga dukkan alamu daga training take. A hankali take lumshe kyawawan idanunta yayin da take ƙara buɗe su. Hannu takai tana gyara gashin kanta da ya leƙo tana ci gaba da faɗi cikin daddaɗar Muryarta mai daɗin saurare.

“Tabbas ba son gaskiya yake miki ba shawara anan ita ce ki rabu da shi Allah ya haɗa kowa da rabon sa.”

Ta ƙari sa maganar sannan ta gyara Bicycle nata tana faɗin.

“Oh ya Teema zo mu wuce.”

“‘Yar uwa na gode sosai da shawara kuma in Allah ya yarda na rabu da shi har abada, dama tun tuni nake zargin ba tsakani da Allah yake ƙaunata ba.”

Kallon Yarinyar tayi ta ce.

“Ina miki fatan haɗuwa da wanda ya fisa kuma mai ƙaunar ki da gaskiya domin akasarin mazan yanzu ba tsakani da Allah suke tare da mace ba sai dan cika wasu burika nasu, sai dai matan basa ganewa domin ruɗin Duniya rufe musu ido yake yi. Nayi farin ciki da ke kika fahimci hakan.”

“Wannan gaskiya kika faɗa ‘yar uwa domin kaso 80 na samarin yanzu ba tsakani da Allah suke tare da Budurwa ba sai dan cika wani buri nasu cikin su kuwa harda wannan tur da Irin wannan Rayuwar.”

Tayi maganar tana nuni da saurayin nata cike da tsanarsa domin yau ya nuna ma ta Asalin kalansa.

“To tun da an gama komai kowa sai ya watse ko. Su Labib ɗan gayu harda Kai ne a hangame baki to a gyara dai kafin ƙuda ya shige.”

Budurwar da ta kira da Teema tayi maganar tana kallon gaba ɗaya mutanen wurin da suka tattaru ana kallon abin da ke faruwa. Sannan ta hau Bicycle ɗin kana ta fara tafiya da su suka bar wurin.

“Hhhh Lallai ma wannan Teema ko yaushe bakin ta ya buɗe da zata dubeka ta gaya maka magana, amma fa kaima ka bani Dariya Kawai daga ganin wannan kyakyawar Baturiyar Budurwar da tazo Garin nan sai ka nema ka kasa controlling kanka kodai…”

Katsesa ya yi da faɗin.

“Ko dai mene karma ka fara wannan tunanin domin kafi kowa sanin Hazel ita ce kaɗai a zuciyar Labib ko dai ka manta ne?.”

Ɓoye dariya Abokin nasa ya yi suna ci gaba da tafiya ya ce.

“A’a kam ban manta ba Aikuwa ga ta can ma mutuniyar taka sai ka ƙari sa kuyi irin gaisuwar taku da kuka saba Kullum.”

Ya yi maganar yana masa nuni da ita da take tsaye daga can cikin jama’a ‘yan kallo, ganin kowa ya watse ne, yasa ta gyara Book’s ɗin dake a hannunta ta rungume su a chest nata sannan ta fara tafiya a hankali cikin nutsuwa kamar yadda ta saba tana kare fuskarta daga hasken Rana da ta fara ɓullo wa kaɗan.

Da sauri ya ƙari sa saitin ta kamar yadda ya saba a kullum sannan ya ciro handkerchief daga trouser pocket nasa kana ya fara tafiya yana goge gumi idanunsa na kallon ƙasa.

Yau ma kamar kullum karo da taji tayi da mutum ne yasa cikin sauri ta ɗa go kanta domin ganin ko wanene.

“I’m so sorry Bro sauri nake yi na tafi school domin nayi late sosai shiyasa nayi karo da kai, ba tare da na sani ba, amma ina mai baka haƙuri.”

