Skip to content

Tsilla-Tsillar Tsuntsaye | Fasaha Haimaniyya 1

4
(1)

<< Previous

Tsilla-tsilla Ta Tsuntsaye

Ga Gantalin Gaulaye

*****

Da fari zan sa Rabbu wanda Shi yai tsuntsaye

Shi yai Bishiya yai mata rassa dogaye

Kuma yai Akuya a gefe can ga kuraye

Ni roƙona ka raba mu da sharrin mugaye

*****

Ya Allaah!

*****

Tsira da aminci gun manzo mai sunaye

Da Sahabbansa haɗa duka har fa da alaye

Da masu sonsa cikin maza har mataye

Domin darajarsa Ilahu raba mu da sharrin ɓeraye

*****

Ya Allaah!

*****

Ku sani jama’a akwai wasu gungun kuraye

Sun ci sun ƙoshi jikinsu kamar fa na giwaye

Gasu can fa him kuma basa shakkar kowaye

Ya Rabbana tsare mu da sharrin zomaye

*****

 Ya Allaah!

*****

Sun ɗau talakawa sai ka ce wasu wawaye

Sun tai gaba bayan su fa basa waiwaye

Ga alama dai imanin su ya tafi ƙaraye

Ya Sarkin mu ka raba mu da sharrin kuraye

*****

‘Yan Ƙota!

*****

Dukiyar jama’a ita suka ciccinye

Ba ruwansu da kowa yara ko ko mataye

Sun ɗauke mu a yaushe kamar wasu banzaye

Sun zamo kaska jinin talakka a shashshanye

*****

‘Yan Ƙota!

*****

Sun tara kuɗi sun auro mata jajaye

Bayan haƙƙin mu shi suka tat-tauye

Matsabbai sun taru kuma gefe can ga bokaye

Sun bar talaka a gefe yana hawaye

*****

‘Yan Ƙota!

*****

Su Burinsu muƙaminnan fa suyo haye

Mazalunta masu son rigima kar ta wanye

Talakka a yau wai shi za ai wa kiranye

Ya Rabbana tsare mu da sharrin guntaye

****

Ya Allaah!

*****

Matasanmu mu taru mu bar Shaye-shaye

Komai nisan dare ku sani fa gari ai zai waye

Domin yanzu kan mage ya fa waye

Ku fito mu bi gaskiya ba garwaye

*****

Don Allaah!

*****

Su a tunaninsu du kaɗai ne gwanaye

Gani fa suke wai ba mu da wayau gaulaye

Wankan nan fa ya fi kama da jirwaye

Duk wanda ya zo da zamba mu taru mu tunkuye

*****

Ɗan ƙota!

*****

Ya Sarkinmu gamu mun ɗaga hannaye

Zuciyoyinmu dukka muna hawaye

Maƙiyanmu dukka Ilahu a tunfaye

Da sun nufo mu da sharri Rabbana Ka kiyaye mu

*****

Ya Allaah!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×