Tayi maganar silently tana sauke idanunta ƙasa daga kallon sa domin ta fara gajiya da karo da suke yi a Kullum kuma ita ke basa haƙuri har hakan ya sa ta fara insulting wani abu kamar dai…

“Oh ni Labibu naga alama fa kamar ba son ganin na biyo hanyar nan kike ba Kullum ke ke nan cikin tafiya idanun ki na kallon sama wasu lokutan kuma ƙasa sannan duk ƙoƙarin guje miki kar muyi Collision da nake yi a banza domin Kullum sai mun buga karo an ya kuwa?…”

Ya yi Maganar yana ɗan Murmushi tare da nuna ta da yatsa.

“I’m so sorry ba wai da wata manufa ba ce kaji late nayi Shiyasa nake sauri har mukayi karo amma ina mai baka haƙuri.”

“Tohm shikenan babu damuwa na haƙura amma da sharaɗi.”

Cikin sauri ta katse sa da tambayar.

“Menene sharaɗin Bro Ina jin ka Please?.”

“Okay ba yanzu ba, idan gobe kika kuma karo dani shi ne zan faɗa sharaɗin. Kiyi kokari kar gobe mu kuma yin karo a hanya.”

“To na gode.”

Ta faɗa tana raɓa wa ta gefansa sannan ta wuce.

*****

Duk irin kira da ya yi ma layin ba’a ɗauka kuma tana ringing bai san dalilin ba yaji ya shiga damuwa na rashin amsa Call nasa da Arissa barayi ba. Gyara training Bicycle nasa ya yi sannan ya ɗauki hanya domin zuwa gida.

****

“Am Teema kike ko?.”

“E Anty haka sunan nawa yake Teema sai dai an fi sanina da kuma kirana da Teema Silent.”

“Okay.”

Ta furta tana shan kwanar hanyar da zata kaita har gidan mai Martaba Sarki. Sannan ta ci gaba faɗin.

“Am yanayin Garin naku ya burgeni sosai, ina ga zuwa da yamma, zaki rakani domin yawatawa domin na zagaye garin na bawa ido na haƙƙinsa.”

Ɓoye dariya Teema tayi ba tare da ta ce komai ba.

“Kamar dariya kikeyi ko?.”

“E, mana Anty ai Dariya maganar ki ta bani, keda kikazo daga ƙasar America shi ne kike cewa wannan Garin namu ya burgeki, shi ne abin ya bani Dariya.”

“Allah Sarki. Ai America daban haka ma nan ma daban ko wanne da irin shauƙi da nakejin kaina idan na kasance a ciki, kinga kamar nan yana tunamin da Yarinta na ne can kuma a can na tashi na girma nasan kaina.”

“Anty ke nan ai duk da haka America ta daban ce kowa dake nan burinsa ke nan zuwa America ciki kuwa har dani. Wai ma Anty menene Sunan ki ne ma nifa ban sani ba?.”

“Okay kina da Burin zuwa America ke nan. Tohm Ubangiji ya cika miki Burin na ki.”

“Ameen ya Allah.”

Teema ta amsa tana dariya cike da farin ciki.

“To Anty baki faɗa min Sunan ba nima ban sani ba kuma ance tun shekaran jiya kike a Garin nan amma ban samu na haɗu dake ba sai yau da yake bana fitowa ne kwana biyu saboda jikin Mamana ya tsananta shiyasa ba kullum nake fitowa gidan Sarki domin aiki ba. Kwatsam kuma yau da Asuba da naje shi ne na haɗu dake har Hajiya Bilkisu Uwar gidan mai Martaba Sarki take cewa na rakoki training na safe da kuke zuwa irin naku na Turawa.”

Murmushi tayi kaɗan domin maganar Yarinyar ya bata dariya sai dai da yake ita ɗin ma’abociya wurin yin Murmushi ne yasa tayi kaɗan tana faɗin.

“Teema ko lallai kina da taɗi. Har na fara insulting kiran ki da Teema Silent da kikace ana yi.”

“Hhh Anty ke nan Allah bani da surutu ko hayaniya Kawai kece da jinin mu ya haɗu shiyasa ma nake miki surutun.”

Zata yi magana bayan shigarsu Babban gate na Gidan daidai lokacin wasu tsalatsalan motoci na alfarma guda uku suka shiga gidan daidai parking lot suka yi parking sannan mutanen ciki suka fara fitowa bayan wasu mintoci da yin parking ɗin.

“Oh Allah kamar a mafarki Mommy Asfiya Uncle Junayd ga kuma Hamrarh da Amrarh wayyo nayi farin ciki sosai ashe kuma kuna hanya?.”

Tayi maganar tana ƙari sa wurin sannan tayi hugging nasu ɗaya bayan ɗaya fuskokin kowannen su ɗauke da fara’a Budurwar ɗaya cikin Biyu da ta kira da Hamrarh da Amrarh ta amsa ma ta da faɗin.

“Sameera Adila Dina wow yaushe rabo gaskiya nayi missing naki sosai sosai fa.”

Murmushi tayi tana kamo hannunta ta ce.

“Ai Hamrarh nima nayi kewarki sosai sisterna an daɗe ba’a haɗu ba. Ina fatan kun ƙari so lafiya Uncle Judge Barka da Hanya.”

Ta ƙarishe maganar tana komawa ga Uncle ɗin nata tana kuma hugging nasa fuskarta ɗauke da Murmushi. Yayin da Teema tayi tsuru a gefe tana kallon su cike da sha’awa sosai suka burgeta.

” ‘Yan Gayu kunji daɗin ku.”

Ta faɗa ƙasa ƙasa tana Dariya.

“Nayi fushi ma tunda an manta dani.”

“Oh sorry sorry Mommyna ta kaina ina zan manta dake Mahaifiyata guda ina fatan kun ƙariso lafiya mu shiga daga ciki Please.”

Tayi maganar tana Karisa wa wurin Amrarh sannan ta riƙe ma ta keken da take zaune akai Irin na guragu waɗanda basa tafiya. Suna gaisawa da Amrarh ɗin da yake Bata da son hayaniya shiyasa bata ce komai ba, lokacin da suke gaisawa. Sannan suka nufa cikin katafaren gidan mai Martaba Sarki Muhammad Raees.
Miss Asfiya ta ce.

“Aina ɗauka ‘yan shekarun da muka yi Bama haɗuwa har kin Manta dani ne da kuwa kin ga fushina a yau.”

Saita zaman Bicycle ɗin tayi a cikin katafaren parking lot na gani na faɗa dake cikin gidan gefan wurin da take tana jin tana bata amsa.

“Sameera Adila Dina…”

Ta maimaita Sunan sosai ya yi ma ta daɗi kuma taji sunan ya dace da ita musamman da ta lura tana da kirki.

*****

“Althaf yi sauri ka tafi anjima zamu haɗu ga Yayana nan zuwa, Bye.”

Sauri sauri ta gyara tsayuwar da nutsuwar ta ba tare da ta amsa sallamar da ya yi ma ta ba. Sannan ta nufe sa.

“Lah Yayana har ka dawo ke nan daga training ɗin?.”

A nazarce ya kalleta ya shafa kanta tare da murmushi ya ce.

“Na dawo Cutie daga ina kike haka da safiyar nan?.”

Sai da gaban ta ya faɗi jin tambayar da ya yi ma ta. A tunaninta ya hangota tare da Althaf ne. Da kyar ta daure ta ce.

“Ah Yayana daga Tahfiz mana ko ka manta yau Friday ne Akwai Tahfiz na Safe.”

“Okay. Na tuna ina fatan kun yi karatu mai yawa kuma kin fahimci komai na karatun?.”

“E, Yayana idan ma naji na manta wani wuri ai ina da kai zata koyamin na sani.”

Ta faɗa tana Dariya da ya bayyana Dimples nata. Kyakykywa ce sosai Yarinyar sannan ba zata haura shekaru Goma sha shida zuwa sha bakwai ba.

“Good Girl baki da matsala yanzu mu shiga daga cikin gida ki bani Labarin abin da ya faru a Tahfiz ɗin.”

“Tohm Yayana baka da matsala.”

Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya kaɗan tare da furzar da iska na farin cikin.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